Skip to content

Fadime 1 | Babi Na Sha Bakwai

4.5
(2)

Karanta Babi Na Sha Shida.

“Yauwa ni ko na tambayeka?” Ta furta tana zame jikinta da ga nasa.

“Ina jinki Fati” ya faɗa da son daidaita kansa.

“Wai a ina ka iya Turanci?”

“Ji da Allah. Da ke gingimemen jahili kike ɗaukata? To har kwalin Degree gardin mijin naki ya mallaka.”

“Dan Allah fa? To ina suke? Mai kuma ya kawoka nan gurin bacin da iliminka? Ina ne ma garinku da iyayenka ko kaima sun rasu?”

“Wai! To duk ki tattara tamboyinki zuwa waccar akwatin, amsarki na ciki.”

Da saurinta ta miƙe za ta je ga inda ya nuna ma tan. Ya kuwa sa hannunsa ya jawo ta ta zube jikinsa.

 “Ba yanzu ba, ki bari sai wataran!”

“Ni dai ka faɗa mini labarinka.”

“Sai kin fara faɗa mini wane ne baban Abbati ?”

Shiru ta yi tana kallon idanuwansa, har ta fara rau-rau da ido.

“Hmm ba na son tuna zaluncinsa.”

“Ni ma haka ai! Bana son tuna zaluncin Abbana.” Da sauri ta matso jikinsa, ci gaba dan Allah me Abbanka ya maka?”

“Tom, Abbana Balarabe ne, muna zaune a Lagos cikin unguwar… shi ke nan na gama.”

“Ka ga ni bana son haka.” 

“Me kuma na yi ni sarkin lefi, Ni fa kinga abin da nake so. Ya furta yana mai mata cakulkuli a hankali tana dariya, ƙarshe ta fara ramawa ita ma, nan dai aka bar batun labari aka koma soyayya.

Life moved on, sosai suke gwada ma junansu soyayyar da kafatanin Ƙaryar sun san shaƙuwa da ke tsakanin Mamuda da Faɗi. Hakan na ƙona ran Jabiru ganin Mamuda ya fi shi kwanciyar hankali da matartasa. Shi kam ya rasa abinda ya hana shi cireta daga ransa. Sai dai dole ya haƙura sanin Imam ya riga da ya musu katanga.

Kamar cikin barci take jin shessheƙar kuka, ƙara kasa kunne ta yi, da dai ta tabbatar sai gata ta miƙe zumbur tana mittsika idanuwa, garin ta kalla har ya yi sha alamun ƙarfe bakwai na safe za ta gota. Kallo inda kukan ke fitowa ta yi, ga mamakinta Mamuda ne ya saka kansa cikin cinya yake yi. Hankali tashe ta isa gare shi tana mai dafa shi. A hankali kuma sai ta zauna gefensa tana mai saka kansa saman kirjinta ta hau shafa bayansa kamar ƙaramin yaro. Jin yana sauke numfashi da sauri-sauri ya sata fara kokawar ɗago fuskarsa, sai dai ina! Karfin ba ɗaya ba, sai ma ƙara cikwikwiyeta da ya yi tamkar wanda zai mai data cikinsa. Hakan ne ya karyamata da zuciya ita ma ta fashe da kukan tana mai kifa kanta saman nasa, mamakinta ɗaya abinda ya haddasama wannan jarumin Namijin zubar hawaye.

 Jin saukar hawayenta saman kansa ya saka shi ɗagowa yana kallonta. A hankali kuma ya hau share mata hawayen yana girgiza mata kai.

“Bana son kukanki Fati, bana so sam! Tsoro nake ji, tsoron na mutu na barki cikin baƙar ƙaryar nan. Bantaɓa zaton akwai ranar da za ta zo na yi nadamar sanin Imam ba sai yau. Ga iyali na ajiye, iyalin da nake son shimfiɗa kyakkyawar rayuwa da su amman ba hali, na tabbata ko ban mutu gurin ƙin bin Imam ba, zan mutu ta hanyar jami’an tsaro, Kaico! Kaicon rayuwar da za ka so ta sa’adda ba ta da wani amfani gare ka. Ya furta cikin hawayen da bai san ya zai hana zubarsu ba.

