Skip to content
Part 64 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Kai tsaye gidan radion suka nufa, kasancewarta yar gida, ba ta sha wahala ba wajen ganin MD, bayan yan gaishe – gaishe ne da gabatarwa, MD din ya shiga bayyana mishi kwazon Fatima da yadda take mayar da hankali a wajen aikin, wanda yana daya daga cikin dalilin da ya sa ya samar mata offer a matsayin (awaiting result).

Mustapha ya yi mishi godiya sosai hade da yaba kokarinshi na yadda yake gabatar da ayyukan.

Sannan MD ya sanarwa Mustapha akwai gida da zasu ba Fatiman idan yana bukata, idan kuma zai kama mata haya ne to ba, damuwa, saboda yanayin aikin dole sai ta na kusa.

Mustapha ya bukaci ganin gidan First, dalilin da ya sa manager yi musu rakiya da kansa har zuwa wajen gidajen ma’aikatan.

Gidaje ne masu kyau da tsari, an, tanadar musu komai na daga ruwa da hasken lantarki.

Babban falo guda daya wanda yake dauke da 2 single room da toilet a cikin ko wanne. Daya bangaren kuma room and parlor ne shi ma da toilet a ciki.

Akwai kofar da ta fita waje, wacce a nan za ka samu kitchen, kuma daga kitchen akwai kofar da, za ta sadaka da waje gaba daya.

Mustapha ya yaba da ginin sannan ya ce zasu yi shawara in sha Allah.

A nan MD yake sanar mishi next Monday ya kamata Fatima ta fara aiki.

Mustapha ya tabbatar mishi da sha Allah ba za a samu matsala ba.

Daga nan makaranta suka wuce kan maganar result, inda aka yi ta, kadasu daga wannan office zuwa wannan, dalilin da ya gajiyar dasu tubis.

Karfe shidda na yamma suka fito daga School, sun dai kammala komai, result din ne dai bai zo hannu ba, sun ce sai Laraba kasancewar basu fara saki ba.

Duk da Fatiman Allah Ya taimaketa ba c/o hakan bai hana Mustapha kashe kudin sama da 20k ba.

Ganin ya dauki hanyar hotel ne ta ce “Ya Mustapha me zai hana mu je gidan Aunty Lami mu kwana, kashe kudin zai yi yawa, kuma ka san ma ni ba sallah nake yi ba.”

Kamar kuwa ta san cike yake da haushin rashin sallahr nata, yadda take ta ƴan tsalle-tsalle a kwanakin nan sosai yake son kasancewa da ita. Amma abu ya zo ya shata mishi lafiya.

Ganin bai tanka ba, sai ta kuma kwantar da murya ta ce” Don Allah Ya Mustapha mu koma gidan Aunty Lami.”

Ya Kalle ta da idanuwan da suka kasa boye halin da yake ciki tare da fadin” Kar ki damu. “Daga haka bai kara cewa komai ba, ita ma kama bakinta ta yi wajen yin shiru.

Bayan sun isa shi ya fara yin wanka hade da yin sallahr magriba wacce ita ce dama bai yi ba, sannan ya fita, ita ma wankan ta shiga hade da gyara jikinta.

Ba jimawa ya dawo dauke da manyan ledoji guda biyu, da sauri ta amsa hade da ajiye tana fitar da abubuwan da ke ciki. Leda ta farko fruits ne, minerals da kuma ruwa.

Dayar ledar kuma abinci ne sai gasasshiyar kaza.

Suna cin abinci hade tattaunawa a kan gidan da MD ya nuna musu, Fatima dai ta fi karkata a kan ta zauna a can, ko ba komai za a rage dawainiyar biyan haya. Shi ya sa ta mayar da hankalinta wajen convincing din shi, har kuma ta samu shawo kan nasa da kyar.

Yadda ta ga yana ta kumburi ne ya sanyata bin hanyar da ta tabbatar za ta saukar da fushin na shi. Kuma sosai ta yi nasara don ta yi abin da ya rage mishi kewar tata.

Da safe dai ta kuma kwantar mishi da hankali sannan suka juyo zuwa Sandamu. Sai da suka biya Daura School of Health suka siyawa Ummi form suka cika sannan suka wuto.

