Skip to content

Fadime 1 | Babi Na Bakwai

5
(1)

<< Previous

Dan kuwa sau uku ana tsaida auren Hansai sai an gama kome an kira Liman za a ɗaura aure daga gidan ango a aiko da goron fasawa. 

Akwai na biyun ma da ya rantse shi cikin barcinsa maimakon ya yi mafarkin amarya tana shafasa sa, sai dai ya ga baƙar karya(Macen Kare) tana kai masa sumba (Kiss) cikin barci. 

Dan haka ya fasa. Musamman da Malaminsa ya tabbatar masa matuƙar ya sake akai auren to a daren amarcin nasa za ta koma Karya. Shi ne fassarar mafarkinsa. 

Sosai hankalin Uwale ya tashi, ba shiri ta tafi mahaifarta garin kaduna gurin Ubanta Mai Salati aka haɗo mata maganin farin jini, na shane, na wanka ne, harda wani kwalli Ɗan Kaɗafi, da wani turare Shaƙarni Ka Aure. 

Waɗannan sune suka taimaka suka jawo hankalin Madu Mai Rake ya gigice a soyayyar Hansai. Zaman sai da raken ma ya dai na, sai zaman ƙofar gidansu Hansai yana lissafa masu shige da fice da karkataccen bakinsa. Ba shiri Malam ya ce masa ya fito. Garin Allah bai waye ba sai da Madu ya ɗaɗɗago Iyayensa aka tsaida rana sati biyu kacal!

Har dai yau da Uwale ke ta juyi tsakar gida cikin farin ciki bayan watsewar ƴan biki da a daren jiya aka kai Amarya ɗakinta.

Kirari take ma kanta cikin nishadin da rabonta dashi tun wani shuɗaɗɗun lokuta kafin Bashari ya shigo rayuwarta.

“Sai ni dakalin majina a hauni a zame, murucin kan dutse ban fito ba sai da na shirya, na kauda Bashari, na kauda Falmata. Yanzu kuma zan tadda Faɗima. Ɗiyar Mai Salati nake , tundaga nono muka kwankwadi baƙar zuciya, da baƙin naci kan abin ya tare mana gab…”

Tsit ta yi jin bugun ƙofar da ake mata da karfi. 

“Waye nan kuma, in dai biki ne an ƙare shi, kayan garar ma tun jiya suna kusa da Amarya, ko wane makwaɗaicin ne gwara ma ya haƙura dan kuwa bazan buɗe ba.” 

“Uwale ni ce ki buɗe, wayyo za su kashe ni.” 

“Hans…” Ta kasa ƙarasawa  jin tsoron a ce ita ɗince. 

“Uwale ki buɗe mini mana!” Da gudu ta isa ƙofar ta zare sakatar, sai dai kafin idanuwanta su gama sauka kan ɗiyar ta ta. Ji kake Tau! An sauke mata dutse bisa goshinta, da hanzari ta dafe goshin tana kallon Hansai dake tsaye gabadaya ta fita a kamanninta, bayan ta tarin yara ne suke ta atilen duwatsu kai kace rabin ƙauyen Bebeji ne. 

Wani dutsen ne ya ƙara sauka bisa karan hancinta ba shiri ta finciko Hansai cikin zauren da gaggawa ta danna sakatar. Tau! Kwal!! Suka rufarwa Kofar ƙarfen nata da duwatsu sai iface ifacensu suke. 

Kafa a tattale Hansai ta ƙarasa ciki nan tsakar gidan ta zube tana tiƙa uban kuka. Baƙin ciki ya hana Uwale magana sai ta koma gefe hannu bi sa kunci tana kallonta.

Da dai taga abin bazai ƙare ba nan ta hau tambayarta. 

“Ina kika baro mijin naki ? Wane sakarci ne ma ya saka ki fitowa yau ina ba jiya kika bar nan ba ? me kuma ya haɗaki da yara suke binki haka kamar mai ciwon hauka ?” Wani kukan ta sake rushewa da shi tana kallon Uwar. 

“Uwale kin cuceni da kika ba ni magani na auri Madu, kin cuce ni. Ya sake ni, shika har uku bayan ya keta mini rigar mutunci n…”

Salatin da Uwale ta doka da ƙarfi game da zubewa kasa dabas ya katse ta.

