Skip to content
Part 18 of 25 in the Series Duniyata by Fatima Dan Borno

Rayuwa ta ci gaba da tafiya, miƙaƙƙiya, wanda akan hanyar akwai tarin ƙalubale ta nasara da kuma akasinsa. Irfaan ya ci gaba da samun girma iri-iri hakan yasa ya ƙara zama cikakken mai ‘yancin kai. Daga shi har mahaifinsa sun yi ta taka matsayi. Da yawa daga cikin mutane basu cika sanin wai uba ɗa bane, sai idan angaya masu. Har a yanzu da Irfaan yake da babban matsayi bai taɓa ɗaga ƙafafu daga tuƙa mahaifinsa ba, musamman idan za su je Office. Sai dai idan baya garin. Ko baya gari mutum ɗaya ya yarda da shi ya ja mahaifinsa a mota.

Za su iya cewa shigowar Ihsaan cikin rayuwarsu kamar wata ɗaukaka ce ta kawo masu. Domin kuwa har kamfanoninsu ya ƙara bunƙasa da suna.

A irin lokacinne kuma Iffan da Sadiq suka dawo ƙasarsu ta haihuwa cike da tarin nasarori. Duk da sun jima da sanin duk abubuwan da suka faru a tsakanin Ihsaan da Yayansu Irfaan, hakan bai hana su cika da mamaki ba, musamman da suka ga Ihsaan ɗin tana nan manne da baƙin nan. Sai dai ƙarun shekaru ya nuna ƙarara a jikinta. Ta cika sosai, a matsayinta na budurwa matashiya mai jini a jiƙa.

Gaba ɗaya sun sake da ita, musamman da suka ji itama ɓangarensu take karanta. Wato aikin likita. Sun sake bata tsoro, kowannensu yana sake jaddada mata ta shirya sosai, dan abun babu sauƙi.

Shaƙuwar Irfaan da Ihsaan wani lamari ne mai ban mamaki da al’ajabi. Kafin ya ankare ya yi nisa sosai a cikin soyayyarta. Ya fahimci ba zai taɓa samun natsuwa ba muddin aka ce babu ita a kusa da shi.

A gefe guda kuma Irfaan yana ci gaba da nemo yadda zai yi ya haye kan kujerar mahaifinsa wato CP.  Hakan yasa ya yi ta zirga-zirga kasancewar Abba ya ce masa ya dage ya karɓi kujerar.

Duk da Irfaan mutum ne mai zafin nama. Baya son wargi ko kaɗan. Ya sami masoya da mahassada iri-iri musamman a wurin aikinsa. Akwai mutanan da suke jin ina ma ace yau ya mutu.

Yau kamar kullum ya dawo a gajiye. Dan da ƙyar yake iya ɗaga ƙafafunsa saboda gajiya. Ihsaan ta ƙaraso ta karɓi kayansa tana yi masa sannu da zuwa. Kallo ɗaya ya yi mata ya fahimci ta yi kuka. Ɗauke kansa ya yi sannan ya wuce ɗaki.

Sai da ya yi wanka ya kintsa ya zauna yana shan ruwan lipton sannan ya jawota sosai jikinsa ya ɗora hancinsa a wuyarta yana shinshinan ƙamshinta mai daɗi.

“Me ya faru?”

Ya tambaya cikin wata murya mai tsananin sanyi.

Ta kasa bashi amsa sai ma lumshe idanun da ta yi, tana sauraren irin saƙon da yake aika mata.

“Gaya min mana.”

A hankali ta motsa baki ta ce,

“Wai gobe zamu je Saulawa.”

Shima ya ɗan yi jimm.. Ya manta gobe ne tafiyar. Yaso ya kai su da kansa, amma kuma yana da wani babban Case a gabansa.

“Ba ki son zuwa ne?”

Ta kasa magana sai ajiyar zuciya da ke ƙwace mata. Sulaiman kawai take hange a cikin ƙwayar idanunta. Sannan kuma duk dalilin da zai sa ta yi nisa da Irfaan bata ƙaunar wannan dalili.

“Kawai dai…”

Sai kuma hawaye.

“Come On Ihsaan ki daina kukan ki gaya min idan baki so sai inhana a tafi da ke.”

