Duk wanda ya ci zomo to tabbas ya ci gudu. Kamar yadda nake faman tsere tsakanin rayuwa da mutuwa. Tunanina da lissafina bai wuce na yi yaƙi da Ƙwarin da suke ƙoƙarin ɓata mana wake ba. Maganar da Atine ta yi mini ɗazu ne ya faɗo min a raina ‘ ‘ ‘Tabawa muddin ba rayuwar ki kike son ganin kin hallaka ba to ki fita cikin sabgar da ba ta ki ba.’
Murmushi na saki madadin na karaya da yadda ta ke hasko min girman kayan da nake son ɗauka ya fi girman gari da kasuwarta. Sai na ji ƙwarin guiwar zan yi wannan yaƙin. Maganar da ta kuma mini a karo na biyu. Na kuma hasko shi a cikin zuciyata ina jin kamar yanzu sautin muryarta ya ke dukan ma’adanan sirrinta saurarona da ke can cikin na zomo na. “Tabawa ina rabaki da kiwon akuya kina kyalla ta haihu, ki fa zauna ki yi wa kanki karatun ta nutsu.” ina lura da yadda ta ke min maganar. Tana mini kallon huhu-lahu mahaukaciyar kasuwa. Takaici da haushinta ya kama ni na figi hijabina na bar gidan. Domin muddin na ƙara ‘yan sakanni a cikin gidan nan sai Atine ta daƙushe mini babban burin da ke adane a birnin zuciyata.
Ina sallama a cikin ɗan akurkin da Allah ya azurta mu da shi. Wanda ba shi da wadataccen tsakar gida. Na ci karo da takaicin da ya sa nake jin tabbas sai na yi wannan yaƙin. Mama tana zaune ta doka tagumi kai kace wata gagarumar mutuwa aka ma ta. Kallo ɗaya za ka yi ma ta ka fahimci ta na jin tamkar ta kurma ihun iska. Ƙannena sun sanyata a tsakiya, sun yi tsamo-tsamo tamkar kajin da aka tsamo a ruwa. Haushi yasa na kasa ƙarasawa gidan na kuma ficewa. Makwabtan mu na shiga, navga ashe duk kanwar ja ce. Domin dai gidan mu da na su ƙwaryar sama ce take dukan ta ƙasa. Haushi ya kuma turniƙe zuciyata hawaye ya biyo kwarmin idanuna. Ganin yadda Inna Dije ta damalawa ‘ya’yanta tuwo da manja, ko arzikin ya ji babu shi ma a hannu a hannu. Koda yake gara su haka ma sun samu abin da za su kai bakin salati, ba irin gidan mu da alamu ke gwada dukan talauci.vIdan har ba lissafina ba ne ya kufce min. Wunin yau kaɗai gida huɗu na shiga ba su ɗaura sanwar abinci ba. Cikin zuciyata ina tunanin me ke faruwa ne? Hannu nasa na share hawayena tare da juyawa jiki a sanyaye duk na yi la’asar. Na fice ba tare da sun ganni ba. Ina tafe ina zance tamkar mahaukaciya. Sai famar mita nake ganin ƙangin rayuwar da al’ummar Annabi ke dakonsa a wannan lokacin. Tuntuɓe na yi da dutse. Idanuna na kai ga ƙafata jin azabar raɗaɗi a babbar yatsata. Sai yanzu na lura da ƙafata ta yi futu futu.
Idanuna na ɗaga ina kallon sararin samaniya cikin yanayin da bazan iya fasalta baƙin cikin da zuciyata ke ciki ba. Tabbas ba gudu ba ja da baya. Sai na yi yaƙi da miyagun shuwagabannin mu da ba sa ƙaunar talaka ya ci gaba. Shi ne zancen da ya min dirar mikiya a Ruhina. Haka na dinga yawo kwararo-kwararo lungu-lungu. Ina zagi da la’antar shugabannin mu da masu kuɗin ƙasar mu. Domin gani nake duk wannan masifar da muke ciki sune suka sanya mu a cikin ta. A firgice na dawo cikin gidan idanuna sun yi wiƙi-wiƙi tsabar baƙar yunwar da ke wasan tsere da hanjina. Karo na ci da kofin kunu wanda na tabbata shi ne abinda aka samu a gidan yau. Wai sunan muna da uba a gidan. Ko da yake bai kamata na ga laifin Baba ba, laifin zamanin da ya mana ɗaurin huhun goro ya kamata na gani.Tunda a hakan yana ƙoƙarinsa wajen ganin ya riƙe sana’ar sayar da ruwansa. Kasuwar ce kawai ba ta ja. A yadda rayuwa ta yi tsada ‘yan kasuwa suka kwashewa kayan abinci albarka. Ba lallai ba ne Sana’ar Baba da bai fi ya samu dubu ɗaya a wuni ba. Ya iya saya mana kwanon shinkafa, dubu da ɗari takwas a kwanon mu na Jigawar Dutse. Balle aje ga sauraran kayan masarufi.
