Irfaan yana kallo aka ɗauke Ihsaan daga jikin Sulaiman. Ya ƙura wa gawan idanu yana fatan ace mafarki yake yi ba gaske ne ba.
Sulaiman yana kwance kamar zai yi magana. Fuskar nan tasa ɗauke da murmushi wanda da ita akan fuskarsa ya tafi. Duk da a lokacin da za a zare ransa ya yi ta kalamai, irin wanda har Irfaan ya mutu ba zai taɓa mance su ba,
_”Yaya Irfaan zan mutu, ka taimakeni.. Numfashina yana kasa min. Ku kira min Ihsaan don Allah.”_
Irfaan ya dinga nanata masa kalmar shahada har ya karɓa. Daga nan idanunsa suka kafe suna kallon sama.
Ta yaya zai iya mance wannan baƙar ranar?
Innayo ta farfaɗo amma wannan karon kukan kawai take yi. Haka zalika itama Ihsaan ta farfaɗo sai dai bata um bare um um.
A mota guda aka kwashi su Innayo aka kai su gidansu Irfaaan inda za ayi wa gawan sutura.
Ihsaan sai zazzare idanu take yi tana kallon yadda mutane suke shigowa suna gaisuwa.
“Ki zo ki yi masa addu’a angama shirya shi.”
Ihsaan ta kasa gane muryar wanda yake sanar da Innayo maganar nan. Tana ganin Innayo ta tashi ta miƙe itama ta bi bayanta.
Irfaan yana tsugunne agaban gawan. Har yanzu zuciyarsa ta ƙi gazgata masa Sulaiman ya rasu.
Jiri ke ɗibansa. Bai san ya shaƙu da Sulaiman ba sai yau. Duk dauriya irin na Irfaan, duk yadda yake jan gwarzo wanda ya saba ganin gwagwarmaya iri-iri yau sai da idanunsa suka kawo ruwa. Ruwan hawayen da zai iya rantsewa tun yana ƙarami rabon da ya gansu.
Zuciyarsa zafi take yi masa. A hankali ya ɗauke ƙwallan idanunsa ya tashi daga gaban gawa. Ɗan adam ba abakin komai yake ba. Sulaiman ya yi ta nanata masu kalman jibi a matsayin ranar da za a sake ganinsa ashe yana nufin ganin ƙarshe za ayi masa jibi.
Ihsaan tana biye da Innayo har gaban gawan. Innayo ta yi masa addu’a, itama ta karanto abin da za ta iya ta yi masa. Irfaan yana kallon yadda idanunta suka bushe. Tsantsar tashin hankali ya hana hawayen zuba. Har aka ɗauki gawan da nufin zuwa yi masa sallah Ihsaan bata daina kallon makaran ba.
Irfaan ya kamota ya jijjiga kafaɗanta da ƙarfi, muryarsa mai cike da amo! Na tashin hankali ya ce,
“Ihsaan! Ki yi kuka kinji? Yi kuka nace ki yi kuka.”
Yana maganar yana bubbuga fuskarta da tafin hannunsa. Jikinsa babu inda baya rawa. Idanunsa sun kaɗa sun yi jazir.
Sai a lokacin zuciyarta ta karye, ta ƙanƙame Irfaan ta fasa wani irin kuka mai taɓa zuciya. Sai yanzu ta iya yin magana jikinta yana kyarma,
“Za…za.. Su tafi min da shi ne. Don Allah ka hanasu don Allah.”
Tana magana jikinta yana ɓari kamar wacce ake girgizata. Irfaan ya yi ƙoƙarin mayar da ƙwallan da ke ƙoƙarin fitowa ya ce,
“Ki yi haƙuri Ihsaan ki yi haƙuri. Ki yi wa Sulaiman addu’a kinji?”
Wani irin numfashi ta ja sai ga jini ta hancinta yana zuba. Gaba ɗaya ya lalata wa Irfaan jiki. Duk da haka bai saketa ba sai magana yake yi mata a hankali,
“Kada ki yi shiru ci gaba da kuka Ihsaan, ki yi kuka sosai ki yi kuka.”
Gaba ɗaya a ruɗe yake. Baya so Ihsaan ta ƙi yin kuka dan yasan illar da hakan zai iya haifarwa. Abba ya ƙaraso bayan ya goge hawayen fuskarsa. Ya janye Ihsaan a jikin Irfaan, sai dai yana janyota ta yi baya luuu bata motsi.
