Skip to content
Part 9 of 65 in the Series Daga Karshe by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Ranar daurin aure kuwa, hatta Fatima da kwalliya ba ta dame ta ba, wannan karon dai ta ɓata lokaci wajen tsara kwalliyar da ta dace da fuskarta.

Dinkin riga da zane ne na farin lace, ba a yi ma rigar wata kwalliya ba, single take mai dauke dagoyen hannu.

Dalilin da ya sa kenan daga Fatima har Zainab suka yi shiga irin ta yoruba.

Ma’ana suka daura zanen a saman rigar, ashobe mai ruwan toka aka yi masu kyakkyawan goggoro da shi. Asalin dankwalin kuma suka daura shi a saman kugunsu.

Farfajiyar gidan hakimin a cike take taf da mutane, musamman matasa, yammata da yara.

Yayin da Dj yake ta sakin sauti a kokarin shi na nunawa mutane lokacin fara partyn fa ya yi.

Fatima zaune a kan kujera tana kallon masu shiga da masu fita, da kuma yaran da ke taka rawa Kala-kala, wasu su ba ta dariya wasu su burge ta.

A daidai lokacin Jamil ya shigo, sanye cikin fara Kal din t-shirt cotton mai guntun hannu hade da normal wandon jeans.

Idon shi ya dora kan ta, kafin ya janye a hankali, zuciyarsa na saka mishi, ya tabbatar mata da abin ke cikin zuciyarsa a yau.

Ko ba komai dai zai kwashe kaso 70 na abin da ke cikin zuciyarta gami da shi. Ya sauke ajiyar zuciya kadan, tare da waiga ko wane gefe na shi tamkar mai neman wani abu. Kafin daga bisani ya tunkari in da take zaune hankalinta akan Dj, don sam ba ta ga shigowarsa ba ma.

Tun kafin ya karaso gurinta, ya ji duk wasu kalmomi da ya tanada ya fada mata sun bata.

Ya rika ganin abin da yake shirin yi tamkar yada girmanshi ne. Kawai ya rabu da ita ba amfanin yin bayani don kare kanshi, lokaci yana zuwa da za ta karyata kanta.

Da wannan tunanin ya karasa kujerar nesa da ita ya zauna, da alama ma ba ta gan shi ba, don ko sau daya ba ta kalli bangaren da yake ba.

Kamar mintuna 30 Mustafa ya fito, yanzu ya canja kayansu zuwa kananan kaya, bakin wandon jeans da riga T-shirt sky blue me guntun hannu.

Kamshin turarenshi ne ya sanyata juyowa.

“Ca nake za ka kwanta ka huta ne?”

“Manta kawai, ko na kwanta za a tashe ni, kuma zan je gida in duba Inna ita ma ba ta ji dadi ba.”

“Har yanzu jikin nata? Ranar da dare su Aunty Hauwa da Aunty A’i sun biyo gidanmu wai sun dawo daga duba jikin nata, na so in je hidimar bikin nan ta dauke mun hankali, amma mu tafi yanzu mana, kafin a fara party dai ai mun dawo. Don so nike a fara a gabana, in kama kujerar gaba.”

“Wai ke ba dalibar Islamiya ba ce?”

“Yo bikin gidanmu ne fa.”

“Na gidan naku, idan na ganki a gun party nan sai ranki ya baci.”

“Kai! Haba!! Ai kaima ka san ba zai yiwu ba, ni fa ruwa biyu ce yauwa, ba gabadayana ne yar Islamiya ba, ina dan rakashewa watarana. Ba ka gani ma Islamiyar yau in je gobe ba zan je ba. Har yau na kasa saukewa.”

Wani lokaci maganar Fatima dariya kuka ce, dalilin da ya hana shi ba ta amsa kenan, sai ma ya canja maganar, “Idan kin shirya mu je.”

Jamil da ke zaune yana kallonsu har suka fice, kanshi ya hake kan majinginar kujerar.

Ya kasa fassara halin da yake ciki, amma dai ya san cewa baya son mu’amalar Mustafa da Fatima haka.

*****

Yau litinin da misalin karfe takwas na dare Fatima ce kwance a kasan bishiyar dalbejiyar gidansu, a hankali sansanyar iska kadata, yayin da bacci ya ke cike tab a idonta.

