Duk suka fice suka bar mata ɗakin. Hakan ya sake bata ƙwarin guiwar rungumar filo tsam a jikinta tana jin ƙamshin turaren Irfaan tamkar ita ce ta fesa turaren.
Acan ɓangaren Amira kuwa, bayan ankaita gida ta kasa zaune ta kasa tsaye. Damuwa ce fal a cikin zuciyarta. Da yake ance so hana ganin laifi, sai ta tsinci kanta da dumu dumu da yiwa Irfaan uzuri. Hasalima ta fi tsanar Ihsaan, a ganinta itace silar komai. Wayarta ta zaro ta kirawo lambar Shamsu, ta zayyane masa komai. Shamsu ya furzar da wani irin huci ya ce ta jira shi gayi. . .