Skip to content

Duniyata | Babi Na Daya

3.8
(13)

Sanye yake cikin wani yadi mai kalar sararin samaniya. Duk shirin da yake yi, cikin natsuwa yake yinsa ba tare da ya takurawa kansa ba, kamar yadda yaga ƙannansa suna yi. A ƙalla ya fesa turaruka sun kai kala biyar. A yadda yake fesa turaren zai gamsar da kai ya san abin da yake yi, domin kuwa kowanne kaɗan-kaɗan yake fesawa.

A tsarinsa baya son sanya hula, bare kuma babbar riga. Namiji ne tsayayye mai cike da kwarjini. Gashin kansa ya sha gyara. Kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci cikakken buzu ne irin buzayen nan na Nijar. Duk da baida hasken fata kasancewar ya ɗibo baƙi daga mahaifinsa, sai kuma hasken mahaifiyarsa hakan yasa kalarsa ta zama irin kalar nan da ke wahalar samu a wannan yanki. Zamu iya cewa hasken ya rinjayi duhun, amma kuma babu yadda za ayi a kira shi fari tas!

Ƙafafunsa masu kyau ya zura cikin takalmansa yana ɗaura tsadaddan agogo a hannu. A lokaci guda yana sake saita kansa a madubi domin tabbatar da gyaran gashin nasa ya yi yadda yake buƙatan gani.

Sallama ya ji daga ƙofar ɗakinsa, hakan yasa ya ɗago, a lokaci guda ya wadata fuskarsa da wani irin murmushi wanda ya ƙara masa kyau.

Abbansa ne tsaye a bakin ƙofar, shi bai shigo ba, bai kuma koma ba, yasha ado da manyan kaya masu kyau.

“Wa alaikassalam.”

Ya amsa yana sake murmushi. Ya sake zura idanunsa a cikin na Alhaji Abbas. Sanin kansa ne idan bai bashi izinin shigowa ba, ba zai taɓa shiga ba. Wannan tarbiyya ce da ya ɗora ‘ya’yansa akai.

“Abba ka shigo.”

Cikin tafiyar ƙasaita ya shiga kai tsaye ya wuce inda ɗan ke ajiye hulunansa ya zaɓi ɗaya da zai dace da kayansa, ya ƙaraso har gabansa ya ɗora masa akai. Ya koma ya ɗauko takalmin da ya yi daidai da hular ya ajiye a gabansa. Babu musu ya zare na ƙafafunsa ya sanya wanda Abbansa ya ajiye masa. Duk da har yanzu murmushin yake yi, amma acan ƙasan zuciyarsa yana jin damuwa dan yasan har babban riga sai Abban ya sanya shi sawa.

Bai kai ƙarshe da tunanin ba, ya hango Abba ya nufi gadonsa ya ɗauko babban rigar ya miƙa masa. Babu musu ya karɓa ya sa. A lokaci guda suka sakarwa juna murmushi. Abba ya kamo hannunsa suka fara tattakawa,

“Yanzu ka fito sak! Bahaushe. Ka daina yarda kana gutsure al’adarka kana sirkata da wata al’ada wacce bansan inda ka sameta ba.”

Shi dai sai gyaɗa kai yake yi alamun ya gamsu, kasancewarsa wanda maganar ma wahala take yi masa.

Da isarsu falo Ƙannansa suka zuba masa idanu. Duk yadda suke shakkansa sai da Sadiq ya ce,

“Yaya ka yi kyau sosai, kafi jiya da kullum kyau.”

Ya dubi mai maganar, ya sakar masa tattausan   murmushi wanda iyakarsa fuska. Da gaske yake jin tsanar tafiyar da za su yi. Yana mamakin dan kawai Maigadinsu yana aurar da ɗa, sai su kwashi jiki wai sun tafi biki. Abin tashin hankakin ma acan wani ƙauye mai cike da rashin tsaro ga rashin kyawun hanya.

Abu ɗaya ya sani, baya taɓa musu da iyayensa, na biyu kuma yana ganin girma da ƙimar Maigadin nan idan ba haka ba, babu wanda ya isa ya sa shi tafiya ƙauye wai ɗaurin aure.

Ya ƙaraso kusa da Ummansa yana dubanta yadda ta saki baki tana kallonsa.

“Umma na sauya maki ko?”

Kallon ta maida kan mijinta ba tare da ta iya bashi amsar tambayarsa ba.

