Skip to content

Duniyata | Babi Na Biyar

0
(0)

<< Previous

Rarrafowa ta yi bisa guiwarsa ta kwantar da kai a jikinsa tana magana cikin shessheka,

“Don Allah Yaya kada ka sake gayawa Innayo magana kaji? Babu kyau Allah zai konaka, ni kuma bana so azaban Allah ya tabbata agareka.”

Sosai yake jin kukanta har tsakiyar kai.

“Saboda wannan kike kuka?”

Ta gyada kai alamun eh. Ya dago fuskarta ya dauke hawayen yana murmushi,

“Babu komai na daina daga yau indai hakan zai faranta maki.”

Tana murmushi ta ce, “Kuma ban taba ganinka kana hira da Innayo ba, kaje ka bata hakuri ta yafe maka shikenan ka zama na gari ko?”

Nan ma murmushin ya yi yaja habarta yana cewa,

“Duk yadda kika ce haka za ayi sarauniya. Anjima zan fara koya maki karatu kinji? Na cireki a wancan Makarantar idan Allah ya hore min zan harhada kudi inkaiki makarantar kudi naji ance sun fi koyarwa.”

Tana dariya ta daga kai.

“Ihsan baki ci abinci ba, bari infita insama maki wani abu.”

Kafin ta yi magana har ya fice. Ta window ta zura kanta tana kallonsa ya nufi kitchen. Innayo tana zaune tana iza wuta ya durkusa har kasa ya bata hakuri. A karo na farko da hirar arziki ta hadasu. Ta tabbatar masa ta yafe masa. Anan suka kama hira irin ta da da uwa. Da lallami ya samu ta bashi ragowan tuwon ya dawo daki suka kama ci da Ihsan. Yadda take ci jikinta na rawa yasa zuciyar Sulaiman yin rauni. Zata kai loman tuwo ya riko hannayenta. Sai asannan ta dago tana dubansa. Murmushi ya sakar mata sannan ya ce, “Ki ci ahankali kinji?” Gyada kanta kawai ta yi ta cigaba da ci hannu baka hannu kwarya. Ya sake rike hannun yana tsoron kada ta kware. Ya ce, “Bude bakin.” Babu musu ta bude ya dibo tuwon ya sa mata a baki. Hannunsa ta rike da dayan hannun tana sidewa. Ya zura mata ido kawai har ta gama sannan ya sake dibowa ya bata a baki. Zuciyar Ihsaan cike da farin ciki Yayanta yana ciyar da ita.

*****

Kwanaki biyu tsakani, Ihsan da Sulaiman suna hanyar dawowa gida daga gurin aikinsa sai suka ga wata bakar mota mai kyau sai sheki take yi.  Ihsan ta kwace hannunta ta karasa da gudu tana shafar motar.

A lokacin Irfaan ya zuge glas din motar bakinsa fal masifa domin shi bai ma gane wacece ba, yana sha yaran garinne aka sami mara kunyar da tazo daidai saitinsa take shafa masa mota.

Ihsan ta zaro idanu. Yana sanye da kakin ‘yan sanda mai kalan rodi-rodi. Yau gaba daya sai kwarjininsa ta bayyana, fuskar nan babu rahama. Ihsan ta daddage ta fasa ihu, ta juya da gudu ta koma jikin Sulaiman jikinta babu inda bai karkarwa. Abba ya fito daga motar yana cewa, “Irfaan ka saki fuskar nan taka tun kafin ka dinga ba jama’a tsoro.”

Irfaan ya yamutsa fuska ya ce, “Ohh wai yanzu Abba har wannan dodon itama tsoron zan bata? Ji min yarinyar nan.”

Yadda ya yi maganar ya ba Abba dariya, don haka ya dara sosai sannan ya nufi inda Baba Sani yake tsaye yana jiran sakkowan Abba.

Gaba daya suka zube suna kwasar gaisuwa daga Baba Sanin har Sulaiman. Ihsan ta karaso kusa da Abba tana dariya. Abba ya shafi kanta ya ce,

“Iyye amarsu ke ce haka kika kara girma? Lallai Dana ya iya kiwo masha Allah. Ya karatun?”

Ta saki dariya sosai ta ce, “Ai bana zuwa Makaranta sai Yaya Sulaiman ya sami kudi zai sa ni a babban Makaranta wacce ake biyan kudi.”

Sulaiman da Baba Sani duk suka yi yake. Abba ya dubi Irfaan da fitowarsa kenan suna gaisawa da Baba Sani, ya ce.

“Irfaan maza ka dauki Sulaiman da Ihsan ku je Makarantar kudi mai kyau dake nan kusa don Allah kayi mata komai da ake bukata. Ai bai kamata ta zauna babu Makaranta ba. Ku je ku dawo zamu zagaya gidan gona, idan kun dawo sai muje wurin malamin.”

