"Kayi haƙuri Yaya wallahi nima bansan dalilin da yasa n, tasss! Abba yaji saukar mari akan kumatunsa, hannunsa yasa ya dafe gurin da Abbu ya mare sa,
ɗago yayi yana kallon Abbu cike da mamaki.
"Kana da hankali Muhammad kasan abunda ka keyi kuwa? ka aikata wannan gagarumin laifin sannan harka iya buɗe baki ka faɗamin cewa bawani dalili? kar kazama Maha'inci Muhammad katuna fa Ahanaf amana ne agurinka Alƙawari kayi zaka kula da shi, zaka bashi farin ciki zaka mantar dashi ƙuncin rayuwa zaka zamar masa Garkuwa.
Ina duk wannan. . .