Skip to content

Fadime 1 | Babi Na Biyar

3
(2)

<< Previous

Sagir kam bai san wace rana ce yau a tarihin rayuwarsa haka ba. Da ƙarfi ya runtse idonsa jin abinda yayansa ma fi soyuwa gare shi ke faɗa masa kan wannan ƙasƙantacciyar yarinyar da a cikin ƙasƙantattun ma ita ɗin mahaukaciya ce, mai kwana a bola ta ci ƙazanta. Wai ita ake cewa zai rayu da ita gida guda. Ba zai yiwu ba, idan ko har ta shiga cikin gidansu, to barin gidan ya kama shi. Idan sama da ƙasa za ta haɗe ba zai ƙara awanni huɗu a cikin Kano ba. Da dai ya buɗi  ido ya ganta kusa da shi gwara ya fita daga rayuwar kowa.

Ya lumshe ido a hankali sa’ilin da ya ga Yayan ya riƙo hannunta cike da wata irin kulawa da bai taɓa ganin ya ma wani mai cikakken hankalin ba. A hankali wata zazzafar ƙiyayyar ke sake shigarsa. Ji yake nan duniya ba wanda zai tsane ta irin tsanar da yake mata…

Um Um dai akwai.

Uwale…(Inji Bingel)

Tsawon lokacin suka ɗauka suna kwarara gudu a titin ne ya sa cikin Faɗime hargitsewa ta fara kwarara a mai a motar sakamakon warin mai da ya cika mata hanci. Akwai alamun ba ta jure doguwar tafiya. 

Kallon Sagir yake yi bayan ya tsaida motar. A hankali kuma sai ya sakar masa murmushi, kafin kuma ya gintse.

“Me kake jira ne da ba za ka fito ka taimaka mata ta kintsa jikinta ba, ko ni kake so na fito na yi ? Ga Tissue nan ɗauki ka gogge mata jikin, ka ga hankalin da ɗan sauƙi, kar ta ƙara damalmala jikinta.” 

Ya furta yana mai tura masa kwalin Tissue ɗin.

Shiru ya yi masa yana kallon waje ta tagar motar, zuciyarsa wani irin tuƙuƙi take yi. ‘Wai shi ne zai goge ma mahaukaciya A ‘mai ?’

“Magana fa nake ma Sagir ka yi kunnen uwar shegu da ni, Allah ka bari na riga ka fita rigarka zaka ciro a goge…” 

A fusace ya buɗe motar ya fita. Hannu ya sa ya finciko hannunta itama sai gata gabansa, Tissuen ya miƙa mata yana huci cike da ƙyanƙyami.”

Goge ki kuskure bakinki.” 

Ya furta yana mai take ƙafarta da ƙarfi da kwaftareren takalminsa. Cike da rashin kula da abinda ya mata duk da tana cije baki ta karɓa cikin nutsuwa ta fara gogewa. 

Daga shi har yayan dake leƙensu daga cikin motar sakin baki suka yi suna kallonta cike da mamakin yadda take yi a nutse. Sai dai kafin Sagir ya farfaɗo daga inda ya dulmiya, ta daidai ci bakinsa, tissuenta da annakiyar hannunta basu zame ko’ina ba sai cikin bakin. Tsallen da ya yi gefene ya hanasu faɗawa ciki. Duk da haka sai da suka sauka gaban rigarsa duk ta ɓaci da haɗaɗɗen shinkafa bil dajajah da Faɗime da ta ce ɗazun. Ai kuwa ta sheƙe da dariya tana kallonsa cikin galabaita harda nuna bakinsa. 

Yaya dake kallonsu ya juya cike da murmushi yana mamakin shegantaka irin ta ta.  lalle ya samu mai masa maganin tsagerancin Sagir. 

Sagir kam bayan ya gama watstsakewa daga takaicin Faɗime, belt jikinsa ya fara ƙoƙarin cirowa da zummar haɗa mata abinda za ta kasa motsi balle dariya.

Yayan ne ya farga ya yi saurin fitowa gabansa.

“A’a wallahi ai kuma baka isa ba. Ina kallon fa sanda kake mata mugunta ko an gayama ban kula da yadda take ciccije baki ba ? Kaga da yake Allah ba azzalumin bawansa ba ne, gashi ta rama da kanta. Ai ka ci sa a ma da baka haɗiye abinda ta dawo da shi ɗin ba. Nan gaba ka ci gaba da cin zalin bayin Allah. Ku shige mu tafi ni kam. Ke kuma ba ruwanki da shi, Yayanki ne ki ba shi girmansa.” Ya furta yana mai komawa motar.

