A natse suka fito daga mota bayan sun isa wurin taron. Hannunsa yana cikin nata, ya dinga gabatar da ita a matsayin matarsa. Mutane da yawa sun cika da mamaki, ta yadda suke ganin duk wayewarsa ace wannan ce matarsa?
Ita kuwa duk wanda ya ɗan gaidata irin gaisuwan wulakancin nan sai ta ɗauke kai kamar bata gani ba. Hakan ya ƙara hasala mutanen wurin gani suke yi dama shi ɗan ƙauye bai iya samun wuri ba.
A ya yin da wasu suke ganin munana sun fi kowa iya faɗin rai. Wasu kuwa jinjina irin baƙin fuskarta suke yi dan basu taɓa ganin irinsa ba, idan ma akwai mai irin wannan bakin to babu ko shakka babu a wannan gari nasu.
Wani ya kasa haƙuri ya juya maganarsa da turanci ya ce,
“Ina ka samo wannan kuma?”
Ta yi murmushi mai ciwo, sai yanzu bakinta ya buɗe cikin siririyar muryarta mai tsananin sanyi da taushi ta mayar masa da amsa cikin lafiyayyen turancinta mai tsananin daɗin saurare,
“A inda ake samo irin mu nan ya je ya samo ni.”
Shi kansa Irfaan kallonta ya yi cikin mamaki. Yasan tana jin turanci, amma yadda ta nuna masa bata iya mayarwa. Shi kuwa wanda ya yi maganar tsananin kunya yasa ya ƙara gaba abinsa.
A high table akayiwa Irfaan wurin zama, don haka ya tafi da matarsa. Yana sane da taron ana haskawa ne live amma ko a gefen jikinsa. Yana so dole sai ya nunawa Ihsaan itama mutum ce kamar kowa, itama tana da cikakken ‘yancin shiga duk inda ta so. Ita mutum ce ba aljanah ba.
Ta ɗan daburce ta dube shi cike da shagwaɓa ta ce,
“Yaya ina tsoro.”
Ya girgiza mata kai,
“A’a kyautatawata banda tsoro.”
Yadda ya yi maganar dole ya sa ta yi dariya. Ta ce,
“Nidai zan je can baya in zauna.”
Ya ɗaga kafaɗa alamun ko a jikinsa sannan ya ce,
“Kina iya zuwa, amma ki tabbata zaki sha duka.”
Ta kama hannayensa ta ce,
“Eh na yarda Walh.”
Ya nuna mata hanya. Tana ƙoƙarin tashi ya danne mata ƙafa. Ta waiwayo tana dubansa, ya ɗaga mata gira haɗi da kashe mata idanu.
Idanunsu suka sarƙe da juna. Zai iya rantsewa bai taɓa kallon ƙwayar idonta ba, a duk tsawon zamansu. Shi gaba ɗaya ma tsoron kallonta yake.
Tana da wasu irin idanu masu matuƙar ɗaukar hankali. Ya yi mamakin samun irin wannan idanun a jikin wannan halittar. Amma da ya tuna da wanda ya halicceta shi yake da ikon sanya mata duk abin da yaso sai ya yi gaggawan kauda tunanin. Yana lura da yadda ta zama wata iri.
_’Anya Ihsaan bata faɗa cikin sonka ba?’
Zuciyarsa ta jefo masa wannan tambayar. Gabansa ya faɗi da ƙarfi. Sai yanzu yake ganin zaƙewarsa ta yi yawa, ya shige mata da yawa. Wanda hakan zai iya sawa yarinyar ta so shi, idan kuma ta so shi yaya zai yi da ita? Yana yin komai ne domin yaga ya faranta mata, yana so ta rayu cikin farin ciki, ba wai ta rayu cikin ƙaunarsa ba.
Yana da wani ƙuduri a cikin zuciyarsa, sai dai ba zai taɓa fitarwa ba, har sai burin Sulaiman ya cika. Shi yasan ƙarya yake yi ya ce zai iya rayuwa da Ihsaan har muddin rai.
Da wannan tunanin ya sake waiwayowa ya yi mata murmushi.
Gaba ɗaya jikinsu babu ƙwari har aka tashi wajen taron, ya kamo hannunta cikin tattausar hannunsa wanda yake sake saukar mata da kasala.
A ciki mota babu wanda yake iya furta komai, shirun yasa ya kai duba gareta, sai kuma ya lura da hankalinta gaba ɗaya baya jikinta, hakan yasa ɗayan hannun ya riƙo nata hannun yana murzawa ahankali.
