Tiryan-tiryan Ihsaan ta bayar da labarin haihuwarta har izuwa yadda Irfaan ya karɓeta ba tare da ya ji ƙyamarta ba. Ya inganta rayuwarta.
(Kasancewar Ihsaan har yanzu bata san dalilin da yasa Irfaan ya karɓeta ba. Batasan Sulaiman ya sadaukar da ƙodarsa ga Abba ba. A ganinta koma mene ne dai tasan Irfaan ya yi abinda da wahala a sami namiji irinsa. Ga kyau, ga ilimi ga kuɗi, kuma ya aureta a yadda take?
Ta dire maganarta cikin jajayen idanunta. Gaba ɗaya ɗakin taron akayi tsit. Abokan aikin Irfaan sun jinjina masa, dan bai taɓa gaya masu yadda akayi ya aureta ba. Haka mutuwar Sulaiman ya ɗaga masu hankali matuƙa, wanda har yasa masu raunin ciki zubda hawaye. Ita kuwa Ihsaan shessheƙa ta fara yi, sai kuma ta yi ƙoƙari ta haɗiye kukanta tana ajiyar zuciya.
A cikin abin maganar suka ji muryar M.C yana cewa,
“To ta yaya akayi kika sami halittarki ta da da kika gaya mana. Baki buɗe mana wannan ba.”
Ta sake duban Irfaan, wannan karon cikin idanunsa ta kalla. Shi kansa ya yi tagumi kawai yana kallonta. Ta sake waiwayawa tana duban jama’a, tabbas kowa ka kalli fuskarsa zaka tabbatar da abin da yake son ji kenan.
Ta dubi Zarah, hakan yasa ta yi saurin ƙarasowa kusa ta goge mata hawayen, sannan ta ɗaga mata gira. Ta sake duban Sadiq shima ya ɗaga mata kansa. Sannan ta ja hanci ta ci gaba da cewa,
“Mahaifiyata tsantsar bafullatana ce, don haka na ɗebo kamanninta sak! Tunda Baba Marka ta tabbatar da kyawuna tun ina ƙarama, sai ta zaɓi ta canza min halittata. Wani abu take shafa mini, wanda ta karɓo daga gun wani bokanta. Wannan abu za a iya kiransa shuni, kuma shi abun nan idan aka shafa maka da wahala agane asalin halittarka duk hasken mutum kuwa.
Tana shafa min abin, tana kuma yi min hayaƙi. Ga kuma rashin wanka. Hatta maganin baƙin jini bani take yi.
Kamar yadda na gaya maku nasha wahala agurinta Sulaiman ne ya taimakeni. A lokacin da na fara girma, sai ya zamana da kaina nake amfani da wannan abun da Baba Marka ta bani. Naso indaina amfani da shi, bansan yadda akayi ba ta zugo mahaifina, ya zo ya ce min magani ne mai kyau saboda aljanu da mayu, don haka indinga amfani da shi, idan ya ƙare inyiwa Baba Marka magana zata dinga kawo mini.
Don haka na ci gaba da laftawa a jikina, ko wanka nayi ina fitowa zan shafe jikina da shi. Ban taɓa shafa mai ba sai wannan abun. Tun wata rana da na shafa mai akai naga ina ta walƙiya, baƙina ya sake fitowa sosai, hakan yasa na tsorata na daina shafa mai. Nasan zaku ce idan nayi wanka abun baya fita ne? Abu ne da aka haɗa shi da sihiri, ko na yi wankan ma baya fita.
“Har na gama rayuwa da Sulaiman ban taɓa sanin asalin kalata ba. Ashe mahaifina ya ba Sulaiman wasiƙa kafin ya rasu, ya gaya masa komai akan rayuwata. Ya tabbatar masa da ni fara ce ba baƙa ba, ga abubuwan da ya ji Baba Marka tana gayawa ƙawarta. Don haka idan na mallaki hankalin kaina ya damƙa min wasu abubuwa inyi wanka da abun har na tsawon kwanaki bakwai. Sulaiman bai taɓa gaya mini ba, bai taɓa bani ba, har sai bayan ya sakeni, na auri Yaya Irfaan. Kwana ɗaya da kawoni gidan sabon mijina, Sulaiman ya kawo mini saƙo yaba maigadi ya bani.
