Lokacin da suka isa airport karfe shidda daidai na yamma, Mustapha da yake jiran saukarsu, tun da ya hango suna sakkowa bakinsa ya ki rufuwa.
Fatima sanye cikin doguwar riga baka mai santsi, tayi rolling din jan mayafi, sai siririn farin glass da ta makala a fuskarta, wanda ya fito mata da kyakkyawan madaidaicin hancinta. Kafadarta sabe da Beauty wacce aka raba dunkulallan gashin ta gida uku aka daure su da kyakkyawan jan ribon na yara mai kyau.
Jar yar kanti ce cotton a jikinta, sai farin takalmi flat mai igiya, wanda duk lokacin da aka taba shi yake bayar da kalolin wuta.
Ya san akwai mutane yawa a wajen da za a tambayesu zasu rantse Beauty ce diyar Fatima ta fari, sosai Mustapha ya shagala da kallon ta, kullum kara gogewa take da zama babbar mace.
Cikin gulma Umaima ta zunguro Fatima tana nuna mata Mustapha.
Sai a lokacin ta gan shi, sanye cikin shirt fara tas da bakin wando mai santsi, hada idonsu ke da wuya duk sai suka sakarwa juna murmushi, yayin da Mustapha ma ya zarce da dariya sosai yana karbar jakar da ke hannun Umaima hade da karbar Beauty wacce ke ta kallon sa.
Yana sanya jakar a boot ne Fatima ta ce “Fadi me kake son fada don Allah, na gaji da dariyar nan”
Cikin dariya ya ce “Kawai ina farin ciki ne kin zo.”
Ta aika mishi da harara kafin ta ce “Fada ma wanda ba Sankar ba haka Ya Mustapha amma ba ni ba. “
“Ke dai mamaki nake Fatima a jirgi, kenan fa har kin riga ni shiga jirgi Ikon Allah. Wato haka Allah ya tsaro za ki riga ni shiga jirgi” ya karasa maganar idanunsa zube a fuskarta.
Cikin siririyar dariya ta ce “Wannan shi ake kira da Sa a ta fi sammako“
“I see” ya fada lokaci daya suna dariya.
“Idan kun gama soyayyar ina jiran ku.” cewar Umaima da ta bude back seat ta fito, alamun ta gaji da zama.
Cikin dariya Mustapha ya ce “Ba fa soyayya muke ba, ta ya ta murna nake yi…”
Kafin ya karasa Fatima ta yi saurin tararshi da fadin “Da zarar ka fadi abin da kake son fada, ka gan shi can bai tashi ba (ta nuna jirgi) idan ban koma ya mayar da ni ba ka ce ba daga Sandamu nake ba”
Daga Mustapha har Umaima dariya suke yi, don Umaima ta fahimci inda maganar Mustapha ta dosa.
Dorawa Umaima Beauty ya yi, kafin ya bude motar ya zauna, Fatima kuma ta zagaya wurin Umaima za ta zauna, Umaiman ta hana dole ta koma wurin Mustapha.
Hankalinta a gefen hanya tana ganin gine-gine da suke wucewa, wani lokaci kuma ta tanka tsokanar da Mustapha ke yi mata, Umaima dai dariya kawai ta ke yi, don sun nishadantar da ita.
Kai tsaye tsohon gidanshi ya zarce (inda wurin aikinshi suka ba shi, ba inda Blessing take ba).
Fatima ba ta yi tsammanin ganin ƴan’uwanta haka ba, amma kaf yayyunta mata babu wacce ba ta zo ba, ga su Aunty Bilki matan yayyu maza, ga Zainab, ga Ummi tare da wasu dangin Mustapha.
Sai ta kuma jin zuciyarta wasai, gida ya kacame da hayaniya, ana ta raha.
Abun da ke burge Umaima, idan ta ga Fatima cikin ƴan’uwanta, sai ta rika jin ina ma ace ita ce, ita kam babu wa bare Kane, shi ya sa rayuwar gidansu Fatima ke burgeta. Musamman idan suna ɗan fadansu, ka ga kamar gaske kamar wasa.
Blessing ita ma tana can da nata ƴan’uwan, ta yi bakin kokarinta wajen ganin abin da ya faru a sunan Ihsan bai kara faruwa ba. Don ita ce tai ta hidima dasu Aunty Hauwa tun da suka iso.
Misalin karfe 7pm na dare ta zubo manyan kuloli zuwa masaukin su Fatima kamar yadda ta kawo ma su Aunty Hauwa da rana, kasancewar karfe biyu a Abujar ta yi musu. Mustapha da Jamil ne suka kwaso su, shi Jamil sabgarshi ya wuce cikin gari.
