Skip to content
Part 14 of 65 in the Series Daga Karshe by Matar J

Duk yadda Mustafa ya so, dakatar da maganar auransu, Fatima ta hana faruwar hakan.

Dole ya hakura, tare da zubawa sarautar Allah ido da kuma addu’ar Allah ya sa haka shi ne ma fi a alkairi a tsakaninsu.

Bangaren Fatima kuwa, duk irin rikicin da ake yi a kan maganar, hakan bai sa ta canja ra’ayi ba. A kwanan nan dai kusan kowa ranshi a bace yake, wasu su ga laifin Fatima wasu su ga na Mama.

Alhaji dai cewa ya yi Mustafa ya je ya ci gaba da shirye-shiryen biki, nan da wata uku sha Allah ba fashi.

Yayin da Mustafa ke shirin auran shi, Jamil kuwa shirin fita Kasar Indiya yake yi, don zurfafa karatunsa na likita. Kamar yadda Mustafa ke samun ci gaba wajen shirye-shiryen auransa, haka Jamil ke samun ci gaba wajen tafiyar sa.

Fatima ma ta ji su Aunty Hauwa na zancen tafiyar Jamil din, ita da Aunty Lami, a lokacin da Aunty Lamin ta zo kan case din Fatiman, amma uffan ba ta ce masu ba.

*****

Yau Juma’a, kamar ko wacce juma’a gidan Hakimi baya yankewa da jama’a, haka ma gidansu Fatima yake kasancewa, musamman idan Alhaji Musa ya zo.

Fatima sanye da atamfar Soso mai ruwan kwai sai farin hijabi madaidaici, ta fito daga gidan Hakimin zuwa gidansu.

Kimanin sati uku kenan rabon ta da gidan. Tun da ta bar gidan, ba ta kara komawa ba sai yau. Shi ma saboda Alhaji ya zo ne.

Ba ta damu da mutanen da ke kofar gidan nasu ba, kasancewar an sakko masallaci ne, dama ita yawan mutane baya hana ta bin hanya.

Hankali kwance ta ratsa cikinsu, wasu ta gaishe su, wasu kuma ta wuce su, har zuwa lokacin da ta shiga cikin gidan nasu.

Kamar kullum su Aunty Sadiya duk suna gidan, tare da yaransu.

Suka amsa gaisuwar da take yi masu, daga haka kuma ba ta kara cewa komai ba, ta shige bangaren Alhajin.

Zaune suke da Jamil, suna tattaunawa a kan batun tafiyarsa zuwa ƙasar Indiyan da zai yi. Ganin ta ya sa suka yi shiru, yayin da Alhaji ya zuba mata ido har ta samu wuri ta zauna.

Kanta ta sadda ƙasa, hade da wasa da lallausan carfet din da ke yashe a tsakiyar falon, a lokacin da ta gama gaishe su.

“Nana Faɗima!” Alhaji ya kira sunanta a tausashe.

Kai ta dago hade da motsa bakinta a hankali alamar amsawa.

“Ki yi hakuri kin ji, komai yana da iyaka ban da Ikon Allah. Ki daina sanya damuwa a ranki. Ni ina tare da ke, da kuma sauran yan’uwanki. Kin ji ko?”

Kai ta daga sama alamar gamsuwa, lokaci daya kuma tana share hawayen da ya ziraro mata.

Haka nan Jamil ya ji tausayinta ya kama shi, karo na farko a rayuwarsa da ya ga Fatima cikin natsuwa, babu wata hayaniya a tare da ita.

Sannan karo na farko da yaga hawaye a kan fuskarta, saboda wata damuwa ta duniya. Amma da idan ka ga hawayenta to ba zai wuce a kan komawa makaranta ba.

“Kun gaisa da Innar ta ki?” Alhaji ya katsewa Jamil tunani da maganar shi.

Kai ta girgiza alamar a’a, har zuwa lokacin hawaye ne ke zarya a kan kuncinta.

“To tashi ki je ki gaishe ta kin ji ko. Allah ya yi miki albarka.”

Mikewa ta yi hade da share hawayen da basu nuna alamar tsayawa ba.

Har ta fita zuwa tsakar gidan kuka take yi, abin da ya ƙara sanyaya gwiwar ƴan’uwanta, da ke ta hayaniya a tsakar gidan.

