Umma da kanta ta shigo ɗakinsa hannunta riƙe da kofin shayi.
“Karɓa kasha.”
Ya ɗago yana dubanta. Yadda ta kafe shi da idanu ne ya hanashi furta komai ya sunkuyar da kai. Umma ta ƙarasa bakin gadon ta zauna a gefensa.
“Ka karɓa nace. Ka gama mu yi magana.”
Hannunsa yasa ya karɓa. Gaba ɗaya bakinsa ɗaci yake masa, don haka ya dinga kurɓa kaman yana shan magani.
Tas! Ya shanye tare da ajiye kofin yana duban Umma.
“Abin da nake so da kai shi ne, ka daure ka cije ka cinye jarabawanka na auren Ihsaan. Idan ka daure za ka ga kamar ba ayi ba. Kaji ko? Yarinyar nan kada ka sake ka wulakantata domin za ka iya yin danasani anan gaba. Yaron nan ya gama mana komai tunda ya miƙawa Abbanku ƙoda, wanda duk ‘yan uwan mahaifinka suka kasa yin hakan, duk kuwa da irin tarin taimakon da yake masu. Ka tashi ka yi wanka ka shiga cikin mutane ka ci gaba da hulɗoɗinka.”
Irfaan ya jijjiga kai tare da sauke ajiyar zuciya. Haƙiƙa Ummansa ta yi gaskiya. Ya zama dole ya ci gaba da nuna jarumtarsa. Yanzu sharrin su Shamsu kawai ya rage masa ya jure daga nan zai iya da sauran matsalolin. A hankali ya ce,
“Umma zanyi yadda kika ce.”
Umma bata bar ɗakin ba har sai da taga ya shiga wanka.
Acan ɓangaren ‘yan ɗauko amarya kuwa, sun fara sarewa da yadda hanyar take. Dukkansu mamaki suke ta yadda Irfaan ya samo yarinya a wannan ƙauye. Gaba ɗaya tunaninsu ya basu matar Irfaan ta zo ƙauyen mahaifinta ne dan a ɗaura mata aure, ba wai anan take ba.
A ƙofar gidansu Sulaiman motar da ta yi masu jagora ta ja burki, hakan yasa dukka sauran motocin suka sami wuri suka yi fakin.
Folisawan nan mata suka yi ta duban unguwan kowacce tana ƙyafe baki. Suna ganin iyaye za su shiga suka yi saurin cusa kansu.
Ƙanwar mahaifin Irfaan Inna Ladidi ita ta dakatar da su,
“A’a ku tsaya mu fito da ita kada a cika masu gida.”
Jiki asanyaye suka koma wurin su Shamsu bakin su cike da gulma.
Ihsaan tana tsugunne a bakin murhu tana hura wuta da baki, idanun nan sun kaɗa sun yi jaa. Jikinta har yanzu da zazzaɓi, sai dai bata sami kulawa ba, sakamakon tunda Sulaiman ya tafi Sallar asuba bai sake dawowa ba. Ko alama bata wani damu ba, a zatonta ko wani aikin ne ya riƙe shi a wurin.
Ganin mutane yasa ta cika da mamaki. Tana jiyosu suna gaisawa da Innayo, kafin Innayon ta kwaɗa mata kira akan ta kawo tabarma.
Bayan sun gaisa ne, suka yi mata bayanin sun zo tafiya da Ihsaan ne. Da yake mijinta ya yi mata bayani, akan auren Ihsaan wanda ya yi mata ƙaryar Abba ne ya bada ita ga wani mai yi masa hidima, sai bata damu ba. Daɗi ne ma ya kasheta Ihsaan za ta bar mata gida.
Da yake akwai mugunta a zuciyar Innayo ko wanka bata sa Ihsaan ta yi ba, ƙarshe ma ta haɗata da hayaƙi. Innayo ta ce,
“Ga Ihsaan ɗin sai ku tafi.”
Dukkansu suka ware idanu,
‘Wannan ce Ihsaan ɗin? Ko dai baki fahimcemu bane baiwar Allah?”
Innayo ta yi dariyar mugunta ta ce,
“Ras! Na fahimceku kuwa. Don haka ku ɗauketa ku tafi. Kuma Wallahi babu mai ɗaukan ko tsinke anan gidan.”
Inna Ladidi ta sake duban Ihsaan da ke yayyanka idanu ta ce,
“Amma dai zaki taimaka ki bata hijabi ko?”
