Bayan sun dawo daga Masallaci suka zauna suna hirarsu. Abin mamaki da al’ajabi wai Irfaan ne ke hira da Sulaiman kamar wani abokinsa.
Ihsaan tana zaune a tsakiyansu, duk hirar da suka yi muddin ya shafi ƙauyensu sai ta sa baki. Shi dai Irfaan sai idanu kawai yake binta da su yana mamakin ashe tana da baki haka.
Har sha biyun dare suna tare, itama Ihsaan ɗin tana nan zaune. Anan suka ci kaji da kayan marmari. Ihsaan ta dube shi ido cikin ido ta ce,
“Yaushe za ka zo ka tafi da ni?”
Ya ƙura mata idanu sannan ya ce,
“Zuwa jibi insha Allahu.”
Farin ciki ya tsirga mata. Ta sake dubansa ta ƙyalƙyace da dariya, sannan ta ce
“Ohhh Yaya kasan me na tuna? Lokacin nan da Baba Marka ta yi min dukan tsiya, ta hankaɗani waje, ka zo wucewa ka ganni ka kaini gefe ka bani gwaiban da kuka je kuka samo a lambu.”
Duk suka kafeta da ido. Babu abin dariya a cikin kalamanta sai ma abin tausayawa. Amma ita sai dariya take yi abinta.
Duk jira suke yi ta yi barci Sulaiman ya wuce ɗakin baƙi, hakan ya gagara, sai ma su da ta bari suna zabga hamma.
“Ihsaan ki je ki kwanta gobe zamu ƙarasa.”
Ta haɗe rai,
“Allah babu inda zanje inbarka. Tare zamu kwana.”
Duk ɗakin ya ɗauki shiru. Irfaan kuwa tausayinsu ne ya ƙara kama shi. Don haka duk suka yi tsit.
Cikin ikon Allah wani irin barci ya yi gana da ita. A tare suka sauke ajiyar zuciya, domin kuwa yau Irfaan yasha wahalan da yake so ya samu ya huta.
Irfaan ya ɗan dube shi,
“Wai Sulaiman ya akayi ka faɗa soyayyan Ihsaan ne har haka? Har yanzu lamarinku yana bani mamaki.”
Sulaiman ya ɗan musƙuta ya ce,
“Ihsaan yarinya ce da ta taso a cikin maraicin uwa. Tun tana ƙarama mahaifiyarta ta rasu domin kuwa bata yayeta ba. Marka aka ba Malam shawaran ya auro saboda bazawara ce kuma tana shayar da yarinyarta.
Duk da baya son Marka haka ya aureta ya miƙa mata Ihsaan. Kasan abin da matar nan ta yi?”
Irfaan ya girgiza kai,
“Nonon akuya ta dinga tatsa tana ba Ihsaan. Shima kuma sau biyu a rana. Yarinyar nan ta rame ta lalace. Daga ƙarshe ciwon yunwa ya shigeta.
Intaƙaita maka da tarin wahala Ihsaan ta buɗi ido. Malam Bala baya iya yin komai domin kuwa ta mallake shi.
Cikin hukuncin Allah ‘yar Marka ta rasu. Yaya Irfaan zaka yi zaton Ihsaan ce ta kashe yarinyar nan. Sai tsanar ta ƙaru. Ruwa da iska baya hana Marka tura Ihsaan talla. Tasha wahala.
“A lokacin da yarinyar nan takai shekaru goma a duniya, kasan me ta yi mata?”
Irfaan ya gaza magana sai faman girgiza kai yake yi yana jinjina ƙarfin rashin imani irin na Marka.
Sulaiman ya furzar da wani irin huci yana jin zuciyarsa tana ɗaci.
“Matar nan sai ta ɗauki Ihsaan ta ɓoyeta a cikin wani ɗaki ɗakin antaɓa kiwon awakai a ciki. Ta ɗaureta kamar wata akuya. Tana bata ƙanzon tuwo sau ɗaya a rana.