Sai da akayi kwanaki sannan na buɗe. Takardu biyu na gani. Ɗayan yafi yawan rubutu, ɗayan kuma rubutun babu yawa.
“Ban fahimci rubutun ba, kasancewar ban iya karatu ba. Sai wasu busassun ganye da na gani da sauran tarkacena. Ban damu ba na ɓoye akan zan tambaye shi ko menene.
“Ban sami daman tambayarsa ba Allah ya yi masa rasuwa.”
Ihsaan ta duƙar da kai tana jin wani baƙin ciki yana ƙara ratsata. Tana jin kamar yau ne ta yi ido biyu da gawan Sulaiman. A hankali ta ci gaba da cewa,
“Tun bayan rasuwar Sulaiman kullum sai na ɗauki wannan takardun ina kallo. Sai alokacin na ji ciwon rashin iya karatuna. A lokacin na ƙudurci aniyar sai na yi ilimi ko domin Sulaiman ya yi alfahari da ni, da kuma inga na iya karatu don inkaranta wannan takardu. Na yi alƙawarin ba zan taɓa kaiwa wani ya karanta mini ba, da kaina zan karanta.
“Waɗannan takardun sun ci gaba da zama abokan hirana har zuwa lokacin da na buƙaci Zarah ta zama malamata. Ba zan iya cewa Zarah komai ba, sai Allah ya saka mata da alkhairi. Ta dage da iya ƙarfinta tana koya min rubutu da karatu. Ita tasa Umma ta shiga kasuwa ta siyo mini littafai na koyan turanci da na koyan Hausa.
“A gefe guda Yaya Irfaan yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen koya min karatu, amma saboda haushinsa da nake ji, sai nake nuna masa bana fahimtar komai. Babban damuwata kawai ya sallamani inkoma ƙauyenmu, gani ma nake yi shi ya kashe min Sulaiman. Shi ne mutum na farko da ya fara rabani da Sulaiman don haka nake yi masa kallon wani azzalumi. Da na gane karatuna shi ne agabansa, sai ni kuma na ci alwashin indinga bashi haushi har ya ji ya tsaneni ya koreni. Kullum a cikin wautar nan nake tafiya. A lokacin da na tabbatar na iya karatu sai na warware takarda ta farko wanda ita ce bata da yawan rubutu.
“Bayanan mahaifina na gani akan halittata, da kuma yadda zanyi amfani da ganyen magarya wajen warware duk wani sihiri da ke jikina. Ya ƙara da cewa indaina amfani da wannan abun, domin shi yake sanyani baƙi, ni ba baƙa bace fara ce.
Na yi ajiyar zuciya ina ƙara mamaki. Domin da abuna na zo gidan, kasancewar Baba Marka ta aiko min da shi da yawa tun kwanaki biyu kafin tafiyata Kaduna.
Na sake warware ɗayan, kalaman Sulaiman na gani yana cewa inyiwa Irfaan biyayya, inyi karatu shi ne babban burinsa. Idan na wulakanta Irfaan tamkar shi na wulakanta.
“A cikin rubutun ne nake jin wai ashe Irfaan ya taɓa yi masa wani taimako, su Irfaan sun je wani aiki a ƙauyen da ke kusa da Saulawa, aranar shi Sulaiman ɗin abokansa suka rinjaye shi akan suje su yi fashi. Bai taɓa sata ba, sai aranar suka shiga wani gida da daddare a cikin wannan ƙauyen. Ashe sun haɗa masa mugunta ne suka kashe matar gidan suka mannawa Sulaiman. A cikin daren nan, su Irfaan suka kama Sulaiman da abokansa. Irfaan shi ya kama Sulaiman ya riƙe shi yana ganin yadda yake kyarma sosai sai ya jawo shi gefe suka dubi juna sosai, Irfaan ya girgiza shi yana tambayarsa me ya faru? Anan ya gaya masa komai. Tare da roƙon Irfaan ya taimake shi, idan mahaifinsa ya ji zai iya haɗiyar zuciya ya mutu.
