ba kowa bace acikin motar face hajiya Turai wacce suke hayar gida a wajenta sai ɗanta muneeb a gefe wanda ba zai wuce shekara goma sha biyar ba.
Dalilin bugun zuciyar mama ko ya samo asaline daga mmugun tsoron da take a matar don batada kirki ko misƙala zarratin.
"Ina zuwa haka da rana tsaka? "Hajiyar ta tambayi mama. Amadadin amsa sai mama ta duƙa har ƙasa tana faɗin "ina wuni hajiya ""Lafiya ƙalau " ta faɗi tana mai yamutsa fuska Ita kuma mama tuni ta cigaba da faɗin "Asibitin zamuje wallahi wani ibtila'ine ya. . .