Skip to content

Daga Karshe | Babi Na Takwas

2.3
(3)

<< Previous

Zainab ce ta fara shigowa gidan, idon Mama da kyar a kofar gida, ganinta ya sa ta mike.

“Ina kika bar Fatima kuma ko har yanzu ba a gama kunshin ba?”

Ba ta amsa tambayar ba, sai ma shigewa daki ta ta yi.

“Ina tambaya kina wucewa zoƙal- zoƙal kin shige mun daki kamar dakinki bayan ba ki amsa mun tambayata ba.”

“Kawu Jamil ne ya barota a can.”

“Me ya sa zai bar ta? Ai ba ke na ce ya je ya dakko ba, yarinyata na ce ya dakko mun. Amma ya je dakko mun wannan abu kamar sandar Fulani.”

Duk dakin suka tuntsire da dariya idan ka dauke Zainab da ta bata rai.

Shigowar Jamil ne ya sa Mama juyawa kanshi.

“Kai ƴata na ce ka dakko mun ba waccan zogalen ba, me ya sa ka barota?”

“Rashin kunya ta yi mun.”

“Kullum dai abu daya kamar hanyar ɗaka, kai dai kullum ta yi ma rashin kunya. Sam ba ka sakewa da yarinyar nan, da ka ganta sai ka daure fuska kamar yaki ya riga ka kofar gida.”

“To Mama kin san fa halin yarinyar nan, kodanake daurewar ma ai ta raina ni.”

“To ya za ku yi, haka Allah ya yo ta, wata rana sai labari.  Zai zama kamar duk ba ta yi wannan ba.”

A daidai lokacin ne Fatima ta shigo, ranta bace ta kumbura fam kamar za ta yi aman wuta.

Ba ta san me ya sa ba, zuciyarta ba ta jure wulakancin Jamil muddin zai yi mata sai ta zubar da hawaye abu ma fi tsada a gurinta.

Yanzu da ta shigo ji ta yi kamar ta yi aljanun karya ta shake shi.

Hawayen da take ta kokarin boyewa suka gangaro a daidai lokacin da Mama ke mata magana.

“Hankalina yana gurinki, tun safe ko abincin kirki ma ba ki ci ba ga ulcer, na aika yayanki ya dakko ki, ya ce kin yi mishi rashin kunya, Fatima bana son wannan halin naki, ace kowa ba zai fadi abu me kyau a kanki ba, kowa kin raina shi.”

Ta kai hannu tana share hawayen, cikin kuka take Magana.

“Ni ban yi mishi komai ba, ba dai ya san daukata ne, ya tsaneni ban san me ya sa ba. Kuma babu yadda zai yi da ni, ko hauka nake yi dole dai ni yar’uwarshi.” ta tsananta kukan ta sosai, yayin da maganganunta da sautin kukanta ya fara janyo hankalin mutane.

“To shi kenan, ya isa yi hakuri, je ki yi wanka ki zo ki ci abinci, ki bar ni da shi.” cewa Mama cikin muryar lallashi.

“Kar ki kara aikawa ya dakkoni a ko ina ma bana so, kuma ko mutuwa zan yi idan motar yaya Jamil ce ta rage a duniya ban so a saka ni a ciki, a bar ni kawai in mutu.”

“Ki wuce daki na ce miki ko”cikin tsawa mama ta yi maganar

“Kuma in sha Allah ni ma sai na sayi mota na huce haushin abin da yake yi mun. Kuma da ban shiga motar ta shi ba, sai ban dawo gida ba?” a daidai lokacin da take shiga daki take fadin haka.

Duk maganganun da take yana jinta.

Jikinshi ya mutu lakwas, shi da kanshi yake jin bai kyauta ba, sannan da gaske a zahiri kowa ma zai iya cewa ya tsanetan, amma a zuciyarshi abun ba haka ba ne, har ranshi ma zai iya bayarwa a kanta.

Ya sauke numfashi me karfi lokaci daya kuma ya nufi dakin Mama, bai damu da mutanen da ke ciki ba, Fatima kawai yake son gani.

Cikin rashin sa’a ta shiga wanka, shi ma kuma fita ya yi daga gidan, don hayaniya ta yi yawa, amma tabbas zai neme ta ya fada mata girman matsayinta a gurinshi.

Bayan fitowar ta daga wanka dakinta ta shiga, pad ta canja, hade da shafa mai, me taushin kamshi.

Riga da sicket na yadin kuskus ta sanya me ruwan madara, kayan sun zauna a jikinta das. Basu yawa ba haka basu yi kadan ba.

Ta dakko farar hoda ta silver line ta shafa, fuskar ta yi smooth daga nan ta shafa man lebe, hade da sharce kanta ta kama da jan ribon.

Turaren humra ta shafa, bayan ta yi daurin dankwali me sauki.

Har yanzu ranta ba dadi, wani irin kunci take ji, yayin da kuma take ta shirya irin shariya da nuna halin ko in kula da za ta yi wa Jamil.

Jamil kuwa  ya kasa natsuwa, amon muryar Fatima yake ji a cikin kunnenshi tana fadin “Ya tsaneni ban san me ya sa ba… Ko mutuwa zan yi ban ce a sanya ni a motar Yaya Jamil ba.”

