CUNKUS DAKIN TSUMMA
A rayuwa akwai lafiya kuma akwai rashinta, akwai cuta kuma akwai maganinta. Akwai manya manyan cututtuka tare da haka akwai qananansu. Allah mabuwayi Shi Ya halicci cutar da maganinta.
Wasun mu zasu mutu ne silar wata cutar yayin da wasun mu zasu tafi ne ta wata silar daban.
Kullum muna fita daga gidajen mu muna dawowa, wata rana idan wasun mu suka fita bazasu dawo ba, sai dai a dawo dasu. Wasun mu zasu dawo amma bazasu sake fita ba sai dai a fitar dasu.
Duk yawan cututtukan da suke wanzuwa a doron qasa, akwai cuta guda daya wacce idan bawa ya mutu akanta zaiyi kaico da kansa. Wannan cutar itace cutar SON ZUCIYA!
*****
Five Years Ago
Lagos University Teaching Hospital, Idi-Araba, Surulere
Duk iya jimawar da Dr. Godwin yayi bayan fitarsa daga office din nasa, still Zahra tana tsaye bata samu wuri ta zauna ba, kamar yadda yace ta zauna ta jira shi. Safa da marwa kawai ta riqa yi a cikin madaidaicin office din.
Tunanin data keyi yayi mata yawa a cikin ‘yar kwakwalwarta, idan ta shiga nazari kafin ta kai qarshensa wani sabon babin zai bijiro mata, shiyasa baiyi mamaki ba lokacin daya dawo ya sameta a tsayen.
“Zahra! Don’t tell me you’ve been standing here for the past thirty minutes or so? Let’s..
“Doctor! Pls tell me who paid the bills for my sister’s surgery
Ta tari numfashinsa batare data bari yama qarasa abinda yakeson sanar da ita ba.
Akwai wasu abubuwa daya fara fahimta a yanxu a tare da yarinyar. Duk da yasan tana cikin tashin hankali a gaba daya kwanakin da aka kwantar da sistern ta saboda rashin wadatar kudin da za’ayi mata dashen qoda.
To amma abinda yake gani a fuskarta a yanxu, ya girmi duk wani tashin hankali da sauran abubuwan daya gani a lokacin daya sanar da ita zunzurutun kudin da ake buqata daga wurinta domin yin dashen qodar.
Daga lokacin da aka kawo masa receipt na shaidar biyan kudin aikin yake ta qoqarin kiranta amma baya samun nambar ta, shi kansa yanason ganin irin farin cikin da zata shiga a yayin data ji cewa an biya musu kudin, a maimakon haka kuma sai tsoro da tarin zulumi yake gani a tare da ita.
“Sincerely, Zahra I don’t know who paid the money. Some staff from the cashier’s office, knocked on this door about an hour ago. He came in and hand me over this receipt.
Ya qarasa maganar yana mai miqa mata farar takardar
Karba tayi a sanyaye ta qura mata fararen qwayar idanunta
“LAGOS UNIVERSITY TEACHING HOSPITAL, P.M.B 12063. LAGOS
OFFICIAL RECEIPT
Receipt No. 66328
Received from: Zahra’u Aliyu Bindawa
The sum of: Twenty three million, one hundred and forty two thousand, five hundred naira only.
Amount in figures: N23,142,500.00
Being payment for: Kidney Transplant Surgery
Signed Stamped
Duk abinda take ta karantawa cikin abinda takardar shedar biyan kudin ta qunsa, abubuwa biyu kadai idanunta suka dauko mata hotonsu, daga Zahra’u Aliyu Bindawa sai Twenty three million naira, one hundred and forty two thousand, five hundred naira only. Su kadai ne abinda ta karanta kuma suka zauna a kwakwalwar ta daram!
Watau har sunanta ma wanda ya biya kudin ya sani. Miliyan ashirin da uku fa? Sune yawan kudin fa da wannan farar takardar ke shaida an biya musu.
Wanene zai biya musu irin wadannan kudade masu yawa haka babu dangin iya ba na baba?
Wanene zai biya masu kudade masu yawa haka babu aikin fari bare na baqi?
Wanene a cikin attajiran da suke garin legas yasan da zamansu, harma da zai kawo musu ‘dauki don ceto rayuwar qanwartata?
“Zara!
Firgigit! Haka ta ‘dago ta zuba mar na mujiya bayan ya katse mata tunanin daya tabbatar idan ya bari ta cigaba dayi, to tana dab da samun matsala. Bugu da qari kuma ga shirye shirye da gwaje gwajen da za’a yiwa qanwar tata kafin a shigar da ita dakin tiyata tunda dai ga kudin sun samu.
