Skip to content
Part 53 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Umaima kam ita ta matsa dole sai Fatima ta je Abuja, duk yadda ba ta son zuwan, dole ta amince.

Shi ya sa Umaima ta karbi kudi wurin Mustapha ta ce zasu yi dinke-dinke, jiki na rawa kuwa ya turo musu 50k.

Umaima da ke kwance a kan katifa ta mike zaune tana fadin “Wowww! 50k!”

Fatima ta dakata da kima kan da take wa Beauty ta ce “Har ya turo?”

Umaima ta juya mata fuskar wayar tana fadin “Wato na fahimci namiji idan ana dan yi mishi yanga ya fi rawar jiki”

Dariya Fatima ta yi sannan ta ce “Wani. Ke maza fa kala-kala, kar ki ga yadda nake zaune da nawa ki ce za ki gwada irin zaman da na ki mijin. Wlh wani namijin kika tsaya yi mishi shan kamshi share ki zai yi”

Umaima ma ta yi dariya lokacin kuma aka daga wayar da take kira. Daga jin muryar Fatima ta gane Ammi ce (Haka Umaiman ke kiran mahaifiyarta.)

Tana jin Umaima na fadawa Ammin lace na mutumci suke so, da kuma kayan gyaran jiki

Cike da mamaki Ammi ta ce “Me za ayi dasu?”

“Momyn Beauty ce za ta yi kwalliyar walimar tarewa sabon gidansu a Abuja. Kuma Ammi ita din kamar amarya ce, ba ta taba zuwa ba, so muke ta fito ba karya”

Ammi ta yi dariyar manya kafin ta ce “Yaushe ake bukata?”

Umaima ta amsa ta “Ranar Laraba za mu zo, mu kwana a nan, Alhamis sai mu wuce Abujar.”

“Allah Ya kai mu.” cewa Ammi muryarta da alamun dariya.

Bayan ta yanke kiran hannayenta du biyun ta jefa gaba, kafin ta dan dawo dasu baya ta kankamesu a jikinta, alamun celebration.

Wayar Fatima ce ta yi haske, alamun sako ya shigo, hakan ne ya sa ta dakata da dariyar da take yi, ta bude sakon da sauri. Musamman da ta ga No Jamil.

“Ga ni a wajen gidan ku.”

Ta kalli Umaima kafin ta ce Ya Jamil ne ya zo.

Umaima ta tamke fuska kafin ta ce “To ni kuma ina ruwana”

Fatima ta aika mata da harara tana fadin “Ban son fa abin da kike min, wai ke abu bai wucewa a wajenki ne?”

Umaima ma hararar ta aika mata kafin ta ce “Ba Za ki gane ba, ko tuna yadda nai ta bin shi a cikin asibitin nan na yi sai in ji wani kududu ya taso min, sai da ya gama round fa, da wasu guntayen meeting, duk ina jira, ya koma office ya bar ni a waje Momyn Ziyad ga yunwa, ga gajiya, sai da na gaji da jira na shiga, nan ma banza ya yi da ni ya hade min fuska, na yi mishi bayanin abin da ya kawo ni, wlh kamar ina magana da gunki, haka na taho ina kuka. Sosai raina ya baci” ta karashe maganar kamar za ta yi kuka.

Fatima ta kunshe dariyarta tana cewa “Ki yi hak’uri bai san ke ce Umaima ba”

“Ko bai sanni ba, ya, kamata ya min haka ne, duk inda za ka hadu da wani ai ta kamata ka girmama shi, ba ka san waye shi ba.”

“Haka ne masoyiyata. Yanzu dai yi hak’uri, mu je ki gaishe shi”

Umaima ta dago fuska kirtif, tana aikawa Fatima harara kamar idon ta zai fado.

Fatima da ke ta dariya ta fice daga dakin tana sanya hijabin da ke hannunta.

Ta gaishe shi cike da dokin ganinshi, kafin ta ce “Ka cika alkawari Ya Jamil”

Ya yi dan murmushi hade da fitowa daga cikin motar yana fadin “Tun jiya ina nan ai”

Zaro ido ta yi “Amma shi ne sai yau?”

