Skip to content
Part 3 of 4 in the Series Danyar Guba by Rukayya Ibrahim Lawal

Sai bayan sallar isha’i adaidaita ta sauke Nu’aymah a kan layinsu ta gangaro zuwa gidanta da ƙafa. A kulle ta tarar da gidan, da mamaki take kallon kwaɗon da ke sarƙafe a ƙofar tare da buɗe jakar hannunta ta ciro mabuɗi a ranta tana mamakin yaushe Salis ya ari ƙafar shanshani, ita dai a iya sanin ta da shi a masallacin layinsu yake sallar isha, ranar da ba ya jin bin jam’i ma a gida yake yi. Kuma daga ya shigo shi kenan ba ya sake fita in dai ba wani uzuri ne ya kama shi ba.

Amma tsakanin jiya da yau ta fara lura da yanayin canji a tare da shi.

‘Bari na ga yau ko sai ƙarfe nawa zai dawo?’ ta faɗa a ranta tana shige wa gidan tare da sanya sakata a ciki.

Kai tsaye uwar ɗakanta ta shige ta cire takurarriyar rigar da ke jikinta ta canza zuwa riga da wando na bacci sannan ta shiga banɗaki ta wanko fuskarta da sabulu ta dawo falo ta baje tana kallon tashar Bollywood a ƙaramin plasma da ke manne a bangon ɗakin.

A ƙoshe take don ta riga ta cika cikinta da kayan sharholiyar wurin kamun masu daɗin gaske, don haka ranta fari ƙal kamar farar takarda ta ci gaba da kallonta.

Kira ne ya shigo wayar ta duba, ɗaya daga cikin maneman ta ne don haka ta ɗaga wayar bayan sun gaisa yake tambayar ta ina aka kwana da zancen su na turo magabatansa?

Wiƙi-wiƙi ta yi da ido kamar wacce ta yi gulma aka kama ta a ranta ta ce ‘Abin ya zo in ji mai tsoron wanka.’ A zahiri kuma wani zancen daɗin bakin ta shiryo ta feshe shi da shi. “Kar ka wani damu tun da ina sonka. Matsalar ɗaya ce abbanmu ba zai taɓa yarda ya yi mini aure ba har sai na ƙare karatuna ga shi kuwa a level 1 nake, ban sani ba ko za ka iya jira zuwa lokacin.”

A can ɓangaren da muryar damuwa wanda ke kan layin ya ce “Tsakani da Allah nake sonki, don haka zan jira komai tsawon zamani in dai za a ba ni ke.”

Dariya ta yi masa a ranta tana cewa ‘Ɗan wahala, ai ni na riga na auru sai dai kuma in ba ran Salis.’ can ta tuna tana kan waya ne don haka ta datse zaren zancen zucinta ta samu ta lallaɓa shi da kalamai masu daɗi ya kashe wayarsa ita kuma ta ci gaba da kallon fim ɗin Dhoom 3 da suke haskawa a lokacin, don ba ta gajiya da kallon shi koda sau ɗari za a haska in dai da sarari to sai ta kalla.

Shiru-shiru ba Salis ba labarin shi har wajajen ƙarfe goma, ta so ta kira shi ta ji ko lafiyarsa sai kuma ta ce a ranta ‘Bari na ga gudun ruwansa.’ Dalili kenan da ya sa ta fasa kiran shi ta ci gaba da gadin gida da ƙirgen lokaci. Sai ƙarfe goma cif-cif ta ji ya ƙwanƙwasa ƙyauren ƙofar.

A lokacin har ta fara gyangyaɗi don akwai gajiya sosai a tare da ita. Don haka sai ta yi kamar ba ta ji ba saboda ba ta son tashi. Sai da ya buga sau uku kafin ta miƙe tana murza ido da lumsashe su ta je ta buɗe masa.

“Sannu da dawowa.” Shi ne kawai abin da ta ce da shi cikin hamma, ta juya ta koma inda ta fito.

Can kamar bayan daƙiƙu biyu muryarsa ta wanzu a falon yana sallama. Ta amsa masa, bayan ya ajiye baƙar leda viva da ya shigo da ita ya nemi wuri ya zauna kan kujera yana sauke gajiyarsa a kai.

“Tun yaushe kika dawo ne?” Ya jefa mata tambaya, “Na fi awa biyu a gidan nan, ina ka je ne haka?”

Sosa ƙeyar kansa ya yi kafin ya ce “Daga wurin wani abokina nake, kin haɗu da wata fuskar sani a wurin kamun ne?” Ya ƙarashe zancen da tambaya.

