Wani malalacin Murmushi D.P.O yayi tare da buɗe motar sa yashiga yabar gidan da mugun gudu.
Zaune suke a part ɗin su Shadow Suna fira Haidar ne ya kalli Abbu yace "Abbu wai dan Allah da gaske su Abba ne suka haifi Ahanaf?"
Iska Mai zafi Abbu ya furzar, tare da gyara Zaman sa ya fuskanci Haidar da Kamal,
Cikin ɗacin rai da ƙunar zuciya Abbu ya ce
"Tabbas Ahanaf Yaron sune, Muhammad shine mahaifin Ahanaf Kuma shine Ɗan sa na farin, Sai Daga baya Allah ya bashi Al kaseem, Muhammad Yana matuƙar son Ahanaf fiye. . .