Skip to content
Part 7 of 25 in the Series Duniyata by Fatima Dan Borno

Yasha zuwa yana gayawa Abba magana Allah bai taba sa ya ci karo da Irfaan ba. Hatta wasu ‘yan sandan sukan yi gulma su ce Allah yana taimakon Hon yana zuwa baya samun Irfaan. Ashe yau dubunsa zata cika.

Abba yana zaune yana duban yadda Irfaan ya zama Kaman zai yi hauka.

“Irfaan ka koma Office dinka.”

Babu musu ya sara masa sannan ya juya kawai. Hankalinsa bai kwanta ba sai da ya sake bin Hon har cikin Cell din ya dube shi sosai, sannan ya nuna masa hannu,

“Kada ka sake kuskuren zagin wanda baka da tabbacin sanin ko shi waye. Idan yau ka bar kujerarka sai ka zama abin tausayi, shi kuwa wanda kake yi masa ihu kana cewa zaka cire masa kaki, idan yau ya bar aikin ‘yan sanda zai iya ciyar da dukka ‘yan unguwan da kake wakilta. Shashasha sakarai! Kotu zan turaku daga kai har ‘yan jagaliyan naka.”

Hon Saminu dai ya kasa ko motsi mai karfi. Tunda yake ba a taba wulakanta shi  irin yau ba. Ji yake dama wannan ranar bata zo ba, ranar da dan sanda zai yi maganin rashin mutuncinsa. Mutanan da ya raina, mutanan da yake ganin basu da wani amfani da ya wuce zama su yi gadinsa.

Bayan lokacin tafiyarsu gida ta yi, suka kama hanya. A hanyar ne Abba ya dubi Irfaan ya ce,

“Ka fahimci girman mahaifi ko? Ba a fushi da mahaifi domin ko kayi kai ne a kasa. Ban yi tunanin zan baka zabina ka wufintar da shi ba. Na ji ciwon yadda nake yabonka yau ni kake watsawa kasa a idanu. Ka juya kan motar nan mu je inrakaka hira ko?”

Ya yi maganar cikin zolaya. Irfaan ya ji wani iri dole ya sassauta murya ya ce,

“Abba naji ciwon abin da mutumin nan ya yi maka. Ji na yi na tsani aikin dan sanda. Shi kenan kuma duk wanda ya ga dama sai ya dinga wulakantamu yana ci mana fuska? Gaskiya tunda baka rasa komai ba, ka ajiye aikinka don Allah Abba. Ina jin ciwon ko manyanmu ne suka yi maka magana harshe a sama sai naji kamar zan mutu. Ko kuma kawai gara a sama min transfer inbar wurin.”

Abba ya yi dariya sosai ya ce, “Irfaan yanzu zaka iya amincewa ka tafi wani wuri kayi aiki a karkashin wani ba ni mahaifinka ba? To idan ka tafi waye zaka barwa kula da ni? Don Allah kada kayi tunanin guje mani ka bari har inkammala aikin nan, tunda na kusa.”

Jikinsa ya yi sanyi da kalaman Abbansa ya ce, “Babu inda zanje Abba. Maganar Safiyya kuma na amince a daura mana auren.”

Abba ya ji dadi matuka, ya yi ta sa masa albarka. Wannan karon ma da suka je babu wata hirar kirki da suka yi ya yi mata sallama.

Umma tana ganin sun dawo aiki, Abba yana rike da kafadan Irfaan suna hirarsu gwanin sha’awa ta saki murmushi.

“Yau mazaje suna cikin annashuwa kenan. To ku karaso nima na yi maku abinci na musamman.”

Duk suka dubi juna, sai kuma suka yi murmushi.

“Sannu da gida Ummana.”

Ta karaso ta rungume shi tsam a jikinta,

“Allah ya yi maka albarka Irfaan.”

Ya amsa da, “Ameen Ummana tare da ‘yan kannena.”