“Take a deep breath Zahra, calm down and put all your troubles aside. Your sister needs this surgery ASAP. She also need you beside her. God willing, we’ll get through this.
“Thank you Sir..
Shine kadai abinda ta iya furta masa a hankali, hawaye na gangarowa daga kyakkyawar fuskarta.
“Don’t address me like that Zahra. You and your sister remind me of my late daughter. She was your age had she lived
Tun ranar da akayi admitting dinsu ya saba da ita kuma a ranar ne ya bata labarin ‘yarsa data mutu. Shekararsu daya inda tana raye.
Dr. Godwin ba musulmine dan uwanta ba, amma abubuwan da yayi musu na taimako, da kuma level of kindness da yayi displaying akansu ita da marar lafiyar qanwarta wani abune da ba zata taba mantawa ba. Zata cigaba da roqa masa shiriya a wurin Mai duka har sai ta kwanta dama.
“You’re welcome.
“And I suggest you go out there and take a walk to free your mind from all your worries and stresses.
“I’ll send Abigail to stay with your sister while you lay off.
Muryarsa ta sake dawo da ita daga sana’artata ta tunani mai zurfi.
“Thank you. I’ll see you later
Daga haka ta juya ta bar office din nasa.
Ko Dr. Godwin bai fada ba dama akwai buqatar ta fice daga asibitin saboda kar time ya qure mata wurin haduwa da mutumin da shi kadai take zargin ya biya musu wannan kudin, saboda duk alamu sun nuna hakan.
Daga haduwar ta dashi a safiyar yau zuwa yanxu yasan numbern ta even though she can’t remember sharing it with him. Ya san damuwarta duk da kuwa bata fada masa ba. Ya kuma san aikinta ko dayake wannan ba wani abu mai wahala bane binciko aikin data keyi
pammmmm!
Wani mai mota ne ya zabga mata ham (horn), saura kadan yayi tafiyar ruwa da ita. Akan titi take ta wannan tufka da warwarar.
“Fine girl where u dey go na?
Wani ‘dan kamasho kenan daya nufo ta bayan ta fito daga babban gate din asibitin, yana sa ran samun passenger akanta
Siririn hannunta ta ‘dago ta duba time; 04:28 pm na yamma. Kuma qarfe biyar zasu hadu dashi.
Drop kawai zata dauka zuwa bar beach din. Ko nawa zasu chaje ta bazai gagara ba saboda akwai kudin da akayi musu karo-karo a lokacin da ake qoqarin hada kudin tiyatar, yanxu kuwa wannan duk ya zama tarihi, fatanta dai Allah Yasa ayi aikin a sa’a Aimana ta samu lafiya.
“Sister! I say where u dey go na?
Da alama bayeraben ‘dan kamoshon motocin ya fara qosawa ne
” Bar beach.. I need drop
“Ok oo.. Your moni na six thousand
Victoria Island, Lagos
Duk da rashin nisan dake tsakanin gidansa da kuma bakin tekun watau bar beach, amma a zuciyarsa ji yake kamar ya tashi ya tafi tun daxu. Yana fatan dai zuwa yanzu ta kamo hanya zuwa beach din.
A iya tsawon rayuwar da yayi, yake kuma kanyi a 6oye, itace mutum ta farko da yaji sam baya shayin bayyana mata ko shi wanene kamar yadda ya nuna mata fuskarsa 6aro 6aro a safiyar yau.
A kuma ‘yar haduwar da sukayi briefly, zai iya cewa he find some piece of comfort and solace around her.
Bai san menene yake fizgarsa zuwa gareta ba, amma ko menene hakan he likes it. He likes staring at her beautiful innocent face, kuma duk da bayason ganinta a tsorace amma hakan na qara qawata her already glowing looks.
Yana sane da yadda su Ali suke mamakin haduwar da zaiyi da yarinyar tare da haka kuma suna tsoro da gujewa duk wani abu da zai iya biyo bayan hakan musamman ma a halin da ake ciki yanzu.
“Ta ya zaka yarda ka bayyanawa ‘yar jarida true identity ‘din ka? Su ‘din fa karnukan labarai ne na gaskiya dana qarya..
Ya tuno muryar Ali a wayar da sukayi ‘dazun nan bayan sun gama meeting sun tafi, ya sake kiransa ya jaddada masa hatsarin dake tattare da haduwarsa da yarinyar, sai dai kuma babu gudu kuma babu ja da baya. Huduwar tasu rubutaccen al’amari ne.