“Nasan wannan aikinka ne Rankashidade.”

Ta yi wa mijinta magana cikin raha.

Abba ya yi dariya ya dubesu ɗaya bayan ɗaya ya ce,

“Ku tashi mu tafi kada mu makara.”

Duk suka yi hanyar waje. Addu’a kowannansu ya yi kafin suka fice zuwa wurin motarsu. A cikin Prado suka yi wa kansu mazauni. IRFAAN shi ke zaune a mazaunin direba, mahaifinsa yana gefensa. A ya yin da Sadiq da Iffaan sai auta Zahra’u da kuma Umma suke baya.

Dukkansu sun ci ado na alfarma sai zuba ƙamshi suke yi.

Tafiya suka yi miƙaƙƙiya daga Kaduna zuwa cikin ƙauyen Saulawa. Tafiya ce mai cike da nishaɗi. Hirarsu suke sha a tsakanin su da ‘ya’yansu. Sai dai shi Irfaan ko tari bai yi ba. Shi gaba ɗaya ma ya nausa wani dogon tunani ne yana jinjina yadda Abba yake da ƙarfin zumunci.

Kasancewar Irfaan ya taɓa zuwa gidan Baba Sani Maigadi, sai hanyar bata ɓace masa ba har zuwa ƙofar gidan. Ba wasu jama’a bane a ƙofar gidan hakan ya nuna masu har yanzu akwai sauran lokacin ɗaurin auren.

Umma da Zahra suka shiga ciki, shi kuma da ƙannansa maza biyu da Abba suka buɗe ƙatuwar dardumansu suka shimfiɗa a inuwa. Yara da matasa suka yi masu caaa suna kallon motar. Daga bisani kuma suka koma kallon su Irfaan, hakan yasa ransa ya kuma ɓaci kawai ya zaro wayarsa yana latsawa.

Can ya hango Abban ya nufi wurin Baba Sani suna tahowa tare hannunsu maƙale da na juna kamar abokai. Har kullum yana sha’awan sauƙin kai irin na mahaifinsa.

Su uku suka ƙaraso da ƙyar Abba ya yi da su, sannan suka hau kan darduman suka zauna. Irfaan ya ɗago tare da sakin fuska sosai ya gaida su. Baba Sani kaman zai kwanta masa a lokacin da yake gaida shi.

Duk da yasan iyayen gidan nasa wajen karamci, amma bai taɓa tunanin za su kwaso jiki su dukka su zo masa bikin ɗansa ba.

Anan hira ya ɓarke a tsakanin su, ɗayan ya sake kallon Irfaan ya ce,

“Yallaɓai kace yaron nan naka bai yi aure ba?”

Abba ya gyaɗa kai,

“Wallahi bai yi aure ba. Aljana ce ta aure shi, muna dai kan neman magani.”

Irfaan ya kirne fuska sosai ta yadda har mutumin ya ji shakkar sake dubansa.

“Kafin ku tafi zan kaiku wajen wani malami mai bayar da taimako. Insha Allah za a dace. Allah ya bashi lafiya.”

A can cikin zuciyarsa ya saki tsaki yana jin kamar ya shaƙe mutumin nan. Shi har mamaki yake yi yadda suka dage akan aljana ce ta aure shi.

Wani matashi ne ya ƙaraso mai kyau da shi, a shekaru ba zai wuce ashirin da uku ba, yana sanye da fararen kaya da hularsa. Kai tsaye ya ƙaraso wurin Abba ya durƙusa ya gaida shi. Sannan ya dawo da dubansa ga Irfaan, Wanda ya rasa dalilin da yaro ƙarami ya yi masa kwarjini, ya kuma rasa dalilin da gabansa yake faɗiwa.

Baba Sani ya yi maganar da yasa Irfaan sake ɗagowa yana duban yaron.

“Yallaɓai wannan shi ne ɗana Sulaiman. Shi ne kuma angon da za ayi aurensa yau insha Allahu.”

Shi kansa Abba sai da ya sake duban Sulaiman cike da mamaki.

“Malam Sani wannan yaron ai ba zai wuce sa’an Sadiq ba. Tayaya zai iya riƙe aure?”

Gaba ɗaya suka yi dariya. Malam Sani ya ce,

“Na yi juyin duniyar nan ya yi haƙuri ya ci gaba da karatunsa amma yaƙi. Ya ce a kashe shi a rufe wannan yarinyar yake so. Na duba wasu dalilai masu girma don haka na amince masa kawai.”