Ihsaan ta fasa kuka tana faɗin babu inda za ta tafi. Innayo ta yi waje, sai gata ta dawo da ƙaton icce ta ce,
“Wallahi idan baki bisu kun tafi ba, sai na fasa wannan kan naki mai kama da ƙwallon giginya. Kin kuma san halina sarai zan aikata.”
Ihsaan ta miƙe jikinta yana kyarma, ta dawo kusa da Inna Ladidi tana kuka wiwi. Tausayi ya karyo zuciyar Inna Ladidi har sai da hawaye suka cika mata idanu.
Haka suka kamo hannunta daga ita sai ɗankwali riga daban zani daban. Har sun kusa fita ta ce,
“Ku bari zan ɗauki abin da Babana ya bani.”
Innayo ta kakare ƙofa ta ce,
“Kinsan Allah? Kika dawo cikin gidan nan zaki gane ruwa ma shayi ne. Bayin Allah ku yi maza ku tafi da ita.”
Babu wanda ya iya tanka mata domin sun fahimci ƙiris take jira ta tara masu jama’a.
Suna fitowa su Shamsu suka yo kansu suna cewa,
“Inna ina amaryar? Ko ba nan bane gidan?”
Inna ta jinjina kai ta ce,
“Ga amaryar nan.”
Duk suka bi Ihsaan da kallo. Babu wanda ya iya furta ƙala, sun dai tsaya suna kallon ikon Allah. Ihsaan aka sanya agaban motar Shamsu. Saboda tsabar ɗoyi da take yi, hatta ƙamshin da motar take yi, ya juye zuwa wari.
Haka kowa ya shiga motarsa kowannensu da irin tunaninsa.
Tafiya ta miƙa, babu abin da ake ji sai shessheƙan kukan Ihsaan. Babu wanda ya iya tankawa saboda tsabar kaɗuwa da mamaki. Su kansu matan Ofis ɗinsu da suka je ganin gulma jikinsu ya yi sanyin da suka kasa kiran kowa su faɗa. So suke sai sun ga ƙarshen wannan abu.
Shamsu ya shaƙi iska ya furzar, a zuciyarsa ya ce,
‘Irfaan ya auro aljana bai sani ba. Idan kuma Sir Abbas ne ya yi masa wannan auren, bai kyauta masa ba. Ya yi amfani da ƙarfin biyayyan da Irfaan yake masa ya aura masa tashin hankali. Idan ada Irfaan bai rasa komai ba, na jin daɗin rayuwa, a yanzu kam ya samo wacce zata raba shi da rabin kwanciyar hankalinsa.’
Shi kaɗai yake surutansa a zuciya. Da zarar ya ɗan karkace ya saci kallonta sai yaji kamar ya yi parking ya ce ta saukar masa a mota. Ɗan kwalin nan saboda datti duk ya dafe.
A haka suka iso cikin Kaduna.
Abba da Umma suna tsaye suna jiran ƙarasowansu. Hatta Baba Sani tagumi kawai ya yi yana jinjina wannan lamari.
Ihsaan tana sauka a motar ta yi hanyar gate da gudu tana kuka. Duk yadda taso ta buɗe gate ɗin ta kasa. Abba da Umma suka dubi juna suna mamakin wacce irin amarya ce aka kawo babu ko lulluɓi? Babu wanka bare asaran samun sabbin kaya a jikinta.
Baba Sani ya yi juyin duniyar nan ta yi haƙuri ta zo su shiga amma fir taƙi kallonsa. Sunan Sulaiman kawai take kira tana ajiyar zuciya. Umma ta ƙarasa tana lallashinta nan ma taƙi tashi.
Mamaki ya hana kowa magana a wurin. Duk suna nan tsaye sunyi cirko-cirko, anrasa wanda zai iya tanƙwara amarya ta shigo ciki.
Yana sanye da shaddarsa mai ruwan toka, kayan sun yi matuƙar amsarsa. Kallo ɗaya idan kayi masa ba zai taɓa gamsar da kai yana cikin damuwa ba, kasancewar ya kori damuwar a bisa fuskarsa ya kuma wadata fuskar da walwala ta yadda dole yasawa mai son sanin halin da yake ciki waswasi.
A hankali yake takowa, wanda yasa idanu suka koma kansa. Kai tsaye wurin da Ihsaan take a tsugunne tana kuka ya dosa. Gaba ɗaya ƙamshinsa ya wadata farfajiyan gidan.