Yau ne gidan nasu ya dawo daidai, kowa ya kama gabanshi, taron biki ya tashi lafiya, yana mai wasa da macijin tsumma yan kallo lafiya yan wasa ma lafiya.

Mama ma da take kwance a falo ta dage labule iska na shigowa, gefenta kuma radio ce me cin batir hudu ta kama tashar Kano tana jin IYA RUWA.

Ita ma ba komai ne take fahimta ba, Saboda baccin da ke a idonta ga gajiyar kujuba-kujuba.

Tun Fatima na jiyo rakadin radion Mama har bacci me dadi ya dauketa.

A cikin baccin ta ji abu kamar cizon cinnaka a babban yatsanta na hagu, sosawa ta yi kadan hade da gyara kwanciyarta.

Ji ta yi zafin ya wuce misali, zumbur ta mike zaune amma kamar ana karo zafin. Tun tana daurewa har ta fara kiran Mama. Cikin muryar bacci Mama ta amsa hade da rage karar radionta.

“Mama ina jin kunama ce ta harbeni, wayyo hannuna.”

Kamar ba daga bacci ta farka ba, haka mama ta mike, ta nufi gurin da Fatima ke ta safa da marwa.

Tocilan din dake hannunta ta fara haskawa bayan ta haska hannun Fatima da yake ta hada gumi.

Kunamar kwance a gefen filon da Fatima ke kwance a kai.

Bayan ta kashe kunamar ne, ta daure hannun Fatima hade da shafa turare, amma kamar ta kara mata azaba.

Tun tana daurewa har ta saki kuka me sauti, mama nata rarrashi.

Abu kamar wasa, haka Mama da Jamil babu wanda ya runtsa har gari ya waye, bare kuma Fatima.

Daga daren dai zuwa safiya ta gane Allah da girma yake, don kuwa ba ta taba tsammanin wayar gari cikin masu  rai ba.

Kamar yanzu ma da Mama ke ta fama da ita ta ce abinci, sai dai Fatima ko kallon abincin ba ta yi, idan ka dauke safa da marwa da take tsakanin cikin daki da tsakar gida hannu a sama.

Kukan ma ba hawaye, sai dai wash Allah! Wayyo! Innalillahi. Addu’o’i kuwa ta yi ba iyaka.

“Ke kuwa ranar haihuwarki da kallo Fatima, ace mutum ba karfin hali ko kadan, tun jiya kike abu guda ko sau daya ba ki bar mu mun runtsa ba. Don Allah ki rika karfafa zuciyarki” cewar Mama da ke tsaye tana kallonta.

“Hmmm! Mama kenan, ke haihuwa kika sani, ba ki san cizon kunama ba, ni kuma cizon kunama na sani. Yanzu da haihuwar ce ma ai kila da tuni na haihu, ki bar ni, ni kawai na san azabar da nake sha.”

Jamil da yake tsaye yana kallonsu kamo hannun Fatima ya yi ya zaunar da ita kan kujera, sosai yake jin wuyar da take sha a jikinshi. Da da halin da zai karbi zafin da take ji, tabbas da tun jiya ya karba. Iyakar dabararsu ta likitoci ya yi amma shiru ne.

Ya zuba mata ido yana kallon yadda ta kwantar da kanta a hannun kujerar hade da lumshe ido.

Ajiyar zuciya ya sauke, yayin da fuskarshi ta nuna cewa tausayawa. Har yanzu hannunta da kunamar ta cijeta yana hannunshi.

“Miko mun furar Mama.” ya fada ba tare da ya kalli Mamar ma ba.

“Ai gara ko furar ma ta sha, amma a ce mutum tun jiya bai ci komai ba, ga shi har karfe biyu ya yi, dama ita ga ulcern nan ta zamani tana fama da ita.”

Mama ta fada a lokacin da take mika mishi furar gero da aka damata da lafiyayyen nono shanu.

Durkasawa ya yi gabanta bayan ya aje furar a kasa, ya yi amfani da hannunshi daya da bai rike hannunta ba, ya debo furar hade da kaiwa bakinta.

Ta bude idonta da suke a rufe ta dora a kanshi. Ba ta iya jure kallon kwayar idonshi, akwai wani sirri na musamman da yake cikinta wanda ke hana mata tsawaita kallonshi.