Dole wasu mata suka ɗauketa suka mayar ciki. Irfaan kuma ya tashi jiki babu ƙwari ya koma ya canza kaya sannan ya nufi inda za ayi sallah.
Tsaye kawai yake har aka idar. Ya dubi makaran, shikenan tashi ta ƙare.
A maƙabarta ya sunkuya yana tunawa da ranar da aka kai mahaifin Ihsaan. Idan bai mance ba Sulaiman ne kaɗai ya rage tsugunne agaban maƙabartan. Yau kuma shi ne kwance a ciki. Dole duk wanda ya ɗauki duniya wurin zama to ya gaggauta mance hakan domin kuwa irin ranar da ta riski Sulaiman tana nan zuwa kan kowa.
Abba ya ƙaraso ya ce,
“Irfaan!”
Bai iya amsawa ba sai ɗago jajayen idanunsa kawai da ya yi yana dubansa,
“Ta zo mu je.”
Abba ya ce da shi, sannan ya kamo hannunsa suka bar wurin. Har suka yi nisa bai daina waiwayen sabon ƙabarin na Sulaiman ba.
Ko da suka dawo gida, sun sami Ihsaan zaune a kusa da Umma. Babu hawayen amma kallo ɗaya za ka yi mata ka tabbatar da tana cikin ruɗani. Gaba ɗaya kallon marainiya yake mata. Ada can bai ɗauketa a marainiya ba, sai yanzu da ta rasa babban bango.
Irfaan ya kasa zama a wurin karɓan gaisuwa ɗakinsa kawai ya wuce yana ta tunanin zuci.
Har sai da aka kira sallar magrib ya samu ya lallaɓa ya fito, ya nufi masallaci. Har isha’i yana tare da su Abba, a lokacin saƙon kira daga Umma ya riske shi.
A ɗakinta ya sameta ta zauna a bakin gado shiru.
“Gani Umma.”
Ta ɗan dube shi ta ce, “Ka ci abinci?”
Ya ɗan sunkui da kai ya ce,
“Wallahi Umma bakina ɗaci yake yi min. Bazan iya cin komai ba. Wai Sulaiman ya rasu! Shekaranjiyan nan muna tare har sha biyun dare. Umma ina cikin ruɗani ina cikin tashin hankali. Umma ko mafarki nake yi?”
Yadda yake magana cikin sanyi ya kashe jikin Umma. Ta goge hawayenta ta ce,
“Rayuwar kenan. Duk wanda ya ɗauketa da zafi sai ya sauke. Kai kuma sai kayi ƙoƙari ka riƙe amanarsa. Kana dai ganin yana gab da rasuwan bakinsa bai daina ambatar Ihsaan ba. Wannan yarinya taga rayuwa. Bata kuka sai wani irin ajiyar zuciya. Tsoro nake ji kada wata cutar ta shigeta. Yanzu ga ruwan tea maza kasha ka samu ka je ka lallaɓata ko ruwan tea ɗinne ka bata.”
Shima ajiyar zuciyar kawai yake yi. Umma ta dage sai da ta ga yasha sannan suka nufi ɗakin da Ihsaan da Innayo suke zaune.
Ihsaan tana zaune ta kwantar da kanta a jikin bango wani barci mara daɗi ya ɗauketa. Irfaan ya sunkuya yana duban fuskarta, ya sake yi wa Innayo gaisuwa.
“Umma tunda ta sami barci mu bari ta tashi.”
Kafin Umma ta furta wata magana, Ihsaan ta fasa wani irin ƙara tana fizge-fizge. Irfaan ya riƙeta sosai amma bata daina fizgewan tana surutai ba,
“Ku ƙyaleni inje wurin Yaya Sulaiman. Na yi mafarki wai.. Wai.. Wai Yaya Sulaiman ya rasu.”
Ta ƙarashe cikin kuka mai tsuma zuciya.
Ta buɗe ido tana kallon yadda Irfaan ya riƙeta ta ce,
“Don Allah ka ƙyaleni inje wurin Yaya Sulaiman don Allah. Idan baka barni ba zan mutu. Ka taimakeni don Allah zan tafi ne wurinsa.”
Umma da Innayo da Zarah suka sa kuka. Kuka suke yi na tsananin tausayin Ihsaan. Kuka suke yi kukan rashin sanin makomar lafiyar Ihsaan a sakamakon wannan gagarumin rashi da ta yi. Rashin da ake ganin da wuya ta sami madadinsa.
Irfaan da ya rasa ta inda zai lallasheta kawai ya rungumeta tsam a jikinsa, yana jin da zai samu shima ya yi kukan tabbas da zuciyarsa ta rage raɗaɗin da take yi.
