Gaba ɗaya sun gama fita hayyacinsu, suka ji bugun ƙofa da ƙarfi. Dole Irfaan ya dakata daga abin da yake shirin yi, ya manneta da ƙirjinsa da yake jin kamar ya tsaga ƙirjin ya cusata a ciki.
Jin bugun ƙofar ya yi yawa yasa Ihsaan ta ɗan ruɗe. Irfaan ya raɗa mata,
"Ki kwantar da hankalinki kinji? Babu wanda zai shigo ki natsu."
Ahankali natsuwar ta dinga zuwar mata. Shi ya taimaka mata ta mayar da komai nata, sannan ya kaita kujera ya zaunar da ita. Shima ya kintsa kansa sannan ya tafi ya buɗe ƙofar.
Cike. . .