“Ban yi kokari ba?”

“Ka yi” ta ba shi amsa da dan murmushinta.

“Ina Maamah?”

“Tana gida” ya amsata yana zaro wayarshi da ke cikin aljihu tana vibration alamun kira.

Sai da ya gama amsa kiran sannan ya ce “I’m going. Ina sauri, da ma na zo mu gaisa ne”

“Aiko na gode. Amma Ya Jamil ka yi mana laifi fa.”

Ya dan daga girarshi du biyun zuwa sama kafin ya ce “na me?”

“Kawata ka ɓatawa rai”

Cike da mamaki ya ce “Wacece ita? “

“Umaima.” ta amsa shi.

Ya dan yi shiru kafin “Did I know her?”

“Ya Jamil! Kana fa yawon ganin hoton ita da Beauty a status dina, wani lokaci kuma a tare da ni, kuma ko ranar da ka fara zuwa ba ta zo ta gaishe ka ba.”

Ya dan tabe ba ki sannan ya ce “Me na yi mata to?”

Fatima ta yi murmushi tare da cewa “Almost 2wks fa, tun zuwanka na farko, wai ta je a kan maganar project din ta, kai ta ba ta wahala, kuma ba ka yi mata bayanin komai ba, ta ce a can ma ta bar ma takardun, kuma ta koma amsa an ce ba ka ba kowa ba, kuma an bincike office din ba a samu ba.”

Ta kai karshen dogon jawabin idanunta zube a kansa.

Ya mayar da hannayensa cikin aljihu hade da tabe baki bai ce komai ba.

Kafin da bisani, ya bude motar ya dakko wani envelope babba, ya bude hade da zaro takardun Umaiman ya mikawa Fatima.

Ta gama bude takardun ta ce “Sune”

“Shi kenan?” Ya tambaya cikin halin ko in kula.

“Ka ba ta hakuri please” a marairaice ta yi maganar.

Ya zuba mata ido hade da jan dogon tsoki, lokaci daya kuma ya bude motar ya yi mata key, ya fice daga gidan.

Ta sauke hannunta daga tagumin da ta yi sannan ta koma daki wajen Umaima.

Mika mata takardun kawai ta yi suka ci gaba da hirarsu.

*****

Ranar Alhamis misalin karfe 10am suka isa Kaduna.

Tun da Fatima take ba ta taba zuwa Kaduna ba sai ranar, ita a Nigeria daga Katsina sai Kano kawai ta taba zuwa, shi ya sa ta ware ido tana kallon gine-gine da suke wucewa, wasu su burge ta, wasu ta ji akwai bukatar su fi haka.

Lokacin da suka isa tasha, wata falleliyar mota ce ta zo daukarsu. Sosai a Familyn su Fatima akwai masu kudi, yayyyunta mata duk masu kudi suke aure, amma ita ko a taron biki ko suna ko nadin sarauta ba ta taba ganin irin motar ba.

Da Bismillahi ta shiga hade da zama cikin luntsuma-luntsuman kujerun da ke cikin motar. Wani kamshi da sanyi ya mai dadi ya bugi hancinta

“Allah Kasa idan mun mutu mu shiga aljanna” Fatima ta fada cikin zuciyarta bayan da motar ta haura kan titi, kamar tana tafiya a ruwa, ba wani kwari bare tudu, ko an shiga rami ba ta ganewa.

Ta kuma dorawa da fadin “Ai wani abun sai dai a aljannar amma dai a nan duniya ka san ya fi karfinka” ta karashe maganarta ta dazu hankalinta a gefen hanya tana kallon manyan gidajen da suke wucewa. Ga lafiyayyun tituna fes kamar ba a Nigeria ba.

Ta kasa hakura ta kalli Umaima wacce suke ta gwarancinsu da Beauty ta ce “Amaryarmu ya sunan nan unguwar?” haka take kiranta idan ta so tsokana, tana nufin amaryar Jamil.