Kai tsaye gidan Mama ya aje ta, shi kuma ya wuce gida, don bacci yake ji.

Mama ce kawai a gidan sai Beauty da Maamah. Sarakan fada, basu ɓatawa basu shiryawa, gasu nan kamar tagwaye, tsawo daya, yanayin jiki daya, hasken fatar ne kawai ya bambanta da sumar kai. Duk da Maamah ta fi kowace Beauty rashin ji nesa ba kusa ba

Bayan gaisuwa da tambayarsu yadda suka dawo sai Maman ta ce “Ina fatan dai babu wata matsala?”

Girgiza kai Fatima ta yi daga kwancen da take ta ce “Ba sosai ba, maganar result gobe ne aka ce in je in karɓa, sannan can wurin aikin sun ba ni gida.”

“To Ma Sha Allah. Abu ya yi kyau, Allah Ya taimaka.

” Amin. ” cewar Fatima lokaci daya kuma ta mike zaune tare da fadin” Hidimomin sun yi yawa Mama, na rasa ta ina za a bullo musu, ba kudi, jiya Ya, Mustapha har tausayi ya ba ni, wlh ya kashe kudi sun kusa dubu hamsin. “

Ido Mama ta fitar waje” Dubu hamsin? “
” Wlh. Ga shi ba a gama ba, gidan dasu ka ba ni baya bukatar wani gyara, saboda akwai tiles a ciki, amma dole akwai bukatar kayan amfanin yau da kullum, ni dai na cewa na yi, gobe zan je Abuja a kwaso kayan a dawo dasu Katsina tun da ba zama zan yi a can ba. Saboda sayen wasu kaya a yanzu da aka sha hidimar ne abu ne da ba zai yiwu ba. “

Cikin jinjina kai Mama ta ce” Gaskiya kam an sha hidima an kishi kudi. Kuma ni maganar kayanki na Abuja tuni muka yi ta da ƴan’uwanki. Kin ga wadannan kayan gadon da kujerun za a mayar dasu kamfanin da aka sawo su ne su saya. Idan za ki tare sabon gidan ki a cika a yi miki wasu. Idan ki kwaso yanzu, kuka sukurkucesu, idan kuma za ki koma sabon gidan ya za a yi? Komai fa kara kudi yake Fatima, kuma kowa nauyi kara hawa kansa yake yi. “

Shiru Fatima ta yi cikin nazarin kalaman Mama. Lallai kam idan za ta koma sabon gida tana bukatar sabbin kaya, kuma ba ta san yadda lokacin zai zo ba, akwai bukatar idan mutum ya hangi baya ya hangi gaba. Ta sauke ajiyar zuciya da fadin” To yanzu ya za a yi? Mama ba na son in dorawa Mustapha wata hidima kuma, saboda yana kokari, ya fara ba ni tausayi. “

“Gaskiya kam yana kokari. Sai dai mu yi masa addu’ar Allah Ya kara mishi budi na alkairi. Kuma kin ga ƴan’uwankin nan sun sha hidima, kin san dai lefen nan kaf su suka hada. Shi ma Jamil din ya, hidimtu, saboda ba karamin kudi ya kashe ba, ban da ma an taimake shi da lefen kila sai dai a daga bikin.”

“Dama ni cikinsu babu wanda zan dorawa yin wani abu, wanda suka yi min ma na gode, saboda ba zan iya saka musu ba. Su suka gyara min kitchen dina na Abuja me ye basu zuba min ba? Sannan hidimar makarantata 80% sune suka min.”

Cikin mutuwar jiki Fatima ta yi maganar.

Kasalance Mama ta ce” Kina da fridge a nan, ga inji, sai atl tafi dasu can Katsinan. Sai ki duba kayan ma’aikaci ki tsuttsinci wasu. Sai ku tafi Abujan gobe, ki kara tsinto yan na’urorin girki na zamani a kitchen din naki, da duk abin da ki ke gani za ki iya dauka. Wannan ragowar san naki da ya rage, za a sayar da shi, a siya miki ko katifu ne. Ai amfanin kiwon kenan.”