“Saki fa kika ce Hansai, ki gaya mini gaskiyar abin da kika masa. Soyayyar da Madu ya nuna miki ba ta yi lalacewar da  zai sau ki ranar da kika tare ba. Kodai kin sai dawa wasu kanki, faɗa mini gaskiya.” 

Harara ta dokawa Uwar jin ƙarshen zancenta. “Na ga da kanki sai da kika duba ni shekaran jiya. Idan ma iskancin nake yi ai ke zaki fara sani. Cewa ya yi shi ba zai iya zama da mai warin jaba ba. Wai tunda ya je wankan tsarki  ya ke a mai, shi wai ba ma ni ya so aure ba. Rufaidatu Mai Taliya ya so aura, ya kuma kasa tuna dalilinsa na aure na.  Da naƙi tafiya ne ina ta roƙansa ya yi haƙuri, ya fincike ni waje. Na ce ya tsaya na ɗau lefena da garata, ya ce uban da ya bashi ni ma ya yi kaɗan, ya cinye, idan ina da ƙarfi na ɗauka. ƙarshe ma ya hau zagina. Da na tsaya ramawa kuma ya hau buguna ya tara mini yara wai su rako ni gida.” 

Ta furta numfashinta na fita sama-sama tsabar kuka.

“Haka fa, umm lalle, to, to.

“Sambatun da Uwale ta kama yi ke nan, ƙarshe ma kai kawai sai ta rushe da kukan baƙin ciki.

Bugun ƙofar da aka fara yi ne ya tsayarta ta ɗago tana kallon ƙofar tana kallon Hansai. Da sauri Hansai ta tare ta.

“Ba dai ni za ki ce na buɗe ba da wannan tsattsaman jikin nawa. Ai wallahi ko Babane sai dai ya hauro.” 

“Wai Mutan gidan basa nan ne ? Uwar Amarya a buɗe  mana ko har yanzu gajiyar bikin bata kwanta ba ?”

Jin muryar Salame ya sata miƙewa da hanzari zuwa ƙofar . 

“Salame ki na ji na?”

Ta furta a hankali.

“Ina jinki Uwar Amarya.”

“Akwai yara a ƙofar gidan nan”

“Babu kowa, me za ki yi da yara kuma?”

“To, Madallah.” 

Ta furta ta na zare sakatar.

Turus! Salame ta yi ganin kumburarran goshin Uwale, kan ta kai ga tambayarta ta hango Hansai yashe a ƙasa. Da karkarwa take kallon Uwale, ba ko ɓata lokaci Uwale ta hau bata labari. Salati da salallami kawai take yi tana kallon Hansai da tausayi.

“Yanzu nufinki sai da ya mayarta bazawara ya sauta ? “

“Ga kuwa shaidan nan Salame, ko wanka bata yi ba ta yo nan.” 

“Allah mai iko, amman Madu ya cika shige.” 

“Ba ruwan Madu, dama duk abinda aka yi ba bisa koyarwar addini ba, to ƙarshensa ke nan jin kunya. Ba yadda ban yi da matar nan ba, karta bata tarkacen da ta kwaso na magunguna amma wai taƙi jina , ita wai tun a ciki ta sha illar mai sukai mata. To yanzu ai gashi nan ta ga ribar ƙaryar banza. Ƙaramar yarinya an mayarta bazawara. Gata nan ai sai ki jiga gashin kanki ki bata ta sha muga kowannan karon Sarkin ruwa za ta aura.”

Cewar Malam da shigowarsa ke nan ya tsinci zancen da suke yi. 

“Haba Malam ƙokari zaka yi a gyara bawai ka hau faɗa ba. Ka fi kowa sanin irin kunyar da zanji a faɗin kauyen nan. Tunda ka zo yanzu kaje ka sami Madun ka ji yarda za a yi.” 

“Caɓ! Wallahi ko zan mutu ba aure bazan koma ba, tsami ma fa yake da ƙarnin kifi bakinsa kuwa kamar ramin masai dan ɗoyi.”

Cewar Salame, kafin kuma Malam ya cafe. 

“A gyare me Uwale?”

“Auren mana Malam, ai saki uku ya mata cikin jumla ɗaya.” Takaici ne ya ƙume shi har ya yi zagi a karon farko.

“Uwale uban wa yace miki ana gyara saki?” 

“A’ah Malam karka zage ni, ajinka bansani ba? To a gabana Mai Salati ya sha gyara irin wanann sakin ya mayar shi ɗaya.”