Irfaan ya ji kamar ya fasa ihu. Bai ce komai ba ya juya ya shiga motar ya hade girar sama da ta kasa. Shi kansa Sulaiman yana kula da shi, don haka shima ya kama kansa. Tafiya kawai suke yi babu wanda yake cewa dan uwansa uffan. Daga baya Irfaan yaga rashin dacewar hakan, kada su yi zaton don suna da arziki ne yake yi masu wulakanci. Da kyar ya sassauta fuskarsa ya ce,

“Sulaiman kaima ya kamata ka koma Makaranta.”

Sulaiman ya dube shi sosai sannan ya ce, “Yaya bana sha’awar komawa wata makaranta. Amma ina so rayuwar Ihsan ta inganta. Ina so watarana masu zaginta su ji kunya.”

Irfaan ya dan sha jinin jikinsa, kada dai yaron yana gasa masa magana ne. Don haka ya danyi murmushi ya ce,

“Ihsan ta Sulaiman. Shakuwarku har yau bata daina bani mamaki ba.”

Sulaiman ya yi dariya kawai, adaidai lokacin da yake nuna masa hanyar da zai shiga. Bayan sun karbi fom sun cike komai Irfaan ya biya kudaden. Har za su fita yaji Sulaiman yana cewa,

“Kada ku taba min ita, kada ku dakteta. Duk ranar da kuka ji zaku iya dukanta gara ku koreta a Makarantar gaba daya. Don zan dauki mummunan mataki akan duk wanda ya taba ta.”

Wani malami daga cikin Ofis din ya yamutsa fuska yana duban Ihsan cike da kyankyami,

“Wai duk akan wannan mummunar halittar kake yi mana irin wannan gargadin?”

Sulaiman ya juyo a fusace. Irfaan ya rike hannunsa. Sai a lokacin malamin ya kula da Irfaan da ke sanye cikin kakin ‘yan sanda. Sannan ya fahimci tare suke don haka ya bi Sulaiman kawai da kallo yana mamakin irin wannan zuciyar.

“Kaci sa’a. Amma idan ka raina halittar nan idan ta fara zuwa ka daketa. Anan zaka gane akwai mai kaunar halittar nan a yadda take fiye da komai da kowa.”

Shi dai Irfaan gaba daya ya rasa me ke yi masa dadi. Kallon Ihsan kadai yana hargitsa shi, bare har ya tsaya kusa da ita. Gani  yake yi ko asiri Ihsan take yi babu yadda za ayi ta iya samun irin soyayyar da Sulaiman yake yi mata.

Suna hanyar dawowa gidansu Sulaiman Irfaan ya dube shi sosai ya ce,

“Amma kuwa Sulaiman babu wani abu da yake damunka?”

Ya gyada kai yana murmushi, “Bani da wata matsala da ta wuce na ganin Ihsan ta sami rayuwa mai kyau.”

Haushi da takaicin Sulaiman suka hadu suka rufe Irfaan dole yaja bakinsa ya yi shiru.

Suna dawowa suka dugunzuma gaba daya zuwa wurin malamin da zai duba Irfaan domin bashi maganin aljana. A kasa suka tako kasancewar gidan babu nisa a tsakaninsu da Baba Sani. Shi dai Irfaan yana biye da su ne kawai, amma Allah kadai yasan yadda zuciyarsa ke suya. Bayan angaggaisa ne ya dubi Irfaan sosai sai kuma ya juyo ya kafe Ihsan da idanu. Itama shi take kallo kamar tsohuwar mayya. Kowa yana mamakin yadda akayi har Ihsan ta biyosu, bayan Baba Sani da kansa ya ce ta wuce ciki za su je su dawo.

“Rankashidade nakai kwanaki bakwai kenan ina Istahara akan lamarin Irfaan. Tabbas kwanan nan zai yi aure, sai dai kuma lamarin auren zai zo da abin mamaki da al’ajabi. Macen da zata kasance matarsa fara ce tas! Mai tsananin kyau. Sai dai kuma akwai wani babban al’amari da yasa…”

Irfaan ya tashi zuciyarsa tana tafarfasa. Muddin mahaifinsa zai ci gaba da biyewa irin wadannan mutanan, babu ko shakka watarana sai sun dulmiyar da shi, sun sanya shi aikata shirka.

“Dakata malam! Istahara kayi ko? Mu ma mun iya. Don Allah Abba ka tashi mu tafi tun kafin mutanan nan su dulmiyar da kai. Bana jin abin da zai ci gaba da fitowa daga bakin malamin nan alkhairi ne. Mu daina yi wa Allah shisshigi akan lamarunsa mu barshi ya nuna mana komai idan lokacin yin hakan ya yi. Tayaya ni da bani da ninyar aure, bana jin wata alama ta yin Aure zai ce kuma wai lokacin aurena ya kusa. Harma yana iya gane kyan matar. Ce maka na yi ina neman kyakkyawar mace? Ko ka ga na yi maka kama da wanda kyau zai rude shi?”