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce” Amma Mama don Allah ya zama sirri a tsakaninmu. Yanzu fa ba ni da komai kenan, komai nawa ina ta siyarwa, sannan ba na mayarwa. “

Yadda ta karasa maganar sai ta ba Mama tausayi, cikin sigar kwantar mata da hankali ta ce” To me ye abun damuwa, ba fa a banza kike kashe kudin ba, kuma sha Allah hanyar mayar dasu ta samu, in Allah Ya yarda za ki samu riba a kan duk abin da kika rasa. “

“To Allah Ya sa. “

“Amin. ” Mama ta ce, kafin ta dora da” Sai ki je ki kintsa duk abin da za ki tafi da shi din, ku fara biyawa can Katsina, ki kira Zainab ku hadu, ta ga gidan, ni kuma zan sanya ta cigita mana abin da kike bukata, sai a tura mata kudin ta siya miki.”

“To. ” cewar Fatima lokacin da take mikewa tsaye.

Ci gaba da kwantar mata da hankali Mama ta yi, ganin har zuwa lokacin ba ta warware ba, da alama siyar da San ya taba ta.

Ranar Laraba haka suka kuma juyawa Katsina. A zuciyarta take fadin neman halak akwai wuya, amma a cikin satin nan tana yawatuwa, kila ma sai ta yi Zazzabi.

Makaranta suka fara shiga, zuwa 11am suka fito dauke da result din Fatima ba dai ta zama overall ba, amma kam result din ya yi kyan da ba za ta ji kunyar nuna shi a ko ina ba.

Gidan da aka ba ta suka wuce, inda Zainab ke jiran isowarsu.

Babu wani abu da suka yi wa gidan, kayan kawai suka sauke, hade da ba Zainab key din, suka dauki hanyar Abuja.

Lokacin da suka isa Abuja karfe shidda na yamma, amma basu karasa gida ba sai ana sallahr isha’i saboda cunkuso.

Gida kam tsab suka taras da shi, Blessing akwai kalkali da tsabta, hatta dakin Fatima a gyare yake tsab.

Haka tai ta hidima dasu, musamman Fatima, sai da ta ga ta tanadar mata duk abin da za ta bukata sannan ta koma wurin Mustapha.

Daga nan Fatima ba ta kara jin duriyar Mustapha ba bare ta Blessing.

Sai da yara tai ta hidimominta har suka yi bacci.

Wanshekare bayan Blessing ta gama hidima da Mustapha ya wuce wurin aiki, wurin Fatima ta dawo, hade da taimaka mata wajen hada kaya. Wani abun ma Blessing din ce ke ba ta shawarar ta dauka zai yi mata amfani kaza.

Haka suka wuni aiki, ga na abinci ga na tattare kaya.

Zuwa yamma sun gama tattare duk abin da zasu tafi da shi sun yi parking din shi wuri daya.

Safiyar juma’a misalin karfe takwas na safe ake ta rikici da Ihsan ita for sai ta bi Fatima, abun da ya ba kowa mamaki, kasancewar ba wani Sanin Fatiman ta yi sosai ba.

Kukan da take yi ne ya sa Blessing ta ce a tafi da ita, idan Mustapha zai dawo sai su dawo tare.

Haka Fatima ta rungumota zuwa Katsina.

Biyu saura Mustapha ya Parker a sabon gidan, inda ya samu Zainab da wasu masu taimaka mata sun sha aiki sosai.

Abin da ya ba Fatima mamaki shi ne har da Umaima.

Cikin Tsokana Mustapha ya ce “Waye ya fito da amaryar sati daya waje?”

Duk suka yi dariya in ka dauke Umaima da ta sunne kai cike da kunya.

Ganin suna da yawa sai Mustapha ya fice ya basu wuri. Ya dai shaidawa Fatima zai je masallaci, amma zuwa biyar na yamma su yi kokarin kammala komai su wuce Sandamu.

Cike da sha’awa Fatima ke kallon yadda gidan ya yi kyau.

Babu wani tarkace da aka zuba, amma sosai ya yi kyau.

A babban falon da ya hada dakunan gidan babu komai sai manyan labulaye masu kyan gaske coffee color.

