Umma ta sauke gajiyayyen ajiyar zuciya ta ce, “Ra’ayina da naka basu taɓa bambanta ba, amma kuma yallaɓai.”
Abba ya yi saurin ɗaga mata hannu. “Kin gama magana. Idan kuwa kikasa amma a cikin maganarki tamkar kin rusa maganar farko ne. Irfaan ka ci gaba da shiri dan ka samu ka koma ka kammala ayyukanka. Allah ya yi maka albarka.”
Ji ya yi gaba daya guiwowinsa sun riƙe. Duk yadda yaso ya tashi abin ya faskara. Dole ya ci gaba da zaman idanunsa jazir. Ƙwaƙwalwarsa ta gaza tuno masa da komai idan ba kamannin Ihsaan ba. Bai taɓa yi mata kallon rahama ba, sai da mahaifinta ya rasu.
Ya samu ya kwantar da kansa a jikin hannun kujera yana jin tashin hankali yana sake mamaye shi.
*****
Ihsaan ta ci gaba da zama a gidansu Innayo domin kuwa babu inda zata je Marka ta gaje gidan. Ita kuma Innayo babu yadda zata yi ta koreta domin kuwa umarnin maigidan ne ya ce abarta a dakinta.
Sulaiman ya zama abin tausayi, baya iya wata magana mai tsawo duk ya rame ya lalace. Tunani ne kawai fal a cikin zuciyarsa. Duk da idan ya tuna Irfaan zai auri Ihsaan sai ya ji wani gefe na zuciyarsa tana sanyi.
Ihsaan kuwa ta ƙara maƙalewa Sulaiman. Ko da wasa bata barin su rabu idan ba dai dare ne ya yi ba, sai ya yi shimfiɗa a tsakar gida ya ce mata ta je ta kwanta zafi ne ya yi masa yawa yake son shan iska. Wataran itama takan kwaso shimfiɗar ta ce zata kwanta a waje.
Bayan Irfaan ya koma ya kasa hassala wani abin kirki. Ya zama kamar zautacce. Duk da bai yarda abokan tafiyarsa sun san yana da wata matsala ba, amma da zarar ya keɓe kansa bai da aiki sai tunani. Rana ɗaya ya je gaban madubi yana kallon kansa yana magana shi ɗaya,
“Haba Irfaan. Me ya sa Ihsaan zata zamar maka matsala? Me ya sa ba zaka yi wa kanka faɗa ba? Ka natsu mana! Ihsaan fa ba akanka zata zauna ba. Kada ka bari ‘yar tatsitsiyar yarinya sa’ar autarku ta nemi haukataka.”
Shiru ya yi yana ambaton sunan Allah a zuciyarsa. A hankali kuma sai ya fara neman damuwar yana rasata. Dole ya nemi wuri ya zauna ya fara tsarawa kansa irin rayuwar da ya kamata ya yi da Ihsaan ta hakanne kawai zai hana kansa damuwa.
Tun daga wannan lokacin ya watsar da duk wani abin da ya shafeta ya ci gaba da ayyukansa.
*****
Haka rayuwarsu ta ci gaba da daɗi babu daɗi, har na tsawon watanni uku da sati biyu.
Innayo bata fasa gallazawa Ihsaan ba, musamman idan ta faki idanun Sulaiman. Duk abubuwan da take yi Sulaiman yana sane. Idan wanke-wanke ta sanyata, shi da kansa yake zama su yi tare. Babu abin da ke sa Ihsaan nishaɗi a duniyarta kamar ta ganta zaune kusa da Sulaiman. Sosai yake sanyata nishaɗi, yake bata labarai wanda take zama ta yi ta ƙyalƙyata dariya.
Yau jirginsu Irfaan ya sauka ya fito yana sanye da wani farin lallausan yadi. Kansa babu hula. Fuskarsa tana wadace da fara’a, acan ƙasan zuciyarsa kuwa gabansa ne ke faɗuwa.