Abba ya dube shi ransa a bace ya ce,

“Tabbas maganarka gaskiya ce Irfaan, sai dai malam ya yi hasashe mai kyau, domin kuwa ko kana so ko baka so Wallahi sai kayi auren nan. Yanzu ne na fahimci lamarinka iya shege ne, ka barmu muna ta nema maka magani muna tunanin ko kayi gamo ne. Shashashan yaro wanda baisan ciwon kansa ba. Mu koma gidan aure zan yi maka insha Allahu kuwa, sai ka hadiyi zuciya ka mutu.”

Malamin nan ya tashi yana ba Abba baki. Idanunsa suka sake sarkewa da na Ihsan. Yana son furta wani abu yana tsoro. Don haka ya dan karkace ya ce,

“Malam Sani wannan kuma ‘yar waye?”

Sai da duk suka dubeta sannan ya bashi amsa da;

“Ihsan kenan diyar Malam Bala. Ita ce Sulaiman ke aure.”

Mamaki ya sake cika zuciyar Malamin nan. Yana mamakin wai Ihsan matar aure ce. Kamar zai sake yin magana sai kuma suka hada idanu da irfaan da sauri ya kauda kansa.

Ahanya babu wanda yake iya cewa uffan a tsakanin Abba da Irfaan. Gaba daya kan Abba ya kulle tunani kawai yake yi ta yadda zai daurawa Irfaan aure da ko wacece. Tunaninsa ya tsaya ne akan Safiyya diyar wani amininsa. A lokacin baya aminin nasa da kansa ya kawo masa tayi akan hadin zumuci a tsakanin Safiyya da Irfaan, amma sai Abba ya nuna bai amince ba, kasancewar baya son yiwa ‘ya’yansa dole.

Basu bata lokaci ba, suka tsince su a garin Kaduna, kasancewar babu cinkoso ahanyar. Abba ya yi magana cikin daure fuska, “Ka kaini gidan Alhaji Surajo.” Irfaan ya dan saci kallon mahaifinsa, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, ya kauda kan motarsa zuwa hanyar gidan Alhaji Surajo kamar yadda Abba ya bukata.

A waje ya tsaya ba tare da ya shiga ba, shi gaba daya ma kakin da ke jikinsa yake damunsa ya kosa ya je ya cire kayan. Yana nan tsaye Kaman gunki, har mahaifinsa ya fito. Da ladabi ya gaida Alhaji Surajo da ke ta faman wage baki yana dariya. Ganin babu fuska yasa shima ya dan rage fara’ar. A daidai lokacinne Safiyya ta fito sanye da hijabinta fuskarta dauke da murmushi. Kallo daya Irfaan ya yi mata ya dauke kansa. Sai da ta gaida shi sau biyu sannan ya dan waiwayo ya amsa. Hakan yasa Alhaji Surajo kama hannun amininsa suka dan yi nesa da su.

Shiru-shiru tana zaton zai yi mata magana har ta gaji ta dago tana jifansa da murmushi. “Barka da warhaka.” Ta karasa da dan rufe fuskarta alamun kunya.

Banza ya yi mata kamar baisan tana yi ba. Har ta gaji ta ce, “Ko dai kurma ne?” A hasale ya dago kamar zai tanka sai kuma yaja bakinsa ya yi shiru. A haka su Abba suka dawo suka riske su. Sai dai basu fahimci komai ba, har suka yi sallama Irfaan yaja mota suka fice.

Ahanya Abba yake sanar da shi, sun gama tattaunawa da Alhaji Surajo har ma sun yanke nan da Sati biyu za a daura auren Irfaan da Safiyya. Hankalin Irfaan idan ya yi dubu ya tashi. Amma a fuskarsa ko alamun damuwa babu, hasalima sosai ya mayar da hankalinsa a wurin tuki. Abba ya dubeshi sosai ya ce, “Kana jin abin da nake cewa kuwa?”

“Eh naji Abba. Sai nake ganin kamar sati biyu ya yi kurkusa, tunda biki yana bukatan shiri ne.”

Abba ya ce, “Kada ka damu dukkanmu a shirye muke.”

Duk suka yi shiru har zuwa isowarsu gida. A falo suka yiwa kawunan su mazauni kowa da irin tunanin da yake yi. Umma ta kafe su da idanunta zuciyarta tana sanar da ita yau mazajen akwai wani abu da yake damunsu.

“Lafiyarku kalau kuwa?”

Ta bukata cike da son jin abin da ke faruwa.

Abba da ke zare safar kafarsa ya ce, “Aure naje na nemawa danki. Sai ku fara shiri nan da Sati biyu Insha Allahu Irfaan zai zama cikakken mutum.”