A gurguje ya fada bandaki ya watsa ruwa, sannan ya fito da kananun kaya. Tuwan shinkafa ta mulka masu miyar danyen kubewa yaji man shanu. Sun kuwa ji dadin abincin nan, ga lemu mai sanyi wanda akayi hadin kwakwa da danyen citta.

*****

Ihsan tana zaune a kofar gidan, tana jiran Sulaiman ya dawo daga inda ya ce mata ta jira shi. Allah-Allah take yi ya dawo saboda tsoron kada Innayo ta fito ta ganta.

“Uban me kike yi a kofar gida?”

Innayo ta tambayeta cikin masifa. Hakan yasa Ihsan ta zabura ta mike tana zazzare idanu. Innayo ta nuna mata hanyar shiga gida ranta a matukar bace. Da gudu ta shige tana waige-waige. Uban wanke-wanken da ta ci karo da shi ne yasa gabanta fadiwa, domin ba karamin gajiya ta yi ba.

Yau a Makaranta noma aka sanyata saboda kawai bata yi aikin gida ba. Innayo ta shigo tana magana, “Au sai nace maki kiyi wanke-wanken? “

Da sauri ta karasa ta  dibo ruwa sannan ta fara wanke-wanken idanunta cike da hawaye. Laifin Sulaiman take gani da ace bai tafi ba, da Innayo bata leko ta sanyata aikin da yafi karfinta ba. Tunowa da rayuwarta ta baya yasa ta yi saurin daina ganin laifinsa. Da ace Sulaiman bai shigo rayuwarta ba, da tuni anmance da ita a duniya. Idan bata gode masa ba, ba zata zage shi ba. Haka ta wanke kayan nan. Ta dauki wani kofin gilas da Innayo ta siye shi wajen larai dillaliya. Tana matukar son kofin nan kamar me. Ihsan ta fasa shi tus! Ji ta yi Innayo tasa Salati da karfi tana fadin, “Shikenan yarinyar nan ta kasheni ta kashe min rayuwa ta fasa min kofin Malam.”

Ihsaan ta yi tsuru-tsuru. Ji ta yi duka ko ta ina a jikinta. Ihu kawai take yi tana ba Innayo hakuri. Haka tafasawa Marka yanzu kuma ta fasa na Innayo. Gudun da zata yi sai ji ta yi ta fada jikin mutum, ta cikuikuye shi tana fadin,

“Kayi min rai zata kasheni.”

Ita kanta Innayo a yadda ta ganshi ta fahimci kiris yake jira ya aikata komai. Don haka ta kyaleta tana huci. Sulaiman ya durkusa ya kama kafadunta yasa hannu yana goge mata hawaye. Bai ce komai ba, ya jawo hannunta suka shiga dakinsu. Kukan ma ya gagara fitowa sai ajiyar zuciya kawai take yi.

“Kiyi hakuri Ihsaan, na gagara rikeki, na kasa samar maki da kwanciyar hankali. Amma ina ji a jikina watarana zaki zama tauraruwa, masu zaginki suna dukanki za su yi danasani. Innayo ta yi min alkawarin ta daina gallaza maki, amma yau kawai bana nan ta dakeki ta sa ki aiki mai wahala, ina kuma ga na bar gidan duniya?”

Ihsaan ta girgiza kai da karfi, “Kada kayi maganar mutuwa don Allah. Duk ranar da ka mutu nima binka zanyi.”

Ya danyi murmushi ya ce, “Zan sama maki farin ciki insha Allahu.” Ya dinga shafar guiguyayyen kanta har barci ya soma dauketa. Sulaiman bai taba neman wani abu agun Ihsaan ba, yana son sai ta fi haka girma a lokacin ta mallaki hankalin kanta, ta kuma san menene aure, sannan zai waiwayi hakkinsa.

Washegari sun je yiwa Innayo Sallama kamar yadda suka saba, sai ta ajiye su a gaba tasa kuka. Hankalin Sulaiman ya kai matuka a tashi don haka bai ce komai ba, ya dai zuba mata idanu.