Sallamar Baba ne ya dawo da ni daga duniyar tunanin da na shilla. Wanda ya sa Mama bayyanowa wajen da muke. Baba ya na ganina ya zauna ya hau faɗa. tare da sanar da ni yau anzo har wajen da yake ɗiban ruwa, an sanar da shi ina shirin jawo masa masifa. wai ance ina yawo lungu da saƙo ina zagin shuwagabanni. Baba ya ƙara da lallai idan ban daina ba sai an zo har gida an kama ni. Baba ya kuma duba na ya ce ” mene ne dalilin da yasa kike furta wannan mummunan kalmar akan shuwagabannin mu.” Cikin nauyin murya da tsanar duniya na furta “Talauci”. Cikin ɓacin rai Baba ya ce “Talauci ai ba hauka ne Tabawa. Kinsan girman kuskuren wannan kalmar da kike faɗa kuwa, Faɗa min dalilin da ya tunzura zuciyarki zuwa ga wannan munanan kalaman ba kya tsoron maganar ta kai ga kunnen ‘yan siyasar unguwar nan, Su kai maganar gaba ki jawo mana masifar da ba zamu iya fita daga cikin sa ba?”
Shine tambayar da Baba ya jefa min. Wanda ya yi matukar sanyaya min jiki. Cikin rashin ƙwarin jiki nake sanar da Baba cewa “Duniyar ce babu daɗi, Talauci da yunwa ya addabi al’ummar Annabi, an hana talaka kataɓus a duniya, Nema ake dole sai an kashe talaka, Rayuwa tayi tsada ‘yan kasuwa sun ƙarawa kayan masarufi, tsadar da abinda talaka zai kai bakinsa shida iyalansa yake neman fin ƙarfinsa, Baba na ga gidaje da yawa da aka sauƙe sanwa a gidan su bayan namu gidan Wani da ƙyar zai samu yaci sau ɗaya, yara da yawa sun lalace ta dalilin yunwa Wasu ta sa su sata wasu ta jefa su zina.” Na ja numfashi na ci gaba da cewa “Kuma duk saboda neman duniya dan kawai su ga sun ƙawatu da kayan alatun duniya, Suka ɗaura mana wannan masifar, na rasa ina ƴan siyasar mu suke shin ba sa ganin abin da ke faruwa da talaka ne? Ta yaya ba za mu zargesu ba? Baba hatta wasu masu akwai ɗin ma yanzu babu, masifa ta sa kasuwar ma ta tsaya cak, wannan dalilin ne yasa nake ganin, gara na tsine musu su lalace kowa ma ya huta, ina son na wayarwa da talakawa kai su gane illar da suke mana, domin zaɓe na gaba muyi gangami wajen durƙusar da su, tunda dama mu muka zaɓe su, da bazar mu suka taka matsayin da suke yanzu, haka ina da burin tara gangamin jama’a domin muyi zanga-zanga da masu sayan abinci da araha, su ɓoye har sai yayi tsada su fito dashi, wannan shi ne yaƙi da na ƙudiri niyyar yi da su.”
Murmushi Baba ya saki ya gyara zamansa ya ce mini. “Tabbas muna cikin yanayin da sai dai mu ce innalillahi wa’inna ilaihiraji’un! Sai dai ki sani wannan halin ha’ula’i da talaka ya ke ciki ba laifin ‘yan siyasar mu ba ne. Laifin mu ne mu a karan kammu, bakin mu baya furta alkairi ga shuwagabannin mu. Ko yaushe muna mugun fata akan su. Mu ne tsinuwa gare su. Allah wadarai ba ma taɓa furta alkairi. Shi yasa Ubangiji yake jarabtar mu akan halin mu. Mugayen ayyukan wasu daga cikin mutane yayi yawa. Muna aikata manyan saɓon Ubangiji muna ganin ba laifi ba ne shiyasa Ubangiji ya aiko mana da shuwagabanni dai-dai da zamanin mu.” Muryar Baba ta sarƙe tamkar zai yi kuka ya yi shiru na wani lokaci Sannan ya ci gaba da cewa “Muddin mu ‘yan Adam ba mu gyara halin mu ba, ba zamu daina ganin masifa ba. Mu gyara mu’amalar mu da juna, na tabbata sauƙi zai zo mana, ni dai a mahangata wannan shi ne dalilin da yasa muke cikin wannan bala’in, babu laifin shuwagabannin mu. laifin ya na daga halayyar mu.” Saukar wannan kalmar da Baba ya furta a cikin kunnena yasa jikina mutuwa murus. Naji na ajiye dukkan makaman da na ɗauka akan shuwagabannin mu. Na kuma tabbatar da duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka.
Rasheedat Usman