Skip to content
Part 63 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Tun da ta koma gida ta kintsa kanta, daga cikin zuciyarta take jin ranar za ta zamo ta musamman a wurin Mustapha, za ta yi mishi abin da zai fahimci lallai a cikin nishadi take da kuma farin ciki.

Sai dai duk shiri gami da saka abubuwan da take son su faru idan ya shigo, hakan bai samu, saboda saka kafarshi cikin dakin nata, ya yi daidai shigowar kira a wayarshi, inda ake shaida mishi Blessing na asibiti, tun magriba amma har zuwa lokacin ba ta haihu ba, sun ce idan ta kai gobe karfe goma na safe aiki za a yi mata.

A kiɗime Mustapha yake shaidawa Fatima abin da aka sanar mishi, sosai ta yi mamakin jin labarin, ba ta san Blessing na da ciki ba, da alama da ciki aka yaye Ihsan.

Ba karamar damuwa Mustapha ya shiga, tamkar ita kadai ce ta rage mishi a duniya kuma take shirin barin shi a cikin ta.

A nan Fatima ta hango tsantsar so da kuma kaunar da yake wa Blessing din.

Saboda ko sau daya bai runtsa ba, to yaushe ma ya kwanta, alwala ma ya yi da nufin yin sallah, amma kasawa ya yi, sai dai ya yi tsaye ko ya shiga zagaye dakin, tun yana addu’a a cikin zuciya har ya fara yi a zahiri.
Cewa yake “Ya Allah! Ga baiwarka nan a hannunka, Allah ka sauke ta lafiya, Ya Allah ka ji kanta, Allah ban so in rasa ta, da in rasa ta gara in rasa abin da ke cikinta. Allah ka duba kyawawan ayyukanta na kwarai ka sauke ta lafiya…”

Fatima da ta zabga tagumi gefen gado, ga jimami ga kishi, ina ma ace yana Abuja ne, da Allah bai nuna mata wannan abu ba. Kai namiji sai Allah, anya kuwa kalaman da yake fada mata, na baya hada sonta da kowa gaskiya ne kuwa.

Tun da dai yau ga zahiri ta gani, idonta ya kwashe mata tarin soyayyar da ke kirjinsa ta wata.

Daurewa kawai ta yi, amma har ga Allah ta ji matukar kishi, ta san kam akwai damuwa ace matarka tana tsakanin rayuwa da mutuwa, amma ta rasa ta yadda za ta mallaki zuciyarta wajen yi mishi adalci, wani irin haushinshi take ji a can kasan zuciyarta.

Asubar fari kuwa ya dauki hanya, dama ta fi shin son ganin garin ya waye, ko ba komai ta samu ta runtsa, tun da ita ma ba ta yi baccin ba.

Sai dai duk yadda ta so ta samu bacci bayan ta yi sallahr kasa komawa ta yi, kaf hankalinta na a kan Blessing din. Kamar yadda Mustapha ya kwashe tsawon daren jiya wajen kiran waya minti-minti yana tambayar ya-ya? Ita ma haka ta tsugguna a tsakiyar gadonta wajen kiranshi tana tambayar ta haihu?

Ana shirye-shirye shiga da ita dakin tiyata ne Allah Ya karbi addu’ar mutane da yawa, wajen sauke ta lafiya tare da lafiyayyen yaronta kato. Girman yaron na daya daga cikin abin da ya kawo mata jinkirin haihuwar.

Cikin mintuna kadan labarin haihuwar Blessing ya zagaye kunnen dangin Mustapha, na Fatima da kuma na Blessing din.

Sai da komai ya lafa sannan Fatima ta kira Blessing ta yi mata barka, da alama kuma hakan ya yi mata dadi daga yadda take amsa kiran.

Ranar da Blessing ta cika kwana hudu da haihuwa ne Fatima ta je gidan Mama, kan maganar mayar da Zainab gidan mijinta da kuma maganar tafiya suna. Don har ga Allah ba ta son zuwa Abuja, Katsina take son zuwa wajen mayar da Zainab, idan kuma Mama ta matsa a kan ta tafi Abujar sai ta je. Don Mustapha bai yi mata ma maganar ko za ta zo ba, da alama baya son ransa ya baci ne.

Lokacin ba kowa a gidan sai Aunty Sadiya, ita ma daga asibiti take ta je ganin likita.