Sai da Umaima ta harareta ta ce nan muna kan titin Alƙali Road ne, yanzu ba da jimawa ba za ki gammu a filin Murtala Square.

“Uh! Na ɗaka bai yi kallon na waje ba, Allah Ya bamu kuɗi masu yawa masu kuma albarka.”

Harara dai Umaima ta kuma aika masa, kafin ta ƙara mayar da hankalinta kan beauty. “Tana fadin amin”

Ita dai Fatima ba ta kuma magana ba, sai cigaba da kallon gefen titi ta yi, tana kallon yadda suke ratsa kyawawan titina, kai tsaye motarsu ta cigaba da tafiya har suka fara shiga yankin unguwar Rimi, kai tsaye motarsu Estate ɗin Naita ta shiga, duk da babu kwalta a cikin unguwar, amma yadda aka tsara gidajen sun burgeta, a get ɗin kofar wani gida wanda faɗin tsaruwarshi ma bata lokaci ne motarsu ta tsaya tana danna horn, wani police ne ya bude musu kofa, motar ta sulala har zuwa gate na biyu, nan ma police din ne ya bude musu, sannan motar ta mike sambal akan kayataccen hanyar da zai sada ka da katon ginin da ke cikin gida.

A parking space motar ta tsaya, Umaima ta fito sabe da Beauty, yayin da Fatima ta fito rike da karamar Jakarta, babbar kuma Umaima ta ce ta bari za a shigo da ita.

Da alama ba Fatima ce kawai ta zama yar kauye ba, har da Beauty don kuwa ware ido ta yi sosai tana kallo kayataccen gidan, musamman da suka fara hawa stairs din da zai sada su da dakin Umaima. Gidan shiru kamar ba kowa.

A kan wani fankacecen gado Fatima ta zauna, wanda ba ta taba ganin irin shi ba, ware ido ta yi sosai tana kallon ko ina, wani ma tashi take yi ta je ta tabo ta dawo zauna. Tun ba da Umaima ta koma kasa ba.

Ba ta taba tunanin Umaima ta fito a irin wannan gidan ba, duk da akwai abubuwa da yawa a tare da Umaiman, amma ba ta yi tunanin tarin dukiyarsu ya kai haka ba.

“OH Allahna!” cewar Fatima lokacin da ta leka toilet.

Sai ta tuno gidansu na Sandamu, gini ne na sarautar gargajiya, kuma gidan na daya daga gidajen da za a iya lissafawa masu kyau da girma.

Sai dai tabbas wanda ya rayu a gida kamar nan, rayuwa ko ta kwana daya a Sandamu ba karamin kokari ya yi ba. Umaima ba ta taba nunawa Fatima ita din yar masu da shi ba ce, a farko ne Fatiman ke mata kallon mai girman kai, amma tun da suka fara mu’amala ta fahimci Umaiman saukin kai ne da ita, ba ta dauki duniya wani abu ba.

Tana cikin wannan tunanin Umaima ta turo kofar, bayanta wasu ƴanmata ne dauke da manyan tire, suka aje a tsakiyar falon.

Cikin girmamawa suka gaishe da Fatima, ta amsa musu cike da kulawa.

Sai a lokacin Umaima ta sauke Beauty daga jikinta ta shiga toilet da sauri.

Fitowarta ya yi daidai da shigowar kiran Ammi.

Umaima ta daga kiran tana shaida mata basu jima da isowa ba, abinci zasu ci su taho yanzu.

Ba ta san me Ammin ta ce ba, Umaima ta yanke kiran tana fadin “Mom Hana sakko mu ci abinci Ammi na jiranmu”

Umaima ce ta hadawa Beauty tea mai kauri, don ita abincinta kenan ba ta cin sauran abinci musamman carbohydrates.