Sosai take kuka, bata fasa roƙonsa da yi masa magiya akan ya kaita wurin Sulaiman ba.
“Ihsaan ki yi haƙuri Sulaiman ya riga ya tafi inda ba a dawowa.”
Innayo ta yi maganar cikin kuka. Kalaman da suka sake jawo ƙafewan idanun Ihsaan. Irfaan ya ɗagota yana jijjigata. Wannan karon sun watsa ruwan amma bata farfaɗo ba, babu shiri aka nufi asibiti da ita.
Su kansu likitocin sunsha wahala kafin suka samu kanta.
Irfaan ya ce duk su koma gida, shi zai zauna da ita.
Cikin dare ta farka ta ga Irfaan zaune a kujera ya yi nisa cikin tunani. A hankali abubuwan da suka faru suka dinga dawo mata cikin kai. Tun ɗazu bata cikin hankalinta sosai, sai yanzu ne ta ba zuciyarta daman tuno cewar gawan Sulaiman ta gani a kwance a asibiti. Babu ko tantama Sulaiman ya tafi ya barta, tafiyar da ba zai dawo ba.
“Innalillahi Wa inna ilahirraji un… Ka tafi ka barni Yaya Sulaiman. Ni mummuna ce, kai kaɗai ka taɓa ce min ina da kyau, kai kaɗai kake raɓata a lokacin da mutane suke guduna. Nima kashe kaina zanyi Wallahi.”
Tana maganar tana buga kanta a bango, ta cizge ƙarin ruwan. Firgigit Irfaan ya yi ya ganta yadda take yi kamar zata sake shiɗewa.
Irfaan ya tashi ya kira dokto suka dawo tare. Dole akayi mata allurar barci, domin jininta ya yi mugun hawa. Tana sumbatu barcin ya ɗauketa.
Haka suka yi kwanan wahala, da ta farfaɗo zata kama sumbatu sai kuma ta sake zubewa.
Kwanaki huɗu cur ta kwashe a asibiti, da taimakon Allah da taimakon addu’o’in da Irfaan yake tofawa aruwa yana bata tana sha, aka samu kanta.
Sai dai fa ta koma wata kala abar a kalla ayi ta kuka. Irfaan kaɗai ke iya bata tea daga nan bata sake karɓan komai. Hakan yasa ta ƙara lalacewa.
Likitoci sun bayar da shawarar kada a dinga barinta tana kwana ita ɗaya, kuma adage wajen kwantar mata da hankali gudun kada ƙwaƙwalwarta ta taɓu dan tana gab.
Su kansu sun kula da abubuwan da take yi kamar mai taɓin ƙwaƙwalwa.
Innayo tasha mamakin jin cewar wai Irfaan ne mijin Ihsaan. Ta daɗe tana al’ajabin ta yadda hakan zai faru.
Bayan anyi sadakan bakwai Innayo ta tattara ta koma Saulawa. A ranar har ƙaramar hauka Ihsaan ta yi, ita a dole sai Innayo ta kaita wurin Sulaiman.
*****
Haka rayuwar ta ci gaba da miƙawa da daɗi babu daɗi. Ihsaan ta samu ta fara zuwa Makaranta da ƙarfin addu’o’in da su Abba suka dage suka sa a dinga yi mata. Haka zalika ta koma Islamiyya. Sai dai fa bata magana idan ba dole ba.
A cikin zuciyarta ta ƙudurci za ta yi karatu domin cika burin Sulaiman. Duk burikan da ya ɗauka akanta za ta yi ƙoƙarin ganin ta cike.
A gefe guda kuma tsanar Irfaan ne cushe a ranta dan gani take yi kamar su suka kashe mata Sulaiman. Shi kansa Irfaan ya kula da yadda take yi masa kamar ta tsane shi. Don haka shima ya ci gaba da nasa sabgogin musamman yanzu da baya zama sosai a gidan.
*****
A hankali Ihsaan tana ƙara girma baƙinta yana ci gaba da bayyana. Sai dai ta murje ƙirjinta sun cika na ‘yan matanci, haka zalika ta samu ta kammala ƙaramin sakandire. A islamiyya ma tana ƙoƙari. Idan tana Qira’a dole ka sake waiwayo ka kalleta. Sai dai kallo ɗaya za ka yi mata kayi saurin kauda kanka.
Daga Islamiyya har boko bata da ƙawa. Dukkansu ƙyamarta suke yi, don sun kula banda baƙin harda ƙazanta musamman idan ka dubi haƙoranta sai kaji kamar za ka yi amai.