Su Hana ne suka fara shigowa, Hana sanye da riga da wando masu kyau na mata, kannan ya sha gyara irin na Iyamurai, sai ta zama kamar ba Fatima ce ta haife ta ba, Ziyad kuwa guntun wando ne iya gwiwa ja, da farar shirt. Dukkansu ruwan Abuja ya karbesu sun yi mul-mul abun su.
Nan fa suka hadu dasu Hassan da sauran yara sai rashin ji ya tashi
Aunty Hauwa na cin abinci ta ce “Mama dai ta ce, wai mun kula da yaran Fatima kuwa sun kusa komawa ba musulmai ba?”
Duk suka yi gajeriyar dariya kafin Aunty Sadiya ta ce “Wlh ni ma ranar haka ta ce min, wai idan bamu yi da gaske ba yaran Fatima nan gaba ba nata ba ne, kullum suna yawo da guntayen kaya kai ba dankwali”
Cikin dariya Aunty Ayyo ta ce ” Af! Ita ma Fatiman ai haka ta yi, tsirara ne kawai ba ta zauna ba” .
Fatima ta ce “ji sharri, ni shi ya sa ban so Aunty Ayyo ta zo a yayata ba”
“Sai ki faɗi ki mutu ai.” cewar Aunty Ayyon.
Aunty Hauwa ta ce “Wlh ranar Mama ta ban dariya sosai, kun san Maamah ma da wuta, da an hura, to ta kafa zarya a wurin sai an kashe, shi ne ranar Mama ta ce, wai ban da Allah Ya sa an dakko ta, kila ma bautar wuta za ta tashi tana yi, tun da su Indiyawa komai ma abun bauta ne a wurin su idan dai ya yi musu.”
Duk suka kwashe da dariya kafin Aunty Bilki ta ce
“Ta ce dai ya dage ya nemo mata, kuma a Sandamu ba ta san kwashe – kwashen nan” .
“Ita fa Mama gani take matan Sandamu dai sune kawai masu hankali, tarbiya da Sanin ya kamata” cewar Aunty Aisha
Sai a lokacin Fatima ta ce “Ai gaskiyarta, ba duk gamu ba”
Aunty Aisha ta tabe kafin ta ce “Yo ke Fatima ban da Allah Ya sa malamin islamiya kika aura, ai da tuni haukanki ya yi nisa”
Duk falon suka kwashe da dariya, Aunty Hauwa ta katse su da fadin “To yanzu ma warkewa ta yi, ai sai dai sauki, amma ko gobe ya kado Fatima ai tana buga shi”
“Don Allah Aunty Hauwa ki yi shiru, kin san ke ina jin kunyarki saboda Zainab. Amma kin ga Aunty Aisha dam a can na san zaman da muke da ita.”
“Ni kike ji ma kunyar? Ni kar ki yi min karya, duk wacce ma kika raina ai bara na ce” Aunty Hauwa ta fada hade mikewa tsaye alamun ta ƙoshi.
“Wai har kin ƙoshi? Fatima ta tambaya cike da mamaki.
Cikin kasa da murya Aunty Aisha ta ce” Ba ta jima da cin abinci ba fa”
Siririyar dariya Fatima ta yi kafin ta ce “Ko da na ji, amma Aunty Hauwa da shinkafa da miya ai sai ta ji kamar za ta yi amai.”
“Kin san dai ai akwai a gidan mijina, kuma kafin in ci ta gidan mijinki, ta nawa gidan mijin kika fara ci daga ke har mijin na ki. ” Aunty Hauwa ta basu amsa kafin ta fice.
” Gori ya tashi” Fatima ta fada cikin dariya.
Daidai lokacin kuma Aunty Lami ta shigo dauke da Zarah diyar Ummi, Ummin kuma na bin ta baya. Pampers suka je saye. Wai Ummi ta dauka ta sako a cikin kaya ashe ba ta sako ba.
Ummi bedroom ta zarce, sai Fatima ta bi bayanta, yayin da ta bar Umaima da Zainab suna hira.
“Tun yanzu za ki sanya mata pampers din?”
Ummi ta dakata da sanya pampers din da take wa Zarahn kafin ta ce “Aunty ta faye yawan fitsari.”
Karbar pampers din Fatima ta yi, ta ci gaba da sanyawa Zarahn, sai da ta gama, sannan ta daga ta samo tana yi mata wasa, ita kuma tana kyalkyala dariya.
