Skip to content
Part 4 of 4 in the Series Danyar Guba by Rukayya Ibrahim Lawal

Bayan awa huɗu suka fito daga lakca lokacin ana kiran sallar azahar. Wannan ɗalibar da ta ja ta mai suna Fatima ita ce ta shawarce su da yin sallah kafin su wuce gida. Haka suka yi alwala da fiyawota suka shimfiɗa ɗankwalinsu suka yi sallar.

Ba don ba ta son a tsinkayo rashin kula da addininta kai tsaye ba da ba abin da zai saka ta yin sallah a wannan yanayin na gajiya da take ciki. Ta riga ta saba da tarukus salati, ta fi son sai dare ya yi ta haɗe duka sallolin wunin ta yi su.

Bayan sun idar da sallar ne suka miƙe suka nufi gate. A zuciyar Fatima tana ta mamaki na rashin iya sallah da kyau na Nu’aymah duba da yadda ta zauna kan ƙafar dama, ta tanƙware ta hagu yayin gabatar da zaman tahiya na ƙarshe. Sa’annan idan ta lura da kyau Nu’aymah ba ta cika ruku’i, don a maimakon ta daidaita ƙashin bayanta sai ya zamana ta yi doro.

Da yake ita ta riga ta gama sallar shi ya sa ta lura da hakan. Zuciyarta sai ingiza ta take a kan ta yi wa Nu’aymar maganar kuskurenta ko za ta gyara. Sai dai wata zuciyar ta kwaɓe ta daga ɗaukar biyewa sashi na farko, duba da cewa yau ce ranar farko ta haɗuwar su da yarinyar bai kamata ta yi saurin yin katsalandan a cikin rayuwarta ba.

Don haka ta bar abin a ranta tare da ƙudurce idan ta ga ta ci gaba da yi za ta yi mata gyara.

Nu’aymah ta so ta yi kiran Ma’aruf sai dai a gajiye take tiɓis ko da zai zo ba za ta iya jiran zuwan na shi ba. Don haka ta tare adaidai da ke akwai kuɗi a hannunta.

Ko a hanya ma tana zaune ne kawai a bayan adaidaitar amma tuni zuciyarta ta cilla tunanin kyakkyawan lakcaransu da ta fara ganin shi a ɗazu, kuma ta ji a ranta cewa duk rintsi da wuya sai ta san yadda ta yi ta sa ya kwarewa soyayyar ta. Sai dai kafin ta aiwatar da komai za ta yi ƙoƙari ta tantance adadin kason dukiyar da Allah ya mallaka masa domin ita ce abin harinta.

Yanayin suturar jikinsa da motarsa kuma ya alamta mata cewa za a mori wani abu a gun shi. A don haka ta kuɗuri aniyar kafa masa tarkon da take fatar ya kama shi gam.

Haka ta wanzu tana karatun wasiƙar jaki har zuwa lokacin da adaidaitar ta shiga layin gidanta. A nan ta sauka ta ƙarasa gidan, daidai za ta shiga gidan sabuwar fargaba ta shige ta dalilin tunawa da wani abin da ya ɗaga mata hankali da ta yi. A gaggauce ta ƙarasa gidan tana ƙwala masa kira kalmomin sunan nasa na fita a rarrabe.

“Hab Habi bie!”

Yana jin motsinta cikin rawar baki ya ce “Zan kirawo daga baya.” Da harshen turanci kafin ya kashe wayar a gaggauce ya janye ta daga saitin kunnensa yana saisaita nutsuwarsa.

Sallama kawai ta yi ya amsa ta nemi wuri ta zauna a kan kujera fuskarta na bayyanar da maɗaukakiyar damuwa mai haɗe da gajiya.

“Me ya faru ne na ganki a damuwa haka? Sai na ji ma kamar tun daga waje kike ƙwalo mini kira meye ne?”

Sai da ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce “Intisar muka haɗu da ita yau a makarantar bayan mun fito darasin farko kafin ma a koma na biyu. Sai a lokacin na tuna cewa a nan makarantar take karatu kuma na san bakinta ƙarara za ta faɗawa mamanmu, ita kuma ta fesawa Baffa. Sarai kuma kasan halinsa da mita. Ko abbanmu kafin ya rasu tsoron shi yake yi balle kuma mu.”

