Skip to content
Part 24 of 25 in the Series Duniyata by Fatima Dan Borno

Lamarin Shamsu da Irfaan ya yi zafin, da dole akasan yadda akayi aka ɓoye duk wata hujja da Irfaan yake nema. Dole Irfaan ya sake shi, tunda bai sami ƙwararan hujjojin da yake nema ba. Ko da yake dama ya kama shi ne adalilin rashin kunyar da ya yi masa.

Irfaan ya ci gaba da mayar da hankali akan aikinsa, a gefe guda kuma yana ci gaba da zuwa wajen Amira, akan bikinsu ya kusa da zarar Ihsaan ta kammala karatunta. Hakan yasa Ihsaan ta dinga fargaba da tsoron ranar da zata kammala karatu.

Alƙawari ne mai girma a tsakanin Shamsu da Amira. Idan Amira ta auri Irfaan za ta taimaka masa ya mallaki Ihsaan cikin ruwan sanyi.

Babu abin da ke baiwa Irfaan mamaki sai ganin yadda Shamsu ya kasa yin fushi da shi, kusan kullum zai dawo gidansa ya same shi a falonsa Ihsaan ta kawo masa abubuwan motsa baki. Bai taɓa yin magana ba, bai kuma taɓa nuna wani abu a fuskarsa ba.

Yau ma kamar kullum acan wajen gate ɗin gidansa yasa ɗansanda da ke tuƙashi ya yi parking. Shi kuma ya taka da ƙafafunsa, yana jin tarin gajiyar da ya kwaso yana sake lulluɓe shi. 

Ihsaan ya samu ta durƙusa agaban Shamsu tana zuba masa lemo. Duk da baƙar abaya tasa wanda ya rufe mata har wuya, hakan bai hana Shamsu ƙoƙarin leƙata ba. Tana gama zubawa ta bar masa a ƙasan tana ƙoƙarin tashi,

“Ahh ki ƙarasa ladanki mana Hajiya Ihsaan. Miƙo min kofin.”

Ko alama bata kawo komai ba, ta ɗauki kofin tana ƙoƙarin miƙa masa. Da sauri Irfaan ya ƙarasa shigowa bayan ya gama kallon komai da ke wakana a tsakanin Ihsaan da Shamsu, ya haɗa da gyaran murya don ya kula sam basu ji takun tafiyarsa ba.

Ihsaan ta waiwayo da kofin ahannunta tana duban mijinta. Nan da nan farin ciki ya bayyana a fuskarta. Tun jiya take kewarsa sosai, bai kwana agidan ba, sannan ta kasa samun lambarsa.

Da murnarta ta ƙaraso gareshi. Yasa hannu ya karɓe kofin da ke hannunta gudun kada ta zubar masa a jiki, sannan yasa ɗayan hannun ya rungumeta. Luf ta kwanta ajikinsa tana shinshinan ƙamshinsa kamar yadda shima yake jin ƙamshinta yana saukar masa da kasala.

“Na yi kewarka. Jiya kuma da baka nan sai da na yi kuka.”

Bakinsa ya kai bisa kanta ya sumbaceta sannan ya ɗan shafi kafaɗarta.

“Miss You more Sweetheart.”

Idanun Shamsu kamar za su faɗo tsabar kallonsu da yake yi. Sai kuma ya yi gyaran murya,

“Wai baka ganni bane kake shirin cinye masu yarinya?”

Irfaan bai ce komai ba, sai da ya kai kofin ya shanye lemun da ke ciki tas, sannan ya dire kofin ya jawota suka zauna kujera ɗaya ya ce,

“Kai da muke tare a ofis tayaya akayi har ka rigani zuwa gidana babu labari?”

Shamsu ya daburce sai kuma ya ce,

“Wallahi na fito ne zanje wani gida shi ne nace bari infara biyowa indubata.”

Ihsaan ta ɗan dube su, sai kuma ta kauda kanta zuwa kallon mijinta,

“Ba za ka sake fita ba ko?”

Wani abu ne a zuciyar Irfaan ya ɗan yi mata murmushi ya ce,

“Idan kika ce kada infita ai sai infasa. Amma kada ki sake yin kukan nan bana so kin ji? Maza ta shi kije ki haɗa min ruwan wanka gani nan zuwa.”