Fargaba ce ta ziyarce ta, har ta buɗe baki za ta yi magana hamma ta ci ƙarfinta, don haka ta jira sai da ta kammala yin ta sannan ta ba shi amsa da cewa “Gaskiya ban lura da kowa ba a wajen, me ya faru ne?” Tana jefa masa tambayar ta miƙe ba tare da ta jira cewarsa ba, ta nufi waje don ta wanko fuskarta. Saboda ta gama lura cewar idan ba hakan ta yi ba baccin ba zai saki idon ta har ta iya saurarar zantukansa da take tunanin suna da matuƙar muhimmanci ba. Shi ma bai yi yunƙurin dakatar da ita ba sai raka ta da ido da ya yi.

Bayan wasu daƙiƙu ta sake shigowa ta zauna kusa da shi tana goge ruwan fuskarta da ƙyallen da ke kusa da ita, ta ce “Ina jin ka Habibie, me ya faru?”

Murmushi ya yi kafin ya ce “Yanzu daga gidan gwaggwo Asabe nake. Ta can na biya bayan na fito wurin abokina shi ne na haɗu da Sadiq ya tare ni da zancen ya gan ki a wurin kamu da wani kuna rawa.” Zazzaro ido waje ta yi tare da dafe ƙirji ta ce “Na shiga uku! Habibie me ka ce masa to?”

Ya kalle ta da wutsiyar ido, “Ni ma na tsorata a lokacin, sai dai kuma na dake zuciyata na ce da shi ba ke ba ce yau duk kina gida ba ki fita ba, amma don Allah ki rage zaƙewa idan kin fita saboda tsaro.”

Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta sauke tana ƙara matsowa kusa da shi ta ce “Na gode Habibie ka rufa mini asiri. In sha Allah zan dinga kulawa.”

Ya yi busasshen murmushi yana faɗar “Na dai rufa mana asiri, ke idan murfin wannan sirrin ya ɓalle ai har da ni ina ruwa.” “Kuma fa haka ne.” ta faɗa tana dariya ta ba shi hannu suka tafa. Shi ma dariyar yake kaɗan-kaɗan.

Bayan sun natsa da dariyar ya ce “Ya to, yau me aka samo mana?”

“Me ko, ka san biki ne ai. Amma dai ai kasan ya biya kuɗin wannan fitar kafin ma a yi ta. Sai dai akwai wani albishir.”

Ya juyo tare da mayar da hankalinsa kacokan a kanta tun bai yi magana ba ta fahimci yana yunwar jin albishirin don haka ta ce “Ya yi mini tayin aikin jarida a wani gidan rediyo, ya ce zai samo mini amma sai na kawo shaidar kammala diploma a ɓangaren. Sanin kanka ne kuma ko shaidar kammala sakandare ba ni da shi.”

‘Tofah! A na wata ga wata, wannan shi ne ga ƙoshi ga kwanan yunwa.’ Salis ya faɗa a ransa a zahiri kuma ya ce “To ke me kika ce masa?”

“Ce masa na yi jarabawata ta kammala sakandare ba ta yi kyau ba, shi ne nake ƙoƙarin gyarawa a wannan shekarar. Kuma ya gamsu da hakan har da alƙawarin ba ni tallafin kuɗin gyaran, duk da cewa bai san ya iyayena za su kalli abin ba a faɗarsa.” Ta ƙarashe tana ‘yar dariya Salis yana taya ta, kafin daga bisani ya ce

“Na san me zan yi. Zan biya kuɗi a zana jarabawa da sunanki immediately idan za a fara waec ta bana, akwai yayan abokina vice pc ne a Fgc Federal Government Collage sai a miki a can.”

Sosai ta yi murnar jin wannan albishir nasa tsabar farinciki sai da ta rungume shi suna ta murnar ƙara samun dama a gaba. Ita da shi sun manta cewa idan an dafa a ɓoye ba fa za a ci a ɓoye ba.

Janye jikinsa ya yi daga nata ya ce da ita “Ɗauki wannan ledar ki jera kayan a firiza.”

“Me ye a ciki?” Ta jefa masa tambaya tana yunƙurawa don ta tashi, saboda har a lokacin baccin bai sake ta duka ba.

“Lemuka ne iri-iri tun daga kan na roba zuwa na kwali da kuma ‘ya’yan itace, nasan ke ba ki fiye cin abinci mai nauyi ba.” Ba ta ce komai ba ta kwashe kayan ta fita. Bayan ta cika umurninsa ta nufi ɗakinsa don kwanciya.

