Skip to content

Fadime 1 | Babi Na Goma

2.7
(3)

<< Previous

Hutun kwana biyu Faɗime ta yi, ta fara bin Maama Rizban tashan Baga inda take sai da doya. A da can kafin zuwan Faɗime, sai ta nemo yaro ta ɗora masa ya kai mata har jikin Bus ɗin da zata tafi ta biya shi, a yanzu ko Faɗime take ɗorawa nannauyar doyar ba ta ko duba nisan dake tsakaninsu da bakin titi, balle cikin dake jikinta, haka nan za ta kai mata, idan sun isa tasha ita zà ta sauke ta zauna gurin siyarwar, Mama kuma ta nausa gurin kwartayenta.

Cikinta na da wata shida ta yi wani irin kumbura musamman ƙafafunta, idan ko ta ɗau tiren doya ji take kamar numfashinta zai fite tsabar azaba, dan haka ta ce bara ta sanar da Mama tunda ita ba za ta kula da hakan ba.

Fasa kai lomar amalarta ta yi tana ƙarewa Faɗime kallo bayan ta gama kora mata jawabin.

“Fasi bansan mugun hali fa, ka na mini baƙin ciki ne, da ka ce asai wheel borrow kana turawa ni ina naga kuɗin saye ? Ni da cikin Rizban wata tara ma ina kai doya, sai kai dan ragwanta ka ce kana jin ciwo, to idan ka gaji da ni ne ka faɗa mini sai na sallameka ka tafi. “

“A’ah Mama bance haka ba, amman ina jiye wataran na faɗi ne kan hanyar kasuwar nan, ki yi hakuri ko hayan baron ne muyi. “

Shiru tayi tana siɗe hannunta kafin kuma ta ce; “she ke nan zan duba.”

A zaton Faɗime tura doyar a baro zai fi sauki sama da ɗorawar, maimakon hakan kuwa sai gashi sun zo ɗaya. Dan kuwa Maama ta dinga hantararta da ta yi sauri karsu rasa mota. Gata da girman ciki kai kace ƴaƴa  biyu take ɗauke da su. Haka nan za ta tana nunfarfashi, hutun ta ɗaya su isa tashan nan take samun sa’ida inda za ta zauna ta hau siyarwa. Haka za ta dunƙule cinikin ta bawa Maama ta kunzuge, daidai da Naira Goma ba za ta bata ba. To itan ma dai ba ta saka rai, tunda tana ci tana sha, asalima girkin gidan tunda ta zo ita ke yinsa tun bata iya ba harta kware.

Yau tana zaune tsakar gidan, da ka kalli kalli fuskarta za ga tarin gajiyawa sai dai ƙarfin zuciyar dai kawai, Mama ta shigo bakinta har ƙeya tana duban Faɗime. “Fasi tashi, zama bai same mu ba, yanzu Chairman ya kirani zamu karasa masa saman ginin  gidansa, wai nasa yaran sun tafi. Muje ko ƙasa ka na miƙo minu daman bansan kiran wancan shegen Blessing ɗin ya faye ragwanta. Blessing dake zaune ƙofar ɗaya, ta dokawa Maman harara gami da sakin tsaki. 

“Tasi Faɗi mu tafi da wuri yake so ayi a gama, ka ga kai ma sai ka samu wanda zaka sai ma Babynka kaya kafin ka haihu.”

Ta furta tana duban Faɗi da tunda aka ambaci gini ta ƙurawa tutsetsen cikinta kallo tana mamakin ko Mama bata ganin girmansa ne.

“Gaskiya Mama ki yi haƙuri bazan iya ba.” 

Ta samu bakinta na furtawa cikin gaggawa.” 

A mamakince maman ke kallonta jin abinda ta fadi.

“Ba za ja ka ba fa ka ke faɗa mini kai tsaye, Fasi ? “

“Ba haka ba ne Mama, ki kalli abinda ke gabana mana, ta ya ya zan iya miƙa ƙasa sama da wanann ƙaton cikin na wata takwas ? Ban iyawa, idan kayan Baby ne Allah ba zai hana abinda za a saka shi ba, kai ko ɗankwalina ne na ƙudundune shi hakan nan.”

“Woooooo Fasiii ? Ni ka kema magana haka kan abinda zai amfanemu, Aww ganin na sakar maka kome ina baka ci da sha ba dangin Iya bare na Baba si ne zaka tonan asiri. Dama fa yarinku sun ce  sintaccen mage basi mage, dama na sani a can Tashan na baro ka.”

Su Blessing da suke gefe suka kwashe da dariya jin zancen Mama na ƙarshe dai.

“Ashe dai ashe dai!” Suka faɗa da shewa har da tafi. 

Hakanne ya ƙara ƙona ran Mama ganin ga ƙoshi ga kwanan yunwa, tasan tunda ta faɗi ma Blessing waccar kalmar babu yadda za a yi ta bita yanzu.

A fusace ta kallo Fadime.

