Rarrafowa ta yi bisa guiwarsa ta kwantar da kai a jikinsa tana magana cikin shessheka,
“Don Allah Yaya kada ka sake gayawa Innayo magana kaji? Babu kyau Allah zai konaka, ni kuma bana so azaban Allah ya tabbata agareka.”
Sosai yake jin kukanta har tsakiyar kai.
“Saboda wannan kike kuka?”
Ta gyada kai alamun eh. Ya dago fuskarta ya dauke hawayen yana murmushi,
“Babu komai na daina daga yau indai hakan zai faranta maki.”
Tana murmushi ta ce, “Kuma ban taba ganinka kana hira da Innayo ba, kaje ka bata hakuri ta yafe maka shikenan ka zama na gari ko. . .