Har kullum yana mamakin taushin hannun yarinyar kamar auduga. Amma jikinta ko alamar maiƙo babu tsabar tauri. Jikinta kamar leda haka yake.
Tana jin yadda yake murza hannun har cikin ƙwaƙwalwarta ta so ta jure amma hakan ya gagara. Nan da nan hawaye suka fara zuba daga idanunta. Bai kula ba sai da yaji ɗumin hawayen a hannunsa sannan ya yi saurin ɗauke hannunsa. Shi kansa ya shagala da yanayin da suke ciki.
“Ihsaan sai yaushe za ki daina kukan nan? Duk yadda nake so inɗauke wannan damuwar kin gagara bani haɗin kai.”
Ta girgiza kai ta ce,
“Na riga na amince da kai. Dalilin kukana ba dalili ne wanda ka sani ba.”
Ya yi shiru daga bisani ya yi ajiyar zuciya ya ce,
“Gaya mini dalilin kukanki a yanzu.”
“Yaya yaushe ka yanke zaka rabu da ni inkoma ƙauyenmu? Ko sai na kammala dukka karatuna?”
Tambayar ta ɗaga masa hankali. Girgiza kansa ya yi ya ce,
“Kina tunanin zan iya rabuwa da ke ne?”
“Kana nufin ka karɓeni a matsayin mata ta har abada?”
Shiru ya biyo bayan zancenta. Tunani ya yi masa shigar bazata.
“Ki bari mu sami lokaci mu yi magana.”
“A’a bani amsar yanzu.”
“Ki saurari zuciyarki, abin da zuciyarki ta gaya maki haka gaskiyar lamarin yake.”
Shiru ta yi tana nazartar zuciyarta. Sai dai har kullum babu abin da zuciyarta ke gaya mata sai Irfaan masoyinta ne na haƙiƙa.
Abin da kowa bai sani ba, tuni Irfaan ya tsunduma tarkon wata yarinya mai suna Amira.
Tun yana kaucewa Amira har ya fara tsintar kansa a cikin soyayyarta. Sai dai shi har yanzu ya kasa tantance menene ma soyayyar, menene kuma shaƙuwa?
Amira Ibira ce, ta gogu da fari amma irin farin nan na bilicin. Shi kuma a duniyarsa ya tsani farar mace. Tasha matuƙar wahala kafin ya yarda ya fara soyayya da ita.
Amma ya kafa mata sharaɗi akan yana da mata, yana kuma sonta yana so ta kiyaye duk wani dalili da zai sa tasan yana da wata budurwa a waje. Hankalin Amira ya dugunzuma ta ce masa tayaya hakan zai yiwu shi da zai aureta?
Ya nuna mata wannan ba komai bane, akwai lokacin da yake jira da zarar lokacin ya yi zai sanarwa iyayensa yana da tabbacin ba za su hana shi ba.
Yakan kwantar mata da hankali a duk lokacin da ta sa masa kuka akan tana so ya turo.
A cikin motar Ihsaan ta kwantar da kanta alamun barci take yi, a zahiri kuma idanunta biyu. Sai a lokacin ya samu ya ɗaga kiran da Amira take yi masa babu ƙaƙƙautawa.
“Haba! Me ya sa kike yi min irin wannan kiran?”
Daga can ɓangaren ta ce,
“Yau na ganka da kai da matar da kake damuna da labarinta. Ashe wata banza ka aura. Mummuna da ita. Har kana zuwa da ita wajen taro. To gara ka zo ka gaya min matsayina a wurinka dan dai nasan ƙarya kake yi kace kana son yarinyar nan da na ganku tare. Wallahi asiri ta yi maka ka aureta.”
Ji yake kamar ba a taɓa gaya masa munanan kalamai irin wannan ba. Ji yake zuciyarsa tana tafarfasa kamar zata fito.
“Ok. Ki jirani yanzu zan zo ingaya maki.”
Gaba ɗaya ya mance Ihsaan tana cikin motar. Gani yake yi ya yi mugun saken da yasa Amira ta raina shi.
Ihsaan ta rintse idanunta tana karanto addu’a. Bata taɓa tunanin Irfaan yana da budurwa ba. Haka kawai ta ji zuciyarta tana zafi. Ba kalaman budurwar ya ɓata mata rai ba. Ba za ta kuma iya cewa ga asalin abin da ya ɓata mata ba. Ita kanta batasan kuka take yi sosai ba.
