Mama na fitowa daga gidan gaban ta ya faɗi da ƙarfi ras! ras!! Saboda wani irin baƙin duhun da ya mamaye garin babu wata babu tauraro duk sun ɓuya saboda gagarumin hadarin dake ta hargowa asararin samaniya, garin yayi tsitt babu kowa don darene, kwaɗina da tsintsaye duk sun fakema hadarin suna sauraron ƙudurar ubangiji, sauro da kwari ma kansu sun ɓuya saboda iskar dake barazanar tarwatsa rayuwarsu, jikake rugugum ƙarar cidar da hadarin yake wanzarwa kafin wata irin iska mai haɗe da guguwa ta taso tare da walƙiya don kuwa hadarin yana gab da. . .