Sulaiman ya sake ɗagowa suka haɗa idanu da Irfaan. Gaba ɗaya sai suka tsinci kansu da sakarwa junansu murmushi. Irfaan ya yafito shi da hannu ya ƙaraso wurinsa. Ya riƙe hannunsa suka bar wurin ya bar Abba da tambayar shekarunsa.

“Malam Sulaiman yanzu kana ganin zaka iya riƙe mace?”

Sulaiman ya ɗanyi shiru daga bisani ya ya murmushinsa ya ce,

“Yaya zan iya insha Allahu.”

Bayan wani gida suka nemi wuri suka zauna. Haka kawai ya ji Allah ya ɗora masa son Sulaiman. Yana ɗan yi masa tambayoyi yana bashi amsa. Juyawa ya yi da nufin sake antayo masa wata tambayar sai ya nemeshi sama ko ƙasa ya rasa. Dan nesa kaɗan ya hango shi tsaye da wata ‘yar yarinya tasha lulluɓi. Ganin suna nufo shi yasa ya zura masu idanu babu ko ƙyaftawa. A lokacin ya sami ƙarewa yarinyar kallo. Baƙa ce irin baƙaƙen nan da har ƙyalli take yi. Kamar ma ta shafawa fuskarta wani abu mai ƙara sa baƙi. Ji ya yi zuciyarsa tana tashi saboda kallon yarinyar da yake yi. Babu shiri ya kauda idanunsa ya mayar kan Sulaiman wanda ya hasketa. So yake ya ƙaryata zuciyarsa da ke sanar da shi ita ce amaryar.

“Yaya Irfaan, wannan ita ce Ihsan amaryar da za a ɗaura mana aure yanzu insha Allahu. Ihsan ga Yayana da ke Kaduna ku gaisa.”

Sulaiman ya katse masa tunani da bayaninsa. Ga mamakinsa sai ya ga ta durƙusa cikin zazzaƙar murya, wanda babu tantama muryarta ce kaɗai abun saurare a jikinta. Zai so ya ƙare mata kallo yaga ko akwai wata baiwa banda wannan. Sai dai ko alama ba zai iya ba. Ƙafafunta ya zurawa idanu kasancewar kansa a ƙasa yake. Ƙafar nan duk ta tsattsage. Irin bagoburin ƙafafun nan gareta. Gashi anshafe da wani abu wai baƙin lalle.

Bai dubeta ba ya ce,

“Lafiya lau Ihsan. Allah ya sanya alkhairi.”

Gaba ɗaya suka yi carab! Suka amsa da Amin. Hakan yasa ya ɗago ya ƙurawa Sulaiman idanu cike da mamaki da kuma wani nazari. Kansa ya maida ƙasa yana jujjuya irin wannan lamari.

Ta juya tana ce masa zata koma gun ƙawayenta. Anan ya sake bin bayanta da kallo. Siririya ce ta lamba ɗaya. Ji yake ma idan akayi iska mai ƙarfi zai iya tafiya da ita.

Irfaan ya dubi Sulaiman dan yaga a halin da yake a ciki, sai ya tsince shi yana binta da kallo, irin kallo ne mai cike da so. Mamaki ya ƙara bayyana kansa a fuskar Irfaan. Ya gyara zamansa akan ɗan dandamalin da suke zaune ya ce,

“Sulaiman kana son Ihsan da yawa.”

Wuri ya nema ya zauna yana gyara zaman babban rigarsa ya ce,

“Yaya Irfaan a yanzu bani da wani buri da ya wuce in ji da kunnuwana anɗaura aurena da Ihsan. Bansan menene so ba sai akanta. Wallahi ba zan iya rayuwa idan babu ita a kusa da ni ba. Ina sonta Yaya. Akan Ihsan zan iya yin komai. Tunda na daina shaye-shaye saboda ita babu abinda ba zan iya ba. Idan naga hawayenta a ranar bana iya barci Yaya.”

Shi Irfaan mamaki ya hanashi rufe baki. Duk da bai san menene so ba, wannan ya firgita shi. Ya dubi ƙwayar idanun yaron, ya tabbatar da gaske yake yi. Kafin ya lalubo amsar bashi ya ce,

“Zan iya kashe rai akan Ihsan. Don Allah Yaya Idan kayi Sallah ko kaje ƙasa mai tsarki kayi min addu’a Allah ya bani ikon riƙe Ihsan da gaskiya.”

