Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Doctor Eysha by Fatima Abdulhadi

Taron mutane ne a wajen sosai dalilin hadarin daya auko a wajen. Duk yawancin mutanen wajen suna cikin wani yanayi domin hadarin da suka tsinci kansu, ga kuma taron ambulance din dake tare da likitoci, domin ba da taimakon gagggawa. 

Kutsawa na yi dan na dauko maku labarin abinda ke faruwa dan nasanku da son labari.

Ko wani likita ƙoƙari yake yaga ya shawo kan patient din dake gabansa, wasu kuma ana daukar su ana saka wa a ambulance domin a samu damar kai su asibiti dan kuwa mutanen da hatsaren ya afka dasu suna da yawan gaske, wata motar asibiti ce ta iso itama, wani wawan burki suka ja domin kowanne a cikin likitocin burin sa ya fito, likitoci biyu ne suka fito kowanne na ƙoƙorin ganin ya nufi cikin majinyatan domin ba su taimakon gagggawa.

“Masha Allah” na fada saboda wata kyakkyawar surar da na ci karo da ita,
kyawun ta ya isa dan kuwa babu babu mutumin da zai ganta ko da kuwa yar uwar ta mace ce ba ta yaba da kyawun surar taba, Doctor Eysha kenan, bara na barku tare da ita ba ku labarin.

Saukowa ta daga mota kenan cikin hanzari na fita domin yadda nake jin ihun mutane yana tashi wasu iyayen sun rasu sai yaran su suna ta kuka, Ni nama rasa ina zan dosa dan Kuwa a wannan wajen kowa na bukatar taimako.

Nishin da na ji ne taga baya na ya saka ni saurin juyawa, “taimako dan Allah wani ya taimaka man”.

Muryar yarinyar da ba ta wuce shekara biyar  na ji daga baya na, sauri nayi naje wajen domin kuwa nasan dole ne tana bukatar taimakon.

Cikin sa a kuwa na same ta cikin wata mota da glass din motar ke rufe, babu yadda na iya sai dai kawai na fasa glass din dan yarinyar tana cikin mawuyacin hali.

“Inna lillahi wa inna ilaihir rajuun” na shiga furtawa saboda tashin hankalin da na gani, yarinya ce kwance cikin jini dalilin karfen daya shiga tsakiyar kirjin ta, sauri nayi na fiddo ta domin tana cikin wani hali nayi saurin ajiye ta a wani kebabben waje saboda cunkuson mutane da yake a wajen ba zai ba ni damar saka ta a ambulance ba.

“Na gode sosai yar uwa ta saboda mutane basa son taimako na duk likitan daya zo zai duba ni mutane basa barinsa ya duba ni a cewar su tunda iyaye nane suka jawo wannan hadarin sai dai na mutu, yar uwa ki yi mani alkawarin ba za ki bar ni ba na mutu saboda ina jin zafi sosai ” yarinyar ta fada.

Rike hannun ta na yi sannan na sakar mata murmushi ina cewa” na yi maki alkawarin zan yi iya bakin ƙoƙari na wajen ganin kin samu lafia in sha Allahu”.  Na fada ina ƙoƙarin na yi wani abu domin ceto ran wannan ƙaramar yarinyar wacce ba ta San komai ba.

“Ya kamata a ce mun tafi da ita domin kuwa tana buƙatar jini sosai kuma muna da buƙatar mata surgery domin ceto rayuwar ta “.

Mutumin da yake baya nane ya faɗi wannan maganar, juyawa nayi domin ko a mafarki na san mai wannan muryar dan kuwa na san ba kowa ba ne illa Doctor Aryan.

“Doctor Aryan kai ne anan ya aka yi kazo nan bayan kuma anyi suspending dinka?”.

“Ki yi hakuri yanzu ba lokacin wannan maganar bace domin kuwa rayuwar yarinyar nan tana cikin hatsari ” ya fada yana ƙoƙarin daukar ta, ya yi gaba ina biye dashi.

Hankalin mutanen wajen ne ya fara dawowa kan mu cikin hargowa suka fara cewa, “babu wanda zai taimaki wannan yarinyar saboda iyayen ta ne suka saka kowa a cikin wannan halin, dole ku kyale ta anan ta mutu “.

Ƙoƙari nake naga na shiga da ita ambulance amma mutane sun hana sai ihu suke suna nuna ba za a taimaki wannan yarinyar ba, da ƙoƙarin jami’an tsaro na muka samu damar saka ta ambulance directly Kashmir muka nufa domin ba ta taimakon gagggawa.

Muna isa asibitin ta ɓarauniyar hanya muka shiga da ita saboda dalilin mutanen da suka yi curko-curko a wajen,

Direct OT na nufa da ita domin gabatar da surgery din ta tare da taimakon Doctor Aryan, cikin rashin sa’a wata mata ta hango mu za mu wuce mu shige bangaren.

Babu bata lokaci ta bayyana ma sauran mutanen abunda ta gani, ai babu ba ta lokaci kuwa wajen ya hargitse da hayaniya, nan take ‘yan jarida suka shigo wajen suka sha gaban mu ta yadda ba mu da yadda zamu tsere masu, ai kuwa babu bata lokaci daya daga cikin su ta fara magana.

“Mun Samu rahoton cewa anan asibitin ana so a taimaka wa diyar mutanen da suka hada hatsari a airport road, Doctor Eysha me za ki iya cewa a kan wannan lamarin.

Shiru na yi ina cira idanu domin kuwa ni yanzu banda abinda zance dan sai yanzu na lura Doctor Aryan ya bar wajen, shiru na yi domin ba ni da abinda zan iya cewa.

Kamar a mafarki naji muryar doctor kaseem yana cewa, “aikin likita shine ya ceci ran al’umma ba wai su yi sakaci dashi ba, ina tunanin in dai mutane za su dogara da likita har su basa yadda akan zai iya ceton rayuwa to ya kamata ace likita ya zage damtse dan ganin ya taimaki rayuwar al’umma.”

“Iyayen tane suka yi laifi ba ita ba dan haka babu inda za ta je sai mun yi mata aiki an ceto rayuwarta” ta kai karshen zancen daidai lokacin da ya iso inda nake.

Tafi mutanen wajen suka shiga yi masa dan kuwa har ga Allah zancen sa ya shiga kunnensu.

“Ki taho mu tafi saboda ba mu da lokaci mai yawa.”

Babu musu na biyo sa Amma kuma abinda ya bani mamaki da shi, shi ne kwata-kwata ba hanyar OT muka nufa ba.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×