Lokacin da ta dakata da yi mata wasan ne, Ummi ta ce “Aunty ni ma gaskiya ki yi wa Ya Mustapha magana makarantar zan koma”
Bude baki Fatima ta yi, kafin daga bisani ta fashe dariya “Makaranta kuma Ummi, me ya sa?”
Sai da Ummi ta tura baki ta ce “Kin ga yadda kika zama kuwa Aunty Fatee, wlh kin canja gabadaya, wayewar ilmi daban take, kin yi wani kyau. Kai ni ban san yadda zan fassara ba, amma tsakani ga Allah kin canja, musamman wannan karon”
Ta sauke hannunta daga kan habarta kafin ta ce “To je ki ma Ya Mustaphan zai yarda, mijinki fa?”
“Shi ma zai yarda”
Ta ba ta amsa cike da kwarin gwiwa.
“To zan yi mishi magana sha Allah. Amma ki jira ki yaye Zarah karatu da goyo ko ciki wlh akwai wahala Ummi”
“Abin da kasa kanka Aunty Fati baya ba ka wahala, ke ma haka a kai ta tsorata ki, amma DAGA KARSHE dai ga shi za ki je inda kike son zuwa, duk wani kalubale da gwagwarmaya kin wuce su. Ni dai kawai ki shige min gaba Ya Mustapha ya yarda”
Nisawa Fatima ta yi, hade da tuna gwagwarmaya da ta sha, har yanzun ma tana kai, tun da ba ta gama ba, cikin sanyin murya ta ce “Ummi akwai challenges sosai, akwai kuma wahala”
“Aunty Fatima kamata ya yi ki ba ni kwarin gwiwa ba wai ki kashe min jiki ba” kamar za ta yi kuka ta yi maganar.
Yau kam bacci kadan suka yi aka kira sallah, hira suka yi sosai, don rabonsu da haduwa irin haka har sun manta.
Misalin karfe takwas Blessing ta kuma aiko da abun kari, sannan ta ce su Hana su dawo gida za a shirya su, don karfe goma za a fara walimar.
Tun karfe tara na safe kuwa suka fara shiri.
Idan dai a sa a fita ne, to ƴan’uwa Fatima zasu sanya, su fita kuma a daga kai a Kalle su a ko ina ne dole.
Sun iya kashewa kansu kudi, musamman idan abun na fita kunya ne, yanzu ma kam sun dau kwalliya, ko wacce na wane waccan dukkansu ba raini, bare su Umaima da Zainab ƴan bana bakwai. Don ma Zainab ana ta laulayi.
Fatima kuwa Umaima ce ta tsara mata light make up, duk ds Sai da su kai ta fada, ace wannan ta ce ba ta so hakan, ita haka take so, ita kar a yi mata haka, sai da Aunty Lami ta zazzageta don duk a cikinsu ita ce mai saurin hasala, yanzu ta yi wa mutum tatas.
Lace omo Blue ta sanya hade da kwalliya fulawa pitch riga da siket dinki ya fita , Umaima ta aje mata dauri mai steps, sai ta zama kamar amarya, ga wasu gwala-gwalai a wuya da hannu.
Duk sai da suka yaba kwalliyar wai ko ranar auranta ba ta zuba kyau na mutumci ba irin na yau.
Haka Mustapha da abokansa biyu suka zo kwasar su don zuwa sabon gidan.
Bai taba tsammanin Fatima ta yi wa abun shiri har haka ba, ya dauka yadda take nuna ko in kula sun karbi kudinsa ne kawai, amma ga mamakinsa kwalliyar ta fi karfin kudin da aka amsa, dama wani mawaki ya ce “Mata da kwalliya sune mata, mata babu kwalliya aikin banza.”
Duk da ba wata kwalliya ta zabga kamar Blessing ba, amma kam ta fita ba karya, kamar a injin ta fado, musamman fuskarta da ta zama subul ba darkspot din nan, duk da wani lokaci sai ta ce son abun ta take yi.
Sai ya rasa tsakanin matan nashi biyu wacce ta fi kyau ne, don Blessing ma sosai ta fita cikin farin lace mai net-net da aka yi wa dinkin doguwar riga kamar ta aure, aka dora mata dauri, kamar dai amaryar, da yake ba ta kai Fatima haske ba, sosai lace din ya karbe ta.
