Skip to content
Part 2 of 6 in the Series Danyar Guba by Rukayya Ibrahim Lawal

Ji ta yi gabaki ɗaya jikinta ya yi mata nauyi, hakan ya sa ta kasa motsawa a take zazzaɓin da yake samamen ta ya yi mata dirar mikiya ganin iska na neman ƙurewa bodari.

Can ƙwaƙwalwarta ta hasko mata irin hotunan da ke ajiye a wayarta da ba ta so a gani, hakan sai ya zama makunnar kuzarinta ta yunƙura da dukkan ƙarfinta ta isa wajen Nusrat ta fisge wayar rai a ɓace tana faɗar “Matsalata da ke kenan, ki dinga yi wa mutum bincike awaya kamar kin ba shi ajiya.” Nusrat ba ta da mu da hakan ba ta ce “Yi haƙuri, ni dai so kawai nake na san waye wannan?”

Juyawa ta yi da nufin barin wurin ba tare da ta bada amsa ba, don kuwa ba ta ma san irin ƙaryar da suke so ta sake yi musu ba, tun da abu ne na zahiri ba za ta taɓa iya faɗa musu cewar saurayinta ba ne, don ko a garin gaɓa-gaɓa ba a wannan aikin. Kafin ta shige ta jiyo muryar Intisar da tun lokacin da aka fara hayaniya a falon ba ta ce komai ba, tana faɗar “Ke kuwa Nu’aymah ki amsa mata mana, kika sani ko ta ga ruwan da ke yi mata wanka ne?”

Juyowa ta yi ta fara bin fuskokinsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, a nan ta fahimci cewa gaba-ɗaya kallon zargi su ke yi mata, saboda haka ta ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali ta yi kafin ta ce “Ɗan gidan kawun Habibie ne da suke a garin Bauchi da matsala ne?” Ta ƙarashe tana kallon Nusrat lokaci ɗaya tana mamakin ƙaryar da bakinta ya furta kai tsaye ba tare da sanin daga inda ta samo dabarar hakan ba.

Nusrat ta yi ƙayataccen murmushi tana faɗar “Allah ne ya san karatun kurma, amma dai abu ɗaya zan faɗa, gayen ya burge ni.”

Gabaki ɗaya sauran ‘yanmatan suka bushe da dariya suna tafa hannu, “An kira sallar magariba ku tashi ku yi sallah ku je gida kar dare ya yi muku, da alama yau za a yi sanyi sosai.” Nu’aymah ta faɗa a yunƙurinta na ɓagarar da maganar sannan ta shige ɗakinta tana sauke ajiyar numfashi.

Jin hakan ya saka dukan su suka ɗunguma zuwa waje suka ɗoro alwala, suna nan suka ga Salis ya fito hannuwansa da fuskarsa suna ɗigar da ruwa alamar alwala ya yo, nan ya wuce su ya tafi masallaci a ransa yana faɗar ‘Masu bin ƙwaƙwafin tsiya, a dai samu a yi muku aure mu huta da wannan zaryar sa’idon da kuke yi mana.’

Bayan sun gama sallah suka sha baƙin shayi da biredin sannan suka fara shirin tafiya. Ashna ce ta kalli sauran ‘yan’uwanta ta ce “Af na manta da saƙon mama, da ko an yi karen aiki.”

Ba ta jira an tamka mata ba ta nufi uwar ɗakan Nu’aymah ta same ta zaune a kan sallaya ta kifa kanta a kan gado.

“Sannu anti zazzaɓin ne?” Da kai kawai ta yi mata alamar I ba tare da ta ɗago ba.

“Da ma mama ce ta aiko ni wurinki, ta ce don Allah idan akwai ragowar maggi ko omo da sauran kayan amfanin gida ki haɗo mata, kin san dai a yanayin da ake ciki, kuma Abba ba bayar wa yake yi ba.” Cewar Ashna.