“Ihsaaan ta lalace ta zama kamar aljanah. Ina nufin siririya sosai hannunta kamar tsinke. Babu wanda yasani, andai san ba a ganinta. Kada kace Malam Bala bai sani ba, yana sane da komai. Idan abin ya ciyo shi sai dai ka ga yana kuka.
“Wata mata ta shiga gidan lokacin babu Marka. A lokacin ta ji wani irin tari sama-sama. Tana leƙawa ta ga mutum. Wallahi bata gane Ihsaan ba ce sai da ta ƙara cusa kai sosai.
“Shi ne matar ta fito da ihunta ta yi gidan mai gari ta sanar masa. A ranar nima naje na kuma ganta, na ji tausayinta na ji tashin hankali. Zuciyata ta dinga gaya min in kashe Marka kawai dan a huta da mugun iri. A lokacin ina ganiyar shaye-shayena. Da ƙyar na tanƙwara kaina na bar abun a raina.
“Ihsaan ta ɗan sami ‘yanci sakamakon gargaɗin mai gari. Amma a cikin gida tana cin kwakwa. Ta koma zuwa Islamiyya. Idan anhanata abinci Malam Bala ke hana kanshi ya faki idanun Marka ya miƙa mata. Allah ya ɗorawa Ihsaan son Babanta, da shi kaɗai take samun farin ciki. Daidai da kayan sawan Ihsaan basu wuce kala biyu ba, su kansu duk sun yayyage.
“Kana ganin Ihsaan a haka ko? Ina tabbatar maka da shekaru biyar da suka wuce ka ganta da gudun gaske zaka arce kana neman taimako akan kayi gamo. Abun babu daɗin misali.
“Bari ka ji mafarin da na fara son Ihsaan. Allah ya jarabceni da son wata yarinya, wacce a zahiri ta fi ƙarfina, musamman yadda na yi suna akan shaye-shaye. Ranar wata asabar naje ƙofar gidansu yarinyar, dama ta tsaneni ta yi ta jan kunnena akan inkiyayeta amma fir na ƙi.
“Yadda take yi min fara’a abin ya bani mamaki. Ban ankara ba ta riƙe rigana ta dinga ihu. Mamaki yasa ko motsi na kasa tsayawa kawai na yi ina kallon ikon Allah.
“Mutane suka fara taruwa, anan take cewa wai ni ne na taɓa mata ƙirji ina ƙoƙarin kwance mata zane.
“Aka rufeni da duka sosai da ƙyar na ƙwaci kaina, sai kuma ruwan duwatsu. Ji na yi anrufeni da wani abu, sannan naji mutum ya yi min rumfa. Ƙoƙari nake yi in ga waye ya yi min rumfa? Waye ya taimakeni?
“Da ƙyar aka cireta a jikina. Inbuɗe idanu sai naga Ihsaan ce take kuka da iya ƙarfinta tana maganar da hayaniya yasa ban iya jin me take cewa ba.
“Haka aka tafi da ni gidan mai gari da wannan yarinyar Sadiya. Bayan ta gama jawabi cikin kuka. Baƙin ciki yasa kawai ina ta kallonta. Na kasa yafe mata na kasa yafe wannan sharrin. Muryar Ihsaan muka ji ta ce,
“Wallahi ba haka ya faru ba, duk abin da ya faru da ni da ƙawayena mun dawo talla babu wanda bamu gani ba. Anan ta zayyane masu duk abin da ya faru. Sai duk aka kalli Sadiya da take sunkuyar da kai. Mai gari ya daka mata tsawa akan ta faɗa gaskiya ko yasa a zaneta. Sai ta kama kuka tana cewa sharri ta yi min saboda ta tsani ina kulata da sunan soyayya.
“Kaji mafarin da naji wani abu ya darsu a zuciyata akan Ihsaan. Tun daga nan idan Ihsaan ta ganni ina shan wani abu, sai ta zo gabana ta yi ta kuka tana roƙona indaina don ana zagina a gari.