Bayan sun gaisa ne Mama ta ce “Yaushe za ki tafi Abujar?”

Dan ɓata rai ta yi kafin ta ce “Ni fa ba na son zuwa . Ai ta wani kallon mutum.”

“Su waye zasu kalle kin? To ina ma ruwanki da wani kallon masu kallo, ki gode ma Allah ma da kika kai a kalle kin.”

“A toh!” cewar Aunty Sadiya daga kwancen da take.

“Ni dai ban son zuwa.”

“Kawai dai ki ce ba kya son zuwa, ai ita ta iya zuwa ta ki sabgar. Kada Allah Ya sa ki je, mu zamu je”

“Da gaske Mama za ki je?” cewar Aunty Sadiya da ta mike cikin sauri.

“In sha Allah.” Mama ta amsa.

Dariya Sadiya ta yi kafin ta ce “Soyayyarku da Ya Mustaphan ta motsa kenan”

Ita ma cikin dariya ta ce “Da gaske ina jin Mustapha kamar ni na haifeshi, saboda kaf yarintarshi ya yi ta ne tsakanin gidan nan da gidan Hakimi. Ya dan bata min rai ne, amma yanzu komai ya wuce.”

Cikin yar karamar dariya Fatima ta ce “Ni ma na ji kuma kamar in je.”

“Ni ma haka.” cewar Aunty Sadiya cikin dariya

“Ku dai kuka sani.” Mama ta fada tana kallonsu.

“Gaskiya yar’uwata zan raka, ni ban iya shisshigi irin nasu Aunty Ayyo ba, ka bar naka ka je na wani, wannan sai su Aunty Aisha, ni kam Katsina zan je in raka diyata.” cewar Fatima hade da kwanciya.

“To ki samu abin da za a kai wa Maman Ihsan din kuwa?”

Ido ta fitar waje kafin ta ce “Mama ni da duka yau kwanana biyar da gama makarantata ina na ga kudi?”

“Oho. Ki nemo su wlh, dubu goma za ki bayar, saboda waccan haihuwar ma ba ki yi mata komai ba, ita kuwa duk haihuwarki sai ta yi miki, koma ba ta yi miki komai ba, ko don yaranki da ta rike ai kin yi mata Kodayake ke ba hankali gare ki ba, ba ki san ya kamata ba.”

“Kai na shige su!” cewar Fatima hade da mikewa zaune.
Kafin ta dora

“Duk lokacin da na yi abu, sai an yi min gorin yarana suna wurinta, to wai ta maido min mana, ni fa ban taba rokar ta rike min yara ba, kuma ni na san rike yaran nan ba don ni take yi ba, don mijinta take yi. Amma kullum gori ake yi min. “

Aunty Sadiya ba ta ce komai ba, sai Maman ce ta ce”To ai abun gorin kika yi, ai Hausawa sun ce, ko ba ka iya kyauta ba, to ka ba mai ba ka.”

“To ni dai yanzu ban da dubu goma”

“Karya kike yi gaskiya.” Aunty Sadiya ta fada hade da kallon ta.

Mikewa zaune sosai Fatima ta yi tare da fadin “Wai don Allah ina ruwanki a maganar nan ne, ni da uwata muke yin ta, kuma a kan Kishiyata ne, ina ruwanki?”

“Da shi.” cewar Aunty Sadiya kafin ta dora da
“idan za ki fasa asusunki, malama ki fasa, akwai kudi a wurin Ummi na dinka hijabai, da dogayen riguna.”

Rike da haba Fatima ta ce “Wato kina nan kina bibiyata, sai na nemo maganin sa’ido mai amsa, saboda ke.”

“Duk inda ma za ta nemo kudin ta nemo.” Cewar Mama
I
“To Aunty Hauwa ta ara min.”

“Tabb! Aunty Hauwa hidimominta sun ishe ta, za a mayar da Zainab, ga ƴarta ta ruwan sanyi ta haihu, ga auran masoyinta Jamil, Kinga ko ai ba ta taro” Cewar Aunty Sadiya

“Kuma fa. Ai Aunty Hauwa uwar sabga ce, idan sabga ta zo ba ta samu Aunty Hauwa ba kuka take yi, saboda ta san tata ta kare.”

Duk suka yi dariya, Mama ta ce “Kuma ita ce karfinku, duk ranar da ba ta za ku yi kuka da idanunku.”