Ya san cewa kisan kan da akayi, aka kuma yi amfani da kalmomin rubutunsa a wurin da akayi laifin, wani kyakkyawan shirine daga ire iren abokan hamayya da suke danqare suke kuma zagaye dashi a birnin na ikko ikon Allah, CUNKUS KENAN DAKIN TSUMMA!
Yasan a ankare yake da komai a garin legas. Basajarsa mai qarfi ce, to amma fa babu dadi ace yau an wayi gari hukuma tana nemanka, duk wasu kafofin yada labarai akwai zancen ka akan harsunan su ko da kuwa daga ‘yan sandan da masu labaran har da sauran mutan gari duk basu sanka ba.
Mutanen da suka sanshi a suna da kuma fuska mutane bakwai ne sai fa ita yanzu da yake shirin qarata ata takwas. A cikin mutum bakwan da suka sanshi kuma, yau an wayi gari wasu sun sace daya daga ciki bayan sun shirya labarin qaryar cewar yayi hatsari ya qone qurmus a motar.
To make it worse an sace shine a lokacin da babu wata jituwa mai kyau a tsakaninsu. Koma su wanene su kai abducting Pedro, ba zaice hakan bai tayar masa da hankali ba. Damuwarsa shine well-being din yaron bawai gudun kar shi yaron ya fadi wasu abubuwan akansa ba. Ya riga yayi qarfin da kafin a cin masa farad daya abune mai matuqar wahala.
Din!.. Din!.. Din!..
Tangamemen wall clock din dake saqale a bangon qayataccen parlourn ne ya ankarar dashi lokacin fitarsa yayi. Bayan sautin alarm na qarfe biyar din yamma ya buga.
Lokacin da yake ta tsumayi kenan, lokacin tafiyarsa bakin tekun, lokacin haduwarsu da ita. Tashi yayi ya dauki wata face cap dake yashe akan three sitter din daya tashi, sannan yayi waje. Wata baqar marsandi formatic jeep ya dannawa remote tayi tsuwa, shiga yayi ya bata wuta ya fice daga gidan gaba daya.
Badagry, Lagos, Nigeria
Kallonsa kawai yakeyi babu ko qiftawa a qoqarinsa na gano inda yasan shi, ko kuma maybe sun ta6a haduwa a wani wurin amma bai tuna hakan ba.
Tun da aka sato shi aka kawoshi gidan kwana na hudu kenan yau, daga shi sai danqareren mutumin dake kawo masa abinci. Yaso ace ma sun kashe shi ya huta daga bakin cikin da yake ciki na rashin masoyiyarsa Yvonne.
Duk maganar da Agent Najib yakeyi bai tanka shi ba banda ido da yake binsa dashi har yanxu.
“Idan kana son ka sake shaqar iskar ‘yanci, idan kuma kana son ka sake rayuwa ba’a cikin dakin nan ba, to dole ka fada min duk abubuwan da nake buqatar sani daga gareka
“Ka bani labarin UBANGIDANKU, da kuma kai da ‘dan uwanka..
Agent Najib jami’in hukuma ne, ya saba yin tambayoyi ga masu laifi idan an kamosu tun zamanin da yake field work.
Mutum ne shi da ya kware wurin tatso bayanai a wurin manyan masu laifi ta hanyoyi daban daban saboda haka baiyi tsammanin qaramin yaro kamar Pedro da yake jar fata, sangartaccen da bai saba da wahala ba, kuma mawaqi ‘dan raye-raye zaiyi taurin kai ba.
Lokaci yana tafiya dare na qara yi, hankalinsa gaba daya ya karkata zuwa ga Mimi wacce yake fatan kafin ya koma Ikeja ta riga ta sha qwayar rohypnol daya aikawa Linda ta saka mata a tea ko wani abin sha.
A yadda ya tsara so yayi ya fara extracting information a wurin wannan tsagerin yaron sai yaje yayi comparing da duk abinda ya samo a wayarta da zai bincika.
Da alama qila Agent Najib bai sani ba ko kuma ya sani ya manta ba komai da kakeso kake samu ba. Sannan ba komai daka tsara bane zai tafi yadda kakeso.
Takawa yayi ya qarasa inda yake zaune yasa hannu ya kamo kananna’da’d’diyar sumar kansa da qarfi yaja, hakan yasa Pedro runtse idanunsa saboda azaba
“Zan tafi yanzu amma ka shiryawa dawowa ta.
Jan sumar tasa ya sakeyi ya jijjigata da qarfi cikin tsantsar mugunta sannan ya sakeshi ya juya ya fice daga dakin ya bar Pedro da jan kumatu abinka da farar fata.
Next pls..
Excellent!
Interesting!
Allah Ya kara fasaha
Very engaging story