Ya yi maganar tare da jawota gaba ɗaya ta koma jikinsa. Ya sani sarai shi kansa bai isa ya hana tafiyar nan ba, domin umarni ne daga Abba. Dole ta je taga ‘yan uwanta.

Ita kanta Ihsaan tana da buƙatan ganin Baba Marka, tana so ta je ta karɓi wasu kayayyakin mahaifinta. Ta tabbata za su taimaketa.

Kiran wayarsa ya dawo da su duniyar tunanin da suka afka. Duk suka dubi wayar. Amira ce ke kiransa. Ta jima da sanin Irfaan bai rabu da Amira ba, ta kuma sakankance Amira ita ce mace ta biyu da zai aura.

Amira tana da nacin da ba kasafai take yin saurayi ya iya rabuwa da ita cikin sauƙi ba.

“Ka ɗauka mana.”

Ta yi maganar cikin danne wani abu da ya taso mata mai tsananin zafi.

“A’a Ihsaan me ya sa zan…”

Bai ƙarasa ba sakamakon ganin ta ɗauki wayar ta ɗauka tare da buɗe muryar wayar ta kai masa daidai baki.

“Hello Dear. Ka ce za ka zo baka zo ba.”

Ihsan ta ƙyafta masa idanu, hakan yasa ya haɗiye wani abu da ƙyar. Ganin ba zai iya magana ba, yasa ta kashe wayar. Ta miƙa masa ta ce,

“Buɗe min wayarka.”

Babu musu ya buɗe mata. Saƙonnin da suka turawa juna ta dinga dubawa. Kalaman soyayya iri iri babu waɗanda bata tura masa ba. Sai dai amsarsa a gajarce yake. Tnks, ok, Sai da safe. Ire-irensu ne. Sai kuma wani saƙo da ya ja hankalinta wanda take yi masa ƙorafi akan Ihsaan, shi kuma ya taka mata burki. Shi ne saƙon da ya yi magana mai tsawo a ciki.

A hankali ta rubuta saƙo kamar haka,

“Ki yi haƙuri yanzu na shigo gida. Amma gani nan zuwa. Amma ba zan daɗe ba minti goma sha biyar zan yi, dan na gaji sosai.”

Ta tura mata. Nan da nan sai ga amsa,

“Ok. Idan kayi min hakan ma zan ji daɗi sosai.”

Ihsaan ta miƙa masa wayar ta tashi ta ɗauko masa wasu kayan. Ya karɓa ta juya masa baya ya sanyasu.

“Na gama.”

Ya ce da ita. Ta dube shi sosai ya yi mata kyau. Ta ɗebo turarukansa ta fesa masa da kanta. Sannan ta yi dariya ta miƙa masa hannu kamar yadda suka saba, idan suna hira harda tafawa. Wannan karon asanyaye ya miƙa mata hannun.

Ta ciro takalmansa ta goge masa, sannan ta ɗauki key ɗin motar suka fito har tsakar gida. Ita ta buɗe masa mota ya shiga sannan ta zuro kanta,

“Mijin ‘yar baƙa kada ka daɗe agun ‘yar fara. Mintuna goma sha biyar na baka idan ka wuce za ka zo ka sameni na yi irin kukan nan da baka so.”

Ta yi maganar cikin dariya. Sannan ta rufo masa ƙofar motar ta juya ciki.

Ya ɗan jima zaune a wurin kamar wanda ƙwai ya fashewa a ciki. Sannan ya tada motar yana mamakin halin Ihsaan. Gani yake kamar a wannan zamanin zai yi wahala a sami mace mai irin halinta.

Ita kuwa tana shiga ɗaki ta yi kukanta sosai, sannan ta share hawayenta, ta tashi ta shiga banɗakinsa ta wanke ƙananan kayansa wanda dama ita ke wanke masa. Sannan ta ƙara tsaftace inda ya ɓata ta ɗan kwanta shiru. Anan barci mai nauyi ya yi awon gaba da ita.

Ko da ya isa wurin Amira, sai ya hau ta da faɗa akan kiransa da ta yi, ya kuma sanar mata Ihsaan ce ta matsa ya zo dan bai yi ninya ba. Jikin Amira ya ɗan yi sanyi, amma zallan kishi ya hana ta yaba mata.