“Tun ba ni ba” cewar Fatima cikin sauri.

“Ni kai” Sadiya ma ta amshe.

Daga nan hirar ta koma kan dawainiyar Aunty Hauwa a kansu.

Ana saura kwana biyu sunan Blessing su Fatima suka tafi Katsina mayar da Zainab.

Aunty Hauwa kuma da Mama dasu Ummi ana gobe sunan Blessing suka daga zuwa Abuja.

Mama kam duk abin da Uwar miji ke yi a gargajiyance shi ta yi, yayin da Aunty Hauwa ta zuba hidima a matsayinta na uwar maijego. Tun daga kayan sanyawar mai jego har na Baby.

Sannan kaf iyalan Mama babu wanda bai aika da gudunmuwa ba, haka Aunty Hauwa ta rika lissafawa Maijego abin da kowa ya bayar, ita kuma tana ta zuba godiya.

Sai da aka zo kan kyautar Fatima ne Blessing din ta saki baki tare da fadin “Really Aunty? Mom Ziyad ce ta bayar da duk wannan a kawo min?”

Cikin murmushi Aunty Hauwa ta jinjina kai.

Murmushi Blessing ta yi hade da jujjuya kudin “Sosai na ji dadin kyautar Aunty, karon farko da Maman Ziyad ta yi min kyauta mai ban mamaki. I don’t know, but I think Kamar tana jin haushina, ta tsani ganina, mutumcina da ita shi ne daga nesa-nesa. Kin ga ko waya zan kira ta yau in kira gobe, to za ki ga idan na kira jibi ba za ta dauka ba. Ita kam ma ba ta kira sai da wani abu muhimmi. Na rasa laifina a wajenta. “

A cikin zuciya Aunty Hauwa ta ce” Ke ko kika yi mata babban laifi tun da kin aure mata miji. ” a zahiri kuma cewa ta yi” Ki yi hak’uri da ita, haka halinta yake, komu da muke ƴan’uwanta hakuri muke da ita, amma idan za mu bi ta halinta babu abin da za mu yi mata. Ke ma ki yi hak’uri da ita. Sannan ki yi kokarin sanin halinta, wannan ne zai ba ki damar jin dadin zama da ita. “

” Sanin halinta shi ne abu mai wahala Aunty. “
Blessing ta fada hade da kallon Aunty Hauwa.

” Kin sani. Kiyayewa ne kawai ba ki yi ba”

Ido Blessing ta zubawa Aunty Hauwa alamun jiran karin bayani.

“Na san zuwa yanzu kin san ba a yi wa Fatima gwaninta. Ita haka take, ba wai a kanki kawai ba, a kan kowa ma.”

Cikin murmushi Blessing ta ce “Na fahimci haka”

Aunty Hauwa ma Murmushin ta yi kafin ta ce “Kuma idan ba ta sanya da ke ba, to kar ki shiga, kuma ki yi kamar ba ki san tana yi ba. Idan ta share ki, ke ma ki yi kokarin hakan, kina zaunenki za ta neme ki. Ki daina nuna kin damu da lamarinta, ba wuya ta gwale ki.”

Dariya Blessing ta kuma yi, kamar dai ta tuna wani abu a kan maganar Aunty Hauwan.

Ita ma Aunty Hauwa dariyar take yi kafin ta ce” Amma tana da kirki idan tana yi da ke, kuma ba ta da rowa dukdl dai kyautar za ta iya zama daidai da karin maganar nan ta a wanki kifi da ruwansa(daidai wurin Aunty Hauwa ta kara sautin dariyarta) na tuna wani abu ne, lokacin da Bashir ya auri Bilki, duk lokacin da Bilki ta zo gidanmu, idan ta ga abun Fatima ta ce “Fatima wannan ya yi kyau” sai Fatima Ita ce dauki na bar miki. “
Duk suka yi dariya, kafin Aunty Hauwa ta ce” Abin da ba ta sani ba shi ne, idan Fatima ta yi ma kyautar 5naira, to sha Allah a hankali sai ka ba ta 20naira. Shi ya sa mu da muka gane ta, ko ta ce dauki na bar ma, bama karɓa. Ita ma Bilki da ta gano hakan sai ta daina dauka. Duk da watarana ma tana iya dakko abu mai kyau ta kawo ma har gida ta ce ta bar ma. Kafin an jima ta yi ma barnar da za ta mantar da kai kyautar da ta yi ma.