“Yanzu Sulaiman har yanzu Ihsaan bata yi batan wata ba? Idan yarinyar nan bata haihuwa ne ka sanar dani.”

Gaba daya suka dubi juna sai kuma Ihsaan ta shafa cikinta. Sai yanzu ta tuna da duk wacce ta yi aure a kauyensu ta haihuwa, wasu kuma suna da katon ciki a gabansu. Ihsaan ta yi nare-nare da idanu kamar zata yi kuka ta ce,

“Yaya Sulaiman me ya sa ni baka bani cikin ba? Me ya sa ban haihu ba, bayan ga su Zulai duk sun haihu abin su. Don Allah ka bani cikin nima.”

Ta fasa kuka da iya karfinta. Innayo sai ta hadiye kukanta ta zurawa Ihsaan ido. Shi kansa Sulaiman abin dariya ya bashi, yana da tabbacin Innayo ta sami daidai da ita. Ya dubi Ihsaan yadda ta takarkare tana kuka tsakaninta da Allah, ya ce “Ihsaan tashi muje kada   ki makara su dakeki. Ciki kuma da haihuwa bani ke bayarwa ba Allah ke badawa, ki yi ta addu’a acikin sallolinki Allah ya baki zuri’a na gari, zaki ga Allah ya amsa maki.”

Sai a sannan ta sassauta kukan tana share hawayenta tare da gyada kai alamun ta gamsu. Ta mitsittsike idanunta ta ce, “To sai mun dawo Innayo.”  Ko tari Innayo ta kasa yi saboda tsabar mamaki da takaici. Suna tafe tana tsalle-tsallenta. Duk abin da ta gani a hanya sai ta kwace hannunta daga cikin na Sulaiman ta je ta dauka sannan ta dawo ta rike hannunsa.

Shakuwa sosai ta shiga tsakanin Sulaiman da Ihsaan, ta yadda daya baya iya zaman sukuni idan babu daya a gefensa. Wataran shi da ita suke buga kwallo a tsakiyan filin tsakar gidansu. Bata da kawa sai shi, haka zalika shima ko menene ke damunsa da ita yake shawara.

Rannan ta zo ta same shi ta ce, “Ina so inje gida ingaida Babana.”

Ta yi maganar cikin son yin kuka. Ya rike kafadunta yana murmushi, “Bana hanaki kuka ba? Kina so inshiga damuwa?” Ta yi saurin girgiza kanta. Ya ce, “Yauwa Ihsaan. Dalilin da yasa bana yawan kaiki gidanku saboda Marka. Na tsani matar nan bana son idanuna suna haduwa da ita. Ina gudun inkaiki ina fita ta kama dukanki.”

Ihsaan ta danyi shiru, daga bisani ta ce, “To muje tare sai ka tsaya ka jirani mu koma tare, tunda idan ka tafi ne zata dakeni, idan kana nan ba zata iya dukana ba.”

Sulaiman ya gamsu da shawarar Ihsan don haka suka shirya suka tafi. Abin mamaki suna isowa suka sami jama’a a kofar gidan. Hakan yasa Ihsaan zazzare idanu. Da gudu ta kwace hannunta ta shiga gidan jikinta babu inda baya kyarma. Gawan mahaifinta ta ci karo da shi a shimfide a cikin makara, da alama yanzu za a tafi ayi masa Sallah. Ihsaan ta durkushe a gaban Makaran ta fasa kara mai gigitarwa.

“Baba don Allah ka tashi, ka tashi Baba don Allah. Wayyo gatana ya tafi, gatana ya tafi ya barni.”

Sulaiman ya kama hannayenta idanunsa cike da hawaye, tabbas Ihsaan bata yi karya ba gatanta ya tafi. Shikenan bata da kowa a duniya daga Allah sai shi.

“Tashi Ihsaan, tashi kinji? Gatanki bai tafi ba Allah ne gatanki ni ne gatanki. Kada ki sake cewa gatanki ya tafi.”