A gabanta ya tsugunna yana ƙare mata kallo.
“Ihsaan ɗin Sulaiman.”
Ya kira sunanta cikin wani irin murya mai tsananin taushi. Cak! Ta dakata da kukan, amma kuma bata ɗago ba. Ya sake sassauta murya ya ce,
“Ki yi haƙuri ki tashi mu shiga ciki kin ji? Insha Allahu zuwa anjima zan kawo maki Sulaiman. Amma sai kin saki jikinki kinyi duk abin da su Umma suka ce kiyi kin ji? Sannan kuma ki daina kukan nan tunda Sulaiman baya son ganin hawayenki. Ko kina so ki ɓata masa rai?”
Da sauri ta ɗago tana girgiza kai. Ada babu halittar da ya tsana ya gani kamar Ihsaan, amma a yanzu tsananin tausayinta yasa ya kafeta da idanunsa ba tare da ya kauda su ba.
Murmushi ya sakar mata, sannan ya tashi tsaye ya miƙa mata hannunsa ta kama. A tare suka jero wanda Allah yaba Salisu sa’a ya dinga ɗaukansu hoto.
“Tsakaninka da Allah zaka kawo min Yaya Sulaiman?”
Ta jefe shi da maganarta, bayan ya yi nisa a cikin wani tunani.
“Eh na yi maki alƙawari. Kema za ki yi abin da nace maki?”
Ga mamakinsa har tana dariya tana rantse masa za ta yi.
Gaban Umma ya tsaidata ya ce,
“Umma ga Ihsaan a shiga da ita.”
Gaba ɗaya matan suka wuce ciki da Ihsaan Umma tana biye da su. Shi kuma ya dawo yana duban Baba Sani ya ce,
“Baba Sani me zai sa a kawo Ihsaan daga ita sai kaya daban-daban?”
Kunya ta ishi Baba Sani ya shiga basu haƙuri yana tabbatar masu ya gayawa Innayo a shirya Ihsaan sosai amma ta yi kunnen uwar shegu da shi.
Abba ya jinjina kai, ya ce,
“Allah shi kyauta.”
Irfaan ma girgiza kansa ya yi ya wuce wurin abokan aikinsa. Duk suka dube shi duba na tausayawa.
“Irfaan banji daɗin yadda…”
Da hannu Irfaan ya dakatar da Shamsu ya dube su ɗaya bayan ɗaya, ya sauke idanunsa akan matan Ofis ɗinsu ya ce,
“Zaku iya tafiya. Mun gode da ɗawainiya.”
Kafin su sake wata magana kawai ya juya abinsa.
Ya shiga cikin gida ya sami anata fafatawa da Ihsaan akan ta tsaya ayi mata wanka a shiryata. Ita kuma ta ce ai ta iya wankan.
Bai ce komai ba ya shige ɗakinsa.
Haka Ihsaan ta shiga ta watsa ruwanta ta fito. Sabbin kaya Umma ta kaiwa Inna Ladidi ita kuma ta kaiwa Ihsaan tasa.
Irfaan ya fito domin cin abinci ya ga Ihsaan tana zaune a ƙasa ta yi tagumi. Sai a lokacin ya fahimci Umma duk ta sallami sauran jama’ar. Ita kanta Zarah ta ƙi zuwa kusa da ita.
“Kin ci abinci?”
Ya tambayeta yana doso inda take. Ta ɗaga kai alamun eh. Bai ce komai ba ya nemi wuri ya zauna. Addu’a kawai yake yi kada Abba ya ce dole ya bar masa gida. Ya fi son Ihsaan ta zauna a wurin Umma, idan suka zauna a gidansu su biyu bai san yadda za ayi ba. Domin komai yana iya lalacewa.
Umma ta shigo ta zauna tana duban yadda Irfaan ya faɗa a lokaci guda.
“Irfaan zuwa gobe zaka koma gidanka da matarka. Abbanka ya ce ingaya maka. Daga nan shi kuma zai sa ido akan zamantakewarka da matarka. Ya ce anjima kada ka yi nisa za ku yi magana.”
Duk yadda yaso kada ya nuna mata firgicinsa sai da hakan ya gagara. Ya yi matuƙar kaɗuwa. Tayaya hakan zai faru? Ta ina zai fara?
Aslm.
Anty Fati fatar kina lfy.