Ya kasa jurewa jin kukanta mai karya zuciyar mai sauraro. Don haka ya yaye bargon da ta lulluɓe shi da shi, ya sakko yana dubanta.
“Ihsaan..”
Ya kira sunanta cikin damuwa. Ta ɗago idanunta ta dube shi. Yasa hannu ya yi mata alamun ta zo gare shi.
Asanyaye ta tashi ta zo kanta a ƙasa. Tana ƙarasowa bata yi aune ba, ya jawota ya haɗeta da ƙirjinsa.
A lokaci guda bugun zuciyoyinsu ya sauya. Wasu abubuwa masu kama da mayen ƙarfe ya dinga jansu.
Wani abu mai kama da so ba sha’awa ba, suka tare suka yi masu kane-kane a lokaci guda, irin lokacin da basu zata ba.
Dukkansu suka dinga sakin ajiyar zuciya akai akai.
Ihsan ta yi ƙoƙarin ƙwace kanta saboda yadda tsoro ya mamayeta, ya ɗan bubbugi bayanta yana magana ahankali,
_”Calm down_ Ihsan babu abin da zan yi maki ki natsu kin ji? Kukan da kike yi yana ɗaga min hankali. Bana son ganin hawayenki ina jin ɗaci a zuciyata. Ina jin kamar na gaza wajen baki farin ciki.”
A hankali take gyaɗa kanta. Jikinta ya yi mugun sanyi. Bata taɓa sanin irin wannan baƙon yanayin ba, sai a ‘yan kwanakin nan da Irfaan yake haɗa jikinsa da ita.
Ya jawo hannunta ta hau kan gadon ya jawota sosai ya rungumeta ya jawo masu bargo.
Wani irin sassanyar ƙamshi ya ziyarceta. Ta dinga jin wasu abubuwa suna yi mata yawo a jiki. Tunani kala-kala babu wanda bata yi ba, har barci ya kwasheta.
Duk yadda ya yi dan ya rabata da hijabinta abin ya faskara, dole ya haƙura ya ƙyaleta. Da Asuba ta riga shi tashi. Abin mamaki da kanta ta gyara gidan, ta tashe shi dan ya yi wanka.
Ya yi addu’a tare da miƙa, sannan ya miƙe ya wuce banɗakin. Kai tsaye wurin Larai ta nufa suka yi abin karyawan tare. Sannan ta wuce ta yi shirin zuwa makaranta.
Ya fito yana wani irin ƙamshi. Gaba ɗaya nauyinsa take ji, ta rasa haƙon lamarin da yake yawaita kawo mata ziyara akan Irfaan.
A tare suka fita zuwa gidansu, anan zai sauketa direba ya wuce da su Makaranta ita da Zarah.
Tana kallonsa shi da Abba kamar abokai. Har kullum zuri’ar nan suna burgeta. Tana jin kamar babu zuri’ar da suka kai su farin ciki da kwanciyar hankali.
Tana kallon yadda suka sa Umma a tsakiya tana yi masu rakiya cike da farin ciki a fuskarsu.
Sulaiman ya faɗo mata a rai tasa hannu tana goge hawayenta. Irfaan ya juyo ya kalleta ya fahimci kuka take so ta yi don haka ya girgiza mata kai. Sannan ya yafito ta da hannu. Ta ƙaraso ya ce,
“Umma ta yi wa mijinta addu’a kema zo ki yi min.”
Umma da Abba suka kalli juna, duk suka yi dariya. Ita kuwa sai ta rufe fuska da tafukan hannunta tana dariya. Dama abin da yake so ya gani kenan. Don haka ya yi ajiyar zuciya. Tana nan tsaye har suka shige mota, ya ɗaga mata hannu. Bata san lokacin da itama ta zaro hannayenta ta ɗaga masa ba. A karo na farko da ta mayar masa da irin ɗaga hannun da kullum yake yi mata idan ya ajiyeta a gidansu.
Tunani ne cike da zuciyarta na yadda rayuwar za ta ci gaba da tafiya ahaka. Tana nan tana ɗaukan darussa kala-kala musamman daga cikin littafan marubuta. Ko babu farin fata, za ta yi amfani da kyawawan halayyarta ta siyawa kanta girma da ƙima agunsa.
Har Umma ta ƙaraso kusa da ita bata sani ba.
“Ihsaan yaushe za ki daina irin wannan dogon tunanin? Baki gudun ki kamu da wata cuta?”
Sunkui da kai ta yi tana ɗan murmushi sannan ta ce,
“Bari inƙarasa ingaida Baba Sani.”
Ta wuce wurinsa yana nan zaune ya yi tagumi. Ganinsa ahaka ya ƙarasa kashe mata guiwa.
“Baba wani abu yana damunka ne?”
Ya girgiza kai tare da cire tagumin,
“Babu abin da yake damuna Ihsaan da ya wuce inga kin cire duk wata damuwa aranki.”
Zama ta yi kusa da shi ta yi ƙasa da kanta. Hawayen da take ta kokawa da su kada su zubo sai da suka ɓalle. Cikin shessheƙa take cewa,
“Baba bazan iya mance Yaya Sulaiman ba. Baba me ya sa zai yi min haka? Me ya sa? Sai yaushe zan yarda Yaya ya rasu? Baba zuciyata tana yi min ciwo saboda rashinsa.”