Take gidan ya koma tsit, lokaci daya kuma suka dafa mata baya zuwa dakin Mama.

A lokacin kuwa Mama zaune take tare da Bashir suna magana a kan tafiyar Jamil, Fatima ta shiga dakin.

Lokaci daya Mama ta canja fuska tare da kawar da kai gefe.

“Ina wuni?” cikin muryar Kuka Fatima ta yi maganar, a lokacin da ta duka kan kofar dakin.

Shiru ya ziyarci wurin, har sai da Sadiya da ke bakin kofa ta ce “Mama ana gaishe ki fa.” a marairace ta yi maganar.

“Ban san inda wunin yake ba…”

“Haba Mama! Haba Mama!! Don Allah, Fatima har yanzu yarinya ce fa, abu kuma ba ya wuce ba?” cewar Aunty Ayyo kamar za ta yi kuka.

“A wurinku ne ya wuce, amma ni a wurina bai wuce ba, tun dai Fatima ta rasa wanda za ta watsawa kasa a ido sai ni. Barka ma da ba ita kadai na haifa ba.”

“Don Allah Mama wannan batu ya wuce mana.” Cewar Ya Bashir.

“Yarinyar nan fa ta raina ni, tsawon sati uku da faruwar wannan abun, amma da yake ba ta dauke ni a bakin komai ba, ba ta tako gidan nan ba sai yau da uban ta ya zo. Ai ta san ta bata min rai. Idan abun na kai da kitso ne, ba za ta zo ta ban hakuri ba? Sai da uban ta ya zo sannan za ta zo.”

Fatima dai Kuka take yi a hankali.

“Ke Fatima tashi ki tafi. ” cewar Ya Bashir

Kamar dama jira take yi, mikewa ta yi lokaci daya kuma tana shesshekar kuka ta yi hanyar fita.

Gidan ya kuma yin tsit, kafin daga bisani, suka rufu a kan Maman kowa na fadin albarkacin bakin shi. Wanda dukkansu ba Maman hakuri suke yi, a kan bai kamata ta dauki wannan matakin wa Fatima ba.

Yayin da Mama ta kafe a kan yanzun ma ta fara. Idan su ma zasu fi bayan Fatiman ne Bismillah.

Dalilin da ya sa kenan kowa ya watse, don a kwanakin Sam zuwan gidan baya ma kowa dadi.

*****

Yammacin Asabar

Da misalin karfe biyar daidai na yamma, Fatima ta fito daga gidan Aunty Hauwa zuwa gidan Ya Bashir. A hankali take tafiya tamkar tana tausayin ƙasa.

Jamil da ke tsaye a kofar gida, ya bi ta da kallo, yayin da ta dauke kai tamkar ba ta gan shi ba. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, bayan da ta bacewa ganinsa.

Sosai ta canja, ta kara wata irin natsuwa, wacce a kallo daya za ka fahimci natsuwar ta ratsa dukkan sassan jikinta.

Har kyau ma ya ga ta kara mishi, ta yi haske, sannan yanayin da ake ciki bai ramar da ita ba. Tana nan a cike bulbul abun ta.

Bayan ta ya bi, akwai bukatar ya yi magana da ita, kafin ya tafi gobe.

Zaune suke da Aunty Bilki suna hira, duk da hirar tasu ta fi karkata a kan rikicin da ke faruwa a gidan.

Duk suka dakata da maganar da suke yi, lokaci daya kuma Aunty Bilki ta amsa sallamar Jamil.

A mutumce suka gaisa, kafin ya ce yana son yin magana da Fatima ne.

Aunty Bilki ce da kanta ta bude sitting room din ta gyare shi tsaf sannan ta ce su shiga.

Ya kwashe wajen 5mns sannan Fatima ta bi bayan shi, hakan ma sai da Aunty Bilki ta yi ta lallashin ta.

Don cewa ta yi ba za ta je ba, me zai fada mata?

Zaune yake kan kujera, ya daga kansa sama yana kallon ceiling, shigowarta ya sanya shi dagowa yana kallon ta.

“Ina wuni?” ta fada daidai tana zama akan kujerar da ke fuskantar shi.

“Alhamdulillahi!” ya amsa a hankali kafin ya yanke shirun nasu da fadin

“Gobe zan tafi, shi ne na ga akwai bukatar mu yi magana.”