Gaban kyakkyawan matsakaicin gidan mai rangwamen girma ya tsaya yana mai latsa horn. Ba daɗewa aka yaye gate din ya danna hancin motan ciki.

Kan ya gama daidai ta ta a muhallinta har Sagir ya buɗe a fusace ya yi cikin gidan.

Faɗime ya kallo yana murmushi ganin ta sau baki sama tana tiƙan barci. A hankali ya fara kiranta. “Ke! Ke!! Tashi mun iso.” 

A nutse ta buɗe idanuwanta tana kallonsa, sai kuma tayi saurin hangame baki tana masa dariya. 

“Ki na ji na ? Idan muka shiga ciki ki nutsu, karki sake ki yi wani abin ashshan da mutanen gidan za su ji haushinki. Duk kuma abinda akace ki yi, ki yi shi bawai ki ɓata ba. Kinga nan gidan iyayena ne ko Yaya kika ɓata musu rai to zaki ga nawa ɓacin ran. Ban da ta’adi da ɓare-ɓaren jiki, ki zama yarinya mai ɗa’a. idan kika yi mini hakan to zamu shirya. Sagir kuma ba ruwanki dashi .

“Um um walahi indai ya taɓa ni bazan ƙyale shi ba, wataranma haƙori zan gutsire masa yadda Uwale ta taɓa yi mini.” Ta furta tana nunamasa karyaryar fiƙarta da ta ƙara ƙawata ma ta bakin.

“To kuwa ki kai hakan zan maidaki gurin Uwalen da kaina na bata abinda zata ƙarasa cire miki sauran haƙoran..”

“Ba zan ba, karka kai ni gurinta. Kasan muguwa ce a gabana ta ke gillewa zakarun Babana kai. Kuma kasan me ? Sanda na ga Salame ta zo kawai naje na laɓe musu, ba sai naji suna hiran Malam ba. Suna cewa za a turare Faɗime da turare za ta haukace, ba zata fita ko ƙofar gida ba, ba za ta je ko bakin rafi gurin Yayanta ba. Tsoro ya kama ni, tsoro mai yawa. Kasan me na yi ni kuwa ? Na tafi bakin rafi gurin Yaya mu kai ta kuka…”

Kawai sai ta saki kuka. 

Da hanzari ya dafa kanta, ah ah me na kuka kuma kina mini labari, ci gaba to wacece Faɗimen da za’a ma turaren?

Dagowa ta yi tana share hawayen da sauri da sauri. Sai kuma ta ɗaga kai sama kamar mai tunani.

“Af ! Kamar fa ni ce , amman ni ai banda hauka ko ?” Ta furta tana dudduba jikinta. 

Zuciyarsa ta tsinke. A hankali ya kai hannu ya goge kwallar da ta maƙale gefen idonsa, sai kuma ya riƙo hannunta suka fara tafiya. 

Maigadi dake ta leƙensu ya saki baki fal tsegumi yana mamakin inda Yallaɓai ya samo wannan annakiyar ‘yar budurwar.

Ƙafarta daya bisa  tattausan kafet ɗin dake falon, ɗayae kuma daga waje ta juyo fuskarta fal murmushi tana dubansa.

“Sunana Tauraruwa.” 

To na ji Tauraruwa shige ga Hajiya can zaune mu isa gareta. Cike da ladabi ya ƙarasa gurin haɗaɗɗiyar Matar dake zaune tasha adon lafaya hannunta ɗauke da casbaha ta na ja. 

“Mun sameku lafiya Hajiya ?” 

Ya furta yana mai zama ƙasan kafet d’in. Kallonsa take Cikin kulawa fuskarta ɗauke da murmushi.

“Lafiya ƙalau Babban Mutum, ya kuka baro can ɗin ? Fatar kome ya daidaita tsakaninsu ?” 

“Kwarai kam Hajiya sai godiyar Allah. ” ” To Alhamdulillah, Allah ya ƙara zumunci. ” 

“La Babban Mutum kalli ƙanin Uwale shi kaɗai ya tsaya baya dariya. Uwale ko tana dariya barin ma idan tana jibgata…” 

Duka suka kallota ɓangaren da ta tsaya ƙiƙam tana kallon tangamemen hotan Sagir  da ya gama haɗuwa da kyawu.

