Shiru ta yi tana juya maganar ta shi, musamman walimar saukar Blessing, kenan har ta yi sauka, amma ita da aka haifa cikin addini musulunci, ta taso cikin musuluncin ba ta sauke ba, Lallai fa akwai aiki a gabanta. Blessing da gaske take yi, so take a komai ta yi mata fintinkau.
Akwai bukatar ta kora daure belt din ta, zama bai ganta ba.
“Hope za ki je?”
Ya katse mata tunaninta.
Cikin basarwa ta ce “Abin da nake tunani kenan, ina son zuwa kam, amma yaushe ne ake yi?”
“Don Allah ba ki jin haushi Fatima?”
“Haushin me?” ta yi saurin tambaya.
“Ba a bakinki ya kamata a ji duk wannan ba. Yana matukar bata min rai ace ku san komai nawa ba ki sani ba. Haka ya kamata ki zama?”
“To ba ka so in sani ba ai.”
Ta ba shi amsa.
“Ke ce dai ba ki so ki sani ba, saboda ko na sanyaki a ciki fita kike yi.”
Murmushi ta yi sannan ta ce “Yanzu dai yaushe ake yi?”
“Nan da sati uku in Allah Ya kai mu.”
“To Allah Ya kai mu”
Ta fada hade da kwashe kayan da ya gama yin breakfast.
Lokacin da ta dawo falon yana bedroom. Shi ya sa ita ma ta wuce bedroom din.
Kwance yake daga shi sai boxer yana taba wayar shi.
“I want you!” ya fada ba tare da ya kalle ta ba.
“Ina jiran baccin Beauty ya yi karfi ne.”
Sai a lokacin ya Kalle ta, goye take da Beautyn tana zagaya dakin da ita.
Abin da ya kashe kakar Blessing kenan goyo, ita kam ta tsani goyo, ba goyo ba duk dawainiya da yaro ma ita ba ta so. Idan Ihsan za ta wuni ba a wurinta ba, hakan baya damunta.
Ita ce dai ta ce a kawo su Hana, amma 80% na dawainiyar yaran shi ke yi.
Sai dai ba duka ba zagi, sannan ba ta jin kyashin kashe musu kudi ko nawa ne.
Ita dai jagalniyar ce Allah Ya hana ta.
Kodayake kamar dabi’arsu ce haka, yana lura da ma fi akasarin ƴan’uwanta suna da masu kular musu da yara.
Fatima ce ta katse mishi tunanin lokacin da ta zauna a gefen gadon bayan ta kwantar da Beauty a falo.
Sosai ya yi kewarta, ji yake kamar ya shekara bassa tare, da kanshi ya janyo ta zuwa jikinsa, sannan ya shiga sarrafata yadda yake bukata.
Fatima ma ta yi mishi fiye da yadda ya yi tunani, sai da ta fahimci bacci ya dauke shi, sannan ta sulale kitchen don tanadar musu abincin rana.
Misalin karfe biyar na yamma, zaune take a gefen gadon, cikin kwatsetsen lace baki mai adon Jara fulawa, din riga da zanene amma sosai suka karbeta, sarka take sanya, a lokacin Mustapha ya shigo rike da Beauty wacce aka sanyawa doguwar farar ƴar kanti mai laushi, sai jar socks wacce aka ci bakinta da kwalliyar farin baki lace mai kyau.
“Ta ƙi tsayawa in sanya mata takalmin.” ya yi maganar hade da aje Beautyn gefen Fatima.
Sarkar ya amsa ya karasa sanya mata sannan ya ce “Wlh ba mai kallon ki ya ce kina da yara biyar, wani zai dauka Beauty ce ta farinki. Auran wuri fa ya yi.” ya karasa maganar idanunsa zube a kanta.
Murmushi ta yi lokaci daya kuma tana sanyawa Beauty baƙin cover shoe mai kyau.
Sai da ta kare sanya mata takalmi sannan ta ce” Kai kuma babu mai ganinka ya ce wannan Mustaphan ne, mai rike yar bulala da jallabiya, da hularsa taɓa ni ka ji hadisi.”