*****

Bayan kamar wata uku Salis ya zo mata da takardun shaidar kammala sakandare masu kyau da suke ɗauke da sunanta ya miƙa mata. Ta yi farinciki sosai kamar ta taka rawa. Yanzu shi kenan za ta zama ‘yar boko za ta ƙara gogewa kuma ta iya turanci sosai. A ganin ta wannan dama ce da za ta ƙara samun shiga wurin mazaje masu yatsu da yawa da suke son yin mu’amala da wayayyin mata. Rashin yin bokon ya taka muhimmiyar rawa wurin tauye wayewarta da hana mata samun wasu damarmaki da tana ji tana gani suke yi mata suɓucewar da ƙwallon mangwaro kan yi a hannun kuturu saboda hakan.

Ranar sai da ta yi wa Salis girki na musamman a cikin aljihunta. Ya ga tarairaya sosai a ranar, ya san kuma ba don komai ba ne sai don farin cikin abin da ya samo mata duk da cewa ko a baya tana kyautata masa iya iyawar ta saboda tana son shi sosai. Zaman lafiya suke shimfiɗawa sosai a gidan auren nasu duk da daga shi har ita ba wanda yake zama a gida. Har gara shi ma ya fi ta kasancewa a gida tun da ba shi da wata ƙwararriyar sana’a ko aikin yi. Idan aka ga ya fice daga gidan to wani uzuri ne na kansa, ko kuma ya je ‘yan buge-bugensa a gari. Amma ita matar tasa kullum tana hanya kamar shanshani, maƙwafta duk sun gama saka mata ido har ana buga misali da ita.

A wannan ranar dai ba a kwana ba sai da ta kira Ma’aruf ta shaida masa takardun ta sun kammala. Shi ne wanda ya yi tsayuwar daka ya jajirce har ya samo mata gurbin karatu a PlaPoly da ke cikin garin jos ɗin, haka shi ne wanda ya biya kuɗin registration nata.

Duk wannan hidimar da yake yi mata ko sau ɗaya bai buƙaci sanin adireshin gidan su ko kuma haɗa alaƙa da wani nata ba. Hasali ma duk za su haɗu shi ne yake ba da wuri da lokaci sai dai ta same shi a can. Ita kanta ba ta damu da hakan ba, da yake ita ma ba wai don Allah take son shi ba kawai tana bin shi ne don kuɗin da ke hannunsa, kuma yake jiƙa ta da su kusan koyaushe.

Shi Ma’aruf irin mazan nan ne da za su iya kashe ko nawa ne a kan mace matuƙar za su samu kulawar daga gare ta, koda a ce kuwa ba sa yin wata ƙazantacciyar mu’amala, muddin za ta dinga washe masa haƙora tana yi masa hira da kalamai masu daɗi to ba abin da ba zai iya yi a kanta ba.

*****

A wannan gaɓar ta ga ya kamata a ce sun shirya wa fuskantar karatun, da daƙile duk wata hanya da za ta iya janyo musu matsala ko ta zama silar tonuwar asirinsu. Don haka ta sami Salis da zancen.

Lokacin da ta zo masa da zancen da yamma ne yana zaune a tsakar gida kan dandamalin barandarsu da ya kasance na siminti yana faman danna waya. lissafi yake na wasu kuɗi masu nauyi da yake tsammanin saukar su a aljihunsa. Abin da yake ba komai ba ne face lissafin Duna, ma’ana dai yana ta lissafin gaibu ne. Tun da yana sane da cewa bai zuba hannun jari a ko’ina ba balle ya ce ƙirgen riba yake yi.

Bai san da wanzuwar ta a wurin ba har sai da ta dafa kafaɗarsa tana faɗar “Wai lissafin me kake yi ne haka?” Sai a lokacin ya ɗago ya kalle ta, “Ke dai bari kawai, wasu kuɗi ne da muke dakon zuwan su ni da Amiru.”

“Kun fara kasuwanci ne?” Ta faɗa tana zama daf da shi. Kashe wayar ya yi ya tura a aljihu kafin ya ce “A’a! Sai dai ‘yan dabarun da aka saba, kin san mu ba ma cin biri sai dai mu ci dila.”

Ta yi ‘yar dariya har haƙoranta suka bayyana ta ce “To Allah ya kama. Da ma na zo mu yi wata shawara ne.”

“Ina jin ki to.” Ya faɗa yana fuskantar ta tare da mayar da hankalinsa kacokan a kanta.