“Tauraruwa taho ki gaisa da Hajiya ta, ba ki ganta ba ne ?”

Da sauri ta baro jikin bangon ta taho game da zubewa ƙasa yadda taga ya yi. “Mun same ku lafiya Hajiya ?”

Hajiyan ta dube ta ta dube shi fuskarta fal mamaki.

“Ina kuka samo wannan kuma ? Ni fa na ɗauka irin yan’uwan Kande ne dake zuwa ? Ko daga can Bebejin aka haɗo ku da ita ?” 

“Ai Hajiya duk baki canko ba, wannan akan titin nan gaban Makarfi kaɗan muka same ta.” 

Nan dai ya hau bata labarin duk yadda aka yi.

Hajiya kafin a gama har ta fara goge kwallar tausayi.

“Yanzu Sagir ne ya mari wannan abar a bawa nonon? Nawa take Babban Mutum ? Ba na jin za ta fice sha uku fa sa’ar Rahane ɗiyar Kande. Ai duk lefin Alhajinku ne da ya kai shi Turai ga abinda ta ja mana nan rashin daraja dan Adam. Kai Allah mungode maka da ka yo mu da cikakken Imani. Ta ƙara kai dubanta ga Faɗime da tayi wuri-wuri tana kallonsu.

“Sai dai fa kayi ragon azanci daka taho da yarinyar nan Babban Mutum. Ba mu san mai zai je ya dawo ba, ka ɗauko  ɗiyar mutane ba tare da sanin iyayenta ba, ba tare da sanin wacece ita ba. Anya ? A yi haka kuwa a rayuwan nan mai cike da kalubale ? Ina ga dai ku hutu gurin gobe ka mayarta garinsu can gaban Danginta su kula da abarsu. Duk dai sonka da mutum ai baka yi ya nasa ba. Ba kuma zaka taɓa iya hana abinda Allah ya ƙadarta wa Bawansa ba. Haka duk ƙiyayyarta da wacce take ambaton ba za ta kai yadda za ta cinna mata wuta, ta babbaka ta ba ina ce ko ? Dan haka go… “

“Caɓ! Alƙur’an ko an mayar ni sai na dawo da wanann ƙarfin nawa.” Ta furta da sauri tana mai ɗaga ƙwanjin hannunta. Sai kuma ta yi zaman daɓaro tana kallon Hajiyar

“Kin san me aka yiwa Uwale ta ce za ta haukata Faɗime ? Wataran ne kawai Salame ta zo, Faɗime tana haɗa sanwar tuwo. Dama Yaya ya ce mata da taga Salame ta dinga laɓewa za ta juyo musu wani abun. Kin san to me Uwale ke cewa Salamen ?” 

Ta furta tana riƙe haɓa, tana mai son kwatanta yadda suka yi

“Zan cinna mata wuta ne yadda na cinnawa Bashari da Falmata.” 

Tsoro ya kama ni, tsoro mai yawa. Kawai garin na yi baya sai na tafi luuuu labulen ya yaye suka gan ni.”

Ta furta tana mai zare idanuwa gami da dafe ƙirji tamkar lokacin abin ke faruwa.

“Shi ke nan fa suka ce Faɗime ta ji sirrinsu za ta tona musu Asiri.” 

A ɗan tsorace suke dubanta duka su biyun.

“Kina nufin Uwale ta kashe Babanki da Mamarki da hannunta ? Me take zame musu ?

Shiru ta yi kanta na kallon sama kamar mai tunani, sai kuma ta saki murmushi tana dubansu duka su biyun.

“Na tuna, Allah kuwa na tuna. Masoyiyarsa ce ya ƙi aurenta ya auri Uwata.” 

Ta furta tana mai kwashewa da dariya kafin kuma ta fashe da kuka. 

A hankali sagir dake tsaye matattakalar benen yana sauraronta sakale da jakar kayansa ya ƙarasa saukowa gabansu. Fuskarsa a ciku ne da fushi, kamar wacce fara’a bata taɓa wanzuwa bisanta ba.

“Hajiya ni zan wuce, yanzu Salman yace Result ɗin mu ya fito, na kuma duba akwai jirgin da zai tashi ƙarfe 4:00 na daren yau, zan je nasan bazan rasa booking ba…” 

Daga Hajiyar har Yayan shiru sukai suna kallonsa, ganin hakan sai ya juya yana me kallon agogansa.

