Skip to content
Part 2 of 10 in the Series Duniyar El-Dorado by Abubakar Abubakar

PREDATOR

Note:

Sau da yawa marubuta, da mawaqa ko masu shirya fina finai sukan samu matsala ne idan aikinsu yaxo da wani aibu kamar munanan kalamai, zancen banza ko batsa ko sabo a cikin waqa ko wani scene da akai shooting a fim wanda bai kyautu ba ko kuma scene din ka iya koyawa mutane wasu munanan dabi’u a cikin shirin da dai sauransu!

*****

Five Years Ago

Situation Room, National Intelligence Agency Headquarters Abuja, Nigeria
12:00AM

“Wannan taron kamar yadda kowa ya sani, hadin guiwa ne tare da State Security Service (SSS). Mun kuma samu kanmu da shigowa cikin case dinnan ne kasancewar ‘yan uwanmu masu uniform suna buqatar agazawarmu, tattare da kuma shi kansa case din akwai foreign intelligence don haka ya juyo ya zama namun a halin da ake ciki.

“Yau sati daya kenan da sakin wata sabuwar waqar turanci mai laqabin suna “Predator“, a shafin yanar gizo na YouTube.
Kamar yadda muka sani YouTube dai a taqaice is a video sharing company…”

Tsahirtawa yayi kadan yana mai duban kowa da kowa na dakin taron, sannan ya cigaba da bayani;

“Ita dai wannan waqa taxo ne da hargitsi, badon komai ba  kuwa sai don abinda ta kunsa.”

“Ita wannan waqar nata salon na daban ne, domin kuwa a waqar ana kwatanta yadda aka kashe wata ‘yar talika ce, aka kumayi gunduwa gunduwa da sassan jikinta bayan anyi amfani da ita.

A waqar an bayyana yadda kisan ya kasance in details wato daki daki.

Bayanai na yadda aka siffanta (description) yadda laifin ya faru, da yadda aka fasalta wurin da akayi laifin watau crime scene duk a cikin waqar kuwa, a cewar hukumar rundunar ‘yan sanda reshen jihar legas shine;

“Duk wasu bayanai da waqar ta qunsa, information ne da baxai yiwu wani ko wata su sani ko su samu ba, sai dai wanda ya aikata laifin da kansa ko kuma a cikin yan sandan dasuka kai ziyara crime scene din, kunga kenan information din da aka samu bayyanawa a cikin waqar, confidential ne. A cikin su ‘yansandan ma sai mai ruwa da tsaki tunda yarinyar da aka kashe diyar Oga kwata kwata ce!”

“Waqar ta fito ne kwana hudu kacal bayan mutuwar yarinya mai suna Yvonne Ajayi, wacce aka samu gawarta cikin mummunan yanayi a ranar ta 15/10/2018. Ta mutu tana da shekaru sha tara na haihuwa da watanni uku da kwana goma sha shida, ta samu gurbin karatu a babbar jami’ar legas watau University of Lagos, inda take fatan karantar ilimin kimiyya na siyasa watau political science, haifaffiyar jihar legas din ce. Mahaifin Yvonne, Samuel Ajayi kwamishinan ‘yan sanda ne na jihar ta legas, a saboda haka dole zai tsaya tsayin daka yaga ko waye, ko su wanene sun gurfana.”

“Menema labarai na gidajen talabijin da redio, da masu sukar waka wato (song critics) da ragowar mutanen gari sun samu musayar ra’ayoyi ne akan ita waqar. Abinda bature yake kira da mixed response. An samu cece ku ce a tsakanin al’ umma.
Wasu da suka soki waqar akan cewa waqar ta’addanci ce, saboda kalaman da ake fada a cikinta sun qara da cewa duk wanda yaso waqar to yayi hakan ne don son zuciyarsa kawai da kuma dadin kida da karin waqa.

“Wadanda kuwa waqa tayiwa dadi sunce ai ita waqa tana zuwa ne da manupa, cikin manupopin ita wannan waqar kuwa, akwai jan hankali, tsoratarwa, kazalika kuma akwai nishadi, ta kuma ja hankulan nasu sa’annan ta nishadantar dasu a cewarsu. Sun ma fada cewa ita wannan waqar ita take trending a shafukan sadarwa na yanar gixo.
Kun ji fa!

“Anamu binciken da mukayi cikin awoyi ashirin da hudu (24 hours), mun gano cewa;

“Allunan talla watau (billboards) ko nace music billboards (allunan talla na waqa) musamman na nan gida najeriya da na qasar amurka (USA) ba zafafa goma ba (billboard hot 10), ba zafafa dari ba (billboard hot 100), harta a zafafa dari biyu watau (billboard hot 200), wannan waqar itace a farko chan saman chart, daga dirarta a yanar gixo karfe goma sha biyu na daren juma’a (19/10/2018) waqar ta samu wadannan nasarorin ne a cikin sati daya kacal, kaga kuwa anci kudinsu, kuma ana kan ci har yanxu.

Duk wadannan bayanan suna pitowa ne daga bakin AGENT NAJIB AHMAD babban jami’i ne na police masu farin kaya.

Najib yana tsaye  ne a bayan podium yana addressing manyansa da sauran abokan aiki a nan cikin situation room dake hedukwatar tasu ta ‘yan sandan farin kayan.

Tsit! cikin daqin yake hakan zai iya bada damar jin faduwar ko da allura ce, duk da yawan jami’an da suke zaune a cikinsa. Daki ne mai dauke da kujerun zama dari to amma wasu jami’an ma a tsaye suke kasancewar taro ne mai zapi, na gaggawa, kuma mai muhimmanci saboda akwai tashin hankali sosai wato tension wurin binciko MARUBUCIN WAQAR ba wai wanda ya rerata ba. Me yasa hakan?