Wannan kalmomin sun fi tsaya mishi.

Ya dan ciji lebenshi na kasa, a fili kuma ya ce

“Ya zan yi in ganta ne yanzu?”

Ta fito tsakar gidan a daidai lokacin da su Mustafa suke shigowa da carton na lemuka da alama daga kasuwa suke.

Tun da ya shigo hankalinshi yake a kanta. Ko bai tambaya ya san tabbas ya san akwai abin da yake damunta, duba da yadda take zaune shiru abun da ba ta saba ba.

Kosawa ya yi a gama sauke lemukan ko ya tambayi Fatima abun da ke damunta.

Cikin sa’a ta dago kai suka hada ido a lokacin da yake tsaye a sashen su Jamil.

Da hannu ya yi mata alamar ta zo. Ta zuba mishi idanunta da suke nuna alamun damuwa.

Ya kuma dago hannu ya kirata.

Mikewa ta yi hade da kakkabe jikinta, lokaci daya kuma ta nufi inda yake tsaye.

Mirginar da kai gefe daya ya yi, hade da saka idanunshi a cikin nata kafin ta yi kasa da nata tana idon hade da wasa da yatsun hannunta.

“Ke da Mama ko?”

Girgiza kai ta yi alamar a’a.

“Aunty Hauwa ko Maryam?”

Ta kuma girgiza kai.

Ya gyara tsayuwarshi hade da harde hannayenshi a kan kirjinshi, har yanzu idonshi a kanta.

“Fada mun to waye?”

Tuni zuciyarta ta gama narkewa hakkan ne ya ba hawayen damar silalowa. “Yaya Jamil ne, ko wane lokaci sai ya yi ta mun wulakanci a kan motarshi. Ya tsane ni ban san dalili ba, shi dai kullum burinshi ya wulakanta ni, ba zan iya kirga ko sau nawa ya yi mun wulakanci a kan motarshi ba.” ta karashe maganar hade da dauke hawayen da ke bin kuncinta.

Ya sauke ajiyar zuciyar da sautinta ya bayyana.

” Don wannan ne kike ta fushi? Zo ki ji.” ya fada hade da kama hannunta daya yana ja.

Ba ta yi gardama ba, ta bi bayanshi har zuwa ka san bishiyar umbrella inda aka tara kujerun robar da za a yi amfani dasu gobe.

Ya zare biyu, ya ajiyesu suna fuskantar juna, shi ne da kanshi ya zaunar da ita.

“Waye ya fada miki Jamil baya sonki? Kin manta tarin abubuwan da ya yi don ke? Har yankarshi aka yi don ke. Ya yi karatun likitanci ne don ke, saboda lokacin da kike yarinya kin cika yawan ciwo, kullum ana hanyar asibiti. Kin manta lokacin da yake yi miki extra lesson a gida ko? Yanzu har kin manta lokacin da kike jin tsoron tsawa da walkiya? Jamil da ya ga hadari baya bacci ko kuma ya fito cikin ruwa ya zo daukeki a dakin Mama ki kwana a gurinshi. Kin manta lokacin da duk zai koma makaranta har rashin lafiya kike yi saboda kuka? Kin manta lokacin da yake goyaki a bayanshi ya kai ki asibiti a duba ki ya dawo da ke? Ba ya sonki ya tsaneki duk me ya sa zai miki wannan?”

Shiru ya ratsa gurin yayin da take tariyo rayuwarsu ta baya, me cike da tsananin so da kulawa na ‘yan’ uwanta ka.

“To me ya sa yanzu tsana da halin ko in kula suka maye gurbin wadancan abubuwan?” Ta yi wa kanta tambayar.

Amsar dai ita ce ba ta sani ba, don kuwa dai ba za ta iya kawo dalili daya da shi ne sanadin hakan ba.

Mayar da hankalinta ta yi kan Mustafa.

“To me ya sa ya tsane ni yanzu?”

“Rashin jin ki, Fatima ba kya ji, wannan shi ne kawai dalili.”

Ta hada bayanta da majinginar kujerar ba tare da ta ce komai ba, har zuwa lokacin da Mustafa ya ce,

“koma dai menene ki manta har kullum da Jamil me sonki da kaunarki ne. Haka bana son ganin wannan yanayin a kan fuskarki.”

Tare suka mike yana fadin, “Gobe abincina dana abokaina duk a kanki ne.”

A karon farko da ta yi murmushi, “Ba ni da kudi.”

Ya ciro 5k ya mika mata. “Mu je ki dauki carton na minerals biyu, sannan ki debi shinkafa da kayan miya a store, kudin kuma kaji biyu nake son ki saya mun, canjin na bar miki.”

Ta fadada fara’arta, “Wallah ka rufa mun asiri ka ga ko kawayena sun zo ba zan ji kunya ba.”

“Ki yi kwalliya me kyau mutuniyata.” Suka yi dariya me sauti a tare.

Tare suka fita daga sashen, daga nan kuwa Fatima tarkata kayanta ta yi zuwa gidan Aunty Hauwa suka hadu da Zainab don cigaba da shirye- shirye.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Share this post on social!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×