“Na tafi Hajiyata ayi mini addu’a” 

Ya furta yana ƙoƙarin barin falon.

Da dai taga da gaske yake sai ta sa baki ta fara kiransa. 

“Zo ka zauna nan kusa na Auta.”

Dawowar ya yi, ya zauna bayan ya bar jakar tasa a ƙofar falon yana mai sunkuyar da kai…

“Anya tafiyarce kuwa ? Ian ma tafiyar ce haka zaka tafi kasa guda kana fushi damu ? Me ke faruwa ne ?” 

“Me ko ya faru Hajiya banda shegantaka ? Jiyan nan da na tambaye shi yaushe Result din zai fito ce mini ya yi sai On 7th oct. Kawai ganin yarinyar nan ne zai saka shi yi mana ƙaura. To wallahi bari ka ji Sagir, ba Kenya ba ko nan da Kaduna ba za ka tafi ba sai sa’adda na so. Tauraruwa kuwa gidan nan yanzu ta fara zamansa in kaga ta barsa to Mijine ya fito mata za a mata aure, ko kuma wani nata ya zo. Sakarai kawai.” 

Babban mutum ya furta cikin fushi.

Fadime ko ta hau tafi da ƙarfi.

“Ai walahi ko Babban Mutum ina son a mini auren, in ga gado na da gurin girki in ta mulmula Ɗan Sululuf ina ci. “

Ba wanda ya bi ta kanta sai Hajiya dake kallon Sagir.

“To kai ka ji abinda Yayanka ya ce sai ka tattara kayanka ka maidasu inda ka ɗauko, ni kam ba abinda zance da duk hukuncinsa gare ka. Sai dai fatan Allah ya shirya mini kai da wanann zafin ran naka.”

Ido jajur ya miƙe ya miƙe ko ta kan kayansa bai bi ba ya yi sama. Suna jin sanda ya buga ƙofar ɗakinsa da ƙarfi kamar ita takar zomon. Sauke ajiyar zuciya Hajiya ta yi tana kallon Faɗime. “To ai shi ke nan Allah ya taya mu riƙo. Amma ya zama dole ka yi bincike game da danginta, dan na tabbata ba za a rasa na kirki ba. ” 

“Ba kome Hajiya in sha Allahu hakan za a yi. Ni ba dan Dr Musbahu bai garin ba ma, da goben nan zan kai ta can su duba mana ita, sai nake ga haukan nata kamar bai yi nisa ba, dan wani sa’in idan ta yi abu za ki ɗauka  mai cikakken hankali ne ya yi. Ƙila idan suka duba su bata abinda za ta warware gabaɗaya. Kinga daga nan sai muji ina dangin nata suke. “

Agogansa ya kalla kana ya miƙe.

“To bari na ƙarasa can gida, na san yaran na can na tsimayi na, Allah ya tash emu lafiya.

“To ai shi ke nan Babban Mutum Allah ya ida nufi, ya kuma ba da ladan taimako. Ka gaida mutan gida. Ita kuma wannan bari na sa Kande ta kaita makwancinta. “

*****

“Tunda nake bantaɓa ganin shashashan yaro irinka ba Yaya. Tun farko akan me za ka barta ta koma gidan, iyee ? A bar shi ma ba ni da wata alaƙa da ɗiyar. Ka na tunanin ba ni da imanin da za ka kawo mini mutum da irin wanann larurar rayuwar na guje shi ? Yanzu wa gari ya waya ? Kunje ku aiwatar da harkarku ta Yan boko, ka zo kuma ka na mini kuka, shin ni na kai ka, ko ka yi shawara da ni ? Kasan abin na da hatsari, ga sharaɗi  na wasu lokuta da aka ware, da yake  kai kasan me ke faruwa a gaba, sai ka yarda aka ɓata rayuwar yarinya. Me ke nan aka yi ? Da wanannn Bokan naku ba gwara abinda Uwar ɗakin nata zata mata ya kama ta ba. Tunda dai ko banza babu abinda Addu’a ba ta maganinsa a nan duniyar. Amman wannnan fa ? Sai an haɗa da surƙullen Bature. To wallahi tun wuri ka tsananta bincike kanta. Falmata ba za ta taɓa yafe mini ace ina raye jininta ya tagayyara haka ba. Maza ka tashi ko tasho shin mota ne ka bi ko zaka same ta can…” 

Hawaye kawai yake zuburwa yana sauraron faɗan Uwarta sa. Bai taɓa zaton lamarin zai juye masa haka ba. Lalle kam kana naka Allah na nasa. Na san kuma shi ne daidai.