“Ina za ka je?”

“Indiya.” ya amsa mata lokacin da yake gyara zaman shi.

“Yin me?” ta kuma tambaya kamar ba ta san komai a kan maganar ba.

“Zan je karin karatu ne.”

“To Allah ya taimaka.”

“Amin.” ya amsa, kafin suka kara yin shiru.

Numfashi ya sauke a hankali “Fatima, na san kina jin haushina a kan abin da ke faruwa. Saboda za ki ga kamar nine silar damuwar da kike ciki yanzu…”

“A’a ni bana jin haushinka.” ta yi saurin katse shi.

Guntun murmushi ya yi hade da fadin “Koma dai kina ji, ki sani ina damuwa da halin da kike ciki, sannan ina bakin kokarina wajen ganin komai ya daidaita. Wallahi ban so na zama silar damuwarki ba.”

Fatima dai wasa take yi da hannunta, ba tare da ta ce komai ba.

“Fatima zan fada miki wata magana, ko ki yarda, ko kar ki yarda, shi ne gaskiyar abin da ke cikin zuciyata. Wallahi ni Jamilu ban taba kin ki ba, sannan ina yi miki Son da Mustafa ko rabin shi baya yi miki.”

Da sauri ta dago kai suka hada ido, babu komai a cikin idanunsa sai gaskiyar abin da ya fada. Amma hakan bai hana ta fadin

“Kai! Haba! Wannan ba zai yiwu ba.” lokaci daya kuma ta yi murmushin da ya ƙasa fassarawa.

Mikewa ya yi tsaye hade da zuba hannuwansa du biyun cikin aljihun wandon sa.

“Dama na san ba za ki gasgata ni ba, amma wannan shi ne gaskiya. Ban taba furta ma wata mace kalmar so ba saboda ke. Ban taba mafarkin rayuwa aure na da ko wace mace ba sai ke. Duk wani tsari na rayuwar aurena, da ke nake tsara shi. Na san na yi nauyin baki, daban taba nuna miki hakan ko furta miki ba. Wannan kuwa ya faru ne, da yadda kullum nake miki kallon yarinya. Sannan na san ba auran ne a gabanki ba. Please Fatima ki yafe min don Allah, na san nine silar duk wani abu da yake faruwa da ke a yanzu. Amma na yi miki alkawarin zan daidaita komai. “

Fatima da yanzu zuciyarta ta zama mai rauni, abu kadan sai ya kara raunanata, yayin da hawayenta suka matso kusa, karamin abu sai ya sa su bayyana.

Hannu ta sanya hade da dauke hawayen, ba tare da ta ce komai ba.

“Fatima ban taba kin ki ba, da kuma Allah ya kaddara zamanmu a karkashin inuwa daya ta aure, tabbas da kin gasgata hakan. Amma ba zan gushe ba ina yi miki fatan alkairi. Mustafa mutumin kirki ne a zahiri, ko wace mace za ta so ya kasance a matsayin mijinta.”

Cikin muryar kuka ta ce” Ya Jamil wallahi ni ma ban taba ƙin ka ba, na kaucewa zabin Mama ne saboda ina ganin kamar yin hakan takura ne kai a wajen ka. Amma da ace ka nuna kana sona ko ba ni da ra’ayi a kanka zan amince…” Kukan da take ya ci karfin ta, shi kuma ya duka kusa da ita, cikin kasalalliyar murya yake magana

“Na sani, na sani Fatima, na san abin da kika fada yanzu shi ne a zuciyarki, ba don ba kya sona ne kika ki karbata a matsayin miji ba, sai don kawai kina ganin hakan zai zama takura a wajena. Zan fahimtar da Mama wannan.”

Suka yi shiru gaba daya, kafin daga bisani Jamil ya kuma mikewa tsaye.

“Fatima kada ki bar karatunki saboda aure, ki yi kokari ki cika burinki komai runtsi. Ni zan tsaya miki ta ko wane fanni in sha Allah. Mace ba ta rasa damuwa a gidan auranta, idan kin fuskanci hakan ki zo gare ni kai tsaye, ni yayanki ne kada ki boye min. Na yi kuskuren da ya zama izna a gare ni nan gaba, ba ni kawai ba, da duk mai irin hali na, ban so na rasa ki a matsayin uwar yarana ba, amma ina fatan hakan shi ne ma fi alkairi a garemu ba ki daya. Sannan Ina yi miki fatan alkairi a dukkan komai na rayuwarki.”