Amma tana daya daga cikin ma fi soyuwa a zuciyoyinmu. Kin san daman an ce da yawan yara marasa ji sun fi shiga rai, ban san me ya sa ba, ga shi dai ba ta ji, amma tana da shiga rai sosai .”

Cikin jinjina kai Blessing ta ce” Na yarda da ke Aunty. Saboda ni kaina ina sonta, duk da ita ba ta wani damu da lamarina ba, amma ina son in ga mun zauna muna hira, abin yana min dadi. “

Shigowar da aka yi ne ya sanyasu kallon kofa gabadayansu.

Kanwar Babanta ce Aunty Gloria ta shigo rungume da jariri Abdallah da yake kuka, cikin tsokana take fadin” Uwa da ƴarta, me kuke tattaunawa ne? “

Cikin dariya Aunty ta ce “Sirrinmu ne”

Yadda mutane suke shigowa dakin ne ya sa dole hirar tasu ta yanke.

Mama kam dama dakin Fatima aka sauke ta, har ga Allah ta yabawa Mustapha da irin kayan da ya zubawa Fatima, ya yi matukar kokari, ya kara daraja da kima a idonta.

Fatiman ce ba a iya mata, amma idan ba haka, ta ya mai wannan gidan da kuma dakin zai je ya rayu a irin dakinta na Sandamu.

Amma ko a jikinta rayuwarta take yi cikin farin ciki da jin dadi abun ta.

Kamar yadda ake shan shagalin suna a Abuja cikin farin ciki da nishadi, haka su Fatima suka raka Zainab gidanta cikin farin ciki , gidan Aunty Lami suka kwana, wanshekare suka dakko hanyar Sandamu.

Su Mama dai sai bayan suna da kwana biyu Mustapha ya kawo su, daga nan ya yi kara’in amarcin da bai yi ba. Soyayya suke sha danya, tamkar jiya aka daura musu aure, musamman da ya kasance Blessing na jego.

Don ma Fatiman ba ta zama sosai, sun shiga hidimar biki Jamil wanda ya rage sati biyar. Hidimar hada lefe kawai ake yi. Shi ya sa ku san duk bayan kwana uku suna hanyar Kano, Fatima ce ta san Size na Umaima da choice nata shi ya sa duk zuwan da zasu yi Kanon da ita ake zuwa.

Ya rage saura sati daya biki aka fara shirin kai lefe, wanda aka ce maza ne zasu kai ba mata ba.

Ana gobe kai lefen iyalan Maman suka hallara kaf a babban falonta har da Mustapha da ango mai jiran gado.

Kayan ne ake fitarwa ana kuma shiryasu zuwa cikin kyawawan akwatuna guda goma sha biyu ringis.

Ko hasadun iza hasadun ya kalli wadannan kaya ba lallai ya samu wurin kushewa ba, saboda an ba naira kashi, an yi bajinta sosai.

Bayan an gama shirya kayan ne a cikin akwatunan tsab, Aunty Aisha ta mike hade da rangada guda, wacce sautinta ya ratsa duk wata masarrafan sautin mutanen da ke wajen.

Cikin dariya mai dauke da nishadi Aunty Ayyo ta ce “Wlh ko ni da ban iya guda ba, sai na yi ma wadannan kayan.”

Atare suka kuma kwallara wata doguwar guda mai zig-za. Aka rufe da shewa. Fatima ta dora da “Wlh ji nake kamar in sake sabon aure. Kai gaskiya tsakani ga Allah ya kamata a rika renewal na lefe, wannan irin shagali haka, ina ma ban yi auran ba sai yanzu.”

Aunty Lami ta ce “Ai da yake ma kin tura sako a daidai, mai canja lefen yana jin ki.”

Duk suka kai kallon su kan Mustapha

Hakan ya sa ya ce “Ki yi addu’a Allah Ya kawo kudi masu yawa da albarka, zan canja miki.”

“Da ka kyauta, saboda ni dai wancan lokacin ban ji irin dadin da ake ji idan an kawo ma mutum lefe ba.”

Aunty Hauwa ta ce “Ai ni ma da za ku taimaka, da kun yi magana an canja min, saboda ni ban san ma ya aka yi da nawa lefen ba”

Duk suka yi dariya cike da nishadi kafin Aunty Lami ta ce “Ke da aka kawo naki a kwalla da fanteka”

Caraf Aunty Ayyo ta ce “Marfin fantekar yana nan tana shanya barkono a ciki .”