Idan ba haka ba tun fari mai ya kai shi yanke shawarar nan, amman kuma ai ba yadda za su yi a lokacin.

“Wallahi Umma a lokacin, wannnan ce kaɗai mafitar da muke ganin za ta kare mu daga sharrinta. Karki manta asirin nan fa gaskiya ne da ka yarda da baka yarda ba, in dai Allah ya yi sai ya same ka . Na so na ɗauke tan mu gudu ko da gidansu Musan ne. Amman da kansa ya ce mini ba gidansu ba ko kabari na haƙa na binne ta babu abinda zai hana su aiwatar da nufinsu. To me akai ke nan Umman ? Hakan kawai shi ne mafita lokacin, sannan likitan fa kwana 24 ya ce idan har ba a dawo ba abin zai taɓa ta sosai yadda ko anyi magani ba lalle ya yi ba. To kinga ai da sauran kwanaki, wanda cikinsu nake sa ran samunta…”

“Au! To madalla tunda harka gama yankewa kanka hukuncin ka sameta, kama san hakan ne me na zuwa ka saka ni gaba kana kuka ? Ni ba fata nake ba, amman wallahi ka kuskura sanadin wanann abun wani abu ya samu yarinyar nan ? Hmmmm!”

“Tsoro nake ji Umma, ba na so abinda nake zato ya faru, ki mini addu’a, Allah shaidata tun ranar da na fara ganinta, har yau ɗin nan ba na jin daɗin rayuwata kamar yadda nake jinta a gabanin saninta…” A hankali ya lumshe idanuwansa zuciyarsa na hararo masa sanda ya fara haɗuwa da ita.

Shekarun Biyu Baya

Idan bai manta ba a wani yammacin laraba ne ciki ƙauyen Bebeji. Ya raka Abokinsa Musa gidan Mai Garin garin kasancewarsa mai son rayuwar kauye.

A bakin rafin garin ya fara ganinta sunkuye tana kuka kamar ranta zai fita. Gaban rigarta ya yi kaca-kaca da jini da wani bakin abu kamar  Gawayi. Magana yake mata amman kukan da take yi ya hana ta amsa masa. Ganin hakan ya sa da hanzarinsa ya ƙarasa gareta yana mai ɗago ta. Yarinya ce sosai da ba za ta gaza shekara goma sha ɗaya ba. Rarrashinta ya fara yi inda da ƙyar ya samu ta yi shiru.

“Me ya same ki kike kuka ke kaɗai bakin rafi ko tsoron duhun maghriba da ybaki yi, Jinin miye haka rigarki ? ” 

“Uwale ce ta yanka mini ƙirji na da wuta wai sai ta mini billen ƙadangare irin na danginsu.” 

Ta furta  cikin shessheƙar kuka tana mai ɗaga masa kirjin da ko ƙirgar dangi ba ta fara ba. Ya yi caɓa- caɓa da shafcecen zanen ƙadangare da aka turbuɗe shi da baƙin Kwalli. 

“Sannu, to me ya sa tun kina yarinya ba a yi miki ba sai yanzu da kika san zafin kome?”

“Ai Babana ba ya so, yanzu ma dan taga ya mutu ne ta mini.”

“Allah ya ji ƙansa, ina Mamarki to ta bari aka yi miki ?” 

“Tare da Babana ta mutu.”

Shiru yayi cike da tausayawa maraicinta.

“Allah ya saka miki to, tunda aka yi miki abinda ba kya so.”

Yanzu dai ki bar kukan. Ko ba ki so  na  zame miki ƙawa kamar Maman ?”

Sai sannan ta ɗago tana ƙare masa kallo, sai kuma ta washe baki tana masa murmushi.

“Dan Gayu da kai za kai ƙawa da ni ?” Kalle ni fa duƙun-duƙun. Kasan me ? Uwale fa ba ta yarda na yi wanka sai bayan jumma’a biyu. Uwale muguwa ce da ma Babana bai mutu ba, da ban zauna gidansu ba.”

“Ni dai yanzu ba ki ƙawar da ni ke nan, harfa karatu zan dinga koya miki, ko baki son ki iya turanci ?”