Fatima ta zubawa wamars din ido, don da gaske ba ta san yadda za ta bude su ba. Kamar Umaima ta sani sai ta bude komai na wurin, Fatima ta rika karewa komai kallo kafin ta ce “To ni nan ma me zan ci. Komai so nake yi”

Murmushi Umaima ta yi kafin ta ce “Allah na gama tafiya za mu yi ko ba ki gama ba”

Fatima ta yi dariya tana fadin “Ke ni fa zan iya kyale duk wani gyaran jiki in zauna cin wannan, akwai wani gyaran jiki da ya wuce wannan garar, to ina cin wannan wlh a, sati jikina zai koma kamar nunannar gwanda”

“Allah Ya yafe ki” cewar Umaima tana zuba pepesoup din kan rago a dan karamin bowl.

Fatima kam ku san komai sai da ta taba, tana fadin yi hakuri kin dai je garinmu da gidanmu kin gani, ba zan bari kaina ya yi murfi, maganar gaskiya komai sai na ci wlh, ke din ai ba bakuwata ba ce.

Dariya kawai Umaima ke yi, sosai Fatima ta cika cikin ta, don ba ta yi da wasa ba.

Umaima ce ta kuma shirya Beauty cikin riga yar kanti baka mai kyau, kasancewarta fara sosai rigar ta yi mata kyau.

Fatima kuwa doguwar riga ta sanya, don sosai Umaima ta koya mata sanya dogayen riguna.

Fas suka fito, Umaima sabe da Beauty yayin da Fatima ke bin su a baya, tun da suka sakko kasan suke karbar gaisuwa daga ma’aikatan gidan.

“Kai jama’a. Allah ka bamu wani ya ga, jariri” Cewar Fatima, har lokacin mamakin daular da ke gidansu Umaima take yi, sai ka ce ba za a mutu.

A cikin motocin da ke fake a parking space din gidan, Umaima ta zira key a jikin wata fara mai kyau.

Fatima ta zauna front seat, Umaima ta dora mata Beauty, cikin kwarewa ta fice daga gidan yayin da polisawan nan ke ta mika musu gaisuwa. Sai Fatima ta ji kanta ya yi gingimeme.

Wani kayataccen wuri suka shiga, wanda tun daga waje kamar za a yi musu numfashi har suka isa ciki, wata girmamawa ta musamman ake basu, mamaki Fatima ke yi irin wannan wurin a Kaduna kamar a Kasar waje.

Wurin Ammi suka fara shiga, kayataccen office wanda ya sha kayan gyara ga sansanyan kamshi mai dadi.

Kyakkyawar mace dattijuwa wacce ba ta wuce shekara hamsin ba, amma kallo daya za ka yi mata ka fahimci ta ƙoshi da ilmin zamani.

Doguwar riga ce ja a jikinta, ta yafa mayafin rigar da alama a nan Umaima ta koyo sanya doguwar riga.

Karasawa Umaima ta yi wurin da Ammin take, suka yi kissing din juna cike da kulawa, abin da ya ba Fatima mamaki. Ita kam dukawa ta yi cikin girmamawa ta gaishe da Ammin, yayin da Ammin ke tsokanarta da Amarya-amarya.

Sai da suka natsa, sannan Ammin ta kira wasu ƴanmata suka tafi da Fatima wurin gyaran jiki, kai aka fara wanke mata hade da yin streaching din shi, turarurruka masu kamshi na kai da maya-mayai aka shafa mata, take kuwa kan ya dauki wani irin kyalli hade da yin timɓis kamar auduga.

Daga wurin wanke kan sai wajen gyara jiki, wani akwaku aka bude aka ce Fatima ta shiga, nan fa ta ce Allah Ya kashe ta batta shiga, kokowa ita da Umaima, Umaima na kokarin tura ta yayin da Fatima ta toge, mutanen wurin kuma na ta dariya.

Cike da takaici Umaima ta kira Ammi ta fada mata abin da ke faruwa.

Ba jimawa kuwa Ammin ta kara so wurin.

“Me ya faru ne?” Ammin ta tambaya tana kallon su Fatima.

Ran Umaima a bace ta ce “Ammin ta ki shiga wurin wankin jikin”

Ammin ta kalli Fatima wacce ke tsaye tana kallon Umaima.

“Wai haka Dota?”