Kallon ta ya yi ya ga hankalinta ya ƙi kwanciya sai ya ce “Ki kwantar da hankali ni da kaina zan je har Rikkos ɗin na samu baffa na yi masa bayanin kin koma makaranta ne kuma ni na buƙaci hakan.”

Ba ta yi magana ba sai dai da alama har a lokacin a tsorace take don haka ya riƙo hannayenta a cikin nasa yana ƙoƙarin kwantar mata da hankali. “Ki daina saka mini kanki a damuwa kin san bana so. Ki kwantar da hankali ba abin da Baffa zai miki idan na yi magana da shi ma kin ga na kashe bakin magulmata.”

Ta gyaɗa kai alamun gamsuwa kafin ta sake cewa “Dole sai na yi taka-tsantsan da Intisar, kada ta saka mini ido a harkokina da zan ke gudanarwa a makarantar.”

Ya amsa mata da, “Haka ne, ai nasan kin san hannunki sosai kamar ƙwararren ɗan wasa a tsakiyar filin wasansa.”

Sai a lokacin murmushi ya bayyana a fuskarta, ya miƙe tare da nufar kitchen yana faɗar “Na san kin kwaso yunwa bari na kawo miki abincin da na girka miki.”

Ta bi shi da kallon ƙauna a ranta ta ce ‘Allah sarki Habibie na so a ce ƙaunar da kake yi mini ba sirki a cikinta. Na so a ce ba abin da kake so sama da ni da na more rayuwa fiye da hakan. Sai dai kash! Ka fi ƙaunar…’ Ba ta ƙarasa zancen zucinta ba ta ga fitowar shi riƙe da farantin da ya shaƙo mata shi da shinkafa da miya wadda aka ƙawatawa da nama har da salak.

Ba ta yi mamaki ba kasancewar ta san ya iya girki sosai, lokuta da dama ma shi yake yi musu girkin idan tana jin son jiki ko kuma ba ta lafiya.

Yadda yake kula da ita yana yi mata daɗi sosai har tana jin cewa ta fi kowacce ‘ya mace yin dace da miji. Sai dai a mafi akasarin lokuta ta kan riski kanta da yin iyo a tafkin mamakin ɗabi’arsa ta rashin kishi da yadda yake zuga ta kuma ya zuba mata ido take aikata abin da ranta ya so. Duk da tasan idan ɓera da sata to daddawa ma da wari. Tun farko da ba ta ɗauko rawar kai ba ba zai samu tsanin da zai ƙale ya kafa ƙahon zuƙar neman cikar burinsa ta hanyar cinikayyar mutuncinta ba. Don kuwa da ma sai bango ya tsage ne ƙadangare ke samun wurin shiga.

Hakan ta ci gaba da saƙe-saƙe a ranta har zuwa lokacin da ta kammala cin abincin ta shiga ciki don watsa ruwa.

*****

A haka lokaci ya ci gaba da gangara musu. Kamar yadda ya kasance a ƙa’idar kowane kasuwanci watarana a kan ƙirga riba wata rana kuma faɗuwa, to su ma a ɓangaren su haka ne. Watarana ta faɗi gasasshiya watarana kuma su rasa wanda za su yagi ko ficika a hannunsa. Ga shi da ma tun bayan da Nu’aymah ta tattare ‘yan kuɗaɗen hannunta ta sayi mota mai dama sai ya kasance kuɗi yana yi mata wahala a hannu. Duk ranar da ba ta samu garan da ta wanka ba sai ta wuni ba ko ficika.

Idan ma ta samu ko yaya ne ba su ajiyuwa a wurin ɗinka suturu na alfarma ta ke ƙarar da kuɗin. Da ma shi abin banza a harkar banza yake ƙarewa.

Daga lokacin ne kuma surutu da zagin maƙwabta ya yi yawa a kanta, aka kafa teburin gulmarta a gidajen unguwar da kewaye. Kowanne gidan ka je zance ɗaya ne na cewa ba a san ya aka fara ba ta fi mijinta kuɗi, ita tana hawa mota shi yana hawa babur.

