Skip to content

Duniyata | Babi Na Hudu

1.5
(2)

<< Previous

Gaba daya suna zaune a falo kowanne da irin abincin da yake ci. Umma tana lura da yadda Irfaan yake caccakar abincin kamar wanda aka sa shi dole sai ya ci. Bata ce masa komai ba, bata kuma yi alkawarin furta wani abu ba.

“Ya maganar zuwa da Irfaan wurin wannan malamin?”

Umma ta tambayi Abba. Hakan yasa Irfaan juyowa da sauri yana dubansu,

“Don Allah Abba kada ku kaini ko ina. Lafiyata kalau.”

Umma ta dago a fusace,

“Dalla wuce ka bani wuri. Wallahi Irfaan ka fara kaini karshe. Zan dauko duk macen da ta yi min in aura maka. Haba! Yaro sai taurin kan tsiya.”

Abba bai ce komai ba, har sai da ya kammala tauna Cake din da ya cika bakinsa da shi, ya kurbi ruwa, sannan ya yi hamdala yana dubansu.

“Irfaan kayi hakuri a nema maka magani kaji?”

Irfaan bai iya cewa komai ba, musamman yadda yaga Ummansa ta fusata.

*****

Sulaiman ne rike da hannun Ihsan zai kaita Makaranta. Innayo ta yi masifar kamar zata mutu, amma ko kallonta bai yi ba. Bayan ya kaita Makarantar ne ya wuce wurin da yake faci. Yana ganin lokacin taso su ya yi ya wuce ya daukota. Wasa-wasa wani irin shakuwa mai zafi ne ya sake shiga tsakanin Ihsan da Sulaiman.

A Makarantarsu Ihsan kuwa, abin sai Hamdala, domin bata fahimtar komai. Ranar wata laraba malamin su Ihsan ya yi mata dukan tsiya saboda yadda bata fahimtar karatu, a cikin ajinsu ita ke daukan na karshe.

Da Sulaiman yazo daukarta ya sameta duk ta galabaita. Idanunsa jazir ya kama kafadunta ya girgiza

“Gaya min waye ya tabaki.”

A karo na farko da ta ji shakkar gaya masa gaskiya. Ta dube shi asanyaye ta ce,

“Babu abin da akayi min Yaya Sulaiman ka yarda dani.”

Kallonta kawai yake ya kasa gazgata maganarta. Daga bayansu wata kawarta da ta yi a cikin Makarantar ta ce,

“Wancan mugun malaminne ya zaneta wai saboda bata fahimtar karatu. Ya zageta dakikiya. Har yana cewa bai taba ganin halitta mai muninta ba.”

Sulaiman ya saki hannun Ihsan ya dubi inda yarinyar take nuna masa. Ya juya da nufin zuwa ya sami malamin. Ihsan ta kama hannunsa idanunta cike da hawaye,

“Sai yaushe zaka daina yin fada saboda ni? Don Allah kayi hakuri ka kyale shi.”

Sulaiman ya fizge hannunsa ya wuce. Malamin nan yana tsaye da sauran malamai sai kawai ya ji duka ko ta ina. Ana rike Sulaiman yana watsar da mutane. Sai da ya yi masa dukan tsiya sannan ya ci kwalarsa jikinsa yana kyarma,

“Ihsan ba dakikiya bace kaine dakikin da har ka kasa koyar da ita yadda zata fahimta. Ihsan ba mummuna bace tunda har zuciyarta ta kasance mai kyau. Wannan shine na karshe da zaka sa hannunka a jikin Ihsan.”

Ya ture shi ya fadi kasa.

Ihsan ta juya da gudu tana kuka da iya karfinta. Da sauri ya je ya kamota yana lallashi. Bayan sun tafi ne malamin nan yaje ya debo ‘yan sanda. Kai tsaye gidansu Sulaiman aka nufa ana nemansa. Innayo ta kurma ihu tana fadin shikenan Ihsan zata jawo akama mata yaro.

Ihsan da Sulaiman suna isowa gida suka sami cinkoson mutane anata cecekuce. ‘Yan sanda suna ganin Sulaiman suka cafke shi. Ihsan ta sa ihu tana fadin sai dai a tafi da su tare. Babu wanda ya kalleta suka wuce da shi. Shi kansa Sulaiman sai ya gwammace da sun hada da Ihsan din kasancewar yasan makomar barinta a gida muddin suka yi ido hudu da Innayo.  Aikuwa ana tafiya da shi Innayo ta damki Ihsan, tana ihu tana komai ta kaita har gidan Malam Bala. Yana kwance ya ji anjefa masa abu mai nauyi. Da kyar ya iya daga idanunsa ya dubi Ihsan a jikinsa.

Marka ta fito tana dubansu,

“Innayo ya kuma haka? Me zai sa ki dawo mana da ita muna murnar mun rabu da masifa.”

Innayo ta dubi Marka ta ce,

“Wato kun rabu da masifa mu kuma kuka kawo mana ko? To Wallahi ga ‘yarku nan na dawo maku da ita dan ba zamu iya ba.”

Ihsan ta rintse ido. Ko a lahira bata fatan Allah ya kara hadata da Marka. Ta gwammace ta rayu a daji da muggan namun daji, da ta sake zama da Marka. Ihsan ta yi wuff ta kamo kafafun Innayo tana wani irin kuka,

“Don Allah Innayo ki yafe min ki mayar dani gidanki don Allah. Wallahi bazan sake ba. Wayyo Yaya Sulaiman ka taimakeni.”

Innayo ta fizge tare da hankada Ihsan ta fadi anan kasa.