“Ban taɓa duba maganganunta ba, sai da watarana na yi shaye-shaye na fita hayyacina. Aka dinga bina ana harbina ana yi min waƙa.
A lokacin ƙarfe goman dare, Ihsaan ta dawo tallan abinci kasancewar bata saida ba, ita kuma Marka ta ce mata idan har bata saida ba kada ta dawo mata gida, shiyasa ta tsaya har ta saida.
“Yarinyar nan ita ta kori masu bina, suna ta zaginta amma bata kula ba. Ta cire ɗankwalinta ta ɗaure min kaina, sannan ta zauna kawai tana kallona tana kuka. Bansan dalilin da yasa Ihsaan take yi min irin wannan soyayyar ba. Bansan me ya sa take tausaya mini ba. Ina nan kwance wani ƙanina ya zo wuce wa ta roƙe shi ya taimaka su kaini chemist. Tare suka kaini Chemist aka gyara min kaina sannan na zauna ina hutawa. Da ƙyar na iya cewa ta wuce gida. Abin da ban sani ba, Ihsaan ta cire kuɗi a cikin kuɗin tallanta ta baiwa mai chemist ɗin nan.
“Da ta koma babu abin da Marka ta fara tambaya sai kuɗinta. Ta gaya mata wasu daga kuɗin sun faɗi. A ranar Ihsaan a asibiti ta kwana, saboda mugun dukan da Marka ta yi mata.
“Da aka gaya min na tafi har gidan da wuƙa na shiga ɗakin Markan na ciro wuƙar nan. Jikinta babu inda baya rawa tana bani haƙuri. Kashedi mai zafi na yi mata, na kuma gargaɗeta da kada naji wata magana ta fito.
“Kaji dalilin da Marka ta rage cuzgunawa Ihsaan. Amma bata daina ba, ta dai sami sassauci. Tun daga nan na daina shaye-shaye na yi wa Ihsaan alƙawarin ba zan sake shan komai ba.
“A lokacin na fara soyayya da ita. Agurin Innayo kawai na sami matsala. Da ƙyar Baba ya tanƙwarata. Mahaifin Ihsaan ya damƙa min amanarta tare da nasiha mai ratsa jiki. Na yi masa alƙawarin zan riƙe wannan amanar. Wallahi soyayyar Ihsaan ta shigeni fiye da tunanin mutum. Ina sonta da gaske. Ansa ranar aurenmu ana ɗagawa yafi a ƙirga. Kuma dukkanmu babu wanda yasan daga inda matsalar take. Shi ya sa ranar da aka ɗaura muka kasa ɓoye farin cikinmu.
“Ban taɓa kisa ba, amma zan iya kisa akan duk wanda ya nemi cusguna mata ko wanene. Hatta yadda nake mayarwa Innayo magana Ihsaan ta ankarar dani rashin dacewar hakan. Na gyara kurakuraina saboda Ihsaan na sami kusanci da iyayena saboda Ihsaan. Me ya sa ba zan so ta a duk yanayin da take ciki ba?”
Irfaan ya yi shiru. Sannan ya sake ɗagowa ya dubi Sulaiman,
“Yanzu shekarun Ihsaan zai kai nawa?”
“Shekarunta goma sha huɗu.”
“Ikon Allah. Sai naga kamar ƙirjin babu komai.”
Sulaiman ya ɗan sunkuyar da kai ya ce,
“Ihsaan tana buƙatan kulawa. Nan da shekaru uku zaka sha mamakin sauyawarta. Wahala ce ta mayar da ita hakan.”
Shi kansa Irfaan sai da ya furta tambayar sannan ya ji wani iri.
“Ka gaya min gaskiya me ya sa ka saki Ihsaan?”
Sulaiman ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce,
“Ina fama da ciwuka ne a jikina a sakamakon shaye-shayen da na yi hanjina ya lalace, zuciyata ta taɓu. Idan ya tashi min zaka yi zaton bazan kwana ba. Ihsaan bata taɓa sani ba, saboda duk lokacin da yake tashi min tana barci ni kuma sai inlallaɓa infita waje inyi ta juyi a ƙasa.”
