THE TWO MEN ON HORSE BACK
Note
Irin qudurin nan da dan adam ya kan qudurce a zuciyarsa, na ganin ya aiwatar da wani abu ko samun wani abu da yakeso kota wace hanya ce kuwa, shidai burinsa kawai buqatar nan tasa ta biya, wanda mafiya yawa idan irin wannan qudirin yayi qarfi a zuciyar bayi to fa babu batun tunani ko shawara domin kuwa an dade da wuce wannan matakin. Tunani, ko shawara, ko fawwala Mai Duka babi ne da aka kulle a zuciya mai dauki da qudiri irin wannan.
Abin da mutum ya shuka shi yakan girbe, in hairan hairan in sharran sharran.. Wannan ya tabbata a littafi maitsarki.
Eid Day (Ranar Idi)
Kano, Northern Nigeria
Bushe bushe kawai kakeji da kade-kade ta ko ina yayin da sautin algaitu, kakaaki, ganguna, goge da sauran kayan kidin hausa suke tashi.
Dubban mutane ne gefe da gefe yayin dana kan dawaki suke wucewa ta tsakiya bisa kwalta, bayan kammaluwar sallar idin ta qaramar sallah. Eh! Lallai yau take sallah duk inda ka juya mutane ne dauke da murmushi mai annuri akan fuskokinsu, suna sanye da sabbin tufafinsu sai walwali suke suna daukar ido.
Gyara gaba gyara baya!..
Shiga lafiya alfanda!..
Bango madafar bayi!..
Ire iren kirare kiraren dake tashi kenan a yayin da tawagar sarkin na garin kano ta doso, daga can nesa ana iya hango qatuwar laimar sa tana juyawa a sama, kafin ya qaraso inda talakawan nasa zasu iya ganinsa ra’ayal aini, inji larabawa.
Bisa ga al’ada, duk wannan bushe-bushen, da kade-kaden, hade da kirare kiraren sukan qara tsamarine, ga kuma qarar bindigu da za’ayi ta saki a yayin da sarkin ya kawo kai, to yauma dai kamar kowanne hawan sallan hakan take a jalla babbar Hausar, kamisilika alfin, YARO KO DA MAI KAXO ANFIKA!..
Wuri yayi wuri kuma wuri ya dau sayi, sha’ani kawai akeyi na zallar hausa. Kirare kiraren da ake aikawa ga san kanon, ba ga mahaya dawaki ba kuma ba ga na qasa ‘yan kallo ba, a dai dai wannan lokacin ne kowa yake qoqarin miqa hannunsa sama ya kuma dunqule yana mai tsayar da babban yatsa, ma’ana dai thumbs up! cewar bature. Jinjina kenan da kuma gaisuwar ban girma gashi san kanon kuma jikan dabo, wannan duk yana daga cikin baiwa ta farin jini da mulki wanda Allah (S.W.T) Ya ara masa a doron duniya.
A cikin wannan karadin, ihu da iface ifacen banda tashin kade-kade da bushe-bushen algaitu, da bazasu katse nan kusa ba, koda wasa mai karatu bazaiyi zaton akwai wanda hankalinsa zaiyi wani wurin ba matuqar ya samu kansa a cikin wannan dandazon na taron shahararriyar al’adar ta qasar Hausa ba.
A kuma irin tunani da baiwa hade da nutsuwa da Allah (S.W.T) Ya azurta dan Adam dasu, mai karatu bazai zaci akwai mutumim da zai so yin wata magana ko hira mai tsawo barin kuma aje ga yin wata tattaunawa a irin wannan wuri ba.
To amma ba fa wai a cikin ‘yan kallo ba, a cikin tawagar sarkin da ta kawo kai, take kuma qoqarin wucewa, akwai mutane biyu wanda tun a jiya jajiberin sallar, sun shirya zantawa akan wani batu nasu, sun kuma haqiqance cewa wannan wurin dai cikin rudu da hayaniyar, shine meeting point din nasu. Nan suka ga ya dace su hadu su kuma tattauna maganar da suke ganin tana da muhimmanci kwarai a wurinsu.