Ya faɗa cikin son mantarta da zancen.

“Ina so mana, kaga Hansai ma kullum sai taje makaranta, ni ce Uwale ta cire ni tunda Baba ya mutu. Da gaske zaka na koya mini ?”

“Sosai ma, in dai zaki bar yi wa Uwale kuka “

“Tab! Bazan iya ba, bansan suna zuwa ba ni ma.”

“Me fa ?”

“Kukan mana.” Nan da nan ya fara dariya yana mamakin daɗin da yake ji ganin harta warware suna hira.

“To me sunan ƙawar tawa ?”

“Faɗime, amman Babana Tauraruwa yake ce mini. Wai a sama akwai wata tauraruwa me haske sosai, ana ce mata ? Um ka ji sunan… “

“Zahra ?” 

“Eh yauwa ita.”

Cikin dariya yake faɗin.

“To me ne kuma Faɗime, suna mai daraja kun ɓata shi . Fatima zaki dinga cewa daga yau. Faɗa na ji.”

“Fatima ” 

Ta fada cikin sanyin murya

“Yauwa Ƙawalli, ni kuma Yaya suna na. Tashi muje na raka ki gida to, kinga sai na gaida Uwale ni ma.”

Zaro ido tayi kallonsa hannunta bisa kirji.

“Ka na so ta biyoka da muciya ke nan! ah ah gaskiya ka yi tafiyarka ni ma zan tafi. Gobe ma za ka zo ai ko, kullum ni sai nazo nan.”

“Zan zo mana kafin mu tafi, amman tunda garinmu da nisa zanna zuwa ganin kanwata duk sati, muna karatunmu, ina son kanwata ta yi ƙoƙari ta zama abin alfahari ga Uwale.” 

Kallonsa ta tsaya yi a hankali kuma sai ta furta; “Maganarka iri ɗaya da ta Babana.”

To, tun daga wannan lokacin fa shaƙuwa mai girma ta wanzu tsakaninsu. Har takai baya cika satin bai zo ya ga Faɗime ba. 

Nisan dake tsakanin Maƙarfi da Bebeji ya daɗe da ɓacewa cikin danuwan Yaya.

Babban burinsa Faɗime ta yi ilimi ta kuma zauna cikin farin ciki. 

Tun yana mamakin yadda kullum ya zo zai sameta cikin baƙin ciki ko cikin jinya mai zafi, har abin ya zame masa jiki.

Akwai ranar da ya zo ya tarda ta da karyayyar fiƙa, bakin nan ya kumbura suntum dan azaba. Ta ke sanarshi da kujera Uwale ta dinga dukanta ranar kawai don tayi ɓarin niƙan Gero da takai kasuwa.

Rungumeta kawai ya yi shi ma yana tsiyayar hawaye, ji yake ina ma yana da ‘yancin da zai ɗauketa zuwa inda za ta huta, wata ƙauna mai ban mamaki ya ke ma Faɗime. Ƙaunar da ta zarce a tsaya lissafa adadinta. Kaunar da tafi irin wacce Chibunzu ya shimfiɗa ma Deluwa (WADA CE).

Sai dai wani zubin har ya kan kasa ɓoyewa gare ta. Sau da yawa yana mata karatu yana kauce hanya da wasu mabanbanta kalmo min da suke da wuyar fassaruwa gare ta, har takan tsare shi da tambayar “Yaya me kake faɗa ne ? ” murmushi ya kanyi ya basar da faɗin. “Wataran za ki sani Fatima !” 

Haka suka ci gaba da rayuwa ya zamana Faɗime ko Uwale zata sa mata tsinin wuƙa dan karta fita gare sa, sai tasan yadda ta yi ta kufce sai dai aga shigowarta gabanin maghriba.

Littattafan karatunta kuwa sune makamashin Uwale na kokon safen, hakan bazai hana wanshegari ta sake ganin ta da wani ba. Ba kuma zai kankare wanda ya shiga cikin nagartacciyar kwanyarta ba.

Har dai zuwa ranar da ba za ta taɓa gogewa a tarihin rayuwarsa ba. Ranar da ya gama ciku-cikun sama ma Faɗime makarantar kwana ta hanyar abokinsa Hedimasta, ya gama haɗo duk wani abin bukata fatansa kawai yazo ya tarda Fadime ta kai shi gurin Baba Malam dan ya yarje masa kan ƙudurinsa. Shekararsu biyu cif a wannan ranar.