Abba ya fara hangowa ‘yan sanda biyu suna tsaye a bayansa. Yana murmushi ya nufi inda ya hango mahaifinsa. Juyowan da zai yi ya hango mahaifiyarsa da Zarah itama tana tsaye a gefe. Dukkansu sun kafe shi da idanu. Ya fahimci abin da suke nufi. Kowannensu yana so yaga wanda ɗansu yafi so a cikin su. Dabara ta faɗo masa ya yi tuntuɓe da gangar, ya rintse idanu tare da durƙusawa ya riƙe ƙafar yana ci gaba da rintse idanu.
Babu shiri Umma da Abba suka ƙaraso da hanzarinsu. Kowannensu suka riƙe shi suna tambayarsa bai dai ji ciwo ba ko?
Irfaan ya yi murmushi ya tashi tsaye. Hakan yasa duk suka tashi suna dubansa cike da mamaki.
“Dukkanku ina sonku Umma da Abba. Kamar yadda dukkanku kuke son ɗanku. Na rasa gurin wanda zan fara zuwa ne alhalin duk na yi kewarku shi ya sa kawai na yi hakan.”
Abba ya kalli Umma duk suka yi dariya. Lallai ɗansu ya fi su wayo. Gaba ɗaya suka rungume shi cike da so. Hannun Zarah ya kama suna tafe suna hira har suka isa gurin motocinsu.
Yana shiga gidansu ya dinga kallon ko ina yana mamakin yadda yake ganin komai ya sauya masa.
“Umma na yi kewan gida sosai. Bazan iya sake tafiya mai nisa inbarku ba.”
Duk suka yi dariya. Ɗakinsa ya wuce angyara masa ko ina sai ƙamshi kawai ke tashi. Wanka ya fara yi ya kintsa sannan ya fito domin kwasar girkin Ummansa.
Sosai ya saki jiki ya kwashi abinci.
*****
Yau satinsa ɗaya da dawowa don haka Abba ya ajiye shi akan maganar Ihsaan. A natse ya dubi mahaifinsa ya ce,
“Duk yadda ka ce hakan za ayi.”
Abba ya jinjina kai,
“Ranar ita yau insha Allahu za a ɗaura aurenka da Ihsaan.”
“Allah ya nuna mana Abba.”
Shi dai Abba sai mamakin sauyawarsa yake. A zuciyarsa kuma yana ta addua kada Irfaan ya cutar masu da yarinya, dan ya sani sarai baya ƙaunarta.
*****
Babu wani shiri da akayi. Abba dai ya buga I.V ya kuma gayyaci abokansa da ‘yan Ofis ɗinsu. Wannan lamari ya jawo cecekuce a cikin Ofis ɗinsu. Mutane da yawa sun yi mamaki. Kai tsaye aka fassara hakan da yadda su Abba suka ƙosa ya yi aure shi ya sa akasa lokacin da wurwuri.
Masu fatan alkhairi suna yi, matan Ofis ɗin kuwa gulma kawai suke yi suna son ganin wacece wannan mai sa’ar? Surutai kala-kala babu irin wanda ba’ayi ba.
Ranar Juma’a aka ɗaura auren Irfaan da Ihsaan akan sadaki naira dubu hamsin. Anan Masallacin Sultan Bello Kaduna. Ana saukowa daga Masallaci. A lokacinne kuma Irfaan ya zame kansa ya wuce gida kawai. Idan bai manta ba, yaga idanun Sulaiman a wurin yasha manyan kaya. Sai dai idan ba gizo idanunsa suke yi masa ba, babu fara’a a fuskar Sulaiman. Yanayinsa kamar yana cikin wata damuwar.
A ɓangaren ‘yan uwan Ihsaan ɗin kuwa, babu wanda yasan da maganar auren, daga Baba Sani, sai Sulaiman sai kuma ƙanin mahaifin Ihsaan Baba Shu’aibu. Shima ko da akayi masa bayani bai tsaya bincike ba ya amince kasancewar yaji maganar kuɗi
Da shigowar Irfaan ya wuce ɗakinsa tare da rage kayan jikinsa. Ya kwanta a bisa gado shiru. Kasancewar gidan babu wasu jama’a domin Umma ta kasa yin gayya, sai ‘yan uwa da suka zama dolensu.