Hararar wasa yake aika mata, yayin da sautin dariyarta ke fita a hankali.” Kalle ka, cikin danyar farar shadda, ka yi fresh abun ka, jiki a mulmule ga ka nan dai sak bugun Abuja. “
Tare suka yi dariya, shi ma cikin tsokana ya ce” Wa zai Kalle ki, ya ce ke ce wannan Fatiman da ke hana kowa sakat, mai kiriniya da rashin jin nan. Wai zai ce ke me zuwa islamiyar nan idan kin ga dama ko ba ki ga dama, wacce kwalliyar nan ba ta dama ba, kullum tana zama da zane a kirji”
Dire maganar tashi ta yi daidai da sakin dariyar Fatima cikin nishadi, lokaci daya kuma ta saba Beauty ta fice daga dakin tana dariya.
Shi ma ya bi yo bayan ta cikin dariyar alamun dai suna cikin nishadi.
Shi ya karbi Beauty a lokacin da take warware babban farin mayafi ta dora a bisa kayataccen daurin dankwalinta.
Tana sanya farin flat shoe din ta ne ta ce “Daurin kirjin duniya ne Ya Mustapha, akwai dadi sosai”
“Har da cire uniform daga kofa ma.”
Cikin dariya ta ce “Yaushe ka san wannan?”
“Watarana na gani kin yi, ganin ba ki ganni ba, sai na koma baya”
“Ka ce ka ga haram.” ta fada cikin gwalo ido.
Har yanzu da dariya a fuskarshi ya ce “halak na gani.”
Ta dauki ledar tsarabar da Mustaphan ya kawo wa Mama ta fice daga falon tana dariya.
Ita ta rufe ko ina na gidan, sannan suka jera shi yana rike da Beauty ita kuma tana rike ledar.
“Wato Fatima Allah Ya sani kin yi rashin ji, na san kowa bai yi tsammanin nutsuwarki haka ba.”
Cikin dariya ta ce “Wasu ma kallon mahaukaciya suke min fa. Kuma wlh tsaf da hankalina, wani lokaci ma da sane na nake yi”
“Kin tuna lokacin da kika budewa Ya Bashir kejin tantabarunshi suka gudu?”
Fatima ta tuntsure da dariya sosai, sai da Mustapha ya ce mata “Ke ba fa a gida muke ba.”
Ta rage saurin dariyar tata tare da fadin “Au! Na manta fa. Wlh Ya Mustapha ko ni kadai na tuna ina yin dariya. Kuma fa ni abun arziki na mishi, na dauka idan za a basu abu budewa ake, ashe wai watsa musu ake yi.” cikin dariya ta karasa maganar.
Mustapha ma cikin dariya ya ce “Cewa yake mahaukaciya banza mahaukaciyar wofi, sai kin biya kudinsu,”
Cikin dariya Fatima ta dora da “Haukacewa ya yi a gidan fa ranar, har kasan gadon Mama ta janyo ni, yay ta nafka, har gidan Aunty Hauwa fa. Aunty kam tai ta dura mishi zagi, tana tantabarun banza tantabarun wofi.”
Duk suka kuma fashewa da dariya a daidai lokacin ne suka kara so gidan Mama.
Da sallama suka shiga, Aunty Aysha ce da Aunty Ayyo tsaye a tsakar gidan, da alama sun gama abin da ya kawo su tafiya zasu yi.
Aunty Aysha ta buga shewa a maimakon amsa sallamar tare da rangada guda daidai saitin fuskar Mustapha ta dora da “Allah dai Ya bar kauna miji ga Fatima Angon Blessing, ko kudi kuna buga naku. Sandamu gida Abuja garin shan iska, Allah Ya kara karfin arziki.”
Ta juya saitin Fatima ta kuma rangada wata doguwar gudar tana fadin “Uwargida sarautar mata, kwari mai kwara miya, duk yadda kika kwara haka za a sha, kowa ya zo ke ya taras, ki ja zarenki yadda kike so, ke ce gaba ko sun ƙiya bare ma sun yarda. Farar mace lantarkin gida.”