“Eh lallai kam sai dai a mazhabar mai Salatin. To ai sai ki je ki same shi, wannan ma ba zai gagara gyarawa ba.”

“Haba Malam ƴarka ce f…”

“Kinga Uwale, ki raba ni da wannan buhun haukan naki, na ji da jin kunyar da kike ƙoƙarin saka mini, koma ince kin saka ɗin. Hansai ce gata nan na barki da ita lamarin aure ne bana ƙara saka hannuna sai dai ku sami wani ya muku. Kinga tafiya ta.”

Ya furta yana saɓa babbar rigarsa gami da ficewa daga gidan.

Salamen ce ta kallo ta cikin tausayawa ƙawarta. Zawarcin ƙaramar yarinyar ba ƙaramin tsayawa a rai gare shi ba. To ya zasu yi da abinda ya riga ya faru sai haƙuri kam. Amman anya babu kuskuren Uwale cikin lamarin nan. 

“Wai ni Uwale baki tunanin wani abu game da lamarin auren Hansai kuwa?”

“Kamar me fa Salame .”

Ta furta tana mai karkato da dukkan hankalinta kanta.

“Ina wannan asirin da kika karɓo ma Faɗime, shin kina iya tuna abinda Malam ya ce?”

“Me zai hana Salame, yarinyar da kullum cikin raina take kwana. Banda abinki in dai wanann ne ai bai kama ta ba, tunda bata riga ta shaƙi maganin ba. Shi kuma cewa ya yi mutuƙar ta shaƙi maganin, har ta fita daga gidan nan,to Hansai ba za ta taɓa auruwa ba.”

“Amman Uwale baki tunanin in dai an riga an karɓo shi an kawo cikin gidan nan daga lokacin zai fara aikinsa? Hmm! Ki dai bincika ki gani.” 

Kallonta ta tsaya yi kamar mai san ganin amsar cikin idanuwanta. Tabbas kam zai iya yiwu hakane, idan kuwa hakane dole ne gobe ta je gurin Malam. “Taɓdijam! Idan kuwa ya kasance haka ne ?…Hmmm….”

Ta furta da ƙarfi tana kallon yashasshiyar Hansai. 

*****

Kwana biyun nan ya rasa me ke damunsa. Ko ya ya ya shigo cikin gidansu sai yaji wani ɓacin rai mai girma na shigar shi. Har takai sai ya daɗe a ofis duk dan ya kaucewa hakan, amman da zarar ya shigo gidan zai fara ganin duhunsa. Barci baya iya yi haka nan zai ta juye-juye yana tsaki ƙarshe ma sai dai ya tattara ya shige masallacin jikin gidan nasu. Nan ne kawai yake jin nutsuwar zuciyarsa. 

Kwanaki na wucewa ƙuncin zuciya na kara mamayarsa. Yanzu har ta kai ko a ofis yake shi kaɗai sai ya kama tsaki abu kaɗan ya kama faɗa da sakateriyarsa. 

Hajiya da kanta ta lura da hakan da ta tambaye shi kawai sai ya saka mata kuka dake zuciyar da ma a sama take. Ita  kam sakin baki ta yi tana kallonsa, rabonta da ganin hawayen Autan nata, tana jin za a ɗau shekara goma sha. Ƙaƙƙarfar zuciya gare shi da bata barin kaga karayarsa cikin sauri. Lalle duk abinda ya saka shi kuka to kuwa ba ƙarami ba ne.

“Me zan ce miki Hajiya ? Bansani ba. Bansan me ke damuna ba. Sam! Ba na jin daɗin rayuwata, ina jin wani abu ya tsaya mini a maƙoshi da ban san menene shi ba. Ina jin kamar ina son wani abu, sai dai ban san menene ba. Ina jin kamar mutuwa zan yi ko kuma wani gagarumin abu ne zai shigo rayuwata. Dazu fa haka nan na sallami Sakateriya ta, yanzu haka idan kika tambaye ni abinda ta mini bansan meye  shi ba. Dan Allah Hajiya ki mini Addu’a ko menene ya zo mini cikin sauki. ” 

Dafa shi ta yi cike da tausayawa. Ita kam a idonta har wata rama taga ya yi, fuskar ta yi fayau, sai dogon karan hancin.