Umma ta koma ta zauna tana yi masu kallon rashin fahimta.

“Acan gidan maganin ya samo mata? Ko kuwa har anyi dace da maganin da ya raba shi da aljanun ne? Wallahi Yallabai ban fahimci komai daga cikin maganganunka ba.”

Abba ya dago daga abin da yake yi ya ce, “Kawo min ruwa.” Sai a lokacin ta tuna da zancen ruwa. Gaba daya ta kawo masu ruwan, sai dai Irfaan ko kallon kofin ruwan bai yi ba.  Abba ya sha sosai, sannan ya yi Hamdala. Sannu ahankali ya kora mata dukkan bayanin abubuwan da suka faru.

Umma ta yi shiru daga bisani ta ce, “To yallabai shi Irfaan din da Safiyyan har sun fahimci juna ne? Kada muje garin fushi mu zo muna danasani.”

Abba ya yi  murmushi ya ce, “Ki bari kawai zanyi maganin yaron nan ne. Sati biyun nan ba za a daga  ba, ku je kawai ku fara shirye-shirye.”

Daga haka Abba ya mike ya shige ciki. Shi kuwa Irfaan tunda ya balle maballin rigarsa ya kasa motsawa daga inda yake zaune. Tunani ne birjik a cikin zuciyarsa wanda ya kasa tantance irin kalan da zaai yi. Ya dade zaune anan da kyar ya ja kafafunsa ya wuce daki.

Washegari ya sanyaye yake shirinsa cikin damuwa har ya kammala ya fito falon ya gaida kowa sannan ya jawo kujera ya kama cin abincinsa. Yana sane da yadda yake cusa abincin zai iya sawa ya yi amai amma hakan baisa ya fasa cusawa ba. Duk hanyar da zai sa Abba kada yaga gazawarsa ita yake kokarin yi. Yau bai yi wa Umma magana mai dadi kamar yadda ya saba idan za su fita ba. Ya riga Abba isowa bakin motar, ya tsaya kyam! Abba yana fitowa ya sara masa, sannan ya bude masa mota ya shiga, shi kuma ya zagaya ya hau mazaunin direba. Har suka isa Office babu mai cewa uffan. Kai tsaye Irfaan ya wuce Office dinsa. Sai bayan da ya kammala hada komai na wani Case sannan ya mike ya nufi Office din Abba domin ya kai masa.

A lokacin ya ji hayaniya hakan yasa ya dan dakata yana sauraren me ke faruwa.

“Kayi kadan kace zaka matsawa yaran siyasana. Akan me? Ka kama min yara nazo ina binka ta lalama amma ka nuna ban isa ba. Sai inyi Sanadin Kakin nan naka da kake takama da shi, kake ciwa mutane mutunci.”

Zuciyar Irfaan ta dinga wani irin tasowa tana tafarfasa. Kai tsaye ya bude kofar ya shigo. Ya dubi Mutunin da ya ci fararen manyan kaya. Sai yanzu ya ganr ashe Chairman ne mai ci a yanzu.  Bai ce komai ba ya fara yiwa Abba bayanin File din da ya kawo masa.

Irfaan ya sake tsinkayo muryarsa yana cewa, “Wallahi sai na dauki mummunan mataki akanka muddin baka sakar min yara ba. Wannan banzan kakin da kake sanye da shi, ni Saminu sai na…”

Irfaan ya juyo da jajayen idanunsa ya rike damko shi sosai. Yana shirin yin magana kawai ya hau dukansa babu ji babu gani. Abba yana zaune yana kallon yadda jikin Irfaan yake kyarma. Ya yi murmushi ya ce, “Irfaan rabu da shi hakannan.”

Irfaan da yake ji kamar ya kashe Hon Saminu ya sake shake shi sosai ya ce,

“Wannan da kake gani ya fi karfinka ya fi karfin barazanarka. Kai din banza! Ka yi kadan ka cire kakin da akayi shekara da shekaru ana gina shi. Dan sanda ba banza bane ya wuce wulakancin ‘yan iska kamarku. Ko kunya baka da ita ka zo belin ‘yan iskan unguwa, kana ikirarin zaka cire kaki mai daraja saboda su. Yau zanyi maganinka. Ni sai na yi sanadin da za a cireka daga kujerarka.”

Da karfi ya kira wasu ‘yan sanda suka shigo da sauri.  Irfaaan ya hankada Hon Saminu sai gashi a kasa a gaban ‘yan sandan. Ya ce, “Sajen a tafi da mutumin nan a rufe min shi. Ko waye yazo kada a fito da shi.”

Suka amsa masa tare da tasa keyar Hon Saminu. Wanda gaba daya idanunsa sun raina fata. Ya muzanta kwarai.

‘Yar mutan Bornonku ce.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×