DRIVE TO BADAGRY
“Yaqi” kalma ce mai sauqin fada a baki haka kuma mai matuqar nauyi da girma wurin aiwatarwa. Duk wani yaqi da aka ta6ayi a tarihi kamar yaqin duniya ko yaqin qasa da qasa ko kuma yaqin basasa ma’ana yaqin cikin gida wato civil war, koma wane irin yaqi ne to yana farawa ne da baki, ana shiryashi ta hanyar makirci, tuggu da zaqon qasa har sai magana ta girma ta kaiga ana zama akan teburi domin tsarata..
*****
Five Years Ago
Ikeja, Lagos, Nigeria
Kamar dai a yawancin lokuta nanatacciyar shigarsa kenan; baqar suit ce a jikinsa ta kampanin armani sai baqin neck tie da baqaqen cover shoe ‘yan ubansu.
A tsanake ya gama shirinsa tsaf har back pack ‘dinsa da brief case duka yaronsa mai kula da ayyukan cikin gida mai suna Tunde yazo ya fitar dasu zuwa mota. Kasancewar yau Saturday hakan na nupin dole gobe zai bi flight zuwa Abuja, ko bakomai akwai meeting na biyu dake jiransa. Fatansa dai ya samu wasu gamsassun bayanai a wurin ajiyarsa ya qara kan wanda yake dasu already.
Shin zai fito ya fada musu gaskiya ne a wurin meeting game da binciken daya keyi tun shekaru takwas baya? Shi dai yasan yayi developing interest ne a dalilin bibiyar da Maryam take yiwa wani singer-songwriter, a cewarta wai content din waqoqinsa are the best she ever come across.
Saboda tsananin son da yake mata ne har yake 6ata lokacinsa ya zauna tana masa hirar mutumin da dukansu basu sanshi ba, a wancan lokacin.
“He’s exactly everything that I idolise about an author or a writer. He’s every single element of what I think is amazing..
This was the exact words she said a wani lokaci daya tambaye ta mai yasa take engaging kanta wurin neman mutumin da bashi da wani muhimmanci a rayuwarta, kuma ta amsa mishi tambayar ne cikin fushi domin kuwa har wata ‘yar kwalla ce ta taru a cikin manyan idanunta, wanda hakan ba qaramin daure mishi kai yayi ba.
Daga baya ne bincikensa da kuma wasu alamomi suka hadu suka gamsar dashi lallai Maryam ba rubutu da waqoqin 6oyayyen mutumin kawai take so ba. Mutumin kansa take so ‘dungurumgum. Wannan shine sole reason dinsa na fara yin nasa binciken.
He pledged himself bazai taba tsayawaba har sai yakai gaci. Dole ne ya gano mutumin daya samu soyayyar Maryam a 6agas. Soyayyar da shi ya dace ya same ta, shi kadai Maryam za taso. Idan kuma baza taso shiba, son da yakeyi mata ai ya ishesu suyi rayuwa mai kyau.
Tafkeken mirrorn dake gabansa ya qurawa ido yana duban kyakkyawar fuskarsa mai cike da rudani. Shi mutum ne mai tarin nasarori a rayuwa, duk wani abu daya ta6a so ko yaci buri akai to fa yana samu. Daidai da position dinsa a wurin aiki, position ne wanda ba’a ta6a samun mai qarancin shekaru irin nasa ba sai shi yanxu da Allah Ya kawo wurin.
Shin zai samu soyayyar Maryam ko kuma mallakar ta a rayuwa?
Shin zai samu nasarar binciko wanda take so, wannan 6oyayyen mutumin daya shafe shekaru takwas yana nema, musamman ma yanzu da ake zargin dasa hannunsa a kisan gillar da aka yiwa ‘yar kwamishinan ‘yan sanda kuma aminiyar ta?
Tambayoyi biyu kenan da yake kwana yake kuma tashi dasu, ya riga ya zama obsessed akan soyayyarta da kuma neman 6oyayyen mutumin da’a dalilinsa ne tasa soyayyar tabi rariya.
Ya sani Allah ne ya jarrabeshi da son yarinyar tun baisan menene so ba, kuma duk qoqarin daya riqayi na kyautata mata domin tayi reciprocating son da yake mata hakan bai yiwu ba. A lokacin data mallaki hankalin kanta ta kuma fuskanci manufarsa akanta sai taqi bawa hakan muhimmanci.
Sai dai kuma duk da haka babu wulaqanci ko rashin kunya a tsakaninsu duk da kuwa raini da tsiwa irin ta mimi. Akwai bond da mu’amala ta ‘yan uwantaka mai kyau a tsakaninsu har yanzu, ko da kuwa sunyi fada ne kamar yadda suka saba.