Irfaan ya kalle shi ya ce,
“Wannan ba dalili bane.”
Sulaiman ya ɗago idanunsa jazir ya ce,
“Na ziyarci likita. Amsa ɗaya suke bani kawai inyi haƙuri in cigaba da shan magani, amma ciwon nan nawa ya riga ya ci ƙarfina. Sun yi mamakin ma da yanzu haka bana kwance. Naga illar shaye-shaye na gama shirya rayuwata da Ihsaan sai gashi ciwo zai yi mana katanga.
“A yadda likitocin nan suke nufi duk da basu fito sun gaya min kai tsaye ba mutuwa zan yi. Hakan ya tashi hankalina, babu abin da nake tunani sai makomar Ihsaan. Idan na mutu na barta a ƙauyen nan babu ko shakka za ta ga tasku.”
Irfaan da ya shiga tashin hankali mara misaltuwa ya dubi Sulaiman duba sosai, ya ce
“Babu abin da zai sameka. Insha Allahu zan fita da kai ƙasar zamu sami ƙwararru waɗanda za su dubaka, su yi maka aiki ka sami lafiya kaji? Ba zaka mutu yanzu ba insha Allahu. Ban ji daɗin da ka kasa sanar mini ba, da tuni anwuce wurin. Kada ka sake barin cuta a jikinka, likitoci basu bane Allah, bare su ce sunsan abinda zai faru da bawa.”
Irfaan ya yi ta ba Sulaiman ƙarfin guiwa yana gaya masa kalamai masu daɗi. Ya yi ajiyar zuciya ya ce,
“Na gode Yaya. Idan ma ban rayu ba, don Allah ka riƙe min Ihsaan amana. Ban taɓa ganin yarinya mai tausayi kamarta ba. Ta juri tashin hankali. Ina so ka samar mata da farin ciki don Allah.”
Irfaan ya ce,
“Kada ka damu Sulaiman kai da kanka zaka yi wa Ihsaan irin kulawan da kake so. Ka tashi kaje ka kwanta daga yau zan fara bincike akan matsalarka.”
Sulaiman ya tashi har ya kai ƙofa ya juyo yana duban Irfaan ya ce,
“Ka kular min da amanata ko bayan bana raye.”
Ya dawo ya ƙurawa Ihsaan idanu da sauri ya goge hawayensa.
Jikin Irfaan ya yi mugun sanyi sai gani yake kamar yana masa bankwana. Ya kasa furta komai har Sulaiman ya fice zuwa ɗakin da ya nuna masa.
Duk da Irfaan ya gaji amma ya gasa runtsawa da sunan barci. A gurguje ya buɗe wayarsa ya fara bincike akan lalurar Sulaiman.
Babu ta inda gabansa baya faɗiwa.
Har asuba Irfaan bai rintsa ba. A lokacin Ihsaan ta farka ta shigo har ɗakinsa domin a falo ta kwana.
“Yaya ina Yaya Sulaiman?”
Miƙewa ya yi ya ce,
“Yanzu zamu haɗu a Masallaci. Zai shigo yanzu.”
Irfaan ya yi ta kwankwatsa masa ƙofa amma bai buɗe ba, don haka ya wuce da sauri yana gudun ya makara. Har ya shiga Masallacin yana dube-dube babu Sulaiman babu dalilinsa. Bayan ya idar da Sallah ne ya dawo ciki yana tambayar Mai gadi ko ya ga Sulaiman.
Sai asannan mai gadin yake gaya masa ai sammako Sulaiman ya yi ya wuce gida wai yana da wani alƙawarin gyara da ya yi yau zai bada.
Irfaan ya saki ajiyar zuciya sannan ya kira shi a waya yana masa faɗan rashin kiransa. Haƙuri kawai yake bashi.