Sai stant mai kyau dauke da madaiciyar TV plasma

Can room and parlorn da suka zabarwa Fatiman kuwa, a falon ma ba komai sai labulayen maroon color masu kyau, center carpet da kuma tuntaye irin na gidan sarauta. Da alama Zainab ce ta kwaso mata su, saboda an yi wa Zainab din su da yawa, kuma ba ta faye amfani dasu ba.

A bedroom ne aka saka gado hade da mirror, dama akwai drower ta jikin bango.

Kitchen kam ya fi ko ina haduwa, saboda shi kam ya samu ku san komai musamman da aka zuba mishi kayan da suka taho dasu daga Abuja.

Single room daya ne kawai ya samu katifa da labulaye, dayan kam ba a sanya mishi komai ba.

Bayan sun gama zagaye wurin ne Zainab ta ce tafiya za ta yi, saboda mutanen da ta zo tasu, sosai Fatima ta yi musu godiya lokacin da zasu wuce.

Ya rage daga Fatima, Umaima da kuma Ihsan wacce ke ta tsalle-tsallenta

Umaima ce ta fara cewa “Yarinyar nan ta burge ni, kalli yadda ta saki jiki.”

Kallon inda Ihsan din take Fatima ta yi hade da fadin “Ni ma ban yi tunanin za ta saki jiki haka ba. Wai don Allah waye ya ce ki fito, yau fa duka satinki daya shi ne har kin fara fita. Amaren zamani.”

Tabe baki Umaima ta yi kafin ta ce “Ina ruwanki, ni haushinki ma nake ji, wai ko waya Fatima, sai dai in ji an ce kin shigo Katsina kin fita.”

Cikin dariya Fatima ta ce “Ina ni ina damunki a waya kina shan amarcinki, rufa min asiri.”

Harara Umaima ta aika mata kafin ta ce “Ki dai yadda kawai ba ka kyauta ba.”

“To na yarda, ki yi hak’uri kuma.”

“Na yi. Next week zamu je Sandamu, kin ji yadda nake jin dadi kuwa?”

Yadda ta karasa maganar cike da nishadi ne ya sanya Fatima dariya, cikin dariyar ta ce “Wai tsakanin Ya Jamil din da kuma ki jiki a Sandamu da auranshi wanne kika fi so ne?”

Sai da ta juya ido kafin ta ce “Duka. Amma yana matukar burge ni, in wani ganku kun cika gida, kuma duk kuna da dangantaka, kai yana min kyau. Yauwa zan dakko Maamah idan na je.”

“To ki ce za a yi wa Mama ɗanɗas kenan, ni ma zan dakko su Beauty dasu Hassan idan zan taho.”

“Gidan Mama ba zai zauna shiru ba ai, jikokin da muka baro mata sun fi wadanda muka dakko yawa.”

“Gaskiya kam.” Fatima ta amsa ta.

Haka suka ci gaba da hira, sai da aka yi la’asar sannan Umaima ta tafi, zuwa lokacin tuni sun kara kintsa gidan sosai ya yi kyau.

Biyar saura Mustapha ya shigo, lokacin Ihsan kwance take tana bacci, Fatima kuma chat take yi da Zainab.

Bayan ya zauna ne ya ce “Gidan nan ya burge ni gaskiya, ya yi kyau sosai. Mata akwai ku da dabara, cikin kankanen lokaci kun gyara shi. Dama ina ta tunanin ta ina za a fara.”

Murmushi ta yi kafin ta ce “Ni ma ya min kyau sosai, ban yi tunanin zai yi kyau haka ba.”

Mikewa ya yi zuwa bisa gadon ya kwanta, rabin kafafunsa a kasa yana fadin “Gaskiya a nan zan ci amarcina, gobe idan Allah Ya kai mu mun tafi Sandamun.”

Baki bude ta ce “dazun na fa na yi wankan”

“To me kike tsoro. Ba kin yi planning ba, koma ba ki yi ba fa, yanzu ba karatu kike ba bare ki rika shata min layi atoh. Yadda na ga dama yanzu haka zan yi, ba kwaɓa ba harara.”

Shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba.

“idan za ki magantu kawai ki magantu saboda duk bashin da kika ci yau sai kin biyashi, tsoho da sabo.”

Cikin dariya ta ce “Kai ne fa, ba wani aka canjo ba Ya Mustapha, na rigingine ai ba bakon farin wata ba ne.”

Ya dago da sauri, hakan ya sa ta mike zuwa babban falon tana dariya.

Haka suka yi kwanan farin ciki, safiyar Asabar suka dauki hanyar Sandamu.

A can ma Fatima ba ta zauna ba, tun da da safe za ta wuce. Ummi ce ta zo taya ta shirya kaya.

Sosai Ummi ke mamakin yadda Ihsan ta saki jiki, musamman da ta samu, Zarah, Maamah da kuma Beauty. Kamar dama ta san su, haka ta shige cikinsu suna ta wasa.

Sai magariba Ummi ta tafi gida.

Duk yadda ta so yin bacci da dare sai ta kasa, wata irin kewa take ji ta gida na shigarta.

Ita kadai ta san irin kaunar da take yi wa garin Sandamu, duk inda ta je, sai ta ji dai ba kamar Sandamu ba.

Kan dole za ta yi nesa da gida, ji take yi kamar ta ce ta fasa aikin, ta dawo gida ta nemi teaching kamar yadda sauran ƴan’uwanta suke yi.

Amma rayuwa nesa dasu akwai kalubale, sai ta fi wata daya ba ta yi wa yaranta wanka ba, kuma basu taba kwana ba a yi musu wankan ba. Idan ta gaji da zama gida, ta je gidan Mama ko gidan yayyunta maza ko mata. Amma ace yanzu ta yi nesa dasu, sai dai ta zo kwana daya ko biyu ta koma, anya za ta iya kuwa?

Haka ta ku san shafe darenta da wannan tunanin, shi ya sa ta tashi da ciwon kai, komai jiki a mace take yin sa.

Sai da Mustapha ya sa hannu sannan ta gama komai, misalin karfe daya na rana ya sauke ta kofar gidan Mama, da sauran yaran, shi kuma ya tafi masallaci.

Lokacin da ta shiga Maman sallah take yi, ita ma alwalar ta yi ta kabbara sallah.

Bayan ta idar ne ta gaishe da Mama.

Mama ta amsa tare da fadin “Har an fito?”

Kai ta jinjina ba tare da ta amsa ba.

Mama ta mayar da hankalinta sosai a kanta tana fadin “akwai wani abu ne? Na ga kamar ba ki da kuzari.”

Dama kamar jira take yi, hawayen da take rikewa ya sakko mata.

“To me ye kuma abun kuka, ke da ya kamata ki yi farin ciki.”

Uffan ba ta ce ba, illa ci gaba da share hawayenta da ta yi.

Cikin karfafa mata giwa Mama ta ce “Ba kuka za ki yi ba, farin ciki ya kamata ki yi, saboda za ki taka matakin da ba ki taba tsammanin takawa ba. Nasihata gare ki anan shi ne, ki zama mai gaskiya, a ko ina a same ki mai gaskiya da rikon amana, ki ji tsoron Allah a wajen aikin ki.”

Mama ta dan tsagaita tana kallon yadda take share hawayenta.

“Kin san dai yanzu inda za ki, ba makaranta ba ce, ba, kuma Sandamu ba, sannan za ki kuma dora rayuwarki da wadanda ba ki sani ba, ba kuma ki san halinsu ba. Don Allah ki zauna da kowa da zuciya daya, da kuma gaskiya, kar ki sake ki cuci abokan zamanki.

Sannan kina da aure ki rike mutumcinki da na auranki, kada ki bayar da wata kofa da za ta haddasa zubewar mutumcinki, na mijinki, na yaranki, iyayenki, ƴan’uwanki da duk wasu masoyanki.

Ga yara nan, yanzu tarbiyarsu ta dawo hannunki, kuma kullum tarbiyar kara wahala take yi, don Allah kar ki bari aiki ya dauke miki hankali, ki manta da tarbiyar yaranki.”