Tsayawa yayi dan gajeren tunani in case ko ya manta wani abu saboda yasan idan ya fice daga gidan zai ‘dan jima kafin yasake waiwayarsa. Daga shi sai masu yi masa hidima a gidan ne kadai suka san da wannan gidan shiyasa duk lokacin da yazo garin legas din yake ware wasu kwanakin koda kuwa kwana dayane ya kwana gidan uncle dinsa watau gidan su Maryam.
Da gudu gudunsa John direba ya taso a lokacin da Najib ya bayyana a harabar gidan cikin shirinsa na fita. Yakan sanar da direban nasa duk wani schedule da yake dashi matuqar yana gari. And today is not an exception.
Budemar qofar motar yayi gidan baya, ya shiga ya zauna sa’an nan ya juya zuwa mazaunin direba yayi igniting motar
“Drive! To Badagry..“
Ya umarci direban nasa.
Tun kafinma motar ta fara motsawa Adekunle gate man ya wangale musu gate, haka John ya fizgi motar a ‘dari suka fice daga gidan.
Suna hawa kan babban titi ya dauki wayar salula ya nemo wata lamba yayi dialling, kara salular yayi a kunnensa sannan ya jingina kansa a sit din motar hade da lumshe idanunsa.
**********
Lekki, Lagos, Nigeria
Kitchen ne tafkeke mai kyan tsari wanda naira tayi kuka yayin gini da kuma tsarashi wurin tabbatar da wanzuwarsa a zahirance. Wata yarinyace kyakkyawa dai dai misali ita kadai tana sanye da apron zaune a tsakiyar kitchen din tana matsa ice akan wani qaton cake. Wayarta dake yashe ce ta fara tsuwa tana neman agajin a amsa ta. A Hankali ta ajiye icing din ta miqa hannu tayi picking wayar.
“SIR” sunan daya bayyana a screen din wayartata kenan. Da sauri ta tashi ta rufo qofar sannan ta dauki kiran
“Good evening Sir.. Ta fada cikin yauqi da wani irin salo na jan hankali.
“I need you to lace her tea, drink or whatever it is. Tonight I’ll need an access to her room.
Ya fada ba tare daya amsa gaisuwar tata ba.
The pills will be delivered to you shortly.
Dauke wayar tayi daga kunnenta ta kalli screen din cikin son tabbatar da ya katse kiran ko bai katse ba.
Bakinta ta cika da iska ta fesar jin wani qululun bakin ciki daya taso daga qasan maqoshinta. Wai yau ita Linda ce take neman janyo hankalin ‘da namiji zuwa gare ta. Kaico!
Dalilai biyu ne kawai suka sa take aiki a qarqashin shegiyar yarinyar nan mai yawan girman kai. Reason din farko saboda kudin da ake biyanta, ba ko’ina bane za’a biyata kudi da yawa kamar haka a kowane wata akan ayyukan da basu taka kara sun karya ba. Dalilinta na biyu kuwa shine ko bakomai idan tana gidan zata riqa ganinsa lokaci zuwa lokaci.
Duk duniya babu wanda take so kamarsa daga ranar da sukayi ido hudu, amma duk irin qoqarin data keyi domin janyo hankalinsa zuwa gareta sam baima san tanayi ba. Batasan meyakeyi idan ya shiga dakin yarinyar nan ba amma tunda hakane abin, yau zata san duk yadda zatayi ta ganewa idanunta.
In dai har ta tabbatar daddy’s girl (sunan data laqabawa Mimi) tasha wannan can juice din nata na tamarind ko kuma green tea abubuwa biyu kenan da kullum sai ta sha babu adadi tamkar rai, wanda a cikinsu ne zata jefa qwayar, to ita kuwa yau bazata koma sashen da aka tanada na ‘yan aiki ba.
Wurin da zata 6uya a qaton gida kamar wannan abune mai sauqi. Dama daga Mimin sai ita ne suke rayuwa a gidan, sai shine na ukunsu yau idan yazo.
****
Kwance take kan makeken gadonta tayi nisa cikin tunanin aminiyarta. She’s still reeling from the pain and shock ‘din da suka daketa a lokacin da taji cewa qawar tata aka yiwa wannan mugun kisan, she was raped, killed and dismembered. Oh! Dear God!
Ta sani cewa mutuwa dole ce, yau da ace Yvonne rashin lafiya tayi ta mutu, yes she’ll be shocked, she will mourn amma not like this. Yvonne batayi deserving such a miserable end ba. She can’t even bring herself to imagine pain din da qawarta tayi going through kafin rayuwa tabar jikinta gaba daya.
Tashin hankali na biyu kuma, da ake cewa wai shi ake nema dangane da kisan aminiyar tata, eh ta yarda bata san shiba amma little informations ‘din da take takurawa kanta wurin nemowa na abin daya shafeshi, batajin zata yarda shi yayi kisan ko kuma yana da hannu a kisan.