“Irfaan ya jinjina lamarin ya tambaye shi daga inda yake ya gaya masa. Don haka ya ciro kuɗi ya bashi ya ce ya bi ta baya ya wuce gida, amma idan ya yi bincike ya gano harda shi akisan nan zai lalubo shi duk inda yake. Ya ɗaga kai alamun ya amince. Har ya yi nisa ya dawo, Irfaan ya daka masa tsawa akan ko so yake sai ankama shi?Sulaiman ya girgiza kai cikin hawaye ya ce sunansa yake son sani. Babu ɓata lokaci ya amsa masa da Irfaan Abbas. Daga nan ya yi ta gudu. Bayan anyi bincike aka gane Sulaiman baida laifin komai sai na binsu zuwa fashi. Haka Irfaan ya kashe Case ɗin Sulaiman ba tare da yasan shi ba, ba tare da yasan shi ɗin ɗan maigadin gidansu bane.
Ina kaiwa ƙarshe na rufe kaina na yi ta kuka. A lokacin sai naji duk wata tsana da nake yiwa Irfaan ta kau. Bayan kwana biyu Irfaan ya kirani ya sake jaddada min akan inyi karatu don mu cika burin Sulaiman. Anan ma na shiga ɗaki na yi kuka. Sai a lokacin nake fahimtar dalilin da yasa Sulaiman yake yawaita gaya mini Yaya Irfaan yana da kirki.
Har na kwashi tarkacen da Baba Marka take bani zan je inzubar. Sai kuma na yi wani tunani akan gara inbar halittata ahaka. Tunda wanda nake so nake da burin inyi masa ado ya rigamu gidan gaskiya.
“Na ci gaba da ganin tsangwama akan wannan halittar, amma baya damuna kasancewar nasan ba haka nake ba. Zarah ta ci gaba da dagewa akaina hatta magana idan za ta yi min da turanci take yi, ga Makarantar da aka samu makaranta ce da ta amsa sunanta, hakan ya ƙaramin ƙwarin guiwa wajen tsayawa inyi karatuna. Zara ke siya min mayuka na gyaran jiki amma ban taɓa amfani da su ba.
“A lokacin da aka kawo mai gyaran jiki bayan na tare a gidan Yaya Irfaan, ban taɓa yarda antaɓa min fatan jiki ba. Roƙonta na dinga yi akan ta ƙyaleni haka halittata take, ni bana son gyaran. Tun bansan kalar jikina ba kenan. Na kuma roƙeta ta ce masu kawai ta yi min ɗin, bayan ta yi min ƙorafi akan kuɗin da za ta samu zan yi mata asara.
“Mutane biyu ne basu taɓa kallona sun kushe halittata ba, sune Yaya Sulaiman da Yaya Irfaan. Duk da ina kallon rashin so a ƙwayar idanun Yaya Irfaan, amma bai taɓa furta min ba, bai taɓa wulakantani ba. A hankali ahankali ƙiyayyata ta dinga sauyawa daga cikin idanunsa. Shaƙuwa ta maye gurbin komai. Haka zalika bai yarda aka wulakantani ba.
Bayan munje Saulawa ne, na zauna da Baba Marka nace mata ina so ta ƙaro min wannan abun nawa ya kusa ƙarewa. Babu kunya ta karɓo min. Ina ta juya abun ina mamaki.