Zuwa lokacin Fatima kuka take yi sosai, a haka Mustapha ya shigo ya same ta, yayin da ƴan’uwanta ma ke ta shigowa don yi mata sallama.

Zuwa karfe biyu suka daga, Fatima kuka take yi sosai, kamar wata amaryar da za a kai gidan miji.

Ba ita kadai ba, su Aunty Sadiya ma sai da aka matse, Mama ma sai da ta share hawayenta. Sai take jin kamar Sandamun ba kowa. Fatima na daya daga cikin irin mutanen nan da idan bassa wuri, wurin baya dadi. Sosai ta ji babu dadi a tafiyarta, sai dai tana yi mata fatan nasara.

Motar shiru, don hatta yaran sun nutsu basu da kuzari.

Ihsan dama tana lafe jikin Fatima, ta hana Beauty ta rabe ta, don ko hannu Beauty ta dora a jikin Fatima sai Ihsan ta cire shi, ta, kuma ture ta

“Kin kashe ma yarana jiki fa.” karon farko da Mustapha ya yanke shirun da ke cikin motar.

Ta juya tana da kallon yadda suka yi zuru-zuru, tun ba Beauty ba da Ihsan ke hana ta rawar gaban hantsi.

Murmushi ta yi hade da yafito Beautyn da hannu, kamar jira take dama, ta sakko daga kan seat, Fatima ta dakko dakyar, ta ajiye ta gefen ta.

Kafin ta fitar da sweet duk ta mika musu, sai ko suka fara warwarewa.

A hankali Mustapha ke jan ta da hira, har ta dan warware.

Karfe shidda na yamma suka isa Katsina.

Dama gidan ba wani datti ya yi ba, don haka gyaran babu yawa. Abinci kuwa Mustapha ya yo musu take away.

Kamar yadda aka sanar mata karfe takwas na safe aka son ganinta a office takwas din kuwa a, office din ta yi mata, yayin da ta bar Mustapha da kuma yara a gida.

Duk da ba bakuwa ba ce a wurin, ranar kam komai bako ya zame mata, a matsayinta na sabuwar ma’aikaciya wacce ke da office mai zaman kansa.

A ranar ne kuma ta yi summitting na duk wasu takardunta, ciki har da result dinta.

Ba ta dawo gidan ba sai uku da wani abu, ta ji dadin yadda ta samu komai tsab, gidan da kuma yaran, uwa uba ga abinci da Mustapha ya girka.

Da dare ne suna kwance ya ce “Ya za a bullo ma wannan sabon al’amarinne, kin ga ni dai Wednesday zan wuce, ke kuma ga yanayin yadda aikinki yake, ga kuma yara.”

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce “Ba tun yanzu nake wannan tunanin ba, ban san ya zan bullowa abun ba.”

Bayan ya yi dogon nazari ya ce “Makaranta za a sanya su duka, har da Beauty din, ai ta gota shekara uku, kuma kin ga tana da girma. A sanya su a school, irin wacce tun safen nan sai yamma. Kafin a nemo wata mafitar.”

Shiru ta yi cikin nazarin maganarsa kafin ta ce “2nd term fa ake, kuma shi ma term din ya yi nisa.”

“To ya zamu yi? Akwai wata mafitar ne? Sannan ki sanya Aunty Lami ta binciko miki yarinyar da za ta dan rika taimakonki.”

Gwauron numfashi ta sauke hade da fadin “Zan sanya a bincika makarantar da kuma yar aikin.”

Haka suka yi ta tattauna yadda za ta rayu cikin bakon yanayin da ta tsinci kanta a ciki kafin ta saba.

Ranar talata ba ta fita ba sai 12pm wannan ya ba ta damar shiga gidajen kusa da ita, ta gabatar musu da kanta, suka gaisa a mutumce, kafin ta fito ta shiga kintsa gidan da kuma yaran.

Yayin da a bangare daya ta sanya ake bincika mata makaranta mai kyau.

Safiyar Laraba Mustapha ya wuce da Ihsan, duk da akwai yara sai take jin gidan ya yi mata shiru, ƴan kwanakin ta saba da yarinyar sosai. Ihsan irin ta yau yarannan ne da idan suna wuri to basu zama shiru, ta tsokani wancan ta tsokani wancan.