Nu’aymah kuwa ba ta damu da duk wannan surutun ba, don ko ta sani mugun nufi ba ya kashe ɗan barewa. Zancen fita kuwa tun da ta samu damar karatu take fakewa da tsinkar zogale tana yagar rama. Mallakar motar da ta yi ya ƙara ta’azzara lamarin yawonta, ko’ina ganin ta ake a gari tana gararamba. Idan ta je makaranta sai ta kwashi tawagar marasa ji ‘yan’uwanta ɗalibai su yi ta yawo a makaranta daga wannan ofis zuwa wannan, koma su fice daga makarantar gaba ɗaya su shiga gari suna zaga gidajen cin abinci da na shaƙatawa da suke nesa da cikin gari. Irin unguwanni da ba ta tsammanin ganin idon sani a gun.

Hankalinsu ba ya kan karatun kwata-kwata sharholiyar su kawai suke yi, sun manta shaf da azancin malam Bahaushe da yake cewa ka yi amfani da damarka kafin ta suɓuce maka. Sai dai da yake su suna taƙama da gurɓatattun malaman da suka tsaya musu waɗan da suke yin cuɗe ni in cuɗe ka. Ko kuma irin kasuwancin nan na ban gishiri in ba ka manja, sai ya zamana komi rashin ganewar su suna samun sakamako mai kyau wani lokacin ma fiye da na masu ganewar. Wannan ne ya taka muhimmiyar rawa wurin ba su damar cin karensu babu babbaka a makarantar.

*****

A ranar Asabar da misalin ƙarfe goma na safiya Nu’aymah ta fito ta shiga jar motarta ƙirar Honda Civic bayan ta zuba kwalliya kamar wacce za ta je gasar sarauniyar kyau. Ta nufi makarantarsu duk da tana sane da cewa ba ta da lakca sam a ranar, amma tana gaggawar tafiya ne don cika nata muradin da ya bambanta da na masu zuwa neman ilimi.

Bayan shafe mintuna ashirin tana tafiya a kan shimfiɗaɗɗun kwaltar da suka ƙara ƙawata garin ta isa daidai inda take muradi.

Ba wani ɓata lokaci ta faka motarta a gaban madaidaicin ginin da ke ɗauke da ofisoshin jagororin makarantar. Ta ɗaga kanta tana kallon wundon ginin sama daga ɓangaren dama tana nazartar wurin kafin ta zaro wayarta da ke ajiye a jaka ta hau daddannawa.

Can bayan wasu daƙiƙu ta kanga wayar a kunne tare da yin amfani da sabuwar muryar da ta ƙirƙira don yaudare zuciyar mazaje ta ce “Sir, kana ofis ne?” Shiru ta yi na ‘yan daƙiƙu kafin ta sake cewa “Hope ba kowa a ciki kuma ba ka expecting zuwan wani.” Ta yi shiru tana sauraren shi har sai da ya tabbatar mata da abin da take son ji kafin ta kashe wayar. Ta saita madubin gaban motar a saitin fuskarta ta hau gyara zaman ɗankwalin jar atamfar da ke jikinta a kanta, sannan ta ciro man leɓe daga jakarta ta ƙara gogawa ta ɗebo cingum masu daɗin ƙamshi da suke ajiye a jakarta kodayaushe ta watsa su a baki tare da kashe motar ta fito.

Ta jikin gilashin motar ta ƙarewa kanta kallo tun daga sama zuwa ƙasa tana jinjina tsaruwar kwalliyarta. Ƙayataccen murmushi ya ƙwace mata lokacin da ta tuna dambarwar da suka sha da Salis kafin ya bar ta ta fito da wannan shigar.

A ɗan gajeren lokacin da take tsaye jikin motar ƙwaƙwalwarta ta shiga hasko mata lokacin da ta fito daga ɗakinta tana zuba ƙamshi kamar wacce aka yi ɓarin turare a jikinta. Salis da ke tsaye kan kayan kallo yana ‘yan gyare-gyare ya dube ta da wani yanayi

“Ba dai a haka za ki je makarantar ba yau?”

Ta langaɓar da kai tare marairaicewa “Uhm! To mene ne a ciki kuma?”

Ya sauke duban shi kan ɗinkin rigarta da aka yi wa adon zif a gaba bugu da ƙari kusan rabin ƙirjinta a waje yake ga rigar ta kama jikinta sosai har tana fitar da numfashi da ƙyar.