Sai a lokacin Nu’aymah ta ɗago kanta a ranta tana jin haushin ɗabi’ar mamansu ta yawan roƙo, ƙarin haushin ma har gidan surukanta ba ta bari ba. Cikin wannan takaicin ta fuskanci ƙanwarta da ƙanƙantaccen ido ta ce “Kin san Allah! Yadda kika ga kitchen nan a bushe haka yake kwana biyun nan, ke ma dai shaida ce Salis ba shi da aikin fari balle na baƙi, mu ma ‘yan dubaru ne kawai mu ke ci, ki san yadda za ki ba ta haƙuri idan kin koma.”

Ashna jiki a sanyaye ta gyaɗa kai alamar gamsuwa a lokacin ne sauran ‘yan matan suka leƙo suka yi mata sallama tare da ɗaukar ledar jiƙaƙƙun kayansu da alƙawarin idan sun dawo watarana za su kawo mata tufafinta. Sai a lokacin ta tashi da ƙyar ta sanar da mijinta cewar za su tafi, dawowarsa kenan daga masallaci a falon ma ta same shi.

Dubu ɗaya ya ciro daga aljihunsa ya miƙa wa Intisar yana faɗar “Ga wannan kwa yi na mota, ku yi haƙuri garin a bushe yake.”

Intisar ta amsa suka yi masa godiya sannan suka fice daga gidan suka nufi titi a lokacin har duhu ya fara sauka ga unguwar ta yi tsit ba kuma wutar lantarki kasancewar idan ana ruwan sama ba a cika bayar da wuta ba.

Har titi ta raka su sai da ta tabbatar sun wuce sannan ta juyo zuwa gidanta. A ƙofar falo ta same shi daga waje yana ganin shigowar ta ya juya ciki, ita ma ta kunna kai cikin falon, dai-dai nan hasken wutar lantarki ya mamaye ilahirin falon.

Kamar zai zauna sai kuma ya ja hannunta yana nufar hanyar cikin ɗaki da faɗar “Mu je ki ba ni kaso na Habibtie jan ran nan ya fara yin yawa.”

Ƙwace hannunta ta yi tana faɗar “Uhm! Gaskiya ni yanzu yunwa nake ji ka nemo mana wani abu na ci, gama ko lafiya ba ni da.” Ta ƙarashe zancen tana nufar kujera tare da zaunawa ta langaɓar da kai. Matsowa ya yi kusa da ita yana faɗar “Kuɗin da ya rage mini kenan na ba wa ‘yan’uwanki kawai ki tashi ki ban kaso na ko na samu na siyo mana abincin ni kaina yunwar nake ji.” Ba don ta so ba amma a haka ta miƙe tana tafiya solai-solai kamar wacce ta shekara tana ciwon ƙafa. Tana tafiyar tana mita murya ƙasa-ƙasa “Ni na rasa inda kake kai kuɗin idan an ba ka, a ce mutum kwata-kwata kuɗi ba ya albarka a hannunsa kamar waɗanda yake cinnawa ashana?”

Ya ji ta sarai sai dai kuma bai sake tamka ta ba sai zarya da ya shiga yi daga tsakiyar falon zuwa ƙofar ɗakinsa yana jiran fitowar ta. Ko mintuna biyu kyawawa ba ta rufa a ciki ba sai ga ta ta fito da jakar gaba ɗaya.

Hannu na ɓari ya warce jakar ya ciro kuɗin tare da daɓashewa kan kafet yana kece rafar da niyyar ƙirgawa har hannunsa na rawa.

Duk da zazzaɓin da ke jikinta bai hana mata biye masa su yi abin da suka saba yi ba. “Sannu fa Habibie! Wannan shi ne kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi.” Ta faɗa tare da wawuro kuɗin ta mayar a gabanta tana aika masa harara tare da murguɗa masa baki.

