Firgigit Alhaji ya dawo daga duniyar tunanin da yake yana kallon hajiya Amina tausayinta ya ƙara kamashi don tabbas yasan akwai ƙauna da shakuwa sosai a tsakaninta da islam.
Dai dai nan likitan ya fara naɗe gawar Islam cikin bargon da take akai ya gyara mata kwanciyar kamar yarda akafi son gawa ta kasance,
Wani irin malolon abune ya tasoma hajiya Amina tun daga zuciyarta har zuwa maƙoshinta wani irin ɗaci da bauri suka mamaye ranta baƙin ciki da kaico sune suka haddasa mata ganin dishi-dishi juwa da hajijiya sukai nasarar jan jikinta ƙasa ji kake. . .