Mama da ke daki ta fito a hanzarce, don guda da kirarin ya ratsa ta.
Take kuwa ta wangale baki, farin ciki taf cikin ta.
Ko wace uwa babban burinta shi ne ganin yarta zaune ƙalau a gidan mijinta. Yau dai da ta ga Mustapha jere da Fatima kamar wasu sabon aure, ji ta yi kamar ta fita ta rungumesu.
Bangaren Mustapha kuwa sai ɓashau-ɓashau yake yi da baki, haka bai san lokacin da ya zaro kudi ya mikawa Aunty Aishar ba tare da ya san ko nawa ba ne.
Fatima ma dariya kawai take tana fadin “Bar ni haka ta gidana, bar ni haka kar kisa dadi ya kar ni”
Cikin dariya Aunty Aisha ta amshe Beauty da ke hannun Mustapha tare fadin “Haba ban yaba yarinyata kun san kuwa ta ta fi cancanta. To me ɗa baƙi ma ya ce mai ɗanɗanso bare ni mai ƴa fara, taralli ta gaban gado madubi sha kallo man gyada ba ka bacci.”
Tsakar gidan ya kuma rudewa da hayaniya game da shewa, sai da Mama ta kora su Aunty Ayyo sannan gidan ya yi shiru.
Mama ta bi bayan Mustapha da ya shige daki, fuskarsa tab nishadi tana fadin” Yarinya kamar marokiya, ni ban san ma lokacin da Aisha ta zama haka ba.”
A badini ita kanta Maman wani nishadi take yi, ƴaƴa Rahma ne, wanda bai samu ba Allah Ya ba shi.
A mutumce suka gaisa da Mustapha hade da yi mishi sannu da zuwa.
Sannan ta shiga tambayar su Hana, yana amsa mata da duk suna lafiya. Sai da suka taba yar hira sannan ya wuce gidan Aunty Hauwa inda ya bar Fatima a gidan.
Bayan fitar sa ne Mama ta juyo kan Fatima tare cewa “Allah mai iko. Wato duk lokacin da na ga Mustapha sai in yi ta tuna baya, idan an ce zai zama haka, mutum sai ya karyata, amma kalli yadda ya zama, shi ya sa mutum ba abun wulakantawa ba ne.”
Murmushi Fatima ta yi ba tare da ta ce komai ba.
Mama ta ce gaba da fitar da tsarabar da Mustaphan ya kawo mata, zannuwa ne masu kyau guda biyu, sabulai, omo, man shafawa, takalma kafa biyu da hijabs guda biyu da suka dace da zannuwan.
“Na gode Allah Ya biya, duk a cikin mazajenku Mustapha ne kawai ke min zane ba sai sallah ba. Ko haihuwarsa na yi ai sai haka. Allah Ya kara arziki.”
“Amin” Fatima ta amsa.
Hira suka yi sosai a nan Maman ke fada mata cewa, ta fadawa Jamil ya baro Indian nan ta dawo gida, kuma ya, taho da yarinyarshi.
A nan ta yi magariba, sannan ta shiga gidan Aunty Hauwa, a can ta samu su Hassan, kullum ta Kalle su, sai ta ga kamar ba na ta ba, sun yi girma ga mi da wayau, a can ta ci abincin dare sannan ta wuce gidan Ya Bashir wajen Aunty Billy, sai da ta yi sallahr isha’i sannan ta dawo gidan Mama don Mustapha ya kira yana jiranta.
Wannan karon kam Fatima soyayya suka ci sosai ita da Mustapha kamar sabbin aure, shi da ya zo da niyyar kwana uku sai ga shi yana niyyar yin sati, abin da ya damu Blessing a can kishi ya motsa, ta shiga marairaicewa wai sun yi kewarshi.
Zamanshi a gidan sai kusanci ya kuma karuwa, wani lokacin sai ya ji kamar dai har lokacin ita kadai ce matarshi ba wata. Ita din ma haka take ji.
