Rayuwa ta ci gaba da tafiya, miƙaƙƙiya, wanda akan hanyar akwai tarin ƙalubale ta nasara da kuma akasinsa. Irfaan ya ci gaba da samun girma iri-iri hakan yasa ya ƙara zama cikakken mai 'yancin kai. Daga shi har mahaifinsa sun yi ta taka matsayi. Da yawa daga cikin mutane basu cika sanin wai uba ɗa bane, sai idan angaya masu. Har a yanzu da Irfaan yake da babban matsayi bai taɓa ɗaga ƙafafu daga tuƙa mahaifinsa ba, musamman idan za su je Office. Sai dai idan baya garin. Ko baya gari mutum ɗaya ya yarda. . .