“Yayan Uwarki ne ba Yaya Sulaiman ba. Mayya!”

Malam Bala yana nan kwance yana kallonsu, idanunsa cike da hawaye. Sai dai ya kasa ko da tari gudun masifan Marka. Bayan Innayo ta fice ne, Marka ta wuce ciki tana sababi. Malam Bala ya yi magana da kyar,

“Zo nan kusa dani Mamana.”

Ihsan ta lallaba ta karaso kusa da shi ta fasa kuka,

“Baba na shiga uku ka taimakeni kaje ka dawo min da Yaya Sulaiman, Wallahi shi ne rayuwata…”

Duk yadda take kokarin jawo numfashinta abin ya gagara. Baba Bala yana kallonta ta sume babu kafafun da zai iya tashi ya taimaketa. Hawayen idanunsa suka sauka a jikinta. Ana haka Marka ta dawo, tana ganinta a jikinsa ta fizgota ta debo ruwa ta sheka mata sai gata ta farfado da sunan Sulaiman. Marka ta daddage ta zabga mata mari. Hakan yasa ta dawo hayyacinta ta shanye kukan tana jin zuciyarta tana kuna.

“Zaki taso ki zo nan ko sai na sake sumar da ke.”

Agigice ta tashi, kasancewar tasan halin Marka farin sani.

A ranar duk wani aikin wahala akan Ihsan ya kare. Cikin dare Malam Bala yana ji yana gani Ihsan ta kwana a dakin awakai kamar yadda ta saba. Duk yadda ake cewa barci barawo ne, ya kasa sace masoyan biyu. Sulaiman yana cikin tashin hankali agame da halin da Ihsan take ciki, ayayin da ita kanta take cike da tunanin halin da yake, da kuma tarin kewarsa. Ta yi kuka har idanunta sun kumbura. Da assalatu tun kafin Marka ta fito Ihsan ta fito ta kama aikin gida. Har sha dayan safe bata huta ba, haka kuma ba abata abin kari ba, duk ta zama wani iri. A lokacinne kuma tsautsayi ya afka akan wani tangaran din Marka wanda Ihsan ta fasa. Marka ta yi kukan kura ta damko Ihsan tana shirin gana mata azaba kamar yadda ta saba, ta ji anrike hannunta. A zabure ta waiwayo tana shirin narka ashar. Sai kuma taja bakinta ta yi shiru ganin yadda idanunsa suka sauya kala zuwa ja, ta tabbata indai Sulaiman din da ta sani ne babu ko shakka zai iya shaketa a wurin nan.

“Ban hanaki dukanta ba? Me nace zanyi maki duk ranar da kika sake sa hannu a jikinta?”

Ya tambayeta cikin tsawa. Ihsan ta shiga girgiza kai, a lokaci guda farin ciki ya mamayeta ta yi saurin zuwa gareshi ta kankame shi, sai kuma tasa kuka,

“Yaya kayi hakuri bata dokeni ba.”

Sai a lokacin Sulaiman ya saki hannun Marka. Yana jin tsantsar tsanarta aransa, tana daya daga cikin dalilan da yasa ya matsa sai ya auri Ihsan. Sai dai kuma auranta da ya yi bai tsinana masa komai ba, tunda har yanzu ya kasa sama mata farin cikin da ya yi wa mahaifinta alkawari.

Sulaiman yaro ne karami, amma zuciyarsa irin na manya ne, kasancewar ya yi rayuwar shaye-shaye a baya da kuma dabanci. Har dakin Malam Bala ya karasa ya tsugunna agabansa. Yana son yin magana amma hawayen dake sauka bisa kuncinsa ya hanashi furta komai.

Kuka sosai Sulaiman yake yi, ya sani ya riga ya gaza da ba Ihsan kulawan da ya yi alkawari. Malam Bala ya girgiza kai, shima idanunsa sun kawo ruwa ya ce,

“Kayya… Sulaimanu daina kukan nan don Allah. Ka yi kokari matuka. Naga Ihsan ta sauya da alamun samun natsuwa acikin rayuwarta. Babu abinda zance da kai sai Allah ya biyaka.”

Sulaiman ya mike kawai dan ya kasa yin magana. Hannun Ihsan ya kama suka wuce gida. Da Sallama ya shigo gidansu anan kuma Innayo ta fara ihu tana fadin sai dai ya mayar da Ihsan tare da takardarta idan ba haka ba ta tsine masa. Yana murmushin takaici ya karaso har gabanta ya ce,

“Idan kika tsine min ke kike da asara. Wallahi Innayo bazan yi abin da kike so ba. Ihsan kuma gata nan don Allah ku kasheta.”

Daga bayansa ya ji an ce,

“Kul! Na sake jin ka gayawa mahaifiyarka irin wadannan kalaman. Ashe Sulaimanu har yanzu baka yi hankali ba? Ace kwata-kwata baka da ladabin magana?”

A razane ya juyo yana mamakin lokacin da Babansa ya dawo garin. Da sauri ya sunkuyar da kai yana sosawa. Sai da ya gama fadansa sannan duk suka zube suna gaida shi. Ya amsa ya ce su shiga dakinsu. Bayan sun wuce ne Baba Sani ya rufe Innayo da fada, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.

Sosai Ihsan tasa wa Sulaiman kuka. Bai hanata ba, sai ma idanunsa da ya kafeta da su. Mutane suna zagin Ihsan akan muninta, shi kuwa gani yake babu macen da ta kaita kyau.

“Ihsan kukan me kike yi haka bayan gani a raye kuma a kusa da ke?”

Taku har kullum, ‘Yar mutan Borno.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×