*****
Irfaan yana zaune a falo yana sanye da jallabiyansa yana latsa laptop, ya ganta ta fito kitchen tana tafiya kamar ba za ta je ba. Shi bai taɓa lura da ƙirjinta ba, kasancewar kullum tana cikin hijabi.
“Ihsaan.”
Ya kirata. Ta dawo ta ce,
“Gani.”
A kullum idan ya kalleta Sulaiman ke faɗo masa a rai. Yana tuna ranar farko da ya fara ganinsu.
“Ki zauna.”
Ta ɗan yi shiru, kafin ta nemi wuri ta zauna.
“Ihsaan me na yi maki kika tsaneni? Bani na kashe Sulaiman ba, ya kamu da ciwo ne adalilin shaye-shayen da ya yi abaya. Ya yi min bayanin komai, har na nemo likita a waje da zai duba shi wannan lamarin ya faru.”
Ihsaan ta ɗago idanunta cike da hawaye ta ce,
“Yanzu da gaske Yaya Sulaiman ya rasu?”
Ya jinjina kai,
“Ya kamata zuwa yanzu ki yarda da ƙaddarar nan. Ki yi haƙuri mu haɗu mu cika masa burinsa da ya tafi ya bari akanki. Don Allah ki daina shiru-shirun nan, kin ga kusan kullum sai jininki ya hau. Kuma na duba result ɗinki na boko baki yi ƙoƙari ba Ihsaan. Tayaya zan sauke nauyin da Sulaiman ya bani ba tare da haɗin kanki ba?”
Kalamansa sun daki zuciyarta. Ta yi ƙasa da kai hawaye suka hau zuba kamar ruwan famfo.
“Kin amince za ki bani haɗin kai?”
Ta gyaɗa kai.
Shi dai har yanzu bai daina mamakin banda girma babu abin da ya canza daga jikin Ihsaan. Babu kalan sabulai da mayukan da ba a siya mata ba. Babu kalan gyaran jikin da bai turo anyi mata ba. Amma yarinyar nan ta ƙi canzawa.
A hankali ya rintse ido ya yi magana a zuciyarsa,
‘Ko ayaya kike zan karɓeki a matsayin mata, darajan Sulaiman. Zan kauda kai daga barin kallon muninki, zan samo kyau a zuciyata inmanna maki, ko da kuwa bazan so ki ba, ba zan taɓa bari ki yi kukan maraici ba.’
Tun daga ranar Ihsaan ta zama ƙawar Irfaan. Shi yake koya mata karatu. Haka zalika Zarah ta zama babbar aminiyarta da suke tattauna matsalolinsu tare.
Babu yadda Abba bai yi ba akan ta je ta ga danginta a Saulawa amma sai cewa take yi ba yanzu ba. Ta dage ta mayar da kanta akan karatu babu ji babu gani.
Irfaan ya yi namijin ƙoƙari wajen ganin ta saki jikinta, harma takan yi dariya. Yau ma kamar kullum ya shigo da Sallamarsa tana falon don haka ta tashi da gudunta tana cewa
“Yauwa Yaya dama kai nake jira.”
Ya ɗan ɓata rai ya ce,
“Babu sannu da zuwa?”
Ta rufe fuskarta tana dariya,
“To sannu da zuwa.”
Ta kamo hannunsa har zuwa gaban littafanta da ta barbaza su a falon. Gaba ɗaya a gajiye yake don haka yana lumshe idanu ya ce,
“Ihsaan ki yi haƙuri inje in huta na gaji.”
Ta maƙale kafaɗa,
“Ni na ƙi wayon.”
Ta manna masa takarda a fuska ya yi murmushi ya cire takardan yana cewa
“Tayaya zan gani bayan kin rufe min idanun?”
Jarabawarsu ta English ya gani ta cinye tas! Farin ciki ya tsirga masa. Yana shan wahala wajen koyar da ita karatu kasancewar ba wani fahimtar bokon take yi ba. Yau ta faranta masa fiye da tunaninsa. Baisan lokacin da ya ɗagata ya dinga juyi da ita a falon ba. Bai direta a ko ina ba sai saman faffaɗan gadonsa. Ya raɗa mata a kunne,
“Jirani in yi wanka inkaiki kisha duk abin da kike so.”
Anan ya shiga wanka ya barta cikin wani yanayi. A yau wani baƙon lamari ya sami tasirin shiga zuciyarta. Tunda take da shi bata taɓa jin abin da ta ji a yau ba. Jikinta a mace ta sake lumewa cikin gadon tana lullumshe idanu.