Godiya ya shiga yi wa Allah, don shi ne kawai zai yi mishi wannan kyautar ba wani ba, mata kyawawa, ko wacce ba kashin yadawa ba, ga yaranshi shida gwanin sha’awa uku maza uku mata, gida, muhalli, abun hawa, to a duniyar nan mai kuma yake nema ban da fatan gamawa lafiya da ita.
Tun kafin su shiga gidan Fatima ta fahimci Mustapha fa yanzu ba shi ne na baya ba, tangamemen gida ne, mai dauke da manyan part biyu a jere wanda direct suke kallon gate, sai kuma wani madaidaicin part din daga bangaren kudu, farfajiyar tsakar gida madaidaiciya shimfide da interlock, wacce za ta iya dauke motoci hudu. Ga wasu fulawoyi masu kyau da suka kawata gidan.
Haka suka fito daga motocin hade da sanya Fatima a tsakiyarsu, kamar wata sarauniya za ta isa fadarta. Ita kanta sai ta ji tafiyarta ta canja, ta kare matsa yar kamar ash color din jakar da ke hannunta taku take cike da kasaita.
Yayin da su Hana suka baro wurin zamansu da gudu suka mamutseta, Hassan ta daga kasancewar Beauty na hannun Umaima, bayan ta daga Hassan ta yi yar tafiya da shi, ta sauke shi hade da daukar Hussaini ta karasa da shi har wurin da aka tanadar mata.
Dangin Blessing ma an ba naira kashi, don abu ne kowa yake yi kamar da gayya. Idan ka kalli bangaren Fatima da na Blessing din sai ka rika tunanin kamar babu talauci a duniya.
Ƴan’uwan Blessing biyu ne suka tako mata baya zuwa inda Fatima take zaune. Don mika gaisuwa.
Fatima fara’a bare Blessing da ita kam kullum bakinta a bude, ita kamar ba ta san fushi ba.
Cike da girmamawa suka gaisa, Fatima ta dauki Ihsan wacce ita ma tafiyarta ta yi kwari, kan cinyarta ta dora ta, yarinyar kuwa sai ta yi zaman ta, haka Blessing ta juya zuwa wurin zamanta ta bar ta.
An gabatar da addu’o’i, an ci an kuma sha.
Da gaske Blessings ta zama malama, don ko gongoni ba a buga ba. Amma komai ya kayatar an yi nishadi an sha hotuna cike da mutuntawa aka yi komai.
Kafin aka fara raha a kan wa za a fara rakawa zuwa dakinta, Blessing ta ce MOm Ziyad, Fatima ta ce “A’a ni zan raka ki, ai ni ce babba.”
Haka aka yi ta raha kafin a karshe suka runguda flat din Blessing.
Daga falo, bedroom , kitchen babu inda bai sha kudi ba, akwai dakin yara wanda aka zuba madaidaitan gadaje guda biyu, wardrobe da kuma karamin TV da tarkacen kayan wasa na yara.
Sai da suka shiga ko ina, suna yabawa, kafin aka nufi part din Fatima
Ba ta tsammaci ganin komai a nata part din ba, tun da dai ta san ba ta sai komai din ba.
Ginin ma ba irin na blessing ba ne, don ita Blessing babban falo, sai stairs din dinning, wanda suka jera da kofar kitchen dakinta ya jera da dakin yara. Amma fa an kawata komai.
Ita kuwa Fatima kana bude kofarta akwai dogon corridor, wanda ta cikin corridorn akwai daki, shi za ka fara isa, kuma shi suka fara budewa, gadaje biyu wardrobe da sauran tarkacen yara, wannan ya tabbatar musu da dakin yara ne, idan ka matsa duk a cikin corridorn kofar kitchen ce, nan ma suka shiga cike da mamaki Fatima ke karewa komai kallo, don gani take yi kamar ba nata ba ne saboda haduwarshi, daga cikin kitchen din kumaakwai store a ciki, kamar dai ciki da falo.
Suka fito daga kitchen din sannan suka kuma bude wata kofa, a nan ne dakin Fatima yake. Kujerun Fatima ba irin na Blessing ba ne, don ita nata wasu irin simple ne farare tas, sun kawata falon musamman labulayen upmilk da aka sanya sai suka kara kawata dakin, sai dai nata babu dinning area a ciki, bayan sun shiga bedroom din suka fito, still corridorn sai ya mike zuwa bangaren yamma, wanda a nan ma akwai karamar kofar, da alama nan din ma dakin yara ne, wanda daga nan flat din ya kare.
Sosai Fatima ke mamakin kayan da aka sanya mata.