Duk suka saki dariya yayin da Aunty Aisha ta ce “Kwallar kuma da ita suke dama kokon safe”

Haka suka kasance cikin nishadi, har zuwa lokacin da aka kira duk wanda ya dace da yaga lefen ya gani.

Safiyar Lahadi da ta kama saura kwana biyar daurin aure su Yaya Bashir suka dauki hanyar Kaduna.

Lallai Hausawa sun yi gaskiya da suka ce tuwon girma miyarshi nama, sannan inda aka darajar goro nan ake yayyafa mishi ruwa a kuma lulllube shi da garara.

Sun sami tarba ta mutumci, an karbi lefe cike da girmamawa gami da mutuntawa.

Misalin karfe uku suka baro Kaduna zuwa gida Sandamu.

Haka aka ci gaba da shirye-shiryen biki ta ko wane bangare, Yayin da Umaima ta matsa lallai Fatima ta biyo yan jere ranar Laraba ta taho Kaduna. Ranar Larabar kuwa aka kawo kayan amarya Katsina da kuma Sandamu, saboda Jamil ya ce zasu rika zuwa Sandamu musamman idan an samu hutu. Shi ya sa aka yi mata kaya 2set

Kan dole Fatima ta bi ƴan kawo kayan nan ba don taso ba, don har ga Allah ta fi sha’awar ta zauna cikin ƴan’uwanta a yi hidimar biki da ita. Akwai nishadantuwa sabga a zuriyar Alhaji Musa Sandamu.

Lokacin da ta isa Kadunar sai ta ga hidimar ta bambanta da ta Sandamu, hidima ce ta wadanda suka ci suka tayar da kai. Hidima ce ta wannan na ke ko ni, wai kyawawa sun hada hanya.

Sai dai kuma yadda Umaima ke sanya ta gaba a kan komai tana jin dadi sosai, kowa ya fahimci lallai Fatima ba karamin gurbi take da shi a zuciyar Umaima ba, akwai wata irin soyayya ta musamman.

Duk wasu dinkuna da za a sanya a wurin bikin Ammy ta yi wa Fatima, wannan abu ba karamin faranta ran ta ya yi ba.

Ita ko Umaima ku san duk maganin matan da ake ba ta tare suke shanye shi da Fatima, wani ma kadan take sha ta bar mata, wai ya ishe ta.

Ranar Larabar da ta je da yamma aka yi mothers day, komai cikin tsari da aji.

Ranar Alhamis kuma suka yi Fulani day a can event center na Ammy.
Fatima na son nishadi,duk da dai ba ta samu ta girgije yadda ya kamata ba, saboda bakin ido. Amma duk da haka ta nishadantu.

Ranar Juma’a da misalin karfe goma aka yi henna day, inda aka sha kidan ƙwarya na zamani, gefe kuma ana rangadawa amarya lalle da kawayenta, daga nan aka zarce da shagalin daurin aure wanda za a daura bayan an sakko masallaci.

Misalin karfe uku dubban mutane suka shaida daurin auran Jamil da Umaima.

Daurin auran da ya samu halartar dubban manyan mutane daga sassa daban daban na duniya .

Misalin karfe hudu na yamma Umaima na cikin motar kai ta gidan mijinta. Motar da mahaifinta ya mallaka mata a matsayin gift na auranta.

A can kuwa Mustapha hana Fatima shiga motar da Umaima take ya yi tun da ya zo, ya kasa ya tsare. Musamman yadda ya ga ta wanku a cikin ankon farin leshen da kawayen amarya suka sha. Babu mai ganinta ya ce ta haifi yara biyar.

Karfe biyar tuni sun mika a hanya zuwa Katsina.

Duk yadda ake labarin haduwar gidan Jamil Fatima ba ta dauka ya kai haka ba, sai da suka isa, musamman da ya kasance bayan sallahr magriba kwayayen lantarki masu kyau sun kawata ko wane lungu da sako na gidan.

Kusan komai na gidan fari ne, sosai tsarin ginin ya tafi da ita, a nan suka samu su Aunty Lami dasu Aunty Hauwa da sauran yara, don har Ziyad ya zo, Hana ce dai ba ta zo ba, kuma ta san saboda haihuwar Blessing, ko ba komai za ta rika taimaka mata da wasu abubuwan.