Ihsaan ta kwanta a kirjinsa tana kuka sosai fadi take, “A’a Yaya Sulaiman Babana ne ya tafi ya barni, don Allah ka ce masa ya tashi. Babaaaa..”

Ta ja sunan mahaifinta, tana jin daci a zuciyarta. Tana tunawa da yadda yake tashi cikin dare ya bata abin da zata ci.. Tana tunawa da yasha barin cikinsa da yunwa don kawai ya sama mata abinci. Yau ya tafi ya barta.

Yadda Ihsaan take kuka, hatta Marka sai da ta tausaya mata. Duk wurin babu wanda bai yiwa Ihsaan kuka ba, tabbas Ihsaan ce abar tausayi. Sulaiman ya rungumeta sai a lokacin hawayen fuskansa suka zubo. Shi kadai yasan me yake tunani, shi kadai yasan me ke cikin zuciyarsa. Da gaske yake son Ihsaan da gaske yake tausaya mata. Ya rasa ta yadda zai yi ya canza rayuwar Ihsaan daga bakin ciki zuwa farin ciki. A hankali ya rabata da jikinsa ya ce,

“Share hawayenki kiyi wa Baba addu’a kinji? Tashi yanzu kiyi masa.”

Bata daina kukan ba, amma kuma ta dage ta karanto addu’a daga wanda ta koya agun malamansu zuwa gurin Sulaiman. Ta yi masa addu’a sosai daga karshe ta kwantar da kanta a jikin makaran tana rizgan kuka. Da kyar aka rabata da Makaran aka dauke mahaifinta. Idanunta ta daga sama tana kallon yadda aka dauke shi, ta sake fasa kuka mai karfi tana rokonsu da su dawo mata da mahaifinta. Da sauri Sulaiman ya je ya yi alwala.

Har an idar da Sallar gawan ana shirin tafiya da shi, aka hango Ihsaan aguje kamar mahaukaciya, tana rokon a dawo mata da Babanta. Hatta limamin sai da hawaye suka sauka a idanunsa. Da kyar aka kamata aka mayar cikin gida.

Bayan anrufe Baba Bala, kowa ya fara watsewa daga makabartan. Sulaiman ya tsugunna shiru a gaban sabon kabarin zuciyarsa tana sake karyewa. Lallai ya sake amincewa mutum ba abakin komai yake ba, duk wanda ya dauki duniyar da girma ya shiga uku ya lalace. Gaba daya zuciyarsa ta yi rauni ya fara magana ahankali,

“Baba ka tafi ka barni da rikon marainiya. Baba baka gaya min ni kadai zan kula da Ihsaan ba. Me ya sa ka tafi ka barni da tarin kalubale? Me ya sa baka zauna ka ga ci gaban ‘yarka ba? Innalillahi wa inna ilaihirraji un..”  Hawaye kawai ke bin fuskarsa kamar ruwa. Ji ya yi andafa kafadarsa. Ya juyo a hankali. Irfaan ya gani tsaye a makabartan. Mamakin lokacin da yazo ya kama shi. Ji ya yi gaba daya ya karaya, sai kawai ya kwantar da kansa a kafadansa yasa kuka mara sauti Kaman wani dan karamin yaro. Irfaan yana jin kowane digon hawayen Sulaiman yana diga har cikin zuciyarsa. Ya tsinci kansa cikin tarin damuwa akan damuwar Sulaiman. Shima bai so zuwa garin ba, Abba ya matsa masa akan lallai su zo shi da Baba Sani su duba masa gidan gona. Da isowarsu suka sami labarin wannan mutuwa.

Da su akayi Sallah da su aka kawo shi Makabartan.

Baba Sani ya zuba masu idanu yana mamakin yadda Irfaan yake yawan nuna damuwarsa akan Sulaiman dansa. Irfaan ya bubbugi bayansa ya ce, “Be a Man mana. Idan kana irin hakan ita kuma matarka ya zata yi? Ka zama mai karfafa mata zuciya ka ji? Kayi hakuri. Dukkanmu nan ita muke jira.”