Da farin ciki ta tashi ta wuce abinta. Shamsu ya dube shi cikin suɓutan baki ya ce,

“Ya zaka korar min ita muna hira?”

Irfaan ya watsa masa wani irin kallo, wanda yasa ya yi saurin dawowa hankalinsa.

“Shamsu me kake zuwa yi agidana?”

Ya watsa masa tambayar cike da zargi. Shamsu ya zaro idanu sannan ya fara magana cikin rauni,

“Allah yasa ba zargina kake yi ba. Ka sanni kasan halina kasan abin da zan aikata da wanda bazan aikata ba. Kawai ina jin takaicin yadda na yi wa Ihsaan ne a lokacin baya, shiyasa nake gyara kuskurena. Ban taɓa zaton ko da ace kowa zai yi min gurguwan fahimta kaima kayi min hakan ba. Ko bayan babu rayuwarka matarka ta haramta agareni.”

Irfaan ya miƙe tsaye ya ƙaraso har inda Shamsu yake, ya dafa kafaɗarsa,

“Ganganci ne yin wasa akusa da dajin da zaki da iyalansa suke rayuwa, bare kuma har tsautsayi yasa ka afka ciki sa sunan laluben gafiya. Ka bi a sannu Shamsu.”

Daga haka ya shige ciki abinsa.

Gaba ɗaya Shamsu ya kasa ko da motsawa. Jikinsa babu ta inda baya kyarma. Sai dai ko alama baya jin zai iya janyewa daga maitarsa.

A zaune ya sameta ta yi tagumi. Har ya ƙaraso kusa da ita bata sani ba, don haka yasa hannu ya janye tagumin.

“Me ke damunki?”

Ta yi murmushi ta girgiza kai alamun babu komai. A gurguje ya faɗa banɗakin ya watsa ruwa. Har ta fiddo masa wasu kayan, ya kammala shiryawa. Yadda ta yi kamar zata yi kuka yasa ya dakata da sanya maɓallin rigarsa yana dubanta,

“Kukan zaki yi?”

Ta ɗaga kai alamun eh. Ya yi hanyar waje yana cewa,

“Zo mu je ki rakani Ofis sai mu dawo tare.”

Wani tsalle ta yi ta haye bayansa. Bai ce mata komai ba, sai murmushi kawai da yake yi. Tsabar rashin yarda yasa ta ƙi sakinsa har sai da ya rakata har ɗaki ta sauya kaya, sannan suka fito tare.

Shamsu yana nan tsaye kusa da motar yana hira da ɗan sandan. Mamaki yasa Irfaan ware idanu,

“Lafiya kuwa?”

Ya tambaye shi. Shamsu ya ɗan kauda kai ya ce,

“Ba da motata na fito ba, shi ne nake so mu koma tare.”

Wani abu ya tsayawa Irfaan a zuciya, ji ya yi kamar ya yi masa wulakanci, sai kuma ya fasa. Shamsu ya buɗe gaba ya shiga, ɗansandan ya buɗewa Irfaan baya suka shiga da Ihsaan.

Shiru suka yi babu mai cewa uffan. Ihsaan ta yi luf a jikinsa kamar mage. Ya raɗa mata a kunne,

“Zan ɗan biya gidansu Amira idan babu matsala.”

Ta gyaɗa kai kawai alamun ta amince.

“Kai Sani juya da motar nan zuwa gidansu Amira.”

Hatta Shamsu sai da ya ɗan razana. Tayaya zai je gidansu budurwa da matarsa? Hakan ya ba Shamsu ƙwarin guiwar samun daman haɗa husuma,

“Rankashidaɗe sai yanzu na tuna jiya Amira ta kirani wai inzo inkarɓa maka agogonka da ka mance da shi cikin dare da ka zo gidansu. Na yi ta dariya nace mata lallai soyayya ta yi daɗi kenan.”

Duk jarumta irin ta Irfaan sai da yaji gabansa ya faɗi. Tabbas ya mance agogonsa agidan, abin da ma zai kai shi kenan, sai dai kuma alwala ya yi ya bar agogon a wurin. Bai ji daɗin yadda Shamsun ya yi irin furucin nan ba. Duk da baya ɓoyewa Ihsaan komai, amma ya mance bai sanar da ita maganar agogon ba.

