Skip to content

Fadime 1 | Babi Na Sha Biyar

0
(0)

Karanta Babi Na Sha Hudu.

Ƙarfin zuciya ne kawai ya saka shi ɗagowa ya fice daga gidan cikin sassarfa. Ya daɗe tsaye ƙofar gidan idanuwansa lumshe yana daidaita luguden da zuciyarsa ke yi, shi kaɗai yasan illar da kalamanta suka yiwa zuciyarsa, shi kaɗai yasan raunin da yake ji a duk ɗora idonsa da zai yi kanta.  Daga in da yake tsayen, yana iya jiyo shessheƙar kukanta da ke barazanar ruguza masa duk wani ƙarfin gwiwa da yake da shi.  Abu ɗaya ya sani a yanzu, ko da ya tafi ba shi da wani sauran ƙarfin da zai iya aikata abinda ya dace.

Sanin dai tsayuwar tasa ba za ta haifar da kome ba sai tarin nadama ya saka shi barin gurin da hanzari, gami da dosar tawagar tasu suka ɗaga.

Kasa zama Faɗime ta yi, ta hau safa da marwa a farfajiyar tsakar gidan nasu. Ta rasa me ye na damuwa ga ɗan ta addan da ya kashe makwafin Ubanta Liman, to, amman abu ɗaya ta sani da kuma zuciyarta ke kwarzabanta kansa, shi ne ta ga dawowarsa lafiya daga wannan fitar.

Ga Abbati da ke binta duk inda ta sauke kafafuwanta shima zai sauke ta sa, sai kuka yake yana kiran Baba kamar yau ya fara tafiya ya bar shi. Da ƙyar ta samu ta jawo shi jikinta gami da saka shi barcin dole, ɗan abincin da ta zuba masa ma nan ya sa ƙafa ya shure garin rikicinsa.

Tun ƙarfe bakwai na dare take jiran dawowarsu amman shiru kake ji, ko dan rahoto babu balle ta sa ran jin halin da suke ciki. Wuraran ƙarfe goma jin shirun ya yi yawa ya saka ta jawo kwanan abincinta ta fara tutturawa kamar mai cin magani. Daga bisani kuma ta jawo Abbati da ya riga ya yi barci ta rumgume jikinta. Da ƙyar ta samu barci ɓarawo ya sace ta.

To, wanshegari ma haka ta tashi sukuku, da taji dan motsi kaɗan za ta leƙa ƙofar gida ta ga ko su ne, amman wayam kake gani. Ba ita ta ji dirin motarsu ba sai bayan la’asar. Aiko da gudunta ta saɓi Abbati zuwa ƙofar gidan, sai dai kan ta kai ƙofar ma ta ci karo da shi yana mai shigowa.

Turus! Suka yi duka su biyun suna kallon juna. Ita tana kallon hannuwansa dake tsiyayar jini, shi kuma yana kallon kumburarrun idanuwanta. Da sauri ta dire masa Abbati dake zillon ganin Babansa, ita kuma ta bi ta gefensa zuwa pharmacy din Imam. Kayan aiki ta ɗebo, nan da nan sai gata ta dawo.

Gefen katifar da yake zaune yana ma Abbati wasa da hannun da bai da ciwon ta zube, tana warware kayan magungunan da ta ɗebo. A hankali ta riƙo hannunsa ta hau goge jinin, tana yi tana kallonsa wai ko zai ji zafi, to, ya ma kauda kansa wani ɓarin daban, kamar bashi take sakawa maganin ba.

“Kuka kikai ta yi ne halan, na ga idanuwanki duk sun kumbura?”

Ta ji saukar muryarsa tana shirin tattara kayan ta fice.

Tsai tayi tana kallonsa, sai kuma ta gyaɗa kanta da sauri.

“Akan me zan yi kuka dan ka tafi ? Sai ka ce wani Ubana…”

“Lahh me kayya, kayya haram, Abba kuka ta yi da yawa ko abinshi ba ta ci ba. ” Abbati ya tare ta yana ƙara lafewa jikin Uban.

Hararar yaron ta yi ganin ya tona ta. Da sauri kuma sai ta kallo shi.

“To ni kukan tuna maraicina na yi, tunda na rasa Liman har akwai wani gardi da zauna ina ma kuka?”

“Uhumm! Hakane, shi ya sa na ci karo da wani zaure a yana safa da marwar jira na.”

Ba ta ce komi ba, illah tattara kayanta da ta ƙarasa yi ta fice daga ɗakin.

Babi Na Sha Shida

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×