Ranar Asabar da misalin karfe takwas na dare, Fatima kwance a kan gado a kakarinta na sanya Beauty bacci, wayar Mustapha a gefen ta, baki ya yi a waje, shi ne ya je wurin su.
Daidai tana zare nono daga bakin Beauty wayar ta yi kara alamun shigowar sako.
Ta zubawa sakon ido, yayin da wata zuciyar ke fada mata ta karanta wata kuma na hana ta.
Kafafunta ta ziro kasa daga kan gadon, har ta yunkura za ta tashi, sai kuma ta fasa hade da dakko wayar Mustapha, sliding sama ta yi, hade da karanta sakon wanda ya fito daga Blessing cikin harshen turanci fada mishi take yi, wai ba haka suka yi da shi ba, ya ce kwana biyu kawai zai yi, amma har wajen kwana goma bai dawo ba, kullum sai ya ce mata ga shi nan amma shiru, yanzu har baya son daukar wayarta, ya wuce gobe bai dawo ba za ta biyo shi.
Ta zubawa sakon ido, yayin da wani murmushi ya kufce mata, sai kuma ta ce “Abu na masu Maza, wai karuwa ta ga matar aure da ciki, aiko zan ba ki mamaki, sai na nuna miki iyakarki wlh, ba zai dawo goben ba.”
Jin takunshi, saurin mayar da wayar ta yi inda take, lokaci daya kuma ta koma inda ta tashi ta kwanta, tamkar dai irin unexpected baccin nan ya dauke ta.
Ko sallamar shi ba ta amsa ba, ta wutsiyar ido take kallon reaction din fuskarshi a lokacin da ya dauki wayar, sosai kuzarinshi ya ragu, alamun sakon ya taba shi.
Gefen gadon ya zauna, cikin kwarewa yake sarrafa wayar da alama reply din sakon yake yi.
Aje wayar yi inda take bayan ya tura sakon sannan ya mike zuwa toilet.
Sai da Fatima ta ji saukar ruwa alamun ya fara wanka sannan ta kuma janyo ta kuma yin sliding zuwa sama.
Sakon da ya tura ya bayyana, shaida mata yake ta yi hak’uri gobe kam sha Allah ba zai karya mata alkawari ba, tana cikin karanta sakon, na Blessing ma ya shigo. Inda take rokonshi da ya cika alkawarinshi.
Wani murmushin Fatima ta yi sannan ta aje wayar inda take, ita ma ta koma yadda take.
Yau kam duk yadda ya so ya samu Fatiman sai hakan ya gagara, don ce mishi ta yi kanta ke ciwo, dole ya hakura.
Sosai wani kishi ne ke cinta, maza sai a hankali, Kalle shi kamar ba shi ne ya gama fada ma wata yana zuwa gobe ba, shi ne zai wani zo ya dame ta.
Duk lokacin da ta so danne irin wannan sai ta ji ta kasa dannewar.
Rai ba dadi ta yi bacci, tun da asuba ta narke mishi a kan ba ta da lafiya, da kanta ta kakalo amai, a lokacin da ya dawo sallahr asuba, sai da ta tabbatar ta kidima shi har ba maganar komawa Abuja a wurin shi. Ba ma ta tafiyar yake yi ba.
Da kanshi ya kira mata Emma mai chemist inda ya shaida Malaria ce da typhoid.
Sam Fatima ba ta nuna akwai sauki duk kuwa da jikinta ba zafi, nono ma shi ke ba Beauty.
Dole ya yi cancel din tafiya a ranar don ya san ma idan ya ce zai tafi Mama ce farkon wacce za ta fara kawo matsala, dole ya kashe wayar sa, saboda yadda Blessing ke ta kira don jin ko ya taho.
Fatima har zuwa dare jiki ba sauki wai ciwon arne, haka suka wayi gari ma ba sauki, abin da ya kara kidima Mustapha a kan lallai su tafi asibiti tun da Monday ce.