“Addu’a kam kullum ina maka Auta. Insha Allah babu abinda zai sameka nan duniyar. Mutuwa kam in kwana ya ƙare dole ta zo. Sai dai ayi fatan cikawa da imani. Kai ma kuma harda rashin addu’ar ke kara dagula maka lissafi. Tun dawowarka daga Ghanar nan na kula salon ibadarka ya canja ba kamar da ba. Ga addu’o’i nan na kauda dukkan wani ƙunci cikin (Hisnul Muslim) ka dage da karanta su ins ha Allah ko menene za ka samu sauƙinsa.”

Shi ke nan Hajiya zan dinga yi. Bari ma na ɗauki naki naje na fara.” 

“Ko kai fa. To sai da safe Allah ya shige mana cikin dukkan lamuran.” 

“Amin Hajiya ta.” Ya furta yana barin wurin.

Can ɓangaren Faɗime kuwa ita ma yau cikin wani ƙunci ta tashi sai ɗan fizge-fizge take yi alamun tana jiran mai takalarta. Har dai bayan sallar isha ta gama zaman falonta ba wanda ya kula ta, sai ta tashi zuwa sama. 

Harta buɗe ƙofar ɗakinta, sai kuma ta juyo tana kallon ɗakin Sagir. A hankali ta juya zuwa ƙofar ɗakin nasa ta murɗa ƙofar. Ga mamakinta kuwa bai rufe ɗakin ba. Haka nan ta shige ciki a karo na farko tun zuwanta gidan. 

Wani sassanyan ƙamshin (Air freshener )na ne ya fara bugun hancinta. kafin lumsassun idanuwanta su sauka bisa tamfatsetsen gadon nasa kai kace na wani maigidanci ne me mata uku. Ahankali ta isa ga gadon ta ɗora hannunta bisa tattausar shimfiɗar tana shafawa. Sunkuyawa ta yi tana mai yaye gefen shimfidar gadon, ga mamakinta kuwa mai karkashin gado ne, ba bata lokaci ta mirgina ƙasan gadon gami da jawo zanin gadon ya rufe gurin. Sannu a hankali wani daddaɗan barci ya sace ta.

Yana shigowa  aje (Hisnul Muslim) ɗin ya yi kan (Drawer) gefen gadonsa, ya faɗa toilet. Wanka ya sillo ya fito, ya ɗanyi kintse-kintsensa na ɗabi’a kana ya baje bisa gadon nasa. Shiru ya yi yana son tuna abin da yake son yi amman ya gaza tunowar. Ƙarshe kawai ya yi tsaki gami da tashi ya kashe wutar  ɗakin ya dawo ya ƙudundune cikin (Blanket) ɗinsa. 

Kamar cikin mafarki yake jin ƙusar-ƙusur ƙasan gadon. Tun bai gasgata ba har dai ya buɗe ido tar yana kasa kunne. Tabbas motsi yake ji ƙasan gadon, to menene ? Ya tambayi kansa. ‘Zai wuce 6era ? ‘ Wata zuciyar ta ba shi amsa. 

Wayarsa ya fara jawowa kafin kuma ya zira hannunsa ƙasan filonsa sai ga wata yar ƙaramar wuƙa ya fito da ita. Saukowa ya yi cikin sanɗa kamar wanda bai so ɓeran ya gudu. Tsayawar da ya yi yana ƙoƙarin zaro wuƙar daga cikin kubenta ne, ya ji wani abu kamar tafiyar ƙadangare na masa yawo a ƙafafu. Da ƙarfinsa ya doka tsalle gefe yana furta. ” Wayyo Hajiya.” 

Fit ta mirgino tana kallonsa. Shi ɗin ma tsayawa ya yi yana kallonta jikinsa na rawa. Gabansa ta ƙaraso cikin ɗan hasken wayar tasa ta kula da wuƙar hannunsa. Bata san sa’adda dariya rushe da dariya ba tana nuna sa. “Yanzu  ƙanin Uwale da wuƙa zaka kori Ɓera, cikin duhu kuma?” 

Da sauri ya yi cilli da wuƙar. Dariya ya saki har yana duƙawa ganin wautar da ya yi. To, ita ɗinma duƙawar tayi tana taya shi cikin wani irin farin ciki da ya saukar musu lokaci guda.