Daga nan Irfaan ya shirya ya wuce gidansu ya ɗauko Abba suka wuce aiki. Ya kasa haƙuri har sai da ya sanarwa Abba komai. Shima hankalinsa ya yi mugun tashi. Don haka duk suka duƙufa da binciken babban likita kuma ƙwararrai a ƙasar masar.
Irfaan ya kira Dokto Salis akan yana son ganinsa. Ya yi ta masa faɗa akan yadda suka iya cirewa Sulaiman Ƙoda bayan suna sane da halin da yake ciki.
Dokto Salisu ya ce babu irin maganar da bai yi masa ba, ya ce muddin bai yi aikin nan ya ceto Abba ba, ya bari wani abu ya sami Abba Wallahi sai ya kashe shi.
Irfaan ya yi shiru yana jin kamar ya yi ta kuka saboda halin da Sulaiman yake ciki. Idan ya mutu ya zai yi da Ihsaan? Shi kansa mutuwar Sulaiman tamkar wani giɓine a cikin rayuwarsa.
Daga nan suka yi shawarwari na yadda za su ɓullowa lamarin, har suka sami matsaya.
A ranar Irfaan ya kasa hasala komai gaba ɗaya jikinsa babu ƙarfi. Ya danna waya ya kira Sulaiman bai ɗaga ba, zuwa can ya ƙara bugawa sai ya ɗaga.
“Hello Yayana.”
“Sulaiman gobe ka zo don Allah. Asibitin nan za su fara ƙoƙari akan matsalarka kafin mu sami tattaunawa da likitan, domin ganinsa ne aka tabbatar mana da akwai wahala, amma yanzu na samu wani amininsa ya yi mana alƙawarin zai yi masa magana akan mu ‘yan uwansa ne ta yadda zai taimakemu ya dubaka da wurwuri.”
Sulaiman ya goge ƙwallan da ya ziraro masa ya ce,
“Na gode da ɗawainiya. Ba zan taɓa mance alkhairanku ba.”
Irfaan ya ɓata rai kamar yana ganinsa ya ce,
“Kada ka sake cewa haka. Kai ɗan uwana ne Sulaiman, zan tsaya tsayin daka akanka kamar yadda zan yi wa Sadiq. Ina jiranka goben.”
Ihsaan ta shigo jikinta itama asanyaye ta ce,
“Ina Yaya Sulaiman ɗin?”
Ya kafeta da ido yana jin wani irin tausayinta yana tsirga masa,
“Ya tafi gobe zai dawo insha Allahu.”
Bata sake magana ba, ta nemi ƙasa ta zauna shiru tare da tagumi.
Shi kuwa Abba kiran Baba Sani ya yi ya gaya masa komai akan matsalar Sulaiman. Kawai Baba Sani ya fashe da kuka yana cewa,
“Me ya sa Sulaiman zai ɓoye wannan lamarin?”
Abba ya yi ta masa nasiha. A ranar ya sanarwa Innayo, ta kira shi har ɗakinta tasa masa kuka. Ya dubeta sosai ya ce,
“Innayo menene abin kuka sai kace na mutu? Kada ki damu don Allah insha Allahu zan sami lafiya. Gobe zan je Yaya Irfaan ya sami wani likitan da zai fara bani taimakon gaggawa. Ƙila riƙeni za su yi. Nidai abin da nake so da ke addu’a sai kuma yafiya.”
Ba ƙaramin dakewa ya yi a lokacin da yake mata wannan maganar ba. Ji yake zuciyarsa ta yi rauni. Soyayyar mahaifiyarsa ya sake dawo masa sabuwa fil! Ya yarda uwa uwa ce, ko da kuwa akan bola take rayuwa.
Innayo ta yi kuka sosai ta ce,
“Ba zan barka ka tafi kai kaɗai ba Sulaiman tare zamu tafi. Baka yi min komai ba na yafe maka. Insha Allahu cikin nasara za ayi maka aiki ka dawo kamar ba kai ba.”
Washegari Sulaiman da Innayo suka taho Kaduna kai tsaye direban Abba ya ɗaukesu ya wuce da su asibiti.