“Ni ne gardin?” Ya faɗa yana nuna kansa da yatsa. Ba ta tamka shi ba sai ma mayar da hankalinta a kan kuɗin da ta yi, ta ƙirga dubu hamsin cas ta miƙa masa tana faɗar “Sai ka sake mini kurwa ko?” Ya karɓe yana washe haƙora kamar gonar auduga sannan ya shiga ƙirga su don ya tabbatar ba ta yi masa rinton da yake ta mita a kai ba.

Ita kuma ta kwashe nata tana mayarwa a jaka da faɗar “Allah mutumin nan na sangarta ka da yawa, don ma dai ka yi sa’a ina matuƙar ƙaunarka ne da kai ka ma isa ka ji ƙamshin wannan kuɗin? Tab!” Ta faɗa tana miƙewa tsaye ta nufi hanyar ɗakinta. Dariya kawai ya yi, don kuwa ba yau suka fara hakan ba. Duk lokacin da za su raba kuɗi sai sun yi don haka abin bai dame shi ba sam. Hankalinsa a kan kuɗin ya ce me za a siyo miki Habibtie?”

Har ta shige daga ciki ta ƙyaro masa magana “Gasasshiyar kazar Suya Spot da Holandia mai sanyi. Kuma babban kwali fa.” Ya yi ɗan murmushi cike da tsolaya ya ɗan ɗaga murya yadda za ta ji ya ce “Ki kawo kuɗinki to Hajiya.”

“Tab! Alaji son banza kai za ka siyo mini, haƙƙin ciyarwar a kanka ya rataya ai.” Murmushi mai sauti ya yi kana ya miƙe ya fice. Nu’aymah da ke kwance kan gado ta ja bargo tare da lulluɓe gaba-ɗayan jikinta, a lokacin ne ta jiyo tashin babur ɗinsa da ƙarar buɗe babban ƙyauran gidan da ya yi ya fita.

Tun bayan ficewarsa jikin nata ya ƙara tsananta ga cikinta da take ji a kwakware rabon ta da abinci tun sha biyun rana. Da ƙyar ta janyo lokar gefen gadonta ta ɓalli pracitimol guda biyu, ta miƙe zaune tare da janyo robar ruwan da ke kan bedside drawer ɗin ta sha sannan ta kuma kwanciya. Daga nan ba ta sake sanin wainar da ake toyawa ba a duniyar, sai a lokacin da ta ji ana bubbuga gadon da take kai a kwance. Ta yi Firgigit ta farka tana rarraba idanun da suke gani dishi-dishi.

Hasken da ya samu kafar shigowa ɗakin ta ƙofar da ke a buɗe ne ya jagoranci ganinta har ta iya hango mutum tsaye a kanta riƙe da yaluwar leda a hannunsa.

“Ki tashi ki ci abincin.” Ya ce da ita yana ajiye mata ledar a kan bedside durowa sannan ya fice zuwa waje.

Sai a lokacin ta tuna cewa ya je nemo musu abin taɓawa ne, ta lalibo wayarta da ke ƙarƙashin filon da ta yi matashi da shi tare da kunna ta. Ta sauke dubanta kan manyan lambobin da ke damɓare kan fuskar wayar da suke nuna lokaci.

Ƙarfe goma da mintuna hamsin ta gani hakan ya sa ta ɗago fuskarta cikin maɗaukakin mamaki ta sauke ganinta a kan fuskar shi yayin da yake shigowa riƙe da filet da glass cup a hannunsa.

“Wai kana nufin sai yanzu ka dawo?” Ta watsa masa tambaya tana ƙoƙarin sauko da ƙafafunta ƙasa. Kayan kawai ya ajiye mata bai ce komi ba sai ita ce ta sake cewa “Ina ka tsaya ne haka?”

Nan ma kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce “Manta da wannan, tashi ki wanko baki ki zo ki ci abincin nan kar yunwa ta illata mini ke.” Ba ta ce masa ci kanka ba sai dai ta bi shi da kallo mai ma’anoni wanda hakan ya haska masa kamar tana zarginsa a kan jimawar da ya yi. Wanko bakin nata ta yi ta dawo ta zauna gefen gadon tana buɗe murfin kwalin Hollandiar ta tsiyaya a kofin ta hau sha.