“Dalili shine wanda ya rubuta shine yasan confidential information da rundunar ‘yansanda ta jihar take zarginsa akai.

“Shi dai wannan shahararren kuma boyayyen marubucin, bincike ya nuna cewa shi freelance song and screenwriter ne, watau shi marubucin waqa ne haka kuma marubucin allo ne mai zaman kansa ba wani yake yiwa aiki ba sai kansa. Yana aikine kuma ta qarqashin qasa ma’ana a boye (underground).

“Nobody knows his physical appearance, babu wanda yasan kamanninsa. Written works dinsa ma’ana  rubuce rubucensa ana sharing  dinsu ne ta encrypted mails (rufaffun wasiku ko saquna a yanar gixo).
Manyan mawaqa na gida najeriya dana qasar waje sukan shiga “auction” ma’ana gasar siyan waqarsa, suna karbar ayyukansa  watau written works su mayar dasu records su biyashi. A da wadannan bayanai jita jita ce amma bincike ya tabbatar da hakan a yanxu.

“Babu bayanan ayyukansa na allo watau screenwriting sosai anan gida najeriya bincike da rahotanni sun nuna cewa yafi tsaida hankalinsa tanan a qasashen qetare.

Najib ya dan dakata yana me duban mutanen dasu ka bashi hankulansu kafin yaci gaba;

“Shi zai fara rera waqarsa ba tare da kida ba bayan ya rubuta ta, irin waqar da bature yake kira acapella, sa’anan su saketa through encrypted mails kamar yadda nayi bayani a baya, daga nan zai siyarwa wani mawaqin su kuma su hau kai suyi recording. He’s not a lyricist he’s a songwriter after all. Shi ake nema.

“Burin rundunar police ne, reshen jihar legas, wannan marubuci yaxo hannu tunda zuwa yanxu mun riga mun fahimci cewa Kenneth Mensah, shahararren inyamurin mawaqin nan da tauraruwarsa ke haskawa, wanda kuma akafi sani da K- Blow, sunansa na take kenan (stage name), shine mawaqi ko artist din da ya hau waqar, siyanta yayi kuma ba wai ya biya marubucin ta hanyar banki bane ko hannu da hannu. Boyayyen marubucin na da hanyoyinsa da dama da ake biyansa.

“Kenneth dai a yayin da yake police custody, watau lokacin da aka gayyace shi hedukwatar yan sandan aka kuma tsareshi yayi bayanin cewa; Mutanensa sun ajiye jakar kudi a wani location da aka basu a Lekki free trade zone. 

Bayanin yadda akai yaci auction kuwa, watau gasar samun waqar ya tabbatarwa ‘yan sanda cewa ba wai kudi bane kawai zasu saka wannan marubuci ya sallama maka aikinsaba. Zai fara gwadawa yaga wane mawaqinne yapi hawa waqar tasa dai dai, ma’ana wanene yafi rerata daidai da ra’ayin marubucin.  Izuwa yanxu, hackers na yansandan basu samu damar gano source din saqonnin yanar gizo na marubucin ba, namu ma’aikatan kuma suna kan nasu qoqarin ko zasu samo mana wani lead a game da saqonnin. An saki Kenneth ta hanyar bada belin sa tare da yarjejeniyar amsa kira duk lokacin da buqatar hakan ta taso.

“Sai dai kuma tuni labari ya canja a lokacin da kungiyoyin mata sukai nasu yunqurin na bore a dalilin sakin K-blow da akayi, sakamakon rubuce rubuce da suka riqayi, da maganganu a gidajen talabijin da radio da kafofin sadarwa na zamani. An sake tsare K-blow yanxu haka, ana cigaba da bincike akan wanda ya qirqira kuma ya siyar da waqar, babbar matsalar itace kungiyoyin kare haqqin dan adam sun shigo suma a gwabza dasu suna bayan mawaqin, a tasu fadar bai kamata acigaba da tsare shi ba, domin kuwa shi hawa waqar yayi bai da masaniyar bayanan cikin waqar confidential ne ba.

Thank you Najib!

Wani jami’in dattijo wanda da gani babba ne a matsayi ya furta, yana mai bude shafi na gaba a file din dake gabansa yana nazari.

Muna buqatar jin kadan daga cikin abinda waqar ta qunsa.

Dattijon ya bada umarni.

Wani jami’i dake gefen damansa a tsaye qiqam tunda aka fara gabatar da taron, Najib ya bawa umarnin kunna projector aka kuma jona hard drive, nan take muryar K-blow ta karade dakin taron;

I can hear some spirit voices
   Begging!..
  Let me rest in one piece

  Screaming!..
  Let me rest in one place

I pray to prey
Of course am a predator

A body laying lifeless
   Head and torso one side..
   About to dismember her legs..
  A crime scene they call such place
  As such is her fate
  Live and remember this date

   I pray to prey
  Of course am a predator

“Minti daya da sakanni uku kenan, cewar Najib yana mai duban agogon robar dake tsintsiyar hannun sa bayan an bada umarnin tsayar da waqar.

“Wannan kadan kenan cikin abinda waqar ta qunsa. Kamar yadda na sanar a baya, ma’aikatanmu zasu cigaba da binciken sources a yanar gizo.

Najib ya sake sanarwa.

“Kada kuma mu manta wannan taron gaggawar is a three phase meeting abin nupi xama daya kenan a cikin uku da za’ayi kafin musan ta inda zamu shiga wannan chakwakiyar.

Da haka wannan taron na tsakar dare ya tashi..

<< Duniyar El-Dorado 1Duniyar El-Dorado 3 >>

15 thoughts on “Duniyar El-Dorado 2”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.