Ana gab da samun matsayin Yaya Irfaan, na sami Zarah na gaya mata komai. Ta yi mamaki ta jinjina ƙarfin halina. Sadiq ya shigo ya ce mana ya ji dukkan abubuwan da muke tattaunawa, ko mu sanya shi a cikin abin da muke shirin yi, ko kuma ya tona mana asiri. Dole muka sa shi a cikin tattaunawarmu. Ya bani shawarar inje ingwada yin amfani da abin da Babana ya bani. Naje na yi ta amfani da abun amma babu canji, don haka ya shirya ya tafi har Saulawa. Bai san gidanmu ba, don haka ya tafi gidansu Sulaiman Innayo tasa aka raka shi. Ya sami Baba Marka ya gaya mata sunsan komai, ta taimaka ta warware sihirin nan. Amma matar nan ta sawa idanunta toka ta ce ita bata yi min sihiri ba. Sadiq ya yi mata jan ido, ya tsoratata akan zai haɗata da ‘yan sanda ta ƙare rayuwarta a kurkuku.
“Sai kuma ta kama rawar jiki ta ce su je ta nuna masa wurin wanda yake bata maganin. Bayan sun je ne, mutunin ya ce da ace na ƙara shekara guda da Sihirin nan ba zai bar jikina ba, kasancewar na jima ina amfani da shi. Ya ciro wani magani ya miƙa masa, ya ce insa a ruwan wanka idan ya narke inwanke har kaina. A take sihirin zai rabu da ni. Sadiq ya karɓa ya fice da wannan maganin.
A ɗakina muka rufe kanmu bayan Yaya Irfaan ya tafi wurin aiki, ya yi min bayanin yadda zanyi amfani da maganin. Haka na yi ta ajiyarsa banyi amfani da shi ba. Munyi hakanne saboda muna tunanin ta hanyar da zamu ba Yaya Irfaan mamaki. Sadiq ke ɗaukata yana kaini wurin wankin haƙori. Haƙorana suka gyaru suka yi tas! Sai nake shafa wannan abun na wurin Baba Marka. Shi da Zarah suke kaini wurin wankin kai, ana gyara min dogon gashina. Wanda a baya saboda tsabar rashin kula ya cukurkuɗe.
Hatta wurin wankin ƙafafu su suke kaini.
Yana samun girman kuma na yi amfani da maganin da Sadiq ya kawo mini. Ni kaina sai naji kamar ancire min ƙaya a jikina, ada ina jin jikina kamar a ɗaɗɗaure amma yanzu sakayau.
Sai dai tunda na yi amfani da maganin na ƙi yarda inyi wankan da zai goge dukkan baƙina. A lokacin Yaya Irfaan yake yi min kallon kamar na shafa wani abu, kasancewar haƙin sai ya zama kamar wani abu na shafa ana hango farina.
Hankalina bai taɓa tashi ba, sai da na ji Umma tana yi masa ƙorafin yadda zan fito a cikin jama’a, ya nuna mata bai damu ba, ya yi kalamai irin na wanda ke sona so na gaske. Ranar da muka je Abuja Sadiq ya je wani babban shago ya ɗauko mai gyaran jiki. Cikakkiyar ‘Yar Maiduguri.
“Gyara ba ƙarya ba ce. Domin kuwa naga ta yadda ‘yan Maiduguri suke ƙwace mazajensu ba tare da boka ko malam ba. Naga abin da ake kira ƙamshi da gyara. A ranar jikina ya dinga walƙiya. Ƙamshi sosai ke fita a jikina.
“Da taimakon Sadiq na ɓoye kaina, har su Umma suka tafi basu sani a idanunsu ba, basu damu ba domin kowa kansa ya yi zafi. Ita ta yi min make up. Zarah kuma ta yi min dressing muka taho wurin taron.”
Tirƙashi! Tana sauke abin maganar wuri ya sake hargitsewa da maganganu. Babu wanda ake yabawa kamar Irfaan, ya zama jan gwarzo ya ciri tuta, ya yi haƙuri yau ga riban haƙurinsa har gida. Duk wanda zai sami Ihsaan a matsayin mata abin ka gode Allah ne. Tana da kyau, irin kyan da ita kanta batasan tana da shi ba. Su Shamsu kuwa sun gaza yin ko da tari. Da sauri Shamsu ya buɗe Gmail ɗinsa ya dubo hoton Irfaan da Ihsaan da ya ɗauka a shekarun baya. Tabbas ita ce, sai dai cike da sauyi kala-kala.