FAƊIME

kaɗa masa kai take yi a hankali tana share masa hawayen.

“Karka fidda rai da rahmar Allah, domin shi mai jin ƙan bayinsa ne musamman idan ka yi kyakkawan tuba. Wane ma ya ce ma zaka mutu ka bar ni? Sam! Baka san kullum na duƙa sujjada sai na roƙi mahallicina da ya ɗauki ranmu tare ba? Ka bar tuna mana mutuwa a sa’adda ba ma fatan kasantuwarta garemu. Allah zai yafe ma, ya wadata ka da tsahon ran da za ka ga jikokinka ba ma ‘ya’ya ba. “

“Kar ki yaudareni Fati, na san hukuncin abinda na aikata a shari’ance. Ko Allah ya yafe mini , ina zanga ɗumbin musulman da na zubar da jininsu ko na nakasta su yafe mini? Nadama ta same ni a lokacin da nake son kasancewa da ke, na gina mana rayuwar da kowa zai yi sambarka, sai dai kash! Na tabbata ina mafarkin da babu ranar farkawa ne, mutuwa zanyi Fati! Na sani ko…” Kasa ƙarasawa ya yi sakamakon toshe masa baki da tayi da ƙarfi tana kaɗa masa kai da sauri da sauri cikin zubar kwalla…

“Kwangwaran!” Suka ji faɗuwar kwano da ga tsakar gidan wanda ya haddasa mata miƙewa da sauri ta leƙa.

Hankali tashe ta juyo tana kallonsa, tana kallon Abbati dake barci, da gudunta ta isa ga Abbati gami da rarumarsa ta ɗaure shi tamau a bayanta cikin rawar jikin.

“Jabiru ne, ka tashi mu gudu, na tabbata ya ji zancenmu, shi ya sa ya saki kwanon ya juya dan ya sanar da Imam, ka tashi tun kafin su iso mana…”

Miƙewa ya yi cikin kaɗuwar  zancenta, sai kuma ya hau girgiza mata kai da sauri da sauri. Laluben bindigarsa da zungureriyar takobinsa ya hau yi, nan da nan ya fiddosu ya rataya saman kafaɗarsa. 

“Ji rani na je fadar, yanzun nan zan dawo.”

Da dukkan karfinta ta riƙo rigarsa tana kallonsa.

“Inaa! Wallahi ba inda za ka fita ka barni, ƙafata ƙafarka sai dai duk abinda zai sameka ya same mu tare.”

Da sanyin jiki yake kallonta, kafin kuma ya jawota ƙirjinsa a hankali yana shafa kanta.  Shiru suka yi gaba ɗaya kowanne yana sauke ajiyar zuciya. mamayarta ya yi jin ta yi nisa cikin tunani, ya hankaɗata da ƙarfi ta yi baya taga-taga ta dafe bango.

“Am sorry Fati.”

Ya furta yana mai falfalwa da gudun bala’i, ya isa ƙofar ya fice game da kulleta ta waje.

Durƙushewa ta yi tana mai toshe kunnuwanta da ƙarfi sa’ilin da taji karar bindigu sun fara tashi, ko dai shi ke harba, ko kuma shi ake harbi. Shi ke nan kuma haskenta na uku ya tafi. Ita kuma haka ta ta rayuwar za ta ƙare, a duk sanda ta fara jin daɗinta, a lokacin ne kuma wata ƙaƙƙarfar ƙaddarar za ta datse ma ta jindaɗin. Shin wane irin lefi ta aikata a rayuwarta ne da ake nufarta da irin waɗannan munanan ƙaddarorin.

“Astghfirullah!” Ta furta da ƙarfi jin za ta ɓata imaninta. Miƙewa ta yi za ta ƙarasa ƙofar, ta ji saukar wani abu gabanta, a hankali ta kai idanuwanta gun. Kan Mamadu ne a gabanta cikin jini an soke idanuwansa da kibiya,  ƙarfin jefo kan ya sanya jininsa fallatsuwa a saman fuskarta, gigitacciyar ƙara ta saki tana ma sulalewa gurin a sume. 

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×