Bude baki ta yi a hankali ta karbi furar, kamar kasa ta ke jin ta, amma haka nan ta daure ta rika karba.

Ta sha kamar spoon goma, kafin ta kawar da kai gefe, mama da ke tsaye tana kallonsu ita ce ta yi saurin cewa, “kara mana.”

Girgiza kai ta yi alamar a’a.

Ya gyara zamanshi a kasa sosai yana fuskantar ta, wannan karon ya saki hannun nata.

Har yanzu nishi take yi, alamar hannun na yi mata zafi.

Tunanin me ya kamata ya yi yake yi, so yake kawai ya ga ta ji sauki yanzu.

Mama ce kawai ta amsa sallamar da Mustafa ya yi.

Ya mikawa Jamil hannu da yake zaune a gaban Fatima bayan sun gaisa da Mama.

“Me ya samu wannan kuma?” ya yi tambayar a lokacin da yake zama daya daga cikin kujerun falon, hankalinshi a kan Fatima.

“Wallahi gamo ta yi, jiya kunama ta harbeta ka ganta nan, ko bacci daga mu har ita ba wanda ya yi.” Cewar Mama da take tsaye tun dazu kamar ta kada suruka.

Zumbur! Ya mike ya nufi inda Fatiman take, yana fadin “Subhanallah! Har yanzu ba ta fadi ba.”

Ya riko hannun yana jujjuyawa. Har a lokacin ba ta yi magana ba, kuma ba ta bude idonta da yake a lumshe ba.

Amma sosai take jin dadi idan hannunta me harbin kunamar yana a hannun wani. Jiya haka su Mama suka kwana rike mata shi, idan ta gaji Jamil ya karba.

Jamil ya ta shi daga zaunen da yake ya koma kan kujera, yana daddanna karamar wayarshi Nokia.

“Samo mun ruwa Mama, a dan zuba gishiri kadan a ciki.”

Cikin yan mintuna Mama ta yi hakan.

Addu’a ya tofa a ruwan hade da mika wa Fatima, ba musu ta karba ta sha, da kanshi ya shafa mata wani ruwan addu’ar a inda kunamar ta cijeta.

Tun suna jin sautin nishinta da karfi, alamar dai tana jin jiki.

Har nishin ya koma saukar numfashi alamar bacci ya dauketa.

Tun da Mama ta ga Fatima ta samu bacci, ita ma sai lallaba zuwa turakar mijinta ta dan matse.

Shi ma Jamil fitar Mama ba dadewa ya fice.

Mustafa ne kawai zaune yana kallon yadda Fatima ke fitar da numfashi a hankali.

Ji yake kamar ya ta shi, ya gyara mata kwanciya, kasancewar a zaune take, kanta ne kawai ta kwantar a kan kujera.

Tsawon awa daya da baccin nata, ta dan bude idon a hankali hade da dorasu a kan Mustafa.

Dama ita yake kallo, bude idon nata ne ya sanya shi saurin nufo in da take.”Ya ya, akwai zafi har yanzu?”

Gyara zama ta yi, hade da girgiza kanta alamar babu

“Ki yi magana mana.”

“Babu zafi sosai irin na dazu, karo mun ruwan addu’ar.” a hankali take maganar cike da mutuwar jiki.

Ya mika mata, bayan ta sha ne, ta rika shafawa a hankali a gurin da kunamar ta cije ta.

“Wace addu’a ka karanta ne? Ina jin sauki sosai idan na sha.”

“Fatiha kafa bakwai.”

Zaro ido ta yi hade da kama habarta da hannu daya mara ciwon.

“Fatiha fa ka ce? To jiya na karanta Fatiha ta fi dari bakwai amma ba sauki.”

Ya dan murmusa kadan.

“Yanzu dai ya kike ji.”

“Yanzu dai iya gurin da ta harbe ni ne yake zafi.”

“Ba mamaki sai lokacin da ta cije ki ya dawo zai daina,”

Sallamar da Jamil ya yi me kama da an yi mishi dole ne ya hana Fatima Magana.

“Ya jikin naki?” ya tambaya a lokacin da yake kallonta.

“Akwai sauki.”

Ya aje ledar hannunshi, da kanshi ya gyara mata kifin da ya siyo ya cire kayar kafin ya ba ta.