Ihsaan ta ci gaba da cewa,
“Umma, Abba, Yaya Irfaan, Zarah, Sadiq da Iffan. Na gode. Bani da dangi, kun zame mani dangi, bani da kyau, kun dage sai da kuka nemo asalin kyawuna kuka dawo min da abuna. Bani da ilimi, na ɗauka ni ɗin daƙiƙiya ce amma sai kuka dage kuka nuna min ni ɗin ina da baiwa. Yaya Sulaiman yana can yana farin ciki, yana can yana gode maku. Ba zan sami kamarku ba har abada. Ankawo maku suruka babu ko gyale, kuka sa hannu kuka karɓeni hannu bibbiyu.”
Ta fasa kuka mai ban tausayi. Ƙafafunta suka gaza ɗaukarta. A hankali ta sulale ta zauna aƙasa tana kuka, irin kukan da za ka kasa fassara ko na menene.
Kukan farin ciki ne? Ko na baƙin ciki?
Irfaan ya kafeta da idanunsa babu ko ƙyaftawa. Shi kaɗai yasan irin tunanin da yake yi. Bai taɓa sanin Sulaiman ne yaron da ya taimaka a cikin abokansa da duk suka girme masa ba. Da farko ya yi taimakon ne bayan ya yi nazarin yaron a matsayinsa na ɗan sanda ya gane yaron bai saba zuwa irin wurin ba, sannan ya yi yaro da yawa. Zai iya rantsuwa bai gane Sulaiman ba, amma a karo na farko da ya fara ganinsa a ranar ɗaurin aurensa ya yi ta yi masa kallon sani, Allah baisa ya gane shi ba. Da zuciya ɗaya ya taimake shi, ashe hakan zai yi masa rana? Ashe shi ne wanda zai kawo masa Ihsaan, zai taimaki mahaifinsa a daidai lokacin da yake da buƙatan taimako. Lallai ya sake amincewa ka taimaki mutum ba tare da kayi tunanin ta ina zai rama maka ba, Allah ya fi kowa sanin hanyar da wanda kake kallo a ƙasƙantacce zai iya taimakonka.
Ya yi ajiyar zuciya yana sake jin mutuwar Sulaiman yana dawowa sabuwa a cikin zuciyarsa.
Ihsaan ta ji andafata, ta ɗago jajayen idanunta ta kalli Umma da ke kusa da ita. Umma ta ɗagota suka rungume juna. Ita ta mayar da ita wurin zamanta. Tsakaninta da Irfaan babu um bare um-um. Yana kula da ita tana share hawaye bai ce komai ba. Da yaji shessheƙan ya yi yawa ne ya yi magana ba tare da ya dubeta ba,
“Kukan nan ya yi yawa. Za ki yi ciwo.”
Dama rashin kulawarsa ke ƙara tunzurata take kukan. Ahankali take goge hawayen, sai dai kukan yaƙi tsayawa.
Ahaka aka tashi wurin taron kowa jikinsa asanyaye. Sun zo shiga mota Amira ta ƙaraso wurinsu tana kame-kame.
“Irfaan nasan ba zaka aureni ba, na san yanzu kafi ƙarfina. Ada ina gadara da na fi matarka kyau, a yanzu kuma na gane ba kowa ya isa ya gane abin da ke rufe ba.”
Ihsaan ta ja ta tsaya tana dubanta. Kafin ta yi magana ta ji Irfaan ya ce,
“Amira kyau baya gabana. Na haɗu da mata kyawawa banji ina sonsu ba. Ki tafi gida kawai. Ki gyara halayyanki zaki sha mamakin samun miji kamana. Zan aureki.”
Kalamansa sun daki zuciyar Ihsaan. Ko zata mutu ba zata bari Irfaan ya auri Amira ba, haka zalika babu wanda ya isa ya gane me ke cikin zuciyarta. Zata so idan Irfaan zai ƙara aure ya auri mai kyawun zuciya kamar yadda ya faɗa ba wai wacce zata tarwatsa farin cikinsa ba. Daga yau zata zamewa Irfaan Garkuwa, zata hana maƙiyinsa zuwa kusa da shi bare ya cuce shi. Ta sake yin murmushi ta ce,
“Amira ki kwantar da hankalinki. Ke dai ki tsarkake zuciyarki, ki samo soyayyar Irfaan, na tabbata sai kin fi mata dubu alfahari da samunsa.”