Sai a lokacin ya ce da ita “Habibtie ya jikin?” Ba ta kalle shi ba ta amsa da “Da sauki, farkawan nan da na yi na ji zazzaɓin ya yi ƙasa.”

Tana gama shanye na cikin kofin ta ajiye kofin tare da sake jan bargo za ta rufa.

Ya kalle ta yana faɗar “Ita kazar fa.”

“Za ta iya saka ni amai, zan ci da safe.” Tana gama faɗa ta ƙarasa rufe fuskarta tare da lumshe ido ta koma bacci.

Ba ya son takura mata don haka ya ɗauki kazar ya saka mata a ƙaramar firizarsu da ke ajiye cikin barandar falo, ya koma ciki yana kulle ƙofar falon daga ciki. Bayan ya ja mata ƙofar ɗakinta ya nufi nasa yana zuba murmushi wanda kallo ɗaya za ka yi masa kasan wani abu ne ya faranto masa rai a waje.

‘Allah ya kai damo ga harawa.’ ya faɗa a ransa a lokacin da ya zauna kan gadonsa ya kunna wayarsa yana neman wani layi.

*****

Ba ita ta farka ba sai wajajen ƙarfe takwas da rabi na safe, a maimakon ta buɗe ido da addu’a a kan leɓɓanta sai kawai ta buga wata uwar hamma tana miƙa, har sai da ko wace jijiya ta jikinta ta motsa. Can bayan wasu daƙiƙu idonta ya washe sosai ta sauka daga kan gadon ta shiga banɗaki ta wanko fuskarta ta fito, ba zancen sallar asuba a gaban ta, ba kuma wani uzurin ne ya hana ta ba kawai sabo da yi ne wai gawa da gatsine, don haka sai ta fice zuwa nashi ɗakin.

Ta yi mamakin ganin har lokacin bai farka ba, sai dai hakan bai wani dame ta ba ta je waje tare da buɗe firiza. Kamar yadda ta yi tunani a ciki ya ajiye mata kazar da ragowar lemonta sai kawai ta ɗauko su ta shiga madafa ta kunna gas ta ɗumama kazar ta juye a faranti ta dawo falo.

Alhamdulillah koda ta tashi ba sauran zazzaɓi ko ciwon kai a tare da ita, hakan ya ba ta damar ta ci ta yi ƙaat kafin daga bisa ni ta je ta ɗora masa ruwan tea ta soya masa wainar ƙwai. Ta juye a faranti mai kyau ta rufe da wani. Kitchen ɗin ta fara gyarawa sannan ta koma uwar ɗakanta tana karkaɗe shimfiɗa. A lokacin ne ta ji ƙarar buɗe ƙofarsa ya fito yana mitsittsika idanu.

Ɗakin nata ya ƙarasa yana kallon hasken da ke shigowa ta windunan da ta yaye labulensu don ta ga haske sosai, ya fara magana a cikin nannauyar murya “Wai har rana ta fito?”

Ci gaba da cusa fillow a cikin rigarsa ta yi ba ta kalle shi ba ta ce “Da ranar za ta jira har ka tashi ne kafin ta fito?” Bai ce da ita kanzil ba ya juya zuwa ɗakinsa ya ɗora alwala ya gabatar da sallar asuba sannan ya sake fitowa ya zauna a kan kujera mai cin mutum ɗaya, lokacin ne ita kuma ta fito cikin adon riga da wando panjamas sai ƙamshi take ta shiga kitchen ta fito masa da abincinsa ta jere masa a kan ƙaramin table ɗin da ta sanya a gabansa.