Babban abin da ke burge ta da ita, yadda ba ta barin kowa ya rabe ta sai ita, ko shigowa ta yi taga Beauty a jikinta, sai ta ture ta koda ita ba za ta hau ba. Hakan kan sanya Fatima cikin nishadi. Wani lokaci har tsokanarta take yi, ta dora wani yaron a kan cinyarta.

Ba ta fahimci Mustapha ya kange mata abubuwa da yawa ba sai da ya tafi, inda Allah Ya taimaketa ma da aikinta duk afternoon ne a wannan watan. Dole ta samarwa yaran emergency islamiyar 2-6pm. Kafin ta tafi take shiryasu da abincinsu, ta kaisu gidan makociyarta Maman Farhan, idan 2pm ta yi sai su tafi da yaranta makaranta.

A duniya komai akwai challenge, cikin sati biyu har ramewa ta yi, saboda babu isasshen bacci ga aiki ga hayaniya da yara.

Misalin karfe biyu zaune take cikin office din ta, laptop din ta a gabanta, inda take editing na wata talla da aka kawo musu. Lokaci daya kuma tana jiran wasu baki da suka gayyato don tattaunawa dasu a kan wani shiri da ake gabatarwa.

Karamar wayarta da ke gefe ta shiga vibration alamun kira na shigowa.

Ganin sunan Maman Ihsan ne ke yawo ta dauka a nutse hade da manna wayar a kunnenta.

Bayan sun gaisa hade da tambayar yara Blessing ta ce “Yarinyarki dai tana nan kullum sabuwar rigima ita a kawo ta wurin Beauty, har da su zazzabi.”

“Wajen sati uku har yanzu ba ta manta ba wai?” Fatima ta tambaya da alamun mamaki a muryarta.

“Ba ta manta ba, duk lokacin da Dadyn Hana zai fita ta yi ta kuka kenan sai ta bi shi wurin Beauty.”

Murmushi mai sauti Fatima ta yi kafin ta ce “A nan din ma ku san kullum sai su Hassan sun ce Momy yaushe Ihsan za ta dawo mu rika zuwa islamiya.”

Blessing ma murmushin ta yi hade da fadin “to in sha Allah muna nan za mu so muku weekend ai.”

Cikin farin ciki Fatima ta ce “Muna jiran ku, Allah Ya kawo ku lafiya.”

“Amin.” Blessing ta amsa, kafin suka yi sallama.

Kasancewar bakin da suka yi, yau ba ta dawo gida ba sai biyar saura.

Kai tsaye gidan Maman Farhan ta shiga don karbar key din gidanta.

Ga mamakinta iske Umaima ta yi zaune suna ta hira da Maman Farhan din.

Cike da mamaki ta ce “Aunty Umai Barka da zuwa, yaushe kika zo? Dama na ga mota a waje kamar ta ki ta da, sai dai na ga wannan akwai canje -canje har da No mota na ga a canja. “

Sai da Umaima ta aika mata da harara sannan ta ce .”ban sani ba.”

Cikin dariya Fatima ta ce “Yi hak’uri Umaimancy, amarya Ya Jamil daga ke an rufe kofa.”

Wata hararar ta kuma aika mata.

Zama ta yi kusa da Umaiman suna gaisawa da Maman Farhan wacce ke ta dariyar diramar tasu. Cikin dariyar suka gaisa hade da tambayarta yadda gidan ya wuni.

Maman Farhan ta amsa mata da komai lafiya, hade da mika mata key din gidan.

Fatima ta amsa hade da yi wa Maman Farhan godiyar kula da yara da take bar mata, kafin suka runguda zuwa gida.

Bayan sun nutsu ne Umaima ta ce “Almost sati uku da tarewarki kin kasa zuwa gidana, tun biki fa, wlh kin ban mamaki, kuma zan yi fushi.”

