Cikin natsuwa yake murza sitiyarin motar, zuciyarsa cike da tunani kala-kala. Duk yadda yaso ya yakice Ihsaan da ke yi masa gizo abin ya faskara. Duk yadda ya rintse ido ya buɗe, sai ya hangota cikin shigarta mai tsananin fizgar hankalin mutane.
Ita kuwa Amira duk irin abubuwan da Ihsaan ta yi mata na karramawa hakan bai sa ta janye daga irin muguwar tsanar da ta yi mata ba. Ji take yi tamkar zuciyarta zata yi bindiga tsabar tsanar Ihsaan. Ta yi rantsuwa ko da bala'i sai ta shiga cikin gidan Irfaan.
Tsaki ta ja a cikin. . .