Mintuna sha biyar suna bugawa ya ce mata sai da safe. Juyin duniya ya tsaya tana son magana da shi. Sai da ya tada motar sannan ya ce,

“Kiyi magana da ni a halastaccen lokaci, ba haramtacce ba. Wannan lokacin ya haramta a gareki domin iya lokacin da aka baki kenan.”

Ya ja motarsa ya wuce ya barta tsaye tana tunanin wani irin boka ne ya samawa Ihsaan irin wannan soyayya agun Irfaan?

A hanya ya tsaya ya siya mata kaza, da abubuwan kwaɗayi da yasan tana so. Yana shigowa ya sami har ta yi barci. Bai tadata ba, ya kintsa sannan ya hayo gadon. A karo na farko da ya yi tunanin ƙura mata ido a tsawon rayuwarsa da ita.

Tana da ɗan ƙaramin baki, da siririn hanci. Doguwar fuska gareta sai kuma gashin girarta da ya kusa haɗewa saboda tsabar rashin gyara.

Fuskarta babu alamun ko ƙuraje ɗaya, amma baƙin nan har yana walƙiya. Yana son ganin gashin kanta. Ya yi ƙoƙarin ganin ya cire hijabin hakan ya gagara dole sai ta saman kanta ya jawo hijabin baya.

Hijabin bai sauka dukka ba, amma kuma kanta sai ahankali. Bata damu da kitso ba, ko ankira mai kitson ba kasafai take bari ayi mata ba. Kitson nan har ya haɗe ba a ganin tsaga.

Gata dai tsaf-tsaf da ita masha Allah. Haƙoranta ma tana brush don haka babu wari, amma basu da haske.

Wani abu ya yi ta zagaye shi yana jin ƙarin ƙaunarta aransa. Da farko ya yi tunanin tana da uban muni musamman idan aka dubi irin wannan baƙin, amma a yanzu da ya ƙare mata kallo ya fahimci Ihsaan tana da sassanyar kyau, irin wanda sai ka ƙura mata idanu sosai sannan za ka iya gani.

Dole ya ja masu bargo ya yi addu’a ya tofa masu.

Washehari da sassafe ya fice a gidan, dan ko ganinsa bata yi ba. Umma tana tsaka da haɗa dinning ta tsinkayi muryarsa. Sai da ta ɗan dakata sannan ta ce,

“Ya akayi ne da sassafe haka? Yallaɓai bai ce min zaku fita da wuri ba.”

Irfaan ya ƙaraso gabanta ya karɓi flask ɗin da ke hannunta ya ƙarasa ya ajiye sannan ya gaidata. Bayan ta amsa ne ya ɗan sosa kansa ya ce,

“Umma na kula Ihsaan rigima za ta yi min shiyasa na gudu tana barci. Tun jiya take koke-koke wai saboda za aje Saulawa. Yanzu kawai zuwa anjima sai Sadiq yaje ya ɗaukota ku wuce.”

Umma ta jinjina kai,

“Ni kaina sai naji bana son zuwa Saulawan nan Wallahi. Kawai kuka za ta dinga yi har sai kowa ya ji babu daɗi.”

Hanyar ɗakinsa ya nufa wanda har yanzu bai ba kowa key ba, gani yake har abada nasa ne ba na kowa ba ya ce,

“Gara aje ɗin Umma. Idan aka ce za a biye Ihsaan to a Kaduna za ta gama rayuwarta.”

Umma bata ce komai ba ta nufi sashin mijinta cike da saƙe-saƙe.

Shi kuwa gadonsa ya haye da takalmin gaba ɗaya. Zai so ya je Saulawan nan. Bai san me ya sa yake jin damuwa akan tafiyar ba. Da yana da yadda zai yi da ya ce abar masa matarsa, musamman ma yadda idan sun je acan za su barta har sai ta yi sati biyu cur. Yana tunanin ta yadda zai iya zama har tsawon sati biyu babu Ihsaan. A zuciyarsa yana ji kamar a karo na farko zai yi wa Abba musu, dan babu wanda zai iya fahimtar halin da zai shiga adalilin rashin Ihsaan ɗinsa.

Muje zuwa…

Fatime Ɗan Borno

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Duniyata 17Duniyata 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×