Ta dube shi ta ce,
“Kaje ka kaita gida, ni zan shiga motar Sadiq. Amira ki gaida mutan gidan, mun gode da ɗawainiya.”
Mamakin Amira ya kasa ɓoyuwa. Shi kuwa Irfaan zuciyarsa ta ci gaba da rawa. Tun lokacin da Ihsaan ta karɓi haɗa akwatuna da sunan na Amira ya ji ya karaya, ya ji ba zai iya haɗa Ihsaan da kowacce mace ba, gudun kada wata ta shigo ta wargaza mata farin ciki. Yasan sharrin wasu matan, tana iya shigowa da sharri da komai ta raba shi da amanar Sulaiman. Tana iya zama sanadin da zai yiwa Ihsaan tsawa ko wulakanci, wanda yake fatan gara ya ga ranar mutuwarsa da ya ga irin wannan ranar. Yana girmama mace macen ma matarsa, baya haɗa matsayinta da na kowacce mace. Sai dai kuma yadda ta ɓoye masa wacece ita bai yi masa daɗi ba, duk da ‘yan uwansa ne suka taimaka mata. Da farko zafinta yake ji, amma bayananta sun wanketa. Duk da hakan baya son kyakkyawar mace, baya ƙaunar zama inuwa ɗaya da kyawawan mata. Ɗaya daga cikin dalilansa sun bayyana tun ranar da Ihsaan ta fito da asalin kamanninta.
Ada idan ya fita da ita sai dai ayi mata kallon mummuna, ba wai kallon sha’awa ba. Amma aranar a gaban idanunsa M.C yake koɗa kyawunta, mutanan wurin suke ta yaba mata.
Kafin ya farga har Ihsaan ta ɓace daga wurin. Ya gama dube-dubensa bai ganta ba. Sai abokan aikinsa da suka ƙaraso suke ta zuzuta matarsa. Ji yake kamar suna rura wuta a cikin zuciyarsa.
“Ya isa don Allah. Kai Shamsu kai munafuki ne Wallahi. Banyi zaton kana da kunyar da zaka iya sake kallona har ka ce zaka yabi Ihsaan ba. Amma dubeka ko kunya baka da ita, wai ni kake gayawa Ihsaan mai kyau ce. Naga kana sake ɗaukarta hoto, shima hoton zaka je ka nunawa ‘yan Ofis ne? Ko kuwa zaka bi mutanen da ka gaya masu Ihsaan mummuna ce, ka sake wanketa kace yanzu kyakkyawa ce? Don Allah ku je na gode.”
Ya buɗe motar ya shiga. Amira ta buɗe itama ta shiga, ya figi motar da ƙarfi.
Shamsu ya yi ajiyar zuciya yana yaƙe. Shi kaɗai yasan me ke cikin zuciyarsa. Ya ci alwashin ko da asiri sai ya raba Irfaan da Ihsaan ko da kuwa hakan shi ne abu na ƙarshe da zai yi ya bar duniya. Soyayyar Ihsaan ne yake yi masa yawo tun a Abuja da ya ɗora idanunsa akanta. Bai taɓa sanin haka so yake da zafi ba, bai taɓa sanin zafin soyayya ba sai da ya ɗora idanunsa akan Ihsaan.
Da biyu ya zo taron nan dan ya ganta, kuma ya ganta ya sami natsuwa. Ya jima yana sauraren siririyar muryarta, ya yi mata video saboda ya sami abin kallo da ɗebe kewa.
Ya ci alwashin sai ya auri Ihsaan duk rintsi. Ya shirya tunkarar tashin hankalin da hakan zai biyo baya.
Tohhhh… Sai mu ce Allah ya bada sa’a Shamsu.
Taku ce ‘yar mutan Borno