Fatima ta bi Umaima da kallo, yayin da Umaiman ke ta watsa mata harara. Cikin kasa da murya ta ce “Kaina ke ciwo, ni ba sai na shiga ba”

Cikin sauri Umaima ta ce “Wlh karya take yi Ammi”

Murmushi Ammi ta yi kafin ta ce, tun da ba ta so, kai wurin su Lola sai su gyara mata jiki kawai hade da, wanke mata kafa, gobe sai a yi mata kunshin”

Wani sanyin dadi Fatima ta ji, da Ammi ba ta matsa sai ta shiga wannan kwamin ba, ina dalili haka kawai zafi ya kar ta.

Umaima kin bin su ta yi, wai ita dole ta ji haushi, sai Ammin ce ta raka Fatima.

Kafar aka fara wanke mata, take kuwa ta yi subul kamar ba ta taba taka kasa ba, dama abu ga farar fata.

Sannan aka juya gyaran jiki, nan Fatima cewa ta yi iya fuska da hannuwa kawai take so.

Wani hadi suka fara shafa mata mai kamshi, after 30mns aka wanke sannan suka bi da wani yellow, shi ma after 30mns suka wanke, haka su kai ta mata shafe-shafe da feshe-feshe. Cikin awa uku Fatima ta canja, babu wannan dark spot din, fata ta yi fresh, gashin ido da na yi gira ya yi santsi hade da yin bakikkirin.

Ita kanta sai ta ji ina ma a duk jikin aka yi, don fuskarta da hannayenta wani irin santsi suke yi.

Har office din Ammi suka rakata bayan an gama, Beauty zaune a kan faffadan table din da ke gaban kujerar Ammi tana cin Chesee yayin da Umaima ke zaune tana daddanna laptop, ta bi Fatima da harara, yayin da Fatima ke dariya kasa-kasa.

Kafin su yi magana Ammi ta shigo.

“Ma sha Allah. A hakan ma kin yi kyau sosai”

Umaima ta bata rai kafin ta ce”Babu wani kyau. “

Cikin dariya Fatima ta ce” Bar ni haka”

Ammi ma dariya ta yi kafin ta ce “We can go now.”

Beauty Umaima ta saba ta nufi kofa, yayin da Fatima ta bi bayan ta, Ammi kuma ta tsaya hada tarkacen ta.

Lokacin da suka isa gida ana kiran sallahr magariba, kai tsaye kuma dakin Umaima suka wuce.

Bayan shigarsu Fatima ta ruko hannun Umaima tana fadin “kina fushi?”

“Ta ya ba zan yi ba?” Umaima ta amsa bayan ta kwantar da Beauty kan fankacecen gadon, don ta yi bacci a hanya.

“Ba Za ki gane ba Umaima, ni fa ban taba shiga wannan abun ba, abu kamar kwale-kwale fisabilillahi a tura ni ciki, bar ni in shiga in yi wankana da kaina yadda na saba. Haka kawai abu ya markade ni”

Umaima da ta tsurawa Fatima ido, ta ce “Ke kika jiyo, amma Allah next time sai kin shiga”

“Allah Ya kai mu next time din”

Cewar Fatima tana cire dankwalin da ta nade kanta.

Matsakaicin gashinta da ya sha gyara ya bayyana.

“Ba laifi kin fa yi kyau” cewar Umaima tana kallon Fatima.

“Da gaske?”

“Wlh!” cewar Umaima, suka dan yi dariya kafin Fatima ta shige toilet.

Wanshekare misalin 10am mai kunshi ta zo, haka kuwa ta, watsawa Fatima kunshi, wanda ko lokacin da ta yi aure ba a yi mata shi ba, musamman da ya kasance ja da baki.

Umaima ce ta yi musu Park na kayansu, yayin da Ammi ta biya musu kudin jirgi zuwa Abuja.

Abun da Fatima ba ta taba tsammani ba, yau ita ce za ta shiga jirgi, ba kuma Saudiyya za ta je ba, lallai sa a ta fi sammako.

Misalin karfe shidda jirginsu ya daga zuwa Abuja.

<< Daga Karshe 52Daga Karshe 54 >>

4 thoughts on “Daga Karshe 53”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×