Akwai wata shakuwa ta musamman tsakanin Blessing da Hana. Don yanzu haka Hana na jin yarensu Blessing, Shuwa da Kanuri.

A nan ma haka aka kusa kwana shagali. Fatima dama da rawa 5&6 ne, ba ta samu daman girgijewa a gidansu Umaima ba saboda bakin ido. Nan kam su Aunty Aisha shi ya sa ta yi kara’i sosai.

Wanshekare kuma da safe aka zo fansa (budar kai) a nan ne fa kowa ya rika nuna bajintarshi a kan amarya da ango.

Jamil dai ya samu kyautar motar kirar camry yar ya yi sabuwa dal daga Baban Amarya.

Yayin da Amarya ta samu kyautar doki fari tas daga Hakami.

Ammy biyawa amarya da ango Umra ta yi.

Haka dai aka yi ta kyauta ta bajinta har zuwa karfe biyu na rana inda yan biki suka fara tattare kayansu domin komawa gida.

Motar Hakimi da ta mijin Aunty Lami su Aunty Hauwa ne da yara, motar Mustapha kuwa kyaututtuka biki ne da sauran tarkace, sai Fatima da ke gaba.

Suna gab shiga da Sandamu wayar Fatima da ke caji a gaban motar Mustapha ta shiga vibration alamun kira.

Shi ne ya miko mata. Ganin Ashir abokin aikinta ya sanya ta saurin dagawa.

Bayan sun gaisa ne ya ce “Ana ta neman ki tun dazu wayar ba ta zuwa.”

Ta amsa shi da “Ina hanya ne, kila shi ya sa ba ta shiga.”

Da sauri ya ce “Za ki shigo Katsinan ne?”

“A’a zan fita ne. Akwai wani abu ne?”

Daga can ya ce “Idan ba a yi nisa ba, ki sauka ki dawo, saboda yanzu haka dai offernki tana teburin MD kuma gobe ake son ganin ki.”

Daga yadda ta zabura ne ya sa Mustapha kallon ta, cike da doki ta ce “Really?”

“Of course!” Ashir ya tabbatar mata cikin dariya.

“OH my God! Alhamdulillahi. Thank you so much Ashir. . I really happy. In sha Allah zan juyo gobe.”

Daga can daya bangaren Ashir ya ce “Allah Ya kai mu. Na taya ki murna.”

“Na gode.” ta fada cikin muryar farin cikin da take ciki.

Ta kalli Mustapha wanda ya kafe ta da ido, yana yi mata wani kallo mai kama da harara.

Ba ta damu da kallon ba ta ce “Ya Mustapha na samu offer.”

“Shi ne kike ta wani kashe murya.”

Cike da mamaki ta ce “Kashe murya kuma” sai kuma ta kwashe da dariya, yayin da take jin motar ba ta sauri. Ta kosa ta isa gida ta fesawa kowa wannan abun farin ciki. Ba ta kara bi ta kan Mustapha ba, wanda ya yi fuska kamar baya kallon yanayin farin cikin da take ciki. Dama tun da ta fada mishi period take yake ta kumburi, kamar ita ta ce period din ya zo.

Ko gama parking din bai yi ba, ta balle kofar ta fita aguje zuwa cikin gida.

Ya bi ta da kallon mamaki, yadda ba ta jin nauyin jikinta, har yanzu ita kuruciya ba ta sake ta ba.

Duk da sauran basu kara so ba, ba ta damu ba, dama burinta kawai ta fadawa Mama.

Kasancewar kaya ne kawai aka lodo a motar Mustaphan, su ya rika dakkowa yana shigowa dasu.

Lokacin da ya shigo Fatima mamutse take jikin Mama tana tsallen murna, cikin zallar farin ciki take shaida mata ta samu offer.

Mama ta ji dadin labarin fiye da zaton Fatima, lokacin da sauran suka iso aka shaida musu abin da ya faru kowa sai murna.

Murnar kam sai aka rasa wacce za a yi, ga na gama biki lafiya, ga murnar samun offern Fatima.

Safiyar Litinin da safe Mustapha ya kuma juyawa da Fatima zuwa Katsina…

<< Daga Karshe 62Daga Karshe 64 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×