Yana kaiwa nan ya fice daga dakin, yayin da sautin kukan Fatima ya ƙaru.

Aunty Bilki da ke tsakar gida tana yan aikace-aikacenta, ta bi Jamil da kallon yadda idonsa ya canja kala zuwa launin ja. Uffan bai ce mata ba ya fice daga gidan a hanzarce.

Tsaye ta yi tana kallon kofar da ya fita din, kafin ta juya zuwa sitting room din ganin Fatima ba ta fito ba.

Ba ki ta saki hade rike haba, ganin yadda Fatima ke kuka kamar an aiko mata da mutuwa.

Sallamar Ya Bashir ce ta sanyata fita, ba tare da ta cewa Fatima komai ba.

Tana tsaka da sanya mishi ruwan alwalar magriba ne, Fatima ta fito daga sitting room din, har zuwa lokacin ba ta daina kukan ba.

Bashir da ke tsaye ya bi ta da kallo har ta fice daga gidan. juyowa ya yi yana kallon Aunty Bilki da ke ajiye mishi buta.

“Me take ma kuka ita kuma waccan?”

Cikin mutuwar jiki Aunty Bilki ta ce “Ban sani ba ni ma, ina shirin tambayarta ka shigo. Amma dai ita da Jamil ne, na ga shi ma ya fita kamar yana kuka.”

Bashir ya bude baki alamun mamaki “Jamil din?”

“Eh.” ta amsa shi.

“To Allah ya kyauta, su dai suka sani, shi ya sa ni ban so Mama ta saka kanta a wannan hidima ba, ta bar yaran nan sun fi kusa, amma ta ki fahimta. Ita dai ala dole Fatima ta watsa mata ƙasa a ido sai ta hukuntata.”

“Kuma ta fi kowa sanin Fatima ba a yi mata dole, a lokacin da ta ga mutum zai yi amfani da karfin shi a kanta, to ita kuma a lokacin za ta nuna ma nuna karfi baya sanya ta yin abu.” Cewar Aunty Bilki.

“To koma ba haka din ba, Jamil fa ba yaro ba ne, idan yana son Fatima ba sai an matsa mishi ba. Allah dai ya kyauta.” ya kai karshen maganar sa hade da mikewa daga kan karamar kujerar da ya yi alwala, ya fice zuwa masallaci.

Fatima duk yadda ta so tsayar da hawayenta abun ya gagareta. Lokacin da ta isa gidan Aunty Hauwa na alwala. Tambayar duniyar nan Fatima babu wacce ta amsawa Aunty Hauwa. Sai ma farashin kukan da ta ƙara. Dalilin da ya sa Auntyn ta kyale ta, ta nufi bedroom don gabatar da sallah.

Amma zuciyarta cike da tausayin yar’uwar tata, lokaci daya duk ta canja, sai yanzu ta fahimci Fatima kadai ma farin ciki gidansu ce.

Da ace lafiya take tabbas Allah kadai ya san irin abubuwan dariyar da ta aikata a cikin wadannan kwanakin. Ita kanta Mama ba ta jin dadin gidan, jin shi take yi shiru saboda rashin Fatima. Jamil ma da yake motsi tana ji shi ma zai kara gaba.

Gidan zai koma shiru kenan, sai jikokinta idan sun leko.

Ranar ko abinci kadan Fatima ta tsakura, ta kwanta, tun tana jin hayaniyar mutanen gidan har bacci ya kwashe ta. Jamil ma bai san cewa ya damu da Fatima ba sai da dare ya yi.

Ya nemi bacci a idonsa ya rasa, ganin abun yake kamar almara, wai har Fatima ta gama makaranta, har ta fitar da miji, kuma za a yi masu aure nan da watanni biyu, yayin da shi kuma yake shirin barin Kasar gobe.

“To ahi kuma kowa zai aura oho?” wannan ita ce tambayar da ko wane lokaci take mishi zarya a cikin kai. Kuma ba shi da amsarta, Allah ne kawai ya sani, fatan shi dai ya samu ta gari, kamar yadda yake ganin Fatima ta dace da na gari.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Daga Karshe 13Daga Karshe 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×