Ya ƙara haɗe girar sama da ƙasa sannan ya ce “Gaskiya wannan shigar ta yi muni da yawa. Cikin mutane fa za ki shiga ke ba kya damuwa da irin kallon da za su yi miki ne?”

Har a ƙasan ranta ta ji daɗin yadda ya fara nuna kishi a kanta lokacin, amma dai ba za ta iya cika masa burin na canza suturar ba saboda hango nata burin da ke jiran ta a waje. Wannan dalilin ya sa ta samu ta lallaɓa shi tare da nuna masa ai hakan ba komai ba ne tun da ba yau aka fara ba. Idan kuma ba ta yi hakan ba da wahala wani ya faɗa tarkonta har su samo kuɗi.

Da ma da wannan kalmar ce kaɗai take iya yin nasarar sarrafa ƙawazucin Salis ya haƙura da koma mene ne take son yin koda bai masa daɗi ba. Sanin lagon shi da ta yi ya taka muhimmiyar rawa wurin ba ta cikakken ‘yanci musamman a irin lokacin nan da suka shafe sati biyu kasuwar ba ta ci.

A lokacin ta lura da cewa bisa ga tilas ne kawai ya bar ta ta fito a hakan.

Tana zuwa daidai nan a gaɓar tunaninta ta saki ƙayataccen murmushi sannan ta shige cikin ginin da ke gabanta tare da nufatar hanyar benen da za ta sada ta da ofishin da take muradin zuwa.

A ƙofar ofis ɗin ta ci burki, har ta ɗora hannunta da nufin ƙwanƙwasawa sai ta ji alamar ƙofar a buɗe take. Ai kuwa ba jira ta tura ƙofar tare da kutsa kai ciki fuska ƙunshe da shu’umin murmushi.

“Sannu da zuwa tauraruwa mai haskaka ‘yanmatan mass com department.” Ya furta yana haske ta da wani makirin murmushi mai cike da ma’anoni.

Ba ta tamka shi ba ta tako a hankali cikin salon jan ra’ayi har ta iso gaban kujerar taron baƙi ta zauna ba tare da ta jira izini ba. Shi kuwa tun lokacin da ta fara tunkaro shi ya kafe ta da ido ko ƙyaftawa ba ya yi. Sai bayan ta samu mazauni ne ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi sannan ya je ya rufe ƙofar ofishin ya dawo.

Tun bai ce wani abu ba ta karto manufarsa sai dai ita sam ba ta da muradi irin nasa. Tun da da ma can ita ba ta cika bada kanta ga kowanne irin mutum ba sai dai kawai tana yin amfani da ‘yan dabaru ne da daɗin baki irin na mata har ta samu ta karɓi ‘yan kuɗaɗen da take burin amsa. Sai ta kama dole ne take ba da kanta. Yanzun ma da irin wannan manufar ta zo saɓanin tashi manufar da ta hango a cikin idanunsa.

“Yawwa ‘yar budurwa ina jin ki, wace buƙata ce ke tafe da ke? Kin ce za mu yi magana.” Ta kafe shi da ido tana wani fari da su yayin da take faɗar.

“Sir da ma na ga lokacin exam ya ƙarato ne kuma dai ka fi kowa sanin cewa ba zan iya karatun jarabawar ba, shi ne na zo a yi mini irin taimakon da aka saba.”

Ya yi wani shu’umin murmushi tare da shafar dokin wuya sai yana faɗar “Ba shakka muna yin taimako, amma mu ma sai an ba mu taimako. Nasan kin fahimci yaren.”

Ganin irin kallon da yake bin ta da shi kamar mage ta yi arba da nama ya sa ta fahimci ba za ta samu yadda take so ba matuƙar ba ta miƙa wuya ba, ga shi kuwa jarabawar ƙarshen zango na biyu ce a aji na farko. Ko kaɗan ba ta son ta samu matsala. Tana son ta fita kunyar Ma’aruf da yake fafutukar biya mata kuɗin makarantar. Tana nan zaune ɗif sai ta tuna ba a wannan lokacin ne suka fara yin haka don ceto jarabawar su ba. Ba ta da kuma wani zaɓi da ya fi ta bayar da kai bori ya hau. Don haka ta miƙe tana kwarkwasa har ta isa gaban shi kamar za ta zauna kuma sai ta juya baya da zimmar komawa inda ta fito duk tana sane ta yi wannan kinibibin don jan ra’ayinsa. Tana jin yaƙinin cewa da wuya wannan fatsar tata ta kasa kama kifin da take hari. Ai ko kafin ta yi taku uku a wurin ta ji ya cafko hannunta ta baya.

