LITTAFI NA DAYA
Kan uban nan!
Uwale! Uwale!! Uwale!!!
Fito ki gani, fito maza ki ga abinda Faɗime ke yi.
Mtss! Uwalen daga ɗaki ta ja tsaki bayan ta ƙara miƙa kan gadon da ta haɗa shi da tarin tsummokara.
'Allah ya yi dare gari ya waye, yanzu za a fara kiran mutum kamar wanda ya gille kan sarkin Mayu.'
Ta faɗa a zuci, sai kuma ta ɗaga muryarta.
"Wai me ya faru ne Hansa'u? Ba fa zan fito daga ɗakin nan ba idan ba kokon nan kika gama damawa..."
"Uwale wallahi. . .