Siririn murmushi Fatima ta yi kafin ta ce “Don Allah ku yi min uzuri, ni kadai na san me nake fuskanta, amma abun isn’t easy wlh, mijinki bai yi miki bayani ba, ranar da ya zo nan ai na fada mishi komai, ina son fita, wlh amma ba lokaci, da weekend ne kawai nake samun time shi ma sai na shiga islamiya, kuma wlh ina jin dadin islamiyar ba na son yin fashi. 9-12pm ne, ina dawowa in fada kitchen, in gama abinci in kaiwa yara tun da su sai 6pm ake tashinsu. Da yamma kuma zan yi tsare-tsaren aikin da zan gabatar ne. Ko editing, ko dora murya. Amma don Allah ki yi hak’uri zan zo in sha Allah. “

Tabe baki Umaima ta yi kafin ta ce” Sannu agogo sarkin aiki. “

“Hmm! Ba za ki gane ba. “

“Yaushe ko zan gane ba a yi min yadda zan gane ba. “
“To ni dai a yi min afuwa Auntynmu. “
Cikin dariya Fatima ta yi maganar.

“Wannan weekend din dai zan je Sandamu in sha Allah.”

Cikin dariya Fatima ta ce “Ni wlh har na gaji da jin wannan weekend din zan je Sandamu, wannan weekend din zan je Sandamu. kuma har yanzu ba ki je ba.”

Sai da ta dan bata rai sannan ta ce “Yayanki ne ya hana, amma wannan karon kam sha Allah zan je.”

“To Allah Ya amince. Ni ma na ji kamar in bi ku.”

“ki zo mu tafi kawai.”

Girgiza kai Fatima ta yi tana fadin “ina da baki. Maman Ihsan ce za ta zo.”

“To! Allah Ya kawo ta. Dadyn Beauty kam shiru.”

Yar karamar dariya Fatima ta yi “Wlh shi ma aikin ne ya masa yawa, seminar suke yi, kamar zai samu promotion ne.”

“Kai ma sha Allah. Allah ya taimaka.”

“Amin.” Fatima ta amsa.

Haka suka ci gaba da hira yayin da Umaima ke taya Fatima aikin abincin dare.

Sun idar da sallahr magariba ne suka rika jin horn a kofar gidan.

Cike da mamaki Fatima ta ce “Kamar Ya Jamil. Ba na ga kin zo da mota ba. Ko tasa ki gaba zai yi? Sannunku masoya.”

Murmushi Umaima ta yi kafin ta ce “Motar ai kawo miki na yi.”

Cikin zaro ido Fatima ta ce “Kamar ya kika kawo min?”

“Kada ki manta yadda ake tukin, kin san idan mutum yana abu yau da kullum ya fi kwarewa. Ga ta nan na bar miki gado, ke ma ki bar wa Hana, Hana ta bar wa ƴarta ko danta, daga karshe sai mu sakata a gidan tarihi na Sandamu.”

Duk suka yi dariya kafin Fatima ta ce” Wai da gaske kike? “

Key din motar ta ajiye kan TV stand tana fadin” Mijina baya son jira, yanzu za ki ga ya hade gabas da yamma. “ta karasa maganar tana fita da dan gudu jin Jamil na kara wani horn din.

Fatima da ta yi tsaye a tsakiyar dakin cike da mamakin kyautar ta zabura aguje zuwa waje jin kamar Jamil na kokarin tafiya.

Daidai Jamil na yin reverse, ganinta ya sanya shi dakatawa.

Ta leka cikin motar tare da fadin “Ina wuni Ya Jamil.” ya amsa hade da tambayarta yanayin aiki.
Ta amsa mishi da Alhamdulillahi.

Tana kokarin fara godiya ne, Umaima ta yi saurin katse ta da fadin “Don Allah ni dai kar ki ce komai. Abban Maamah mu je.”

Ya murza key din motar cikin kwarewa ya fice.

Fatima da ta koma daki ba ta san lokacin da ta kai goshinta kasa ba, ta godewa Allah. Kafin ta dago ita kadai a daki tai ta tsallen murna, yau ga ta da motar kanta, ikon Allah.

Daga bisani ta rika kiran ƴan’uwa tana shaida musu cike da farin ciki.

<< Daga Karshe 63Daga Karshe 65 >>

1 thought on “Daga Karshe 64”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×