Bayan an natsa ne su Aunty Hauwa ke cewa sai ta mayar da farfajiyar corridor din dinning, tun da akwai art design ga Kuma Pilar guda biyu da suka kawata art din.
“Wai Aunty Hauwa duk waye ya sa yi wadannan kayan?” cike da mamaki Fatima ta yi maganar.
“To su wa kike dasu?” Aunty Lami ta tambaye ta.
Shiru Fatima ta yi ba ta ce komai ba.
Aunty Aisha ta ce “Idan an ce ba ki da hankali ki ce kina da. Ke yanzu da an bi ta ta ki fa haka zamu zo mu tsugungunna a dakin nan ba komai, kalli dakin abokiyar zamanki, yanzu don Allah da ba ki ji kunya ba.”
Fatima ta ce “Ni kuwa kunyar me zan ji Aunty Aisha”
“Kin ji ta ko mahaukaciyar.” Aunty Lami ta fada cike da bacin rai.
“Don ubanki ai sai ki kwashe kayan ki bamu, ki tsugungunna a dakin haka nan, tun da ke ba ki san abun arziki ba.” Aunty Hauwa ma ta fada rai bace.
Dariya Fatima ta yi kafin ta ce “Ni fa ban ce ban ji dadi ba Aunty Hauwa, wlh na ji dadi sosai kuma na y farin ciki, da Aunty Aisha ta ce wai zan ji kunya, ni wlh ba kunyar da zan ji, abu da gobe ma zan tafi ni”
“Ina za ki je” Aunty Sadiya ta tambaya
“Makaranta mana, ai mun yi da shi dama ni kwana biyu zan yi.”
“Kin ji wani haukan ko. Ace Fatima na ds hankali, to ki ta fin don Allah”
Cikin kasa da murya ta ce “Aiko tafiyata zan yi.”
Ganin basu ji me ta ce ba, ta ce “To wai duk wa ya sayi wannan?” ta yi tambayar tana bin su da kallo.
“Aka ce su wakike dasu?”
Aunty Bilki ta ba ta amsa, hakan ya sa ta juya wurin Aunty Bilkin ta ce “Wai su Aunty Lamin ne?”
Kai Aunty Bilki ta daga kafin ta ce “Su da kuma Mustapha, duk abin da ke cikin bedroom, falo da dakin yara Mustapha ne ya zuba, kayan kitchen kuma ƴan’uwanki ne suka saya.”
Baki bude Fatima ta ce “Duka wai?”
Aunty Bilki ta ce “Kwarai”
“Kuma har da Aunty Hauwa?”
Lokacin da Fatima ta yi maganar kin kallon Aunty Hauwan ta yi, shi ya sa ba ta ga hararar da Aunty Hauwan ke aika mata ba.
“ita ba yar gidanku ba ce hala” cewar Aunty Bilki.
“Tun yaushe Aunty Hauwa ta koma gidan Hakimi, ai yanzu ita ce head of Hakimi house Kowa bin ta yake yi, ita ke juya su.”
Duk suka yi dariya idan ka dauke Aunty Hauwa da ta ke da na wayarta. Kafin ta ce ” ki yi fatan ki zama kamar ni”
Bayan sun dakata da dariyar ne Fatima ta ce “Gaskiya ban san da me zan gode maku ba, Allah Ya kara budi da karfin arziki, ina jin dadi da farin ciki da na zama daya daga cikinku, Allah Ya ba ni abin da ni ma zan yi muku. Tun da aka haife ni zuwa yanzu kuke dawainiya da ni, duk da ni ba na yi muku komai, kullum kune kuke min, yau kam na yi farin ciki fiye da ko wace rana a rayuwata, a yau kam ji nake yi kamar na fi kowa sa’ar yan’uwa” ta karasa maganar hade da share hawayen farin ciki da suka biyo sakko mata.
“Saura ki godewa Mustaphan” Aunty Bilki ta fada tana kallon Fatima, wannan ya sa mutanen dakin suka zuba mata ido
Da jikakkun idanuwanta, ta watsawa Aunty Bilki harara, tana fadin “To ina ruwanki kazallahu, ba mun fi kusa da shi Ya Mustaphan ba, gwana kishiyar Larai, ke tun nake da ke na taba jin kin godewa Ya Bashir ne?”
Suka kwashe da dariya har da Aunty Bilki wacce ta ce “To ke ma ina ruwanki, ba mun fi kusa ba ni da Ya Bashir din, lokacin da zan gode mishi kin sani ne?”
Fatima dai share hawayen farin cikinta ta ci gaba da yi, yayin da dakin suke ta surutansu.