WASHEGARI
Tun safe mama ta tashi da niyyar yima baba wanki don haka, ta umarci nura da ɗebo mata ruwan bohal anan bayan gida tahau wankin kayan baba duka da na Nuraddin da Fadila, inda ta tura Fadila da Nuraddin makarantar Allo.
Bangaren inna ita ma tun safe ta tashi ranta fes kamar an mata bushara da gidan Aljanna ba don komai ba sai don zataje taima Ali albushir da ƙarin aure, sai da ta watsa ruwa sana ta shirya cikin wata koɗaɗɗiyar atanfa ta hau mashin har cikin farin yaro, tana isa ƙofar gidan murmushi ya subuce. . .