*****

Bayan kamar awa ɗaya da rabi ta fito daga cikin ginin tana gyara zaman mayafinta a kafaɗart. Ɗagowar da za ta yi haka suka yi ido biyu da Fatima. Da ɗan gudunta ta ƙarasa ta rungume Fatimar tana faɗar “Oyoyo! Shegiyar gari! Me kika zo yi?”

Fatima ta janye jikinta ana Nu’aymah haƙora a yashe ta ce “Na zo gyara jarabawata ne a wurin Dr. Kar dai ki ce mini ke ma abin da kika zo yi kenan?” Ta gyaɗa mata kai alamun tabbatarwa.

A tare suka kece da dariya tare da tafawa. Fatima ta ce “Ke ma kenan mai ɗan ganewar balle ni. Wa ma zai bari ya sha ƙasa bayan Allah ya hore masa hanyoyin gyara? Ai kin taimake ni da kika koya mini wannan dabarar.”

Suka sake ƙyalƙyalewa da dariya tare da tafawa alamar zance ya yi daɗi, “Bari na shiga ciki kafin ya fita, gara ke kin fita wuya.” Cewar Fatima tana shigewa ciki da hanzari.

Nu’aymah ta koma gefe ɗaya ta zauna da nufin jiran Fatima don ba ta ƙoshi da ganin ta ba kasancewar akwai tarin tufkar da suka yi take neman hanyar warwara.

Bayan fitowar Fatima suka je kafteriya a can suka shiga tattauna abin da za su tattauna yayin da Madam ta kawo musu kayan ƙwalama suna ci suna ci gaba da hirar su. Ba su suka miƙe ba sai bayan awa ɗaya da yan mintuna suka nufi inda Nuaymah ta yi parking motarta. Ta danna mata key, tare da shiga mazaunin direba Fatima kuma ta nufi mazaunin mai zaman banza.

Kai tsaye unguwar su ƙawartata ta nufa ta sauke kan layinsu kana ta nufi gidanta.

Tun a hanya take yunƙurin amai, sai taso mata yake tana ji kamar za ta amaye zuciyarta. A haka ta daure ta ci gaba da jan motar a hanzarce don ta samu ta isa kafin mai afkuwa ta afku.

Da ƙyar da siɗin goshi ta samu ta ƙarasa ƙofar gidan ta fara bubbugawa da iya ƙarfin da ya rage mata.

Lokacin Salis na shirin fita kenan ya ci ado cikin dakakkiyar shadda fara da ake yi wa laƙabi da gizna, ya ɗaura tsadadden agogon iwatch a tsintsiyar hannunsa. Doguwar baƙar fuskar nan tasa ta yi fayau da ita cike da annuri.

A ɗan tsorace ya ja gajerun ƙafafuwansa ya nufi gyat ɗin don ƙwanƙwasar da ake yi masa ta wuce mizanin hankali.

Yana buɗe gidan ta afka ciki aguje tamkar wacce mahaukacin kare ya biyo ta nufi bakin rariya ta fara fesa amai. Ta fi mintuna biyar tana fesawa kamar za ta amayar da ‘yan hanjinta, kafin ta samu abin ya lafa mata. Ruwa ya ɗebo mata daga baƙin droom ɗin ruwan da ke ajiye a tsakiyar madaidaicin gidan, sannan ya miƙa mata butar yana jera mata sannu.

Ta karɓa ta wanke fuskarta sosai kafin ta ɗago tana sauke ajiyar zuciya a hankali. Nan da nan ya ga fuskarta ta canza, har ‘yar wata ramar wucin gadi ta yi, idanunta sun yi zururu kamar wadda ta kwana uku tana jinya.