Ƙarfe sha daya daidai ta masa bakin rafin. Ya haɗe cikin shaddarsa mai kalar sararin samaniya. 

Bai da wata makusa ta cikar halitta, sai dai ma a kalla ayi sam barka. Sumar nan ta kwanta luff-luff tana ɗaukar ido, kai ka ce taɗi yazo gurin wata gandamemiyar budurwa ba kwaila Faɗime ba. 

Jefi-jefi yakan duba agogan hannunsa yana ɗan tsaki, san samunsa su gama kome a yau ya danƙata hannun (Principal ) shi ma hankalinsa ya kwanta yayi abinda zai fisshe shi. Yana shirin tashi ya zazzaga yaga tahowarta. Sassanyan murmushi ya saki yana mai kara gyara zaman hularsa. Jikinsa ne ya fara sanyi sa’ilin da ya kula ba ma a cikin hayyacinta take tahowa ba, dan ko hannunta bisa kanta, fuskarta na tsiyayar hawaye, da saurinsa ya isa gare ta yana mai ƙare mata kallo, bako takalmi a kafarta haka ta ratsa dan jejin ta taho. ‘Kome dai ya kusa zuwa ƙarshe.’ Ya furta a zuciyarsa bayan ya gama nazarinta

Kafin ya yi magana ta riga shi tana mai ƙanƙame hannuwansa, bakinta na karkarwa,

“Yaya ka gudu da ni, Uwale za ta kashe ni , ita ta kashe su Baba, wuta ta sama Baba… ” 

Sai ta ƙara ƙankameshi alamunta na nuna a tsorace take sosai. Shi kansa kalamanta sun razana shi.

‘Anya akwai ƙiyayyar da za ta sa ka kona mutum ?’ Da hanzari ya hau girgiza ta goshinsa har ya fara tsattsafo da gumi

“Me..me me… kike fadi ne haka ? Ban hana ki ƙarya ba ? Ina kika ji wannan yasasshen zancen ? Wa ma ya gaya maki Mace na iya kisa, maza ne kawai suke ki…”

“Da gaske nake Yaya, tun shekaran jiya na ji suna faɗa ita da Salame tana cewa ni ma za ta ƙona ni yadda ta ƙona Babana. Ta kuma san na ji , sai dai ba suyi mini kome ba da suka ganni, sai ɗazu na ji abinda zasu mini. Tsoro nake ji Yaya ka gudu da ni, hauka ta ce za ta saka mini. Ba na so na zama mahaukaciya irin Madu mahaukaci, ba zan yi karatu ba, zan dinga cin abincin bola ne ina yawo ba kaya…” 

Ganin ta fara fita hayyacinta ya yi saurin janta bakin rafin a hankali ya fara ɗiban ruwan yana zuba mata a fuskarta jikinsa kawai rawa yake. 

Duk yarda sanyin ruwan ke ratsa ta bakinta ya kasa shiru, kawai zubo maganganu take cikin fitar hayyaci. Ji yayi kansa na juyawa, kuwwar “Za ta haukatani” kunnuwansa ke ɗauka.

Da ƙarfi ya daka mata tsawa yana mai toshe mata baki.

“Stop this nonsense Fatima!” 

Tsit ta yi jikinta na ɓari , sai kuma ta juya da sauri ta kama tafiya tana haɗa hanya. Tunawa da ya yi da bata son tsawa,  yanzu za ta gigice ta fita hayyacinta, ya sa shi binta da hanzari ya cimmata, jawo ta ya yi jikinsa yana mai ƙankameta.

“Ke, ina, sam, kai, haba, bazata yiwu ba, ya kuma isa haka , kisa fa ? Ina, mu tafi kawai ko gurin Umma na ne ” Sambatun da ya kama ke nan yana mai bubbuga bayanta. Sai kuma ya kama hannunta suka bar gurin.

Kai tsaye gida Makarfi ya yi da ita, sai dai maimakon ya wuce gidansu kai tsaye , sai ya yi gidansu Musa, inda Allah ya taimake shi ɗakin Musa a zaure yake bai kuma rufe ƙofar ba ɗan saka ya ta ya yi. Nan ya cewa Faɗime ta zauna shi kuma ya ba zama neman Musa. 