Sai da ya ƙare mata kallo tsaf kafin ya buɗe ledar biredin a ransa yana faɗar ‘Lallai ma matar nan, yanzu cinye kazar ta yi? Da ban ci a waje ba fa?’ a zahiri kuma sai ya ce “Ki shirya da wuri na kai ki gidan ƙunshin nan, kin san yau ne fa kamun da Ma’aruf ya gayyace ki, so nake ki yi kyau sosai yadda ba zai ji ciwon ba ki kuɗi masu ciwo ba.”

Ta jefe shi da murmushi tana gyara zamanta a kan kujerar da ke fuskantarsa sannan ta ce “Na so na sha’afa ma, amma ba komai za mu iya fita tun ƙarfe goma don daga nan ma ina so zan je saloon, ga zuwa wurin kwalliya ma, yau fa mai wuni ce fitar.” Zuƙar shayinsa ya yi ya haɗiye biredin da ke bakinsa kafin ya ce “Ba damuwa Allah dai ya ba mu sa’a.” Ta amsa masa da amin sannan ta tashi ta ci gaba da sabgogin gabanta.

*****

Da misalin ƙarfe biyar na yammacin ranar ta alhamis Nu’aymah ta yi wa ɗakin taron zobe, a yangance ta ƙarasa cikin hall ɗin lokacin an kashe sautin kiɗa ana ƙoƙarin sauyawa da wani. Ƙarar haɗuwar tsinin takalmin ƙafarta da shimfiɗaɗɗen tiles ɗin da ya mamaye ilahirin hall ɗin ne ya janyo hankalin mafi yawancin mazauna hall ɗin musamman maza. Wasu daga cikin su suka kafe ta da ido ko ƙyaftawa basa yi. A lokacin ne Ma’aruf ya miƙe yana ƙare mata kallo daga nesa.

Matashiyar budurwa ce da a shekaru ba za ta haura shekara sha takwas ba. Sanye take cikin doguwar rigar yadi light pink mai sassauƙan zane da ya sha adon ƙayataccen ɗinki mai hannun net, rigar ta ɗame jikinta sosai wanda hakan ne ya bayyanar da asirin fasalin jikin nata. Doguwa ce a zubin halitta, siririya a yanayi na ƙirar jiki. Tana da faɗi daga ƙasa cikinta a shafe kamar filasta saman kuma ya yi tudu, a taƙaice dai tana da ƙira irin ta kwalbar fanta, banbancin su da kwalbar Kawai shi ne ita bayanta ba a lotse yake ba.

Da murmushi a fuskarsa ya ɗaga duban shi ya sauke idanunsa a kan faffaɗar kewayayyiyar fuskarta mai ɗauke da manyan idanuwa da ɗan madaidaicin hanci da madaidaicin baki mai ɗauke da Laɓɓa masu kauri da duhu sosai. Fuskar nan ta sha make-up dalilin da ya sanya shi tsayawa muhawara da zuciyarsa kenan, yana ƙoƙarin tantance ita ce ko wata.

Kafin ya yi wani kyakkyawan motsi tuni ta ƙaraso gabansa tana faɗar “My king wannan kallon fa? Ai sai ka sa na tintsire.”

Murmushi ya sakar mata da faɗar “Sannu da zuwa Queen mu je mu zauna. A dai-dai lokacin ne kuma masu kula da kayan sauti suka sako wata waƙar soyayya ta Ingilishi mai armashin gaske.

Don haka sai waƙar ta saukar musu da yanayi na masoya a fuskokinsu, ba ɓata lokaci suka saƙalo hannun juna suka ci gaba da takowa zuwa mazauninsa da ke gefen dama na ɓangaren ‘yan ango.

Idanu ne suka yi yawa a kan su wasu na yi musu kallon birgewa wasu kuma suna yi musu kallon mamaki. Zahiri ba wai suna mamaki ba ne a kan kalar suturar da ke jikinta saboda ita ce kalar suturar da ke sanye a jikin kowacce macen da ke hall ɗin kasancewar shi ne ankon kamun na mata, kawai dai suna mamaki ne a kan yadda matasan suka saje da yanayi na masoya musamman ga waɗanda suka san Ma’aruf da matarsa sun kuma tantance wannan ba ita ba ce.