“Fasi ka tashi mu tafi tunkan na shiga na watso maka kayayyakin ka ka bar mini gidana.”

Sanin babu inda za ta tafin idan ta koreta ya sakata miƙewa tana goge zafafan hawayen da suke zubo mata. A karon farko tun shigowarta garin Barno ta tuna maraicinta, yau da ace tana da uwa da uba ko wasu dangin kamar kowa har akwai wanda zai sakata yin gini da tsohon ciki ? Aka ce wai ba maraya sai rago, dole ko ta jure duk wani abu da zai tunkarato tunda dai ita haka za ta ƙarar da rayuwarta a wahala. “Babban Burina ki yi ilimi mai yawa ta yadda Uwale za ta ci moriyarki.” Kalaman Yayanta da ba za ta taɓa mantawa da shi ba suka wanzu cikin kunnuwanta tamkar a lokacin ya ke furta mata su. Murmushi kawai ta yi mai ciwo da ta tuna ba za ta taɓa cika burin nasa ba. Sagir ya riga da ya rusa ɗan abinda ya rage na rayuwarta ta, rushewar da ba za ta iya wani ginin ba. Ta dai bar shi da mahallicinsa, ba kuma za ta yafe masa ba ko da kuwa mahaifiyarsa ce za ta sunkuya a kan gwiwowinta ta roƙeta, ba za ta yafe ba. Ko’ina ma za ta sake ganin Yaya yanzu ? Masani sai Allah.

Dan baƙar zuciyar Maama Rizban rantsewa ta yi tunda ta musanta mata binta gurin ginin, to ba za su hau mota ba, hakavnan zasu daba duk kuwa da tsohon cikin da take da shi, tundaga Madganary har Shagari lowcost inda zasu yi ginin ke nan. Tana hawayen azaba take miƙa kwaɓaɓɓan simintin da duk miƙawa ɗaya sai abinda ke cikinta ya yunƙura kamar mai son fitowa ta baki, amman Maama Rizban bai sa ta dubeta da salama ba, sai ma sababi da take ta saki na ɓacin ran da Faɗime ta sakata.

To fa, tundaga ranar Maama Rizban ta fara jin haushin Faɗime, duk kuwa da kullum sai ta bita har suka cika kwana ashirin sannan suka kammala ta karɓi kuɗin aikinta gami da sokewa, a cewarta za ta sai musu kayan abinci ne dan ta kula cin Faɗime na mutum uku ne yanzu. Baiwar Allah bata ce kome ba tana fama da kanta da a kwanakin nan sosai take jin ciwon cikinta. Kallo guda zaka mata kasan ta fara fita hayyacinta.

Yau tana zaune ita kaɗai cikin ɗakin Maman sanye take da yar shimi da zani ta tasa tirtsetsen cikinta gaba tana kallonsa cike da soyayyar Uwa. Kasancewar kafatanin mutanen gidan sun tafi gurin jana’iza wai pastor nasu ya rasu. Sai ga Rizban ya faɗo dakin cikin hali na maye, da hanzarinta ta zari hijabinta ta kima jikinta tana mai toshe hancinta jin wani wari da yake yi. Kallonta ya yi cikin maye tsaf ta rikeɗe masa da fuskarsa budurwarsa Chine.

“Hey! Chine ni kike tose ma hanci?”

Waige-waige ta fara yi tana neman Chine ɗin, ita dai tasan ita kaɗai ce a ɗakin.

Ganin yayo kanta ya saka ta tashi da ƙyar tana kallonsa.

Yanzu tar yake kallonta

“Aww! Fasi dan kin rainani ki ke tose mini hanci? To maso ki ciren wannan abin na jikinki na gani. 

Ƙamewa ta yi tana kallonsa a mamakince, shi kuma wanann da tsohon ciki na shi iskancin ke bayyana. 

Saurin doke hannunsa ta yi ganin zai taɓo mata fuska. Aiko ya kai mata wafta, da wuri ta kauce, ya wafci iska. 

“Ka saya mana Fasi ba da yawa zanyi ba fa.”

Ya furta yana mai kare ƙofar ganin za ta fice. A gigice ta yi baya ta fara waige-waigen neman abinda za ta kare kanta. Hango kwalbar Pepsin da Mama tasha ne ta yi, dan haka da hanzarinta ta ɗauko ta.

“Wallahi ka kauce na fita ko na sauke ma ita a kanka.”

“Heyyyyy! Ki buga mini Maama ta kaseki, gwara ma ki saya na yi abinda nake so.”

Ganin ya juya yana ƙoƙarin saka sakatar ɗakin, ba tai wata-wata ba ta sauke masa kwalbaŕ saman kansa. Ihu ya yi yana dafe gurin ganin jini ya saka shi zubewa gurin, da wuri ta tsallake shi ta isa ƙofar, aiko caraf ya riƙe hijabinta yana sambatun ta tsaya. Ba ɓata lokaci ta cire masa hijabin, ta zari wani zani data gani a igiya ta rufa a jikinta, cikin gaggawa ta fice daga gidan.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×