Ji yake kansa yana sarawa kamar zai cire. Idanunsa a lumshe suke yaji takun tafiya. Bai buɗe idanun ba. Shi a zatonsa mahaifinsa ne. Shirun da yaji ne yasa shi ware jajayen idanun.
Sulaiman ya gani hawaye suna ta zuba kamar ruwan famfo. Da farko tunda aka ɗaura auren Irfaan ke jin haushin Sulaiman. A yanzu kuma sai duk jikinsa ya yi sanyi.
“Sulaiman me ya sa kuka kuma? Ko akwai wani abu da kake buƙata insake yi maka ne?”
Sulaiman ya kasa magana sai duban Irfaan kawai yake yi. Irfaan ya tashi zaune ya juyo sosai yana fuskantarsa.
“Sulaiman na yi zaton a yanzu zan daina ganin irin wannan tarin damuwar daga fuskarka?”
Sulaiman ya goge hawayensa ya ƙirƙiro murmushi ya ɗora bisa fuskarsa.
“Wannan karon ba damuwa ba ce a fuskata. Farin ciki nake yi burina ya cika. Ina farin ciki ne Ihsaan za ta sami ‘yanci. Za ta huta da azaban da take ciki. Ka gama mini komai Yaya Irfaaan. Ina fatan wataran ka so Ihsaan fiye da yadda ni na sota. Yanzu zan koma gida. Za ka yi haƙuri da Ihsaan a yanzu har zuwa lokacin da zata saba da rashina akusa, dan nasan anan aikin yake.”
Irfaan ya kasa magana sai gyaɗa kansa kawai yake yi. A lokacinne kuma abokansa su uku suka sawo kai ɗakin.
“Ango ango kasha ƙamshi. Yau dai sai mun ga irin matar da ta yi zarra.”
Shamsu ya yi maganar cikin barkwanci. Salisu ya taɓe baki ya ce,
“Baka ga irin bikin da akayi bane? Naji labarin yarinyar akwai ɗan banzan muni.”
Sulaiman ya taso yana jin zuciyarsa tana suya. Zuciyarsa ke gaya masa ya shaƙe shi duk abin da zai faru sai dai ya faru. Irfaan ya yi gyaran murya yana kallon Sulaiman.
“A’a Sulaiman. Ka je kawai Allah ya tsare.”
Ya fahimci abin da Irfaan yake nufi, don haka ya tanƙwara kansa ya fice. Irfaan ya dubi Salisu ya ce,
“Waye ya gaya maka haka?”
Salisu ya yi dariyan shaƙiyanci ya ce,
“To idan ka shirya abin arziki me zai sa mu ji zancen daga sama? Kuma kalleka fa jiki asanyaye kamar wani mara lafiya. Da ba a faɗa a Ofis ba baza mu taɓa jin labari ba, tunda kai baka ɗaukemu a aminai ba.”
Anan suka ci gaba da caftarsu. Ganin Abba suka yi a ƙofar ɗakin yana masu sallama. Gaba ɗaya suka amsa masa tare da miƙewa suka sara masa. Yana murmushi ya ce,
“Gobe insha Allah zaku je ku kai iyayen Irfaan mata zuwa ɗauko amarya.”
Duk suka amsa masa da “Ok Sir!”
Shi kuwa Irfaaan ji yake shikenan asirinsa ya tonu.
Dole yasa riga suka fito tare gudun ya ɓatawa Abba rai.
“Mutumin Gobe fa akwai shan lagwada.”
Cewar Nazifi da tunda aka fara maganar bai ce uffan ba. Duk sauran suka yi dariya harda tafawa. Shi dai Irfaan bai ce uffan ba. Shamsu ya raɗa masa a kunne
“Akwai wani magani da zan baka gudun ta rainaka.”
Wannan karon zuciyar Irfaan ya fara wani irin tafarfasa yana jin kamar ya ci mutuncin abokansa ya koresu. Da ƙyar ya iya tausar zuciyarsa, sannan ya yi magana cikin ɗaure fuska.