“Da ma na ga shirin fara karatuna ya kammala shi ne na ga dacewar mu shirya komai a tsari yadda haƙarmu za ta cimma ruwa ba tare da mun kuskurewa idaniyar ruwan ba.”

“Me kike ganin yakamata mu yi?” Ya tambaye ta yana ƙara saita nutsuwarsa tare da zuge tazugen kunnensa don saurarar samfuran jawaban da za su zama amsar tambayarsa.

“Abu uku ya kamata mu yi, na farko dai zan yi ƙoƙari na cafcafta ‘yan kuɗin hanuna na sayi mota koda mai arha ce na je na koyo tuƙin saboda zaryar makaranta da ƙara kankaro ƙima kamar yadda wayar hannuna ke kare mini yawa. Na biyu dole sai mun yi family planning gudun ɗaukar ciki yayin da nake karatu idan ciki ya bayyana sanin kanka ne ba iya karatun ba komai zai wargaje don ba wanda zai sake yi mini kallon budurwa balle ya taya. Sai na ukun dole ne ka ci gaba da kawar da kai a duk lokacin da hanya ta haɗa mu a waje kamar yadda ka saba yi don gujewa zargi.”

Gyaɗa kai sama ya yi alamun gamsuwa kafin ya ce “Tabbas kin zo da shawara mai kyau, za a yi hakan shawara ta biyu ce nake ji miki tsoron a yi amfani da ita saboda lafiyarki. Kuma Allah ya sani ina son haihuwa don dai Allah bai kawo ba ne.” Ya ƙarasa zancen yana miƙewa ita ma ta miƙe ta bi bayansa zuwa ciki tana ƙara jaddada masa alfanun yin hakan, da ƙoƙarin wanke masa damuwarsa da faɗar “Ai iya planning na shekaru biyu zan yi daga na gama karatun ka ga haihuwa ba matsala.” Shi dai bai tamka mata ba duk da cewa ba wani zurfi ya yi sosai a karatun Muhammadiya ba amma ya san cewa Allah shi ne yake ƙadarta samuwar halitta da jefo ta a duniya a duk lokacin da ya so komi planning ɗin da aka yi kuwa.

******

Bayan shuɗewar kwanaki biyu ya goya ta a Babur ɗinsa suka je asibiti aka sanya mata roba (inflano) bayan an jere mata matsololin da akwai yiwuwar samun su bayan an saka mata robar. Amma da yake idanunta a makance yake da neman duniya sai ta sa ƙafa ta yi fatali da shawarorin da likitar ta ba ta a kan cewar da ta bari ta yi haihuwar fari kafin ta saka.

Ganin ta ƙi jin shawara likitar ta gudanar da aikinta. Bayan wasu awanni suka fito daga asibitin suka nufi kasuwa don yin sayayyar abubuwan da za ta buƙata don fara zuwa makarantar. Sai da yamma lis suka dawo gidansu.

*****

Ranar wata litinin tun da hantsi Nu’aymah ta gama shirin ta tsaf ta fito sanye cikin rigar yadin roba fara wacce aka yi wa ado da zanen fulawa bulu, ba ta yi kwalliya ba ko kaɗan iya kwalli da man leɓe ta saka ta fito suka yi break fast ita da mijinta sannan ta ɗauki hijabin ta bulu da ta ajiye a kan kujera ta saka, ta ce da shi.

“Mu tafi ka sauke ni inda za mu haɗu da shi ko?”

Ya kalle ta sosai. Hijabin ya yi mata kyau duk da ba ɗabi’arta ba ce saka shi, kuma iyakacinsa gwuiwa amma sai ya ga kamar shigar ta fi yi mata kyau. Ya ce “Yawwa, mu je, amma kin san kin fi yin kyau a shigar nan?”

Ta yi busasshen murmushi da murya ƙasa ta ce “Allah ko?”

“Da gaske fa, kamar kullum ki dinga fita a haka.” Ta kauda kai gefe tana ficewa daga ɗakin bayan ta ɗauki takardunta tana faɗar “Idan haka kake so sai in dinga sakawa, sai dai ka sani ba zan ƙara burge kowa ba balle ka yi tunanin mu samu kuɗi.”

Shi ma biyo ta ya yi hannunsa riƙe da makullin babur ɗinsa yana faɗar “Ina, inah! Kawai a ci gaba da yadda aka saba.”