A tare suka tsaida dariyar idanuwansu cikin na juna kowanne so yake ya gano abinda ya haddasa masa wanann nishaɗin. Ita ta fara sauke nata cike da kunya, shi ɗinma kauda kai ya yi cikin basarwa. Miƙewa ta yi zata wuce, kome ya tadɗe ta sai gata ɗim ta faɗo kansa sunyi wanwar a kasa. Maimakon suji zafin hakan, sai ma wata dariyar da suka ƙara kwashewa da ita, kanta bisa kirjinsa ta ji maganarsa cikin kunnuwanta.

“Kinga shi ke nan nima an rama mini” “Kai Ƙanin Uwale ai dai ka fi ni jin zafi”

“Uhum, wannan muryar..” 

Ya furta da sigar muryarta.

“Lah wai dama kana magana mai daɗi ?”

“Lah wai dama kina magana mai daɗi?” Ya maimaita zancenta. 

“Bata san sa’adda ta ƙara cusa kanta cikin ƙirjinsa. Shi ɗinma yadda take yin ba ƙaramin kauda masa da nutsuwarsa yake ba. Dan haka ya dube ta.

“Ɗaga ni ni karki karya ni da wanannn nauyin naki, ji nake kamar buhun Alkama ne a kaina.”

A kunyace ta tashi, ita fa harta mance samansa ma take. Kallonta yake yi yadda take taku cikin nutsuwarta sai yanzu ya lura da shigar jikinta. Matsattsen wando ne da ya saukar mata ƙasan gwiwa, sai yar kamar Top mai zip a gaba da ta bayyana har shacin bra ɗinta. Wata irin sha’awace ya ji ta tsirga masa wacce bai taɓa jin irin ta ba tunda ya mallaki hankalinsa. Ji ya yi idsn bai sake haɗa jikinsa da na ta ba, ba zai ƙara samun nutsuwar zuciya ba.

“Fatima!” Ya furta cikin dasasshiyar murya ganin tana shirin buɗe ɗakin ta fice. Ita dinma cak ta tsaya. Yadda ya kira sunan nata ya sata jin abinda a iya shekarunta ta rasa gane menene. Ita kawai tasan ba ta son barin ɗakin. Sonta su dawwama a haka daga nan har ƙarshen rayuwarsu. 

Dan haka ba ɓata lokaci ta juyo tana kallonsa da lumsassun idanuwanta da suka ƙara ta da masa hankali. Da kansa ya ƙaraso ya riƙo hannunwanta gami da zaunar da ita gefen gadon. 

A hankali ya zauna gefenta shi ma, hannunsa bisa hannunta yana kallon idanuwanta, kafin kuma ya sa hannu ya zare hular kanta, lallausan gashin nata da ta ƙudundune ciki ya sauka saman kafaɗunta.

“Ya salam!” 

Ya furta a ransa shaidan na ƙara ƙawata masa yadda zai same ta. Ga mamakinsa ita ɗinma kanta ta ɗora saman kafaɗarsa tana ƙara damtse hannnunsa da ke cikin nata. Shiru ya gifta a tsakanin matasan biyu cikin talatainin daren da yazo musu da sauyin yanayin. Kowanne zuciyarsa na ƙissima abubuwa da dama da suka kasa gasgata shi. Shi ya kauda shirun ta hanyar mirginata saman gadon, shi ma ya kishingiɗa gefenta.

“Fatima! Kina jin irin abinda nake ji?”

Ya furta a hankali hannunsa bisa zip ɗin rigarta yana jujjuya shi. 

Itakam runtse idonta ta yi, wani yar-yar take ji a jikinta da ta kasa gane menene. Jin ta yi shiru ya saka shi zuge zip ɗin a hankali. Kyakkyawan zanen Ƙadangaren da aka yi shi da sigar mugunta, tana girma shi ma yana ƙawata farar fatar ta ta gami da rikiɗewa kamar (Tatoo) da turawa ke yi, shi ya fara ɗaukar hankalinsa. 

A nutse ya sa hannunsa yana shafawa, wanda ya saka ta ɗauke numfashi da ƙarfi tana kallonsa.

A can wani ɓari na zuciyarta na gargaɗinta da ta hana sa abin nan fa. Hajiya ta sha gaya mata haramcinsa. Allah na ƙona Macen da take riƙe hannun Namijin da ba muharraminta, balle akai ga taɓa jiki. Sai dai ga mamakinta harshenta da jikinta sunyi nauyin da ta kasa ɗaga ko da yatsunta ne, ballantana ta samu bakin magana. Ƙarshe ma sai ta lumshe idanuwanta cike da fatar kar ya dakata da wannan abin da yake yi…

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×