Ko meyasa hakan? To koma dai menene dalilinsu, hakan da mamaki. Matuqa! Gaya!..
“‘Ya ta bazata auri mawaqi dan raye raye ba, kuma mai jajayen kunnuwa, alhalin ga yaron ‘dan uwana ina gani yana nema kuma na hana shiba. Gara na mutu ko na ga mutuwarta da hakan ta kasance.
Mahayin farin dokin na daga gefen hagu, dan tsamurmurin mutum, mai hasken fata, sanye da farin gilashi na ado, cikin shigar silke, kuma mai fari da jan rawani, wanda bazai gaza shekarun haihuwa hamsin da biyar ba, yake fadiwa abokinsa.
“Eh! Maganar ka haka take. Idan nine a matsayin da kake a yanzu, to ko shakka babu zan dauki mataki.“
Kakkauran bakin mutumin da yasha shuni cikin shigar ‘damara ya amsawa abokin nasa. Shi dinma a qiyasce shekarun nasa bazasu gaza hakan ba.
“To lokaci yayi. Kasan dama mun tsaida magana.
Dan tsamurmurin mahayin mai shigar silke ya sake fada.
“Ina sane da hakan, ai ni kai nake saurare. Daga nan fa? Sai kuma ina?
Kakkauran baqin mutumin dake sanye da shuni cikin ‘damara ya sake amsawa abokin nasa, hade da wata tambayar
“Daga nan kuma shikenan..
Tsamurmurin mutumin ya amsa a taqaice
Ya kuma qara da cewa;
“Zamu zo muna masu nuna alhininmu, zamu firgita kamar ragowar ‘yan uwa da abokan arziki. Zamu zauna karbar gaisuwa, za’a zo kuma yi mana gaisuwar. Za kuma a jajanta mana.
“Kamar yadda kasan ruwan sama..
Ya cigaba..
..irin ruwan nan mai kecewa cikin dare, wanda zaka ji ana cewa ” Ruwan dare..
“..Game duniya!..
Kakkauran mutumin ya amshe qarshen zancen yana sakin wata irin qatuwar dariya.
A lokaci guda yana qoqarin saita laitarsa, bayan ya sanya karan sigarin bensin a tsakanin baqaqen la66ansa da suka jima da dafewa tun wani zamani mai tsawo daya wuce.
Kwallin sigarin da yake qoqarin mayarwa aljihun rigarsa ta cikin ne ya su6uce ya nemi hanyarsa zuwa qasa kan qwalta. Wani yaro ‘dan sane (dan yankan aljihu), da ya ankare da hakan, har yayi taku biyu domin ceto kwallin sigarin daga qar, kofaton wani akawalin doki ya rigashi.
“To irin wannan ruwan daza kaga iya tsawon dare ana tsula shi kamar da bakin kwarya..
Mai rigar silke ya cigaba..
” Ruwan da zakayi zaton bazai dena zuba ba, bayan ya cika ko’ina taf! Daga baya idan ya dauke dif! Sai kaga qasa ta tsotse shi tsaf! Ko ina ya dawo kamar da can..
Juyowa yayi ya fuskanci abokin cin mushen nasa sosai, with a serious face, sa’an nan ya nisa yace;
“Kasan fa an dade ana ruwa..
“..Qasa ke shanyewa!..
The Two Men On Horse Back,
Watau, mahayan biyu dake bisa dawaki suka hada baki in unison suka qarashe maganar suna masu kecewa da wata irin muguwar dariyar da ko a addinance an hana bata kyautu ba..
Wannan kenan!
I’m enjoying this story
The pleasure’s mine. Thank you
Gaskiya inajin dadin labarin nan
Ina farin ciki da hakan. Nagode sosai
Hmm makirci
Sosai fa!
Kana capturing image din labarinka da kyau. Keep it up
Thanks much
Good
Thanks
Nice one