Yau da gobe kayan Allah ana haka wani abokin babana ya samu shago ana cikin kasuwar yana sai da kayan shafa, garinsu ɗaya da mahaifina kuma shine ya bama babana shawara akan ya dinga zama yana sayar da kayansa da kansa zaifi samun riba saɓanin da da yake bama ƴan sari sai sun sayar sana subiyashi.
Koda ya yi shawara da mahaifinsa ya yarje masa don haka ya fara zama gaban shagon ya na sana arsa, daga gefe kullum idan ya sayar sai ya tafi gida da tsaraba niƙi- niƙi, koda ya fara zama ɗan gari sai. . .