Sulaiman ya hadiye kukansa ya ce, “Na yi tunanin zan iya rike amanar Ihsaan abin ya gagara. Kullum mahaifiyata gallaza mata take yi. Ihsaan har abincin awaki ta ci. Yanzu ya tabbata Ihsaan bata da kowa daga ni sai Allah.” Irfaan ya dan murmusa kadan,

“Na ji dadi da ka fahimci kaima gatanta ne. Ka sake dagewa zaka iya Sulaimanu kana da karfin hali, kana da halayyar manya bana jinka.”

Sai a lokacin Sulaiman ya ga Babansa. Duk suka dugunzuma suka koma gidan gaisuwan. Irfaan ya cire kudi ya bada akayi siyayyan ruwan gora, buhunan shinkafa da mangyada. Wannan siyayya da ya yi ya jawo cecekuce a kauyen domin abin da ba a taba ganin anyi bane. Karshe ya dire dubu ashirin ya ce su siyi kayan miya. Sulaiman da mahaifinsa sun ji dadin irin wannan kara da akayi masu. Irfaan ya ce zai koma shi kadai tunda ya sanar da mahaifinsa komai, idan yaso idan akayi uku sai Baba Sanin ya dawo. Gaba daya suka rakoshi wajen motarsa. Irfaan yana rike da hannun Sulaiman.

“Na gode Yaya Irfaan. Allah ya saka maka da alkhairi. Zuciyarka tana da kyau, ba kowa zai gane hakan ba sai wanda ya zauna da kai.”

Irfaan ya danyi murmushi ya ce, “Kaine mutum na farko da kayi min kyakkyawan fahimta. Na ji dadi kuma na gode.”

Juyawa suka yi su dukka sakamakon kuka da suka ji a bayansu. Ihsaan ce aka kamo hannunta aka kawowa Sulaiman saboda irin kukan da take yi. Irfaan ya fasa shiga motar ya juyo sosai yana dubanta. A karo na farko ya yi mata duban rahama ya ce,

“Ihsaan!”

Ya kira sunan cikin wani siga. Ta dago idanunta suka kalli juna a karo na farko. Yana so ya yi nazarin irin wannan baqin nata. Domin shi bai taba ganin mace mai baqi irin nata ba. Hakoran nan jazir. Ita kanta wari take yi, duk da ta canza sosai ba kamar farkon ganinta ba. Ta kasa amsawa sai kallonsa da take yi, idanunta cike da hawaye.

“Ihsaan kiyi hakuri kin ji? Dani da ke da Sulaiman dukkanmu irin wannan ranar muke jira. Ki yi masa addu’a kin ji?”

Ta gyada kai tana share kwallan da ya biyo fuskarta.

“Ya karatun kina kokari ko?”

Ta girgiza kai alamun a’a. Duk suka danyi murmushi sannan ya juya ya shiga motarsa. Yana tafe a hanya tunani ne cike da kwakwalwarsa. Gidansu Safiyya yake son zuwa kamar yadda Abba ya bashi umarni. Yana zuwa ya sameta da wani suna hira. Suka dubi juna shi da mutumin, sannan Irfaan ya mika masa hannu. A wulakance ya dubi Irfaan sannan ya ce,

“Kana ji ko? Ka gaggauta fita harkan Safiyya domin ni ne mijinta. Kai gani kake yi nan da Sati daya zaka aureta ko? Kayi kuskure, zan iya sanadin barinka duniyar gaba daya idan baka yi wasa ba.”

Irfaan ya yi murmushin jin dadi ya fizgo Sadam da karfi sai gashi a gabansa, ya dauke shi cak ya yi bayan motarsa ya bude boot din motar ya cusa shi ya rufe. Safiyya ta fasa ihu ta yi cikin gida aguje. Kafin mutanan gidan su fito Irfaan ya figi motarsa ya bar gidan. Kai tsaye Station dinsu ya wuce da shi ya sa yara suka bude boot suka fito masa da shi. A lokacin ya hadu da Abba yana fitowa. Ya dube shi ya dubi wanda aka rike Kaman barawo ya ce,

“Irfaan yaushe ka dawo? Wannan kuma me ya yi?”