Ganin hakan ne ya sa Mustafa fita, da zummar zai yi sallahr la’asar.

Abu kamar wasa kwana uku da cizon kunama amma kullum basa barci.

Kuma Mustafa bai kara dawowa gidan ba.

Dalilin da ya sa yau ta matsa su nemo mata shi ya yi mata addu’a kar ta mutu.

Jamil ne da kanshi ya fita nemanshi, cikin mintuna talatin suka shiga.

“Wannan fa ya zama ciwon yatsa kuma (Dan banza”) “

Mustafa ya fada bayan sun gama gaishe -gaishe.

“Ba ga shi ba, da za ku kashe ni, kun ki ku nemar mun magani don baku san wahalar da nake sha ba, sai dura mun maganin asibiti da allura kuke.” Cikin kuka Fatima ke maganar, don da gaske ba karamar azaba take sha ba.

Ji take kamar ta yanke hannun ta yar. Wannan azabar gara ta cizon kunama.

“Wallahi ranar can da Aisha ta zo, ta fadi haka, na ce kar ta jawo mun ciwon dan banza a cikin gidana, ashe kuwa shi ne.” fadin Mama cikin tausayawa

“Ni ba zan kara shan maganin asibiti ba, a nemo mun na gargajiya, wallahi ji nake kamar zan mutu Mama.”

“Yi hakuri na san ciwon yatsa akwai masifa sosai, wannan hutu dai duk cikin ciwo kika yi shi, Allah ya sa ya zama kaffara.”

Dukkansu suka amsa da amin.

“To yanzu ina za a samu mai maganin” Jamil ya yi tambayar yana kallonsu.

“Akwai wani a can kauyen Katsayal gobe sai aje gurinshi.” cewar Mustafa yana kallon Fatima.

“Gobe fa ka ce, ni yanzu za a kai ni, ka san yadda nake ji ne da za ka ce gobe?” cewar Fatima cikin kuka bayan ta mike tsaye hannunta daya a saman kanta.

Jamil ne ya matsa wayarshi kirar Nokia 1110, wacce ake ya yi a shekarar 2006

“Yanzu fa takwas saura ki hakura zuwa goben.”

“Eh ki yi hakuri zuwa goben, ana fitowa sallahr asuba zan zo in kai ki.” Cewar Mustafa cikin sigar lallashi.

Ba ta yi magana ba, ta dai koma ta zauna, ita kawai ce ta san irin azabar da take sha, ko makiyinta ba ta yi mishi fatar ciwon yatsa.

Ana fitowa daga masallaci kuwa Mustafa ya zo a kan mashin din shi kirar kanchen shi ake ya yi a lokacin.

Basu bata lokaci ba suka wuce zuwa Katsayal.

A can ma basu bata lokacin ba, mai maganin ya hada masu, da wanda za a kwaba da lalle da kuma wanda za a shafa bayan ciwon ya fashe, don ya tabbatar masu muddin suka kwaba wanda za a hada  lalle da dare suka daura mata kafin safiya zai yi ruwa, zuwa safiya kuma zai fashe.

Zuwa dare kuwa suka aiwatar kamar yadda mai maganin ya fada.

Amma dai a daren Fatima suma ne kawai ba ta yi ba, kamar ta rasa hankalinta, har da gudu take yin waje sai sun kamo ta.

Hatta Mustafa a gidan ya kwana, har ya fara dana sanin karbar maganin ma.

Yadda suka ga dare haka suka ga safiya, zuwa lokacin kuwa hannun ya yi sumtum alamar ya ja ruwa saura fashewa.

Fashewar ce sai goma na safe ya yi ta, zuwa lokacin kuwa yayyunta mata da matan yayyunta duk suna gidan, saboda jin abin da ke faruwa.

Sosai take ganin kokarin Jamil musamman yanzu da hannun ya fashe shi ne yake ta kokarin gyara wurin ba tare da jin kyama ba.

Mintuna goma ruwan ya gama zubewa, kuma zuwa lokacin ba ta jin wani ciwo ko kadan. Idan ka dauke rashin karfin jiki.

A lokacin ne kuma bacci me nauyi ya dauketa.

<< Daga Karshe 8Daga Karshe 10 >>

1 thought on “Daga Karshe 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×