Kukanta take yi sosai. Zuciyar Baba Sani ta karye. Shima ya dinga goge ƙwalla yana cewa,
“Allah ya jiƙanka Sulaiman, Allah yasa ka huta. Haƙiƙa munyi rashi babba. Amma haƙurin shi ya fi dacewa da mu, a matsayinmu na musulmai da muka yarda akwai mutuwa da rayuwa.”
Zarah ta fito tana cewa,
“Anti Ihsaan ina kike?”
Da sauri ta goge hawayen sannan ta tashi tana cewa,
“Sai mun dawo Baba.”
Tana jin tausayinsa ƙwarai. Babu yadda ba ayi da shi ba, akan ya bar aikin gadin nan amma ya ƙi yarda. Sun so ko wani aikin ne a sauya masa, ya nuna shi babu aikin da yafi so kaman gadin da yake yi. Duk da haka sai da Abba ya ƙara wani mai gadin, don ya dinga taya shi hira da kuma buɗe gate da rufewa.
Bayan sun shiga mota Ihsaan ta dinga ɗagawa Baba Sani hannu har suka fice.
“Anti Ihsaan wani abu yana damunki ne?”
Ta girgiza kai,
“Babu abin da ke damuna Zarah da ya wuce inga na yi ilmi mai zurfi.”
Ta ɗan yi dariya sannan ta ce
“Kada ki damu insha Allahu za ki yi ilimi har sai kin gaji. Yauwa kin yi amfani da mayukan nan da na baki kuwa?”
Ta dubeta da murmushi ta ce,
“Eh na yi. Me kika gani?”
Zarah ta taɓe baki,
“Gani na yi baki canza ba.”
Girgiza kai ta yi ta ce,
“Zarah ya kamata ki daina wahal da kanki haka. Ni haka Allah ya halicci fatata. Bata ɗaukan duk wani ƙyale-ƙyale. Duk wanda zai soni zai iya sona ahaka ba tare da na zama yadda ake so ba.
Zarah ta ɗan kalleta ta ce,
“Indai hakane ban taɓa ganin irin wannan fatar ba. Haba! Wallahi ji nake kamar inɗibo koda kalan Choco ne inmanna maki. Lokaci ya yi da ya kamata ku mori soyayyarku ke da Yaya Irfaan.
Sosai ta dubeta,
“Yaya Irfaan fa kika ce… Yaya Irfaan baya sona, yana dai ɓoye ƙiyayyata ce kawai aransa saboda Yaya Sulaiman. Zarah na yi hankalin da nake iya bambance fari da baƙi, so kuma da tausayi duk ina iya bambance su.”
Zarah ta ɗan yi shiru, sannan ta ce,
“Ni kuma a nawa wautan sai nake hango wani abu mai kama da so a cikin idanun Yayana. Amma dai mu bar maganar lokaci zai nuna.”
Da haka suka ci gaba da hirarsu har suka isa Makaranta.
*****
Yau asabar tana zaune a falo ta ji Sallamarsa. Ta ɗago tana dubansa ya ce,
“Ihsaan tashi ki rakani wajen wani taro.”
Ta ware idanu sosai ta ce,
“Haba ya zaka shiga dani cikin jama’a ahaka?”
Ya ɓata rai,
“Ahakan menene? Kayan jikinki duk lafiya lau zamu iya tafiya. Sai dai ko zaki sauya hijabi.”
Ta girgiza kai bata sake magana ba ta koma ciki ta canza kaya tasa wani sabon hijabi sannan tasa turare kaɗan ta ɗauki niƙab ɗinta ta ɗaura ta fito ta same shi a inda ta barshi yana latsa waya.
“Mu je Yaya.”
Bai kalleta ba ya kama hanyar waje yana latsa waya. Sai da suka fito kamar ance masa ya waiwayo ya ga fuskarta a rufe. Ware idanu ya yi,
“Menene haka? Me ya sa zaki rufe fuskarki?”
Ta girgiza kai ta ce,
“Hakanne kaɗai zai yi maka katanga agun masu yi maka dariya idan suka ganka tare da ni. Ina jin damuwa idan naga yadda ake yi maka shaguɓe duk saboda ni.”
Sai da ya ɗan yi shiru, sannan ya ƙaraso gabanta yasa hannu ya kwance mata niƙabin ya dunƙule ya jefar. Yadda ya yi har sai da ta rintse ido a zatonta dukanta zai yi.
“Ihsaan Allah ne ya halicceki ahaka akwai wanda zai iya gyara tsayuwan wata? Duk wanda ya yi maki dariya izgilanci yake yi. Bana jin kunyar nuna iyalina agaban kowa. Ki natsu ki kwantar da hankalinki sai dai ayi maki dariya daga nesa ba dai azo gabana ayi ba. Ko kinga na taɓa ɓoyeki ne agaban mutanena?”
Zuciyar Ihsaan ta yi rauni. Kalamansa suna sake janyo wasu abubuwa masu girma a cikin zuciyarta. A yanzu ta daina shakku akansa, ta yarda Sulaiman ya tafi ya barta a hannu na gari.
“Akwai ranar da zan saka maka akan irin wannan sadaukarwan da kake yi min. Nima insha Allahu watarana zan biyaka.”
Ya yi ɗan murmushi ya ce,
“Da me zaki saka min? Oya shiga mota mu wuce tun kafin inyi latti.”
Cike da jin daɗi ta shiga mota. A karo na farko da zata shiga cikin jama’a ba tare da damuwa ba. Ta yarda idan Irfaan yana gefenta babu wani wanda zai iya wulakantata.
Fatima Ɗan Borno