Irfaan ya gayawa Abban komai ya hada da dauke shi da mari ta keya yana cewa,

“Irinsu ne matsalar kasar nan, shi ya sa na kawo shi nan in koya masa hankali.”

Abba ya dawo da baya yana dubansa ransa a bace. Bai taba tunanin yarinyar tana hulda da irin wadannan samarin ba, da har zai yi ikirarin kashe masa yaro.

“Kuje ku kulle shi bari Alhaji Surajon ya zo, domin wannan magana ce babba.”

Abba yaba yaran umarni. Su kuma suka  yi gaba da shi  suna cewa,

“Kai dan rashin hankali ogan namu zaka ga bayansa ko? Yau ka tabo abin da yafi karfinka idan Oga Irfaan ne sai ya yi maganinka.”

Sadam dai sai zazzare idanu yake yi. Bai  taba zaton dan sanda bane shiyasa ya yi rashin kunyarsa. Abba da Irfaan suka ci gaba da tafiya yana masa bayani akan Chairman din da suka kama kwanaki shida da suka wuce, yana gaya masa yadda ya yi ta bashi hakuri don haka ya saki Chairman din su kuma yaran ya tura su kotu.

Irfaan ya jijjiga kai bai so Abba ya hakura ba, yaso ne ya yi rubutun da sai Chairman din ya raina kansa. Daga nan suka kama hanyar gida. Irfaan yana bashi labarin halin da ya sami Sulaiman da Matarsa. Abba ya tausaya kwarai ya kuma jinjinawa Sulaiman irin yadda yana yaro karami amma yasan darajan mace. Duk hirar da suke yi hankalin Abba yana kan Sadam da ya yi ikirarin kashe masa yaro. Da shigarsu gida suka sami Alhaji Surajo yana tsaye wurin motarsa. Abba ya karaso tare da mika masa hannu. Sai yaki karba yana masifa yana sababi.

“Akan me Irfaan zai kama min yaron dan uwa? Me yake tunanin duniya zata kirani?”

Irfaan ya dube shi sosai. Sanin halin Irfaan yasa Abba ya dube shi ya ce,

“Irfaan wuce ciki gani nan zuwa.”

Irfaan ya ce, “Sorry Sir! Hakkina ne kula da lafiyarka.”

Abba ya ce, “Irfaan nace ka wuce ciki.” Ransa bai so ba ya wuce kawai.  Ya shiga falon babu kowa, gaba daya yaran gidan Abba ya watsa su wasu duniya karatu. Gara ma Zara’u tana nan Nigeria amma sauran biyun duk basu kasan. Umma ta fito tana duban Irfaan, “Ina Abban naku yake?” Sai da ya gaidata sannan ya bata amsa da yana waje. Bai wani jima ba sai gashi ya shigo fuskarsa a daure. Da kyar ya daure suka ci abinci sannan ya kora masu bayanin anfasa auren Irfaan da ‘yar gidan Alhaji Surajo.

Wani farin ciki ya rufe Irfaan, dama da biyu ya kama Sadam kasancewar yasan da wahala Abba ya bari ayi wannan bikin bayan anyi barazanan taba gudan jininsa. Abba ya kara da cewa,

“Irfaan kana daya daga cikin wadanda za su tafi London karo karatu, ina son kwazonka ya wuce yadda nake hange. Wata biyar zaka yi acan sai ka dawo, a lokacin kuma insha Allahu kana dawowa zamu yi maka aure, ko ka zabi mace ko mu zaba maka.”

Cike da farin ciki ya ce, “Duk yadda kuka yi daidai ne Abba. Ina godiya.”

Muje zuwa.

‘Yar mutan Bornonku ce

<< Duniyata 6Duniyata 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×