A ƙofar wani gida ya yi parking ya fito tare da manna waya a kunne.
Ihsaan tana so ta ji me zai ce mata, tana da tabbacin zuwa ya yi ya bata haƙuri. Don haka ta sauke glas ɗin motar tana so ta ji me za su ce.
Cike da yanga ta fito tana yamutsa fuska. Tana ƙarasowa ta dubi fuskarsa sai kuma tsoro ya shigeta.
A fusace yake dubanta,
‘Kin bani mamaki Amira. Tayaya na zama abokin wasanki da har za ki dinga gaya min magana haka? Idan aure zan yi sai in auri wacce za ta dinga gaya min magana tana gayawa uwargidana?”
Bai bari ta bashi amsa ba, ya buɗe mota ya jawo Ihsaan da ƙarfi hakan yasa ta sake ruɗewa.
Ya nuna Ihsaan da hannu ya ce,
“Wannan kike zagi? Ita ce mummuna? Ita kike ganin a banza? Bata isa inshiga taro da ita ba? Kinyi kuskure Amira. Kyawun Ihsaan yana cikin zuciyarta, dalilin haka yasa ta ciri tuta a cikin mata. Ihsaan ba banza ba ce. Za ta iya zama banza a wurinki, amma a wurin Irfaan ba haka abun yake ba. Daga yau, daga yanzu kada ki sake kirana kada ki sake nuna kin sanni. Sakarai ne kaɗai zai bari wata a waje ta zagar masa mata ya kasa nuna mata kuskurenta. Ihsaan zo mu je.”
Ya jawo hannunta ya mayar cikin mota sannan ya zagaya ya fizgi motarsa da gudu ya bar wurin.
Yadda yake gudu a titi yasa Ihsaan riƙe kanta tsoro mai tsanani ya shigeta. Lallai zuciyar Irfaan babu kyau idan ya yi fushi.
Har bayan Isha’i bai nemeta ba, bai bi ta kanta ba, har a lokacin zuciyarsa bata huce ba. Gani yake yi Amira ta raina shi. Ita kuwa Ihsaan sai ta ji zuciyarta ta yi sanyi, ko wasa Irfaan yake yi, ko bai damu da ita da gaske ba, ta yarda ta amince da shi. Ya yi mata abin da har abada ba za ta iya mance shi ba. Ya siya mata girma da mutunci a idanun budurwarsa.
Da daddare ta haɗa baƙin shayi, da kayan ƙamshi ta kwankwasa ƙofar ɗakinsa. Sai da ta jira ya yi mata izini sannan ta shiga.
“Dama tun ɗazu baka ci komai bane shi ne na kawo maka ruwan tea ko zaka sha.”
Ya yi ajiyar zuciya yana kallo ta ajiye a gabansa, ya miƙa mata hannu alamun ta zo kusa da shi. Babu musu ta ƙaraso ta kwantar da kanta a kafaɗarsa shiru. Zuwa can ta yi magana cikin rawar murya,
“Kayi haƙuri.”
Ya ɗan bubbugi kafaɗarta ya ce,
“Ke zan ba haƙuri Kyautatawa. Ba ki yi min komai ba.”
Duk suka yi shiru. Da ƙarfin tsiya Irfaan yake ƙaryata kansa akan abin da zuciyarsa take gaya masa akan Ihsaan. Tayaya hakan zai faru? Tayaya zai so Ihsaan? A ganinsa zuciyarsa ƙarya kawai take gaya masa. Amma kuma yadda ya hasala akan antaɓata abin ya bashi tsoro. Domkn haf cikin zuciyarsa yake jin ɓacin ran abun.
Kiran Amira ya sake shigowa a karo na hamsin da uku, ya ɗauki wayar ya kashe gaba ɗaya, sannan ya ɗauki shayin yana kurɓa ahankali,
“Kai tea ɗin nan ya yi daɗi ga wani irin ƙamshi. Waye ya koya maki?”
Ta ji daɗin yabawan da ya yi ta ce,
“A wani littafi na gani, shi ne da zamu je Makaranta na nunawa Umma sai tasa aka siyo min.”
Ya gyaɗa kai,
“Da kyau ‘yar gatan Umma. Ina so sai kin gama Makaranta sai insiya maki waya ko?”
Ta gyaɗa kai. Wani sassanyar ajiyar zuciya take saki.
‘Yar mutan Borno.
Fatima Ɗan Borno