Suna ƙarasawa wurin ƙayataccen teburin na musamman da aka tanadar don manyan abokanan ango ya ja mata kujera a kusa da ta Mariya budurwar abokinsa. Ta zauna a kai shi kuma ya zagaya ɓangaren ta na dama ya ja kujerarsa ya zauna. Da yake table ɗin rounded ne sai aka zagaya masa chairs, babba ne sosai, wurin zaman mutum shida ne.

Waiters da suke zagaye a hall ɗin riƙe da teburin abinci na zamani suna turawa ne suka tokare tayar teburin nasu a gaban teburin na su Ma’aruf, sa’annan suka cika musu teburin da kayan maƙulashe da abinci iri-iri. Akan idanunta sauran ‘yan matan da ke zaune a kan teburin suka fara cin nasu ba jira, sai dai ita rawanin tsiyar da ta ɗorawa kanta ya hana ta ci duk da yawunta sai tsinkewa suke, musamman da ta sauke dubanta a kan kyakkyawan farantin ƙashin da aka ciki shi dam da snacks, meat pies, donuts, Samosa, cakes, pizza wasu ma har ba ta san sunan su ba.

“Ki ci wani abu mana Queen.” Tana wani shan ƙamshi da ɗage kai ta ce “Ai zan ci ne…”

Dai-dai lokacin muryar m.c ta karaɗe ɗakin taron yana faɗar “Yanzu kuma lokaci ne na babban aminin ango wato Ma’aruf Salisu. Idan Ma’aruf yana kusa muna son ganin shi tare da iyalinsa ko budurwarsa a kan wannan dandamali.”

Jin wannan ya sa Ma’aruf ya dubi Nu’aymah da ke zaune a kusa da shi ya ce “Queen mu je ko?” Ba musu kuwa ta miƙe suka jera suna takawa zuwa saman dandamalin.

Mc da yake bakinsa ba mutuwa yake yi ba sai ya hau bakinsa “Wow! Abin burgewa, wannan zazzafan aminin angon ya yi katari da zazzafar budurwa, a yanzu kuma lokaci ne da za mu sanya musu kiɗa domin su zazzagar da zallar farincikinsu a wannan ranar.”

Yana rufe bakinsa ya yi wa D.J umurnin da saka waƙar ƙauna mai armashi.

A hankali suka fara takawa, da ma ga ta gwanar iya rawa sai ta saki jiki sosai suka sha rawa ita da shi, ango Sagir da amaryarsa da sauran masu son su burge Ma’aruf ɗin suka fito suna yi musu ɓarin nera. Sadiq ɗan gidan aminin Abban Salis kuma ɗa ga gwaggwonsa ya miƙe yana ƙara kafe ta da ido don tun a lokacin da suka zo wuce wa ta gabansa yake ƙare mata kallo yana son tuna inda ya san fuskar.

‘Kai! Kamar matar Salis ce fa.’ zuciyarsa ta tsegumta masa, ya so ya yarda da hakan sai ya samu kansa da tuhumar kansa “Me zai kawo matar Salis a nan, kuma tare da wani saurayi?’ ya jefa wa kansa tambayar. ‘Amma fa kamar tasu har ta ɓaci idan har ba itan ba ce.’ Ya sake rayawa a ransa, Kodayake Allah ya taimake ta an yi mata irin kwalliyar nan mai canzawa mutum kammani, amma duk da haka ya so ya tantance ta. Da dai ya ga zai shiga ruɗani sai ya yanke a zuciyarsa zai samu wanda zai tambaya don ya tantance. Dalili kenan da ya sanya shi komawa ya zauna har suka gama rawar su suka koma mazauninsu.

<< Danyar Guba 1Danyar Guba 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×