Second 1,2,3 sai taji kamar anyi tilli da ita da sauri kuma da azama ta kama gyalen samira ta riƙe matakam jikinta na rawa lumfashinta yana fata da ƙarfi kamar zata shiɗe.
"Wannan shine saurayin naki "
Da sauri ta kalli cikin kwaryar sai ga fuskar wannan gayen ta bayyana, mamaki, al'ajabi, ruɗewa da firgici suka saka jikinta ɗaukar rawa kamar mazari kafin tace "shine wallahi shine " tai maganar muryarta na sarƙewa.
Hahh! hahhh !! Bokan ya kwashe da wata muguwar dariya kafin yace " ke yarinya wannan saurayi yafi ƙarfinki domin shima ashirye yake don. . .