Ko da Musan ya ji zancen ba ƙaramar razana shi ma ya yi ba. Sai dai ya tabbatar musu sun gudu ba su tsira ba ne, dan kuwa Asiri ko haƙa rami yayi ya binneta cikinsa, sai ya bita har can ɗin. Sai dai kasancewar karatunsa kenan ɓangaren masu taɓin hankali, akwai wata shawara da yake ganin zata fidda su amman fa tana da matuƙar hatsari. 

Hararar Musan ya fara yi bayan ya ji gurguwar shawarar ta sa, sai dai ga mamakinsa Faɗime cewa ta yi ta yarda harda dan murmushinta tana mai share hawayenta, Musan ne ya dafa kafaɗarsa cikin rarrashi.

“Haƙuri kawai zaka yi ayi hakan, ba fa dawwama za ta yi da shi ba, ta kwana ashirin da huɗu kawai za ta yi. Da lokacin ya yi zaku dawo sai a mata wacce za ta dawo da ita cikakken hankalinta. Ba tada wani (Side Effect) sai dai idan an haura lokacin da aka ɗiba ne, shi ne yake zama kila wa kala. Amman idan ba haka ba ba abinda zaku yi da zai kauda tunanin marikiyar tata daga kanta. Ba dai hauka take so ta yi ba ? To idan ta haukace ɗin a hankali kai kuma bayan yan kwanaki sai ka dauke ta daga ƙauyen duka. ka ga ke nan mutanen gari zasu ɗauka Fatima ta haukace ta bi dawa. Shi ke nan sai ki je gurin Umma har zuwa sanda zata gama karatun musha biki. ” Ya kara she cike da zolaya.

Sauke numfashi yaya yayi yana dubansa.

“Ni fa hankali na ya gaza kwanciya da wannnan abin, baka tunanin a samu akasin da zai hana mu zuwa a kan lokaci?”

“Karka yawaita tunani kan abinda bai faru ba, abinda ya riga faru shi ake so a tattauna kansa. Idan har hankalinka bai kwanta da hakan ba shi ke nan sai a ƙyale , amman ni ina tausayin yadda za a ɓata rayuwar yarinyar da yanzu za ta fara shuka ta ta rayuwar. Ba fa hauka zata yi tubaran ba, ah’ah , ita Allurar ta na dan karkatar da wasu na’urorin ne dake sarrafa dukkan wani motsi na ɗan Adam daga wannan sashi zuwa wancan, ta yadda zai dinga yin mu amala ba bisa hankali ba. Ba kuma fa lalle a samu matsalar da kake tunanin ba, ka yarda kawai tunda har ita ta amince Insha Allah ba abinda zai faru tunda da kyakkyawar niyya zaku yi hakan. Babban daɗinma da babu wani hukunci da ya hau kanta.

“Hmm! Shi ke nan Allah kareem!”

Ba ƙaramar kwakwa suka sha da Babban likitan ba kafin ya yarda ya musu bisa zunzurutun kudi har Naira dubu tamanin.

A cewarsa hujjarsu ta yi kaɗan da zasu

aikata wannan ɗanyen aikin. Shi badan ya ga yadda yarinyar ke girmamasu ba, da fari ɗauka ya yi sato ta suka yi suke son ɓatar da tunaninta dan karta tona musu asiri. Sau uku yana tambayarta ta amince tana ce masa eh, karshe ma sai ta fashe masa da kuka tana mai roƙansa da ya yi mata. Ya dai yi bisa sharaɗin duk abinda ya faru karsu tuhume shi su tuhumi jahilin tunaninsu da yake gasgata musu akwai asiri a duniya. Dan ko shi zuzzurfan ilimin bokansa bai yi zurfin da zai yarda akwai wani Aljani da ke yawo jikin bil’adama ba, balle uwa uba asirin. Ya fi saninsu cikin mabanbantan tatsuniyoyinmu na tun iyaye da kakanni. Haka dai suka rabu yana ƙara gargaɗinsu kan da zarar lokacin da ya d’ɗiba ya cika su yi gaggawar dawo da ita. 

Gishiri-gishirin da yaji bisa leɓɓansa ne ya ankarar da shi da zurfin tunanin da ya nausa kan rayuwarsa da Fatima. A sannu ya ɗora kansa bisa cinyar Umman nasa jikinsa ya yi sanyi kalau. ido lumshe yake furta.

“Allah ga baiwarka, ka kareta duk in da take faɗin duniyar nan.”

Next >>

How many stars will you give this story?

Click to rate it!

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Share the story on social media.

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.