“Wai ku idan mutum baya jin daɗi baku taɓa fahimta ne? Ko kuwa sai na fito na gaya maku? Don Allah ku rabu da ni mu zauna lafiya.”
Yadda suka ga ya ɓata fuska sai duk suka kama kansu.
*****
Ihsaan tana zaune bayan ta gama yiwa Innayo wanke-wanke ta tuƙa uban tuwon da yau da gobe yasa ta iya. Sai kuma ta zauna ta yi tagumi tana jin damuwar rashin mahaifinta. Sosai take kuka babu gaira babu dalili.
A haka Sulaiman ya risketa bayan ya shigo falon.
“Kyautatawata wa ya taɓa min ke?”
Ya yi maganar cikin ƙarfin hali da jawo fara’a da ƙarfi da yaji.
“Yaya Sulaiman… Ina tunawa da Babana ne.”
Ta bashi amsa cikin kuka. Zama ya yi a gefenta sannan ya ce,
“Idan antuna mahaifi ba kuka akeyi ba. Addu’a za ki dinga yi masa da zarar kin tuna da shi.”
Bata amsa ba, bata kuma ce komai ba.
“Ihsaan ina so ki kwantar da hankalinki da abin da zan gaya maki. Kinyi min alƙawarin yi min biyayya?”
Bata kawo komai aranta ba ta gyaɗa kanta.
“Yauwa. Ai na gaya maki zansa kiyi auren kisan wuta ko? Da ƙyar na samu wani a birni ya ce ya amince zai aureki. Kinga asirinmu a rufe zamu sake yin aure. Don haka kiyi haƙuri zuwa gobe insha Allah za akaiki ɗakinki yau aka ɗaura maki aure.”
Wata ƙara da tasa sai da ya hautsina masa ‘yan hanji. Innayo tayo ɗakin da gudu har tana tuntuɓe. Kalaman da Ihsaan take faɗa ne yasa ta tsaya turus.
“Wallahi bazan auri kowa ba idan ba kai ba. Ni bazan zauna da kowa ba. Ka barni kawai inzauna anan idan ba dai kaima ka gaji da ganina ba. Wayyoo Innanmu ki taimakeni ki dawo kiyiwa Yaya Sulaiman. Babanmu ka taimakeni.”
Yadda take yi idan wani bai sani ba zai ce aljanu gareta. Kuma ta riƙe shi sosai tana sambatu.
Sulaiman yasan za ayi hakan, ya sani akwai rigima a ƙasa a wurin raba shi da ita. Gaba ɗaya dabara ta ƙare masa. Don haka ya yi tagumi kawai yana kallonta. Innayo ta ja tsaki kawai ta juya tana masifa tana cewa,
“Uban wa zai aureki sakarya? Mu dai mun samu mun rabu da masifa, duk ƙwaƙwarki babu sauran igiyoyi a tsakaninki da Sulaiman.”
A ranar Ihsaan ta kwana cikin zazzaɓi mai zafi. Kasancewar ba ƙaramar kuka ta yi ba.
*****
Abokan ango sunsha manyan kaya, sun shirya tsaf domin zuwa ɗauko amarya. Kafin su tafi sai da suka sanar a Ofis akan za su je ɗauko Amarya.
Mata biyu suka shirya suka ce Wallahi sai sun je ganin ƙwam.
Ƙannen Umma biyu da na Abba suka shirya suka rankaya a motocin su Shamsu. A tare suka kama hanyar Zariya. Wanda suke fatan har Saulawa insha Allahu.
Kaf cikin mutanan nan babu wanda bai ƙosa yaga amaryar ba. Kowa da yadda yake kisma kamanninta a zuciyarsa.
Shi kuwa Irfaan yana ganin ‘yan sandan nan mata sun shiga mota yasan kashinsa ya bushe. A ranar duk iya dauriyarsa ya kasa kai koda kofin shayi ne bakinsa.
Muje zuwa.
‘Yar mutan Bornonku ce