“This is not the person I visualize you to be.. Ta fada a fili kafin ta miqa hannunta ta lalubo kan wayar land line dake saman headboard din gadonta ta daddana wasu nambobi.
“Yes Ma..
Muryar Linda ta karade mata kunne a lokacin da aka amsa kiran wayar
“To my room now.. Ta kife kan wayar ta sake lumshe manyan idanunta
Tayi zaton cewa idan tayi occupying kanta ta zama busy damuwarta zata ragu, shiyasa ta shiga kitchen ta 6ata lokaci tana baking wani qaton cake data dade da zanawa amma lalaci ya hanata baking dinsa.
Zanawa da kuma baking cake yana cikin hobbies dinta, in fact it’s her passion. Data gama baking ne kuma taji wani irin throbbing headache wanda take zargin qila rashin bacci ne yake haddasa mata, shiyasa tabarwa Linda icing ‘din tazo ta kwanta. Amma ta riga tasan bazata iya manoeuvering damuwar da take ciki ba.
**********
Badagry, Lagos, Nigeria
Badagry wani gari ne dake bakin ruwa, kuma garin karamar hukuma ce a jihar legas din. Yana kuma kan iyakar arewacin qasar Kwatanou.
A kusa da kan iyakar ne Agent Najib Ahmad ya umarci John ya tsayar da mota. Doguwar tafiyace ta kimanin awa biyu da ‘yan mintuna shiyasa basu samu qarasowa ba sai da shida na yamma ta gota, gashi har duhun almuru ya fara lullu6e garin, a hakan ma saboda basu da matsala da check points.
Lambar motar da suke ciki kadai ta isa ta hana a tsayar dasu, bare kuma aje ga mamallakin motar. Duk masu uniform din da sukai tozali dashi sai sun qame sun sara masa.
Bai dauki wani dogon lokaci yana nazari ba ya gano kwantancen da sukayi masa, kasancewarsa field agent a wasu shekaru da suka gabata, shiyasa yake applying experience a irin wannan yanayin.
“Drive!
Itace kalma ‘daya tal data dawo da driver John daga nasa nazarin daya tafi. Wuta ya bawa motar kamar yadda ubangidan nasa ya umarta, ya kuma taka mota
” Turn left and then another right
“Ok Sir. John ya amsa
“Stop!
Bude motar yayi bayan ya kashe, ya zagayo da sauri ya budemasa tasa qofar. Fitowa yayi ya taka zuwa bakin gate din yayi knocking inda ba’a fi sakanni biyu ba wani danqareren mutumi ya bude wanda kallo daya zaisa a gane sunyi hannun riga da imani.
Hanya ya bawa Agent Najib ya shige cikin gidan shi kadai. Wata siririyar doguwar hanya ya cigaba dabi har yazo wata qofa a qarshe. Sakatar jikin qofar ya zare sannan ya bude qofar yasa kai cikin dakin.
Matashin saurayine da bazai wuce shekarun haihuwa ashirin da uku zuwa da hudu ba. Kallo daya masu karatu za suyi masa su fahimci matashin ya fito ne daga tsatson masu jajayen kunnuwa.
Rigar da akeyiwa laqabi da “baba na balaga” ce sanye a jikinsa, irin rigar nan mara hannu wato sleeveless da kuma wandon three quarter. Dagowa yayi ya kafe Agent Najib da idanunsa.
“Identical twins ne wadanda idan suka tsaya a gabanka banbance su zaiyi matuqar wahala. Ubangidan nasu ne kadai yake iya gane su by mere looking.
A halayya suna da bambamci saboda Pablo bashi da hayaniya, mai sanyin hali ne kuma shine babba shine hassan.
“Pedro, husainin sa kenan shine me hayaniyar cikinsu. Ajiyarka kenan wanda a yanzu haka yana qarqashin ikon ka, mun kaishi can downtown Badagry kamar yadda ka tsara..
Katse tunanin daya ratso cikin kwakwalwarsa yayi. Ya kamata yayi sauri ya koma cikin garin legas saboda dare na qara shiga, bugu da qari kuma yau dole sai ya dauko wayar Maryam ya binciketa gaba daya. For now dai zai fara gamawa da wannan yaron dake gabansa.
Kallon junansu sukeyi ido hudu four eyes inji bature, kowanne da abinda yake qissimawa a zuci.
“Hello Pedro..
Agent Najib yayi breaking silence din dake tsakaninsu with an evil smile on his face.
“Babu abinda yake trending kamar labarin mutuwar ka..
“Kayi hatsari ka kuma kone qurmus a cikin motar ta yanda babu wanda zai buqaci ganin gawarka..
Good
Thanks
Masha Allah
Jazakhillah
Interesting..
Keep going
Great work
Gaskiya akwai cakwakiya..