Kama ta ya yi ya kai ta ɗaki ya kwantar da ita kan gadonta tare da ƙure mata fanka sannan ya koma waje ya ɗauki makullin da ta yada lokacin da ta shigo gidan. Bayan ya buɗe gate ya fita waje ya shigo mata da motarta ciki ya je ya kai mata makullin.

A lokacin ne da ya ga hankalinta ya dawo jikinta sai ya ce da ita “Wai me ya same ki ne haka?”

“Ni ma ban sani ba, amma ina zargin ko chips ɗin da muka ci a capteria ne.” Ta amsa a wahalce lokacin da take lafe luf a kan gado.

“Allah ya sawwaƙa, ku ne ba ku barin cin abincin da ba ku san tayaya aka dafa shi da yadda aka ajiye shi ba. Sau tari a irin wuraren siyar da abincin da ba a restaurant ba ko ma a gidaje ana barin abinci a buɗe koda mantuwa ko aikin ganganci, hakan ka janyo bushewar abincin ko kuma bayan ƙudaje sun gama yin salati a kansa sai a siyar muku. Ku kuma ku ɗura a cikinku ba tare da sanin illar da za ta biyo baya ba. Allah dai ya sawwaƙa.”

Ya ajiye zancensa yana juyawa da faɗar “Idan zan dawo zan biyo miki da magani, yanzu ina sauri ne zan je ɗaurin auren wani abokinmu.” Ba ta tamka shi ba don har a lokacin a wahalce take, har ta fara jin sabon tashin zuciya sai maida numfashi take.

*****

Tun lokacin da Salis ya fice daga gidan bai dawo ba har bayan magariba, haka ko a waya bai kira ta ba a ranta tana ta mamakin abin da ya sauya shi a yau. Iya abin da ta sani ba ya iya yin nisa da ita musamman a lokutan da take cikin jinya, amma yau sai ga shi ya ɗau tsahon lokaci ba ya kusa da ita duk da ya san tana buƙatar hakan.

Zuciyarta ta sosu ainun ga ciwo ga yunwa ga ba magani a gidan, shi da zai kawo mata kuma ya je ya mayar da gari nashi.

Da ƙyar ta samu ta tashi ta jona ruwan zafi ta haɗa baƙin tea mai na’a-na’a a ciki ta sha, don ba ta jin za ta iya cin komai duk abin da ta saka a bakinta yana isa cikinta zai biyo hanyar da ya shiga ya dawo. Ganin hakan sai ta haƙura da cin komai ta zubawa sarautar Allah ido.

Shiru-shiru har ƙarfe tara ba labarin Salis yadda ka san bawan da aka aika garinsu. Zuwa lokacin tsoro ya fara ɗarsar mata a rai, duk da ba ta fatan wani mummunan abu ya sami maigidan nata.

Cikin rawar hannu ta janyo wayarta ta fara laluben layinsa, sai dai ga mamakinta sai ta ji muryar matar kamfanin layi tana shaida mata wayar a kashe take, duk da haka ba ta haƙura ba ta sake gwadawa a karo na biyu, nan ma duk labarin bai sauya ba hakan ya ƙara sakawa hantarta ta kaɗa.

Abu kamar wasa sai da ta jera masa kira uku amma ba abin da ya sauya har a lokacin layin a rufe yake.

“Innalillahi wa Inna ilaihir rajiun! Meke faruwa?” Ta furta da kasalalliyar murya.

A lokacin ne kuma fargabar da take ciki ta ƙaru ga fargabar wannan ciwon da ya same ta take tsoron ko shigar ciki ne duk da ta tabbatar da cewa ta saka inflanon amma a firgice take kar ya zamana Allah ya yi ikonsa a kanta. Yanzu kuma ga fargabar halin da Salis yake ciki, zuciyarta ta shiga wani yanayi na ruɗu.

‘Shin meke faruwa da shi ne? Da gangan ya kashe wayarsa ko kuma ya afka wata matsalar ne?’ ita dai ta san tun da take tare da shi shekaru uku kenan wani abu makamancin wannan bai taɓa faruwa ba a tsakanin su ko da kuwa a lokutan da suka samu saɓani ne, iyakacin shi ya ƙauracewa shimfiɗarta ko kuma ya ƙi cin abincin da ta girka. Tabbas da walakin goro a miya.

<< Danyar Guba 3

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×