Girgiza kai kawai ta yi don zuwa lokacin ta daina damun kanta da tunani a kan Salis wane irin mara kishi ne. Da a ce ba a ƙabilar hausawa kuma a hannun musulmai kuma malamai ya tashi ba sai ta yi tunanin ko yana cin naman alade ne. Don a iya sanin ta ko a cikin dabbobi alade ne kawai ba shi da kishi, kuma abin ƙyamata ne shi ko a jinsin dabbobi.

A daidai kan titin Anguwar Rogo ya ajiye ta bayan ta kirawo Ma’aruf a waya ya shaida mata zai ƙaraso nan da mintuna biyar. A gaggauce ya yi mata sallama ya lula cikin gari.

Kafin cikar mintuna huɗu ta ga tsayuwar motarsa gaba kaɗan da inda take tsaye alamar birki ne ya ƙwace masa bai tsaya a daidai gabanta da ya so ba.

Matsawa ta yi kaɗan ta buɗe motar ta shige hankali a kwance. suka gaisa ya tada motar sai Plateau Politechnic. Tun daga main gate ta fara kallon sabuwar duniya. Katafariyar makaranta ce wacce aka gina a kan tsari irin na ingantattun makaratun gaba da sakandare. A hankali motarsa ta sulala cikin gate ɗin makarantar kamar yadda maciji ke sulalawa cikin raminsa.

Tun da suka shiga gate ɗin ba ta kuma cewa komai ba sai bin ko’ina take da kallo kamar wadda ta riski kanta a duniyar mafarki mai ban al’ajabi.

Ganin yadda tarin ɗalibai daga mabanbanta addinai da ƙabilu ke kai kawo a farfajiyar makarantar kowannen su cikin shiga da ta dace da al’adarsa ko son zuciyarsa, ya sa ta ji fargaba a ranta tare da yaƙinin cewa ta shigo wata sabuwar duniyar da kowa yake cin gashin kansa.

Da ma ta daɗe tana jin ana faɗar hakan sai dai ba ta taɓa gasgatawa ba sai a yanzu da ta riski kanta a tsakiyar su.

A gaban wani madaidaicin gini ya faka motarsa sannan ya mata umurnin fitowa. Ya yi gaba tana biye da shi kamar jela har suka shiga wani ofishi.

Bayan gaisawa da mamallakin ofishin ya karɓi takardun hannunta ya miƙa wa mutumin, ba ta san me hakan ke nufi ba ta dai ga ya yi rubutu a jiki ya ba su sannan ya ambata musu sunan wani ofishi suka nufi can. A ranta tana jin haushin yadda mamallakin ofishin ya kafe da da ababen tinƙahon mujiyarsa tun lokacin da suka shiga ofishin. Duk da tana son ta ga maza suna kallon ta tare da kware mata a lokaci ɗaya, don a ganinta kyawun dirinta ya cancanci hakan. Amma wannan karon sai ta ji ta tsani yadda wannan mutumin ya kafe ta da mayatattun idanunsa. Don haka ta ja dogon tsaki “Mtsw.”

Wanda kuma hakan ne ya janyo hankalin Ma’aruf da ke gaban ta kaɗan, ya waigo yana faɗar “Me ya faru ne Queen?” Girgiza masa kai kawai ta yi alamar ba komai. Shi ma bai sake tamkawa ba ya yi gaba, tana take sawunsa.

Ita dai da ido kawai ta ke raka shi sai da suka shiga ofishi uku kafin suka sake shiga mota ya ajiye ta gaban wani makeken ɗakin karatu da yake kan wani dandamali mai matattakala.

Sai a lokacin ya ce da ita.

“Ina taya ki murnar zuwa sabuwar duniya, ki shiga nan shi ne ajinku.” Ya nuna mata ginin, sannan ya kawo dubu uku ya miƙa mata tare da fatan alkhairi.

Nan ta tsaya tana kallon shi har sai da motarsa ta ɓace. Sabuwar fargabar da ta ziyarce ta ce ta hana mata motsawa ko nan da can, har sai da wata ɗaliba musulma ta lura da ita ta zo ta ja hannunta tana faɗar “Sannu da zuwa Mass Com Department, da gani dai ke baƙuwa ce ko?”

Da kai Nu’aymah ta yi mata alamar Eh. Sai kawai ta ja hannun Nu’aymah tana faɗar “Zo mu shige ciki ga lakcaranmu ya zo.” Kamar raƙumi da akala ta bi bayan matashiyar da ba za ta wuce sa’ar ta ba.

<< Danyar Guba 2Danyar Guba >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×