Irfaan ya haɗiye yamu da ƙyar, sannan ya yi ajiyar zuciya.

“Allah ya baku zaman lafiya. Zan kuma tayaka da addu’a. Tashi mu je lokaci ya yi.”

Irfaan yana riƙe da hannun Sulaiman har suka isa wurin ɗaurin aure. Abba ne waliyyin ango, wanda bai sani ba sai da yazo aka bashi. Ana ɗaura auren Irfaan ya lura da kamar kuka Sulaiman yake yi. Don haka ya jawo shi gefe yana son yi masa kalaman lallashi. Sai dai me zai gani? Ihsan ce ta ratso ta kawo kanta wurin da suke tsaye a gefe. Ta ƙanƙame shi ta fasa kuka. Sulaiman yasa hannu ya rungumeta ba tare da ya damu da jama’a ba.

“Kiyi haƙuri ki daina kuka. Kinsan illan da kukanki yake yi min kinji Kyautatawa ta?”

Ya ɗagota yana goge mata hawayen. A lokacin idanun Irfaan suka sake afkawa kan fuskar Ihsan. Gabansa ya faɗi ya yi saurin kauda idanunsa. ‘Anya yarinyar nan ba aljana ba ce?’

Irfaan ya tambayi kansa. Domin kuwa bai taɓa ganin halitta mai munin Ihsan ba. Da sauri ya sake kaiwa ƙafafunta duba domin tabbatar da babu kwafato. Ƙafafun da ya gani ɗazu su ya sake gani a yanzu.

Bai ma san lokacin da wasu mata suka janye Ihsan ba. Yadda  Sulaiman yake kallonsa ne yasa ya ɗan tsargu. Murmushi ya yi masa ya ce,

“Yaya Irfaan, Ihsan ba aljanah bace mutum ce cikakkiya kamar kowa.”

Irfaan dai yamun bakinsa ya ƙafe babu shiri ya nufi mota ba tare da ya iya cewa uffan ba, ya buɗe ya shiga.

Ruwan gora ya fara ɗaɗɗaka har sai da yaji maƙoshinsa ya jiƙe sannan ya ajiye ya kwantar da seat ɗin motar ya kwanta shiru.

Gaba ɗaya ya rasa me ke yi masa daɗi. Ya yi danasanin zuwa garin nan yafi a ƙirga. Kafin wani lokaci kansa ya kama ciwo, a hankali ya dinga lumshe idanunsa yana jin suna yi masa nauyi.

Can wani lokaci ya ji ana ƙwanƙwasa motar. Da ƙyar ya iya tashi ya buɗe yana duban iyayensa.

“Kai ashe kana nan kasa muke ta nemanka. Sai ka tashi mu je, tunda kai ka rantse ka tsani jama’a.”

Bibbiyu yake kallon mahaifinsa da ke ta sababi. Sai Umma ce ta dube shi a ruɗe,

“Irfaan me ya sameka haka?”

Sai a lokacin Abba ya dakata da masifan da yake yana dubansa. Kai kawai ya nuna masu daga nan bai iya sake cewa komai ba ya mayar da kan.

Abba ya zare key ɗin motar ya ce su shiga ya ja su, idan sun shiga gari sai su wuce wani asibiti.

Har bakin motar aka rako su Abba ana yi masu godiya. Daga nan suka kama hanya kowa jikinsa asanyaye. Ga mamakinsu suna shiga cikin gari Irfaan ya tashi zaune ya ce kansa ya yi sauƙi. Sai a lokacin duk suka ware suka fara hirar biki.

“Wallahi Yallaɓai tunda nake ganin soyayya ban taɓa ganin kamar na yaron nan Sulaiman da Ihsan ba.”

“Kin kuwa ga amaryar?”

Abba ya tari numfashinta.

“Na ganta Yallaɓai. Halan munin amaryar kake son bani labari ko? Shi kuma ganinta yake tafi matan duniya kyau.”

Ta bashi amsa tana dariya. Alhaji Abbas ya jinjina kai,

“Kin fi ni gaskiya anan wurin kam. Sai dai ya yi yaro da yawa ya ajiye iyali.”

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

1 thought on “Duniyata | Babi Na Daya”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×