Zainab ce ta fara shigowa gidan, idon Mama da kyar a kofar gida, ganinta ya sa ta mike.
"Ina kika bar Fatima kuma ko har yanzu ba a gama kunshin ba?"
Ba ta amsa tambayar ba, sai ma shigewa daki ta ta yi.
"Ina tambaya kina wucewa zoƙal- zoƙal kin shige mun daki kamar dakinki bayan ba ki amsa mun tambayata ba."
"Kawu Jamil ne ya barota a can."
"Me ya sa zai bar ta? Ai ba ke na ce ya je ya dakko ba, yarinyata na ce ya dakko mun. Amma ya je dakko mun wannan abu. . .