Irfaan ya ɗago fuskar Ihsaan ko zai hango damuwa a cikinsu, sai ya hango akasin hakan. Don haka ya manna mata kiss a laɓɓanta sannan ya ce,

“Nima abin da zai kaini kenan inkarɓi agogona da na mance. Da ka karɓo min da ban wahala zuwa ba.”

Mamakin Irfaan ya ci gaba da kama shi, bai taɓa ganin namiji mai ƙarfin halinsa ba.

Yadda jikin Ihsaan da na Irfaan suke manne da juna, ya sake haddasa masu shiga wani yanayi. Gaba ɗaya sun yi tsit a motar don ma Allah yasa ankunna radio a ciki, da babu abin da zai hana na gaba bai jiyo yadda zuciyoyinsu ke bugawa da sauri da sauri ba. A kunne ya yi mata magana cikin wata siga mai wahalar fasaltawa,

“Kina jin abin da nake ji? Ki yi min magana Ihsaan.”

Ta kasa yin magana sai shige masa da take sake yi. Idanun Irfaan ya kaɗa ya yi jazir. Ji yake anya zai iya ci gaba da haƙuri har zuwa lokacin da ya alƙarwantawa kansa?

Har aka iso gidansu Amira basu sani ba. Ji ya yi anbuɗe motar. Ya juyo suka yi ido huɗu da Amira. Bai saki Ihsaan ɗin ba, bai kuma janye jikinsa daga nata ba. Amira kamar zata yi kuka, musamman yadda ta dubi idanunsa sun kaɗa sunyi jazir. Shi kuwa Shamsu ji yake kamar zai mutu tsabar kishi. Bai sami daman waiwayowa ya kallesu ba, sai da suka iso gidansu Amira.

“Ga agogonka.”

Ta furta cike da kishi. Sai a lokacin ya musƙuta, amma hannunsa yana cikin na Ihsaan ɗin.

“Babu gaisuwa babu komai? Kinsan yadda na damu inzo inganki ne shi ne zaki yi min irin wannan tarban?”

Anan kuma sai ta ɗan saki ranta, ta yi farin ciki da ya furta waɗannan kalaman agaban matarsa.

Ihsaan ta cira kai da ƙyar ta lalufo fara’a ta manna abisa fuskarta sannan ta ce,

“Amira ya kwana biyu?”

Amiran ta dubeta sosai sannan ta amsa ciki ciki,

“Lafiya lau.”

Daga nan duk suka yi shiru.

“Ya naga kinsa min agogo ahannu ko yayi maki kyau ne?”

Cike da rausaya ta ce,

“Wallahi baka ji yadda ake ta maganar agogon ba.”

Shima ya sakar mata murmushinsa sannan ya ce,

“To ki riƙe na baki aro. Amma da sharaɗin zaki yi min takatsantsan da shi, har zuwa lokacin da zan buƙata. Domin ina son agogon sosai.”

Amira ta yi wani irin tsalle ta ce,

“Wallahi na amince. Kafin ka karɓa ai na gama cin ado da shi. Na gode da wannan aro, zan kuma riƙe shi da mahimmanci kamar yadda nake riƙe da mai shi.”

Ya sake yin murmushi ya ce,

“Bari mu je ofis sai mun yi magana.”

Ihsaan tana jin su bata ce uffan ba. Haka suka iso har ofis ɗin, bata nuna komai ba. Suna shiga cikin ƙaton ofis ɗinsa ya mayar da ƙofa ya datse, ya jawota sosai jikinsa yana jin komai nata yana rikita shi. Dama neman wata dama yake yi da zai fidda abin da yake ɗauke da shi ko zai sami sassaucin halin da ya shiga.

Sannu ahankali yake aika mata da saƙonni masu wahalar fassara. Zuciyoyinsu da suka haɗu wuri guda suka ci gaba da bugawa. Wani baƙon al’amari ya ci gaba da wanzuwa a cikin zuciyoyinsu. Gaba ɗaya sun gama fita a cikin hayyacinsu.

Fatima Ɗan Borno

<< Duniyata 23             Duniyata 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×