A take tunanin Sulaiman ya bijiro mata wanda ya ci nasarar yin fatali da abin da take ji. Sai dai har yanzu jikinta a mace yake.
Tana kallonsa ya fito wanka ɗaure da tawul, ta yi saurin rufe idanunta. Har sai da ya kammala shiryawa sannan ya ce,
“Ki tashi mu je. Idan kin gama jin kunyar.”
Ta yi dariya ta tashi ta je ta sauya kaya ta fito.
Wuri mai kyau da rashin hayaniya ya samu, ya shiga da ita. Duk wanda yazo wuce wa ta kusa da su sai ya waiwaya ya dubeta ya dube shi. Musamman ma yadda suka ga Irfaan yana riƙe da hannunta.
Wasu har kasa ɓoye dariya da mamaki suke yi. Babu ta yadda Irfaan da Ihsaan za su iya haɗuwa a inuwa guda, domin bambancin a bayyane yake. Shi kuwa ko a jikinsa.
A yau yake so ya fara gwada irin kalaman da Sulaiman yake amfani da su akan Ihsaan saboda bai da burin da ya wuce ganin Ihsaan ta sami ilimi, ya fahimci hakan ba zai faru ba har sai ya nuna mata irin soyayyar da Sulaiman yake gwada mata.
A ɗan zaman da suka yi ya shaƙu da ita, ta iya hira tana da tausayi matuƙa. Ko ciwon kai yake yi ita ke kawo masa magani, ta yi ta jera masa sannu babu ƙaƙƙautawa.
Yadda take nuna tausayawarta akansa ya ƙara mata wani matsayi mai girma agurinsa.
Bayan sun sami wuri sun zauna ne ya yi order ɗin abubuwan da yake so ya dubeta ba tare da ya bari ya kalli fuskarta ba,
“Ihsaan ke kyakkyawace a idanuna. Ko da duk duniya suna ganin muninki ni saɓanin hakanne a wurina. Ki rabu da masu kushe halittarki, ki yi karatunki ki ci kawa Sulaiman burinsa. Na tabbata yau shima yana cikin farin ciki. Ki ƙara dagewa kin ji?”
Asanyaye ta ɗaga kai idanunta cike da hawaye. Maganarsa kuwa da ya ce tana da kyau ya yi ta amsa kuuwa a zuciyarta. Gani take yi kawai yaudarar kai ne Irfaan ba zai taɓa sonta ba.
Da aka kawo masu Ice Cream a baki ya dinga bata tana sha cike da farin ciki. Sun jima yana zagaye wurare da ita, wanda tunda ta zo bata taɓa gani ba. Tabbas ya ci nasarar jefa zuciyarta a cikin nishaɗi.
Ƙarshe a gidan Umma suka dire.
Sai dare sosai suka dawo gida. Lokacin Larai ta jere masu abinci sai dai babu wanda ya kalli abincin suka shige ɗakunansu.
Da kansa ya tako har ɗakinta ya ce,
“Zo mu je ɗakina mu yi hira.”
Ta amsa da “To.” ta miƙe ta bi bayansa.
“Wai ke har a ɗakinki ma da hijabin kike rayuwa?”
Tana dariya ta ce,
“Ehmana.”
A ɗakinsa ya yi ta biyewa shirmanta, daga bisani ya ce ta yi masa tausa.. Ga mamakinsa yarinyar ta iya tausa duk da iya ƙafafunsa take matsawa. Sosai ya ji daɗin tausar don haka ya yi ta lumshe idanu, har barci ya kwashe shi.
Cikin dare ya ji shessheƙan kukan Ihsaan. Idanunsa a rufe baya so ta fahimci ya tashi. Kalamanta sun ƙarasa kashe masa jiki.
_”Yaya Sulaiman nasan kana jina. Na kasa daina tunaka daidai da minti ɗaya. Bazan iya manceka ba. Nasan yau kayi farin ciki ko? Da gaske na sa ka a cikin farin ciki? Ka gode wa Yaya Irfaan ya taimaka min. Ina nan zuwa gareka da zarar na kammala cika burinka.”_
Kuka ya goce mata. Ya sake rintse idanunsa yana jin lallai akwai aiki a gabansa akan Ihsaan. Yana fatan watarana Ihsaan ta gane cewa shi ne madadin Sulaiman, domin Sulaiman ba zai sake dawowa ba.
‘Yar mutan Bornonku ce