Irfaan yana ta sauri shima ya isa asibitin a lokacin Ihsaan ta faki idanunsa saboda ta ji ana maganar zuwa asibiti amma bata san wa za a kai ba. Ta nufi motarsa cikin sa’a tana ɗaga boot ɗin motar ta buɗe da alamun a buɗe ya bari. Ta shige tare da rufe kanta.
Ko tsayawa dubata bai yi ba ya fice abinsa. A gurguje ya tafi gidansu ya ɗauki Abba suka wuce asibitin. A lokacin har anbashi gado, domin kuwa kamar jira yake yana isa asibitin ya dinga aman guda-gudan jini.
Sun sami anyi masa allurai har barci ya fara fizgarsa. Abba da Irfaan da Baba Sani sai Innayo, sune tsaye akansa kowanne addu’a yake masa.
“Yaya Irfaan.”
Da sauri duk suka ƙaraso gaban gadon. Ya kama hannun Irfaan ya ce,
“Ka kular min da Ihsaan don Allah. Na gode maku na gode.”
Dukka ɗakin babu wanda bai yi kuka ba, sai Irfaan da yake na zuci.
“Sulaiman zaka warke insha Allahu.”
Ya kama hannun Irfaan yakai gefen zuciyarsa ya ce,
“Nan wurin yana min ciwo. Cikina kamar wuta. Abin da yasa kenan na lallaɓa na tafi da asuba saboda jin cikina da nake yi kamar wuta. Ina Innayo?”
Da sauri ta ƙaraso. Ta kasa riƙe kanta sai kuka kawai take yi,
“Innayo ki yafe min. Baba ku yafe min mutuwa zanyi. Ku kira min Ihsaan ku bata haƙuri ta riƙe Irfaan a madadina.”
Tuni ɗaki ya sake rikicewa. Irfaan ya yi ƙoƙarin ya samu ya kira likita amma Sulaiman ya ƙi sakinsa, ya riƙe shi sosai yana Salati.
Kafin wani lokaci jikinsa ya yi wani irin haske. Irfaan kuwa sai shafa kansa yake yi da ɗayan hannunsa. Ya gaza furta komai. Ji yake zuciyarsa tana wani irin suya.
Ihsaan wacce da ƙyar ta gane inda suka shiga ta shigo ɗakin tare da yaye labulai. A lokacin ta tsinkayi muryar wani likita da shigowarsa kenan yana cewa,
“Allah ya yi wa Sulaiman rasuwa.”
Irfaan ya samu da ƙyar ya haɗa kalmomi ya furta,
“Innalillahi Wa inna ilaihirraji un…”
Tun daga nan bakinsa ya rufe. Hannunsa yake kallo yadda Sulaiman ya sake shi.
Innayo kuwa warwas ta faɗi a wurin. Abba da Baba Sani suka yi ta Salati. Baba Sani yana cewa
“Allah ya baka sa’an tafiya Sulaimanu. Na yafe maka na yafe maka Sulaimanu. Baka yi gaggawa ba bamu yi jinkiri ba. Ihsaan Allah ya baki haƙurin rashin Sulaimanu.”
Ita kanta Ihsaan batasan yadda akayi ba sai ganinta ta yi a gaban gawan Sulaiman wanda likitan ya rufe shi, yana riƙe da hannun Irfaan.
Bata yi wata-wata ba ta yaye lulluɓin. Shi ɗinne kwance.
_Yaya yaushe za ka zo ka tafi da ni?_
_Sai jibi Ihsaan_
Maganar da ya dinga yi mata amsa kuuwa kenan a tsakiyar kai. Duk basu lura da ita ba, sai ihunta da suka ji tana jijjiga shi da ƙarfinta.
Ihunta yasa jama’a da dama shigowa anan ma aka kula da Innayo da ke kwance bata numfashi. Ana riƙeta tana fizgewa. Da ta yi wata ƙara sai